NOVELSUncategorized

KWARATA 7

???? —— 7

           Haba Amisty wannan ai ba mafita bace, Sultana kenan wannan kuwa itace babar mafita, domin mazan yanzu yawancin su yanda kika san kura da nama haka suke akan mata, d’aid’aikun su ne Allah yatsare su, sai kuma wanda suka had’u da jajirtaccin mataye.


           Ni nan da kika ganni Sultana nasan abinda nakeyi kuma haka nasan irin mazan da nake tarayya dasu, banajin kunya asan ni “yar iska ce haka kuma bana b’oyon iskancina dan ta haka ne kad’ai za’a san ni karuwar gidan ce har na samu costomers.

       Na samu dubban kud’ad’e ta hanyar karuwanci ban san adadi ba, dubu goma dubu ishirin ga kud’ina kuma inji dad’i abu na babu wanda yaji ba wanda ya gani, in rik’e babbar waya irin wacce nake so haka kuma in d’inka sutura da talakalmi da jaka, abu d’aya yasa ban sayi motar hawa ba saboda bana so Baba ya harbo jirgina da wuri amma badan babu ba,

        Gyara zama nayi tare da tattara hankali na wurin Amisty, nace to ke mi yasa kike sha’awar karuwanci ne ? Murmushi tayi sannan tace gaskiya daga kalle kallen B F tun inajin tsoron abun har ya fara bani sha’awa,

        Tsare ta nayi da ido sannan na tambayeta a ina take samu ? Tsoki tayi tare da cewa tambaya kamar “yar jarida, idan zakiyi na had’aki da wani mak’ocinmu sakaran banza baisan darajar kud’i ba, kije yai miki yaimin muci gaba da k’wak’wale banza tunda matar tasa sakaryar banza ce, kud’i gareshi na tashin hankali amma matar bata wani iya sauk’e hak’k’insa kinji yanda yake tona mata asiri ? Gata da kyau kamar ita tai kanta amma kyan ya zama hoto tunda mijinta ke neman mata.

        Tou ke Amisty ya akayi kuka had’u kuma ya akayi yasan kina neman maza ? Hmm yarinya kenan ! Amisty tace min sannan taci gaba da cewa……. Gidan nake zuwa ita kuma bata da wani sirri bud’e take shegen surutu kamar an sakawa radio sabon battery,

       Kullum naje sai ta bani labarin mijinta d’an jaraba ne, da a tunani na mafad’aci ne, sai nace mata niko sai naga yana da kirki sosai bashi da wata damuwa, sai tacemin ba fad’a na baki ba jaraba kullum zai nemeni daga dare zuwa asuba yakai sau biyar.

        Cikin rashin fahimta na tambayeta, ban gane ba….. Tamin bayani na gagara fahimta shine ta fahimtar dani ta hanyar nunamin vidio a wayarta,

Tana kunna min ta tashi dan zuwa duba girki, ni kuma tuni dama na fara iskanci na amma a lokacin ban dad’e da farawa ba, dan haka tana tashi na sace number mijin a wayarta, tunda iskancin kawai nakeyi a lokacin amma bansan fa’idar abun ba……

      Tana madafar abinci naje na bata wayarta nayi mata sai anjima, ina fita ba gida na tafi ba kawai na sharce wurin uwar d’akina, wadda nace miki zan had’aki da ita kema ta mayar dake gahurtacciya kuma abun kwatacce a harkar barikanci. To ita naje ta sake bani haske a harkar, dan haka ina dawowa gida na fara tura masa sak’on gaisuwa ta whatsApp.

     Shareni yayi bayan yaga sak’on baiyi reply ba, ni kuma na nace na kwakwafe banyi zuciya ba naci gaba da aika sak’on, kusan sati biyu babu wani bayani, dan haka na fara tura mishi da irin vidios in B F da nake kallo na tura mishi masu zafi da yamutsa tunani dan wani lokaci sai yakai 1:30am yana online.

Wai wace ce ? Ya tambayeni bayan yaga vidio inyi, nima basar wa nayi ban bashi amsa ba na sauka online, ina sauka yana kirana a waya….. Murmushi nayi a bayyane nace ashe kuwa mayen ne ? Mu zuba dani dakai….. Kuma ban d’auki wayar ba,

          Text ya turomin ta inbox, kamar haka….

       Wai wace ce ke ? Ki hau Online muyi magana don Allah !

         Ai nayi fushi nima…..

      Shine amsar dana bashi,

       Kiyi hakuri don Allah ki hau online muyi magana

       Shareshi nayi na kashe wata duka nayi kwanciyata…… Saida na kwana biyu wayata na kashe, ranar dana bud’e wayar kuwa sak’onsa ne yai ta shigo babu iyaka, wasu na duba wasu kuma na share.

