NOVELSUncategorized

KWARATA 55

???? —— 55
         Tunda na samu na kwanta bacci har gari ya waye ko fitsarin dare ban farka ba , wadataccen baccin dana samu shine ya bani damar tashi asubahin farko , kuma tunda na tashi nayi sallah asuba ban koma
bacci ba , wayata na ɗauka saidai na kunno maganar mutumin nan da nake tunanin shine ya kwakwalewa Aunty Mamy ido ta mutu , Allah ɗaya gari ban² shi nan magana yake , da , da yare na yakeyin magana zanji abinda yake cewa to banaji saidai na saurara amma ba damar na fihimta , hmmm ya zamar min dole na miƙe da zuciyata da kwalwata nima nayi ilimi kodan ceton rayuwata daga duhun jahilci….

         Bayan na gama saurare na kashe wayar na saƙata a gefen katifa na koma nayi kwanciyata ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗaukeni , na ɗauki lokaci mai tsayi ina bacci hankalina kwance banda wata damuwa data wuce yunwa , sai ɗaya saura na farka ,

      Koda na farka wanka nayi nayo alwalla kaya na canja ni “yar gayu dan ina cire kaya na ajiye a palo za’a ɗauka a wanke a gogemin shi yasa ni kuma kullum saina canja kaya sau biyu , idan nayi wankan safe na saka idan nayi na marece ma na sake !

      Bayan na gama sallah azahar na ɗauki kuɗi na fito da zumar in ba mai gadi ya siyomin abinci , amma ina shigowa palo naga ɗika²n kulolin abinci da filets da cokula kamar dai yadda aka saba ajiyewa a kullum idan Dikko yana gari idan har yana nan haka ake ajiye wannan abinci da rana da daddare shi yasa ko wane lokaci gidan baya rabuwa da mutane  kalacin safe ne dai bana tunani ana kawowa gaskiya dan bana gani saidai iya wanda zan karya dashi.

     Saida na zuba abinci dai² wanda zai isheni nakai ɗaki na ajiye sannan na dawo nace ma mai gadi wai Dikko baya nan ne ? Yace min yana nan mana , nace tou ai ban ganshi ba , yace min yana nan ciki tun ɗazu ya shiga kila bacci yakeyi , nace yayi mishi kyau , na juyo na dawo a raina ina cewa miya faru bai nemeni ba ? Wurin mai gadin na sake komawa nace yasan nazo kuwa ? Yace Eh na faɗa masa , ya yace maka ? Baice komai ba , daya zo yace ina ne ? A , a bai tambayeki ba , tou ya yanayin fuskarshi ? Yayi farin ciki ko yayi yanayin damuwa ne ? Yace ni bansan ya yayi ba.

     Ban sake magana ba na koma na ɗauki abinci na naci gaba da ci , bayan na gama nazo na ajiye filet in a inda na zuba abincin , ban daɗe da komawa ɗaki ba gidan ya fara ɗaukar taron mutane kamar yadda ya saba a ko wace rana , wannan zama haka zasuyi tayinshi har sai dare yayi sannan kowa zai kama gabanshi.

       Hayaniyar sai ƙara ƙaruwa takeyi palon sai ƙara cika yakeyi harabar gidan kuwa an cika ta da motoci , aikin gardamar suka fara kenan basu da aiki sai maganar “yan kwallo , ƙaramin palon na fito na zauna inga ta ina Dikko zai fito amma har akayi la’asar naje nayi sallah na dawo banji Dikko ya fito ba , gajiya nayi na koma ɗakina naci gaba zaman jiran tsammani.

      Yau ko abincin dare banci ba inayin sallah isha’e nayi kwanciyata jiya banga Dikko ba yauma ban ganshi ba haka nan na haƙura na kwanta , amma ba haka naso ba naso mu haɗu ko so ɗaya , tou ko baiso nazo masa gida bane shi yasa yake ta ɓoyewa kila yayi haka ne idan na gaji da zama in kama gabana ,

      Bandai yi bacci ba ina kwance ina ta tunanin duniya har 11:05pm a hankali gidan ya fara ragewa har yanzu banyi bacci ba , wurin misalin 11:49pm gidan yayi shiru gaba ɗaya , yau gaskiya sun tashi da wuri dan wani lokaci suna kai har 1:30am suna fira !

      Duk masu fita gidan akan idona suke fita amma har yanzu babu Dikko a cikinsu kuma har akayi zaman nan aka tashi banji an kira sunashi ko so ɗaya ba , kuma banji maganarshi ba , saida gidan ya zama babu kowa na haƙura nayi bacci.

     Wasa² har nayi kwana 3 gidan banga Dikko ba kuma mai gadi ya tabbatarmin yana nan ya dawo , na duba ɗakinshi ban ganshi ba , kuma idan na kira wayarshi yanzu tana shiga amma baya ɗauka , haka nan naji duk na takura gaba ɗaya na kama kaina saima na daina cin abincinsu kwata² saidai in tura a siyomin abincin da nake so naci lashe ² da duk wani abun kwaɗayi da zuciyata take sha’awar ci ko sha da kuɗin da Baban Hafsa ya bani,

      Ranki ya daɗe yau kwananki 2 da dawowa amma har yanzu shiru nakeji , gyara zama Jiddah tayi tare da cewa waini tayama zan fara samoshi ne ? Kwantar da murya Al ‘ Ameen yayi cewa haba ranki ya daɗe duk wayewarki da gogewarki kice baki san yadda zakiyi ki samo ba ? Tou taya akayi kika kwanta da shi ? Jiddah tace kwanciya daban maganar samun abinda boka yake magana daban ya bani “yar ƙaramar kwalba yace a ciki zan matso taya zan fara tara kwalbar nan na matso bayan kuma yana kallona.

Al ‘ Ameen yace ranki ya daɗe idan ya kwanta dake bayan kun gama abinda kukeyi sai kiyi kamar irin kina masa wasa naku na ma’aurata saiki lallaɓa kiyi dabara ko a hannunki ki samu , dama kin ajiye “yar kwalbarki a toilet kina matsowa sai ki tafi toilet kamar zaki wanke hannunki kina shiga sai ki zuba a kwalbar , ki maida hankali kinga abun kullum gaba yakeyi , kuma anje kamo yarinyar nan ta gudu yanzu babu wanda yasan inda take ma ,

       Jiddah tace gaskiya wannan shawara haka tayi , tou insha Allah zanyi , Al ‘ Ameen yace dadai kin taimaki rayuwarki , haka yaita ɗora Jiddah yana kaita yana baro.

          Da marece bayan na gama abinda nakeyi na fice daga gida , kasuwa na fara zuwa na siya niƙaf kamar yadda Baban Hafsa yace , banyi hijabi ko ɗaya ba saboda ina da hijabai sunkai goma a gidan Dikko , ina sayen nikaf in na lulluɓe fuskata na haye napep , ban sharce ko ina ba sai majalissar su Baban Hafsa , mai napep na sallama ya tafi ni kuma na isa wurin tare da sallama.

       Gaba ɗaya suka ansa sallamar yayin da Baban Hafsa ya taso fuskarshi ɗauke da yanayin kishi yana cewa sai ki kama kizo nan kuma bazaki faɗamin ba ? Wurin motarshi ya nufa ya ɗauko leda yana cewa da Allah kada ki sake zuwa nan kinji ko ? Nace tou , yawwa ga kayan makarantarki nan da littafanki komai akwai a ciki , nace ngode Dady shi kuma yacemin idan Allah ya kaimu goben zanzo makarantar taku nace Allah ya kaimu lafiya , ya ansa da am3n da kanshi ya tsaida min napep ya biya kuɗin , saida na samo abinda zanci da daddare da wanda zanyi kalaci da safe idan Allah ya kaimu sannan na wuce gida.

        Yauma gidan ɗinke yake da mutane babu masaka tsinke ko dana tunkari palon dole tasa na dawo saboda babu ta hanyar da zanbi in wuce , gaba ɗaya palon ya gauraye da ƙamshin turare iri² har baka iya gane na wani , kowa dai ɗan gaye ne babu sakarai kuma babu ƙazami dan duk “ya “yan attajirai ne , kowa dai yanaji da kanshi dan babu wanda yake so a fishi ,

        Bayan gida na zagaya wurin masallacin dake cikin gidan , a ƙofar masallacin na samu wuri na zauna sannan na fara duba kayan da nazo dasu , hada waya a ciki da layin waya kila Dady yana tunanin banda waya shi yasa ya haɗomin da ita , ƙaramar waya ce nokia ko kwali bata da sai caja , murmushi nayi tare da maida wayar na fiddo abinci naci gaba da ci saboda yunwa nakeji ,

      Ban daɗe da gama cin abinci ba suka fara fitowa danyin sallah magrib dan haka na tashi na zagaya ta ɗayar hanyar dan gaba ɗaya a wurin ƙofar masallacin suke alwallah , lokacin dana zagayo gaba ɗaya babu kowa a wurin sai Dikko kaɗai dake alwalla a ƙofar palon , gaishe shi nayi tare da mishi sannu da zuwa kallona yayi amma baiyi magana ba ,

        Sake gaishe shi nayi ya ƙara basarwa , raɓashi nayi zan wuce ciki a dai² lokacin daya gama alwalla ya ciko bakinshi da ruwa kamar da yayi niyar watsamin su sai kuma ya zubar a gefe yana warware hannun rigarshi daya naɗe yace ina kikaje tun ɗazu ? A daburce nace ina ina ta can na nuna mishi baya da hannuna , kina ta can ko ? Yayi maganar tare da jinjina kanshi yace yayi kyau,

      Daga haka bai sake magana ba ya wuce nima na shige ciki , ina shiga ɗaki na ajiye kayan dana zo dasu nayo alwallah nayi sallah , ina gama sallah na fara haɗa littafaina a cikin jikkar makaranta wani irin farin ciki nakeji naga Dikko kuma naji daɗi dana ganshi kullum nidai ƙara burgeni yakeyi addu’a ta ɗaya Allah yasa idan ya gama sallah yazo , ni kuma ince masa me yasa baka ɗaukar wayata idan na kiraka……?

     Zuciyata tace karki sake ki tambayeshi raina ki zaiyi , a bayyane nace ko yane gaskiya ya kamata nasan miye dalilin da yasa baya ɗaukar wayata , zuciyata ta sake gargaɗina a karo na biyu cewa ki kama kanki shi namiji ma ya riƙe ajinshi sai ke banza zaki damu dashi , murmushi nayi a bayyane nace ina wani maganar aji kuma bayan ina zaune a gidanshi , anya akwai wanda ya taɓa shiga rayuwa irin tawa ? Nidai ko a labari ko littafi ban taɓajin wanda yayi bahaguwar rayuwa mai tattare da ƙalu bale ba kamar tawa , 

Babana ya rasu , gidana kuma dana siya “yan uwana sun siyar dashi , ƙanin Babana kuma yace min zamana a tare dashi babban riskine , Yayun Babana kuma basu ma sanmu ba , Mamana ta gujeni ta tafi ta barni ina ta gararin rayuwa me nayi ma duniya ta juya min baya haka da ƙuruciyata ? Dole in cire wani girman kai inbi Dikko in zauna lafiya idan ba haka ba shima ya juyamin baya bansan ya rayuwata zata koma ba , ga mahaifiyarshi ta ɗanawa rayuwata tarko idan kuwa har nayi kuskuren bari ta kamani kashina ya bushe ,

      “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” Allah ngode maka ubangiji ka yafemin ka yaye min ƙunci da damuwa dan alfarmar sayyadis sadati , ka tausayamin ka karkato da hankalin mahaifiyata gareni kaji ƙaina badan halina ba , Inna kina wace duniya haka kika manta dani ? Niko duk halin dana shiga bana mantawa dake har abadan duniya kuma ina sanki Allah ya dafa miki ya jiƙanki a duk inda kike a faɗin duniyar nan kuma ya huci zuciyarki , Allah kaji ƙan Babana kasa ya huta….

      7:19am a cikin makaranta tayimin , ina cikin ayarin ɗalibai har a wurin taron assembly ko a wurin taron komai da turanci ake faɗa kuma abinda na fahimta kowa idan zaiyi magana da ɗan uwanshi bayayi da yaren hausa saidai da harshen bature ,

     Bayan an gama ko wane ɗalibi yayi ajinshi nima nayi nawa ajin JSS 1B shine ajina , duk “yan ajin nafi su girma kuma sai dariya sukemin suna kallona , wuri na samu na zauna ina tunanin idan har yaran nan nabar suka shiga gabana a karatu raini zasumin bana wasa ba , idan har na bar wani ɗalibi yayi na 1 a ajin nan bani ba naji kunya , dan haka na tattaro hankalina da natsuwata na fara ɗaukar karatu yadda ya kamata domin malamai sun fara shigowa.

     Babu laifi ina fahimta dan ina da ilimin addini sosai shi yasa nake ganin karatun boko bazai wani bani wahala ba , lokacin da aka fita break banje ko ina ba ina cikin aji ina ta naci , bayan an dawo malamai suka ci gaba da shigowa har aka tashi daga makaranta , bayan an tashi saida nayi azahar tare da addu’a ubangiji ya dafamin sannan na shiga ajin koyon darasi na musamman ,

     Saida la’asar muka tashi muna tashi saida nayi la’asar nabar makaranta kuma Dady bai zo ba , daga makarantar boko tsohuwar islamiyarmu na nufa na siya form na shiga ajin harda kuma ni na cika abuna da kaina da larabci , daga islamiya na wuce kasuwa na ɗinka hijabi da wando na islamiya sai gab magrib na isa gida.

        Yau duk taron su bai hanani wucewa ba , tunda na shiga kowa yabi ni da kallo har na shige , ina shiga wanka nayi tare da ɗauro alwallah na saka kayana ko mai ban shafa ba nayi sallar magrib dan an kira sallah , ina gama sallah wayar da Dady ya bani ta fara tsuwa tashi nayi na ɗauko ta a inda na ajiyeta , bayan na ɗauka muka gaisa yacemin kiyi haƙuri don Allah yau baƙi nayi a Office amma ina san ganinki yanzu ina zan sameki ne ? Nace saidai kai ka faɗamin a inda zan sameka , inda zan sameshi ya faɗamin nace tou gani nan zuwa yace sai kinzo ,

      Daga saman abin sallah dana miƙe wayata kawai na ɗauka wanda zanyo recording idan an taɓo labarin daya shafi Babana , haka na sake ratsowa na fito ina fitowa Dikko yace ina kuma zaki ? Nace yanzu zan dawo ina faɗin haka nayi gaba , yace ke karki sake fita daga gidan nan sai kuma gobe idan Allah ya kaimu , banma saurareshi ba na fice abuna.

      Ina fitowa daga palon na samu wuri na ɓoye dan nasan dole saiya biyo bayana , ina ɓoyewa kuwa ya fito yana kirana amma abun mamaki ya fita waje ko sahuna bai gani ba na ɓace kamar walƙiya , mai gadi ya tambaya ta wace hanya “Yar mata tabi ? Yace mai gida banga fitarta ba , Dikko yace baka ga fitarta ba ? Yace Eh , tabi ta gabanka ta wuce kace baka ga fitarta ba dan ka ɗaukeni sakarai ? Cikin girmamawa yace wallahi mai gida ban ganta ba , kallonshi Dikko yayi yace amma ai duk wanda zai shiga ko fita a gabanka idonka , kusa dashi ya matsa yace ta wace hanya tabi ? Mai gadi yace mai gida wallahi bata fita ba ,

       Dikko yace to rufe ƙofar karka sake kabar wani ya sake shigowa kuma karka sake ka bar kowa ya sake fita yace tou , daga ƙofar palon ya koma ya tsaya bayan wani lokaci kuma ya taho da sauri ya tunkari hanyar fita daga gida bayan yaje ya sake komawa ƙofar palon ya tsaya , magana yayi ma mai gadi cewa lokacin dana fito ƙofa a buɗe take ko a rufe ?

     Mai gadi yace a buɗe , Dikko yace buɗemin ƙofar , buɗewa yayi Dikko ya sake tahowa saida yazo fita yace tabbas bata fita ba tana cikin gidan nan dan ko da gudu ta fita fitowa ta ya isa na hangota ko yane , zanga ta inda zaki bi ki fita yarinya , yana faɗin haka ya koma motarshi ya zauna , dariya nayi a raina tare da cewa mu zuba wallahi babu wanda ya isa ya hanani fita a daren nan saina fita.

     Har aka kira sallah isha’e ina tsugunne cikin filawowi Dikko yana cikin mota , gaba ɗaya suka fito suka zagaya hanyar masallaci Dikko yace ma mai gadi karka sake ka bar wani ya shigo kuma kar wanda ya fita bari muyi sallah , dariya nayi nace aiko na fita na gama kuma tunda har ka bar motarka buɗe da ita zanje ,

      Yana zagayawa na fito na shige motarshi tunanin mai gadi Dikko ne ya buɗemin get na fice da gudu sakarai ya manta Dikko yace mishi zaiyi sallah , ina fita na kira Dady nace har yanzu kana wurin ne ? Yace min yabar wurin daya ji shiru kuma ya kira wayata a kashe , nace tou yanzu kana ina ne ? Yace ina nan asibiti , nace lafiya a asibiti ? Yace Hajiyarmu ce batajin daɗi , nace wace asibiti haka ? Yace min fmc nace wane ɗaki yacemin zuwa zakiyi ne ? Na gane wayanshi idan zanzo bazai faɗamin ba , dan haka nace aini tsoron asibiti ma nakeyi Allah ya bata lafiya dama ko nazo sauƙi zan nema mata daga nan ma nayi mata addu’a Allah ya bata lafiya , yace amin , cikin nuna damuwa da tausayin matar nace amma dan Allah da kun sake mata asibiti , yace ai anan likitan ta yake , nace tou Dady ai kuma da ɗakin sarakai kuka kaita tunda Allah yasa kana da iko , yace ai nan take nace tou Allah ya sawaƙa yace amin , sallama mukayi dashi na dawo gida ,

    Ina dawowa nayi horn ya leƙo yaga Dikko ya buɗe na shige a inda ya ajiye motar na ajiye na shige ciki da sauri , ina shiga nace fmc ɗakin sarakuna , gani nan zuwa gareki muguwar tsohuwa , hayaniyar Dikko najiyo yana cewa waye ya fita kuma waye ya shigo ? Ina alwallah naji ka buɗe ƙofa yanzun nan ina fitowa naji ka sake buɗewa , mai gadi yace mai gida ai kaine ka fita , Dikko yace na fita naje gidan wa ? Mai gadi yace na rantse da Allah kaine ka fita , Dikko yace idan ka sake cewa nine na fita saina mareka wallahi , mahaukaci ka ɗaukeni ko kuwa me ? Shiru yayi yana nunawa da hannunshi wallahi Allah kaine ,

      Dikko yace aiko ubanka zanci , abokanshi suka