       Ko online dana hau sak’unan sa birjik, dan haka naci gaba da tura vidion iskanci, kuma idan natashi sai tsakar dare nake turawa, jakar tana can tana bacci, 

        A hankali ya saba dani, amma ban fad’a mishi kaina ba, yau da gobe bata bar komai ba, har na tambayeshi dalilin da yake kai tsakar dare yana chat, kawai cewa yayi yana da damuwa da iyalinshi, bata bashi hak’k’inshi wai tace yawan sex da mace yana sa tayi saurin tsufa….

      Amsar dana bashi itace, ya barta can ta k’unshe abunta har yayi wari, indai yana da buk’ata tou ni zan rik’a bashi nawa duk lokacin daya buk’ata, kinji shine fa idan bata nan nake zuwa gidan muyi komai namu cikin sirri.

       ‘Dan gajeren murmushi nayi sannan nace Amisty kenan…… Idan dai har bin maza zanyi tou pha tabbas babu macen data bini ilimin iskanci, kinji hausa suna cewa d’an gado saiya zarta, nawa ba kalar naku bane, saboda naku iskanci mai arha kukeyi, tunda har banji kunyar mahalicci ba na tsab’a masa babu abinda zaisa naji kunyar wani banza,

           Hannu na nakai saitin prvt prt ina sannan nace idan dai wannan ne abinda maza suke buk’ata ni kuma duk saina halaka da yawansu dashi, kallon Amisty nayi sannan nace, babu wanda ya koya min saishi d’aya, ban fara ba shine ya fara, ban iya ba yayi da k’arfin bala’e, ba’ayi da zafi yayi min saboda k’eta, ke Amisty karki manta a caca aka sakani duk saboda talauci idan har ban tara kud’i ba ta sanadiyar karuwanci nayi suna a duniya lallai ni ba d’iyar Aliyu Binnaa bace,

      Tunda har ya bada budurci na saboda san duniya ni kuma zanci gaba da basu su bani dan na tara mishi abunda ya buk’ata, 

        Amfanin zunubi roma Amisty, tunda zanyi kawai zanyi amma babu fashi, saidai ki sani akan sab’awa Allah babu namijin daya isa yaga ko pant ina da naira dubu goma ko ishirin, kud’in shigar ciniki naira dubu d’ari ne shine harajin da na yankawa duk mai sha’awar yin iskanci dani, idan kuma zaka shiga gidan dubu d’ari biyar, idan har haka yayi tou na siyar idan haka baima mutum ba tou ya tattara buk’atarshi ya koma,

       Amma tabbas duk namijin da yace zaiyi, saiya bada dubu d’ari, idan na yadda yayi idan kuma ban amince da dashi ba zai koma, amma dubu d’arinshi tazo kenan kamar gawa tazo lahira.

     Ki sani bana iskancin wahala, kuma bana iskancin cini incin tuwo, zan zauna gida bazan bar k’asata ba amma zan zama tarihi a duniyar nan, ki fad’awa uwar d’akin taki cewa ina gayyatar ta shigowa k’ungiyata da nake fatan kafuwarta daga yanzu zuwa ranar da numfashina zai k’are, ki sanar da ita cewa ni banda ilimin boko amma akwai na tsoron Allah kuma sanin ilimin bazai hanani bujire masa ba, nasan hukuncin mazina daga wacce tayi aure har wacce bata tab’a ba, hukunci kisa ga masu aure, bulala ce ga irinmu “yan mata, to anan duniya zan sameta ko sai naje can ? Duk na sani, kuma nasan a ina ake amso su, mik’ewa tsaye nayi tare da dafa wa Amisty kafad’a sannan nace bana buk’atar shiriya, kuma bana so a tausaya min, daga yanzu zuwa lokacin da zan gama kammalawa…….., BARIKI ASSALAMU ALAIKUM

      Murmushi nayi sannan nace wa Amisty suna na , MARYAM ALIYU BINNA, na bud’e k’ungiyata daga yanzu, idan kina sha’awar shiga bisimillah, na barki lafiya……… Ina fad’in haka ban sake magana ba na juya na fita daga gidansu……

          Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, shine abunda Dikko ya fad’a adaidai wannan lokacin, tare da cewa Allah na tuba………. ????????

          Ina fita na tare napep nace malam ka kaini kambarawa, can ne anguwar da muke zama. Abinda zan bashi ya fad’amin bayan ni ban tambayeshi ba,

      Shiga nayi yaja muka tafi, duk inda yaga fasinja ya tsaya zai d’auka cewa nakeyi muje bana so ka d’auki kowa, har muka iso filin gidanmu da yasha ado da darnin kara……

       Ina fita na wuce abuna, malama kud’in fa ? Juyowa nayi tare da ce masa nawa ne ma ? 250, murmushi nayi tare da kallonsa k’asa da sama sannan nace naci na Allah bud’a, da kuma tsarinka yamin dana baka wani abu ka kalla sai kayomin ciko,

Fitowa yayi daga cikin napep d’in yana fad’in ke zanci uwarki ko ki bani kud’ina, murmushi nayi tare da cewa tayi maka tsufa…… Ina fad’in haka nayi gaba abuna, haya haya ya fara hayani tare da ci gaba da d’uramin zagi irin na “yan tasha. Ja nayi na tsaya ba tare dana juyo ba.

          Saida ya gama zage zagensa sannan naci tou ka zagi kud’inka, kuma naci na cinyesu duk garin nan inga mai amsar su wurina, kaina yayo da zumar kaimin duka, nace ka dakeni ka dako ma kanka bala’e da kabi ta hankali daka tsira amma tunda iskanci ne abun dani dakai dan iska ka fasa,…

Wani mak’ocinmu ne yazo wucewa, na fashe da kuka tare da cewa malam lawal kaga wannan shine yayi min fyad’e, dama nace muku ina ganeshi, yana jin zance fyad’e ya ruga zai nufi napep malam lawal ya fara a kawo d’auki, a tak’aice dai kafin ya bar anguwar bayan yaci shegen duka saida aka fasa mishi gilashin mota na gaba sannan suka k’wak’ule masa cini kin da yayi yabar anguwar a wahalce……

       Yana tafiya na shiga gidanmu natashi masifa cewa sai an siyar da filin nan an bani hak’k’ina, yanda na birkice lokaci guda ya bawa al’ummar anguwarmu mamaki, an nuna min cewa ayi kud’i wa filin sai a fitar min da kud’ina su kuma su zauni fili, nace bansan wannan zance ba duka nake so a siyar uban kowa ya kama gabanshi,

       Tambayata akayi me zanyi da kud’in ?Babu kunya bare shakku nace, karuwanci zan fara shi yasa nake so a siyar a bani kud’i na naje na siyo kayan da zan zama karuwar……

       Gaba d’aya wurin salati aka d’auka ! Yayin da wasu dattawa suka fara sulalewa suna barin wurin, ni kuma na shiga cikin gidan naci gaba da yanyara ruwan iskanci na san raina,

        Bayan kwana biyu mak’ocinmu ya kawo kud’in filin gidanmu domin shine ya siya, aka raba aka bani nawa, sallama nayi musu tare da cewa kuyi k’ok’ori kuna ziyarta na domin inaji a jikina nan da kwanaki kad’an zanyi muku wahalar gani…….

Babu wanda ya bani amsa, murmushi nayi tare da tafiyata dan dai nasan nasha dasu…. Nima bak’in ciki yasa nace duka filin za’a siyar dan kar na shiga gararin rayuwa ni d’aya kowa ya lalace dan zuwa yanzu gaba d’aya na koma kamar wata kafira dan babu sauran tausayi a zuciyata……

         Bakin titi na fito na samu mai abin hawa, inda zanje ya tambayeni……….. Shiru nayi na wani lokaci sannan nace masa gidan karuwai zaka kaini,

      Kallona yayi sosai sannan yace ina ? Nasan yaji sarai iskanci ne yasa ya sake tambayata, dan haka nace gidan da “yan iska ke zama wanda suka gagari iyayensu,

          Jinjina kai yayi amma baiyi magana ba, ko har yanzu baka gane ba ? Na tambaye shi ? Shiru yayi baicemin komai ba, ni kuma nace tou ina nufin inda maza da mata ake had’uwa ayi bad’ala, kallona yayi cikin yanayin tausayi sannan yace ke yarinya ki rufawa kanki asiri rayuwar bariki tafi k’arfin ki, aure shine yafi dacewa da rayuwarki,

        Kai malam zaka kaini ko kuwa dai ? Tashin napep inshi yayi tare da cewa Allah ya shiryaki, amma nikam bana kaiki gidan karuwai, tsoki nayi tare da cewa jeka d’an munafika shege  marar rabo… Gaki nan katuwar marar rabo duniya da lahira, indai mazan bariki ne sai sun kasheki murus kin kasa morawa rayuwarki, dan mace bata kashe namiji saidai ya kashe ta, baki san dafin namiji ba da baki hayewa mazan zamani ba kin koma gida, basu da imani haka kuma basa tausayi tunda sun san kud’insu suka biya, tou fa basa sassafta wa kamar mai gidan haya ne da “yan haya, tunda sun san ke ba tasu bace hawa d’aya zuwa biyu zasu tashe ki aiki kina kallon maza suna kallonki amma dan uwarki bazasu ciwu gareki………… Yana kaiwa nan yaja napep inshi yayi gaba.

          A bayyane nace komi zakace kaje kace saina zama cikakkiyar karuwa, kuma ni karuwanci nawa mai aji zanyi ba irin wanda kowa yake tunani ba.

           Bai dad’e da tafiya ba na samu abin hawa, kuma na fad’a masa gidan karuwai zai kaini, yace min na ina gidan karuwai d’in ? Nace inda fek’ak’k’un suke can zaka kaini, shigo muje, shiga nayi yaja muka tafi……..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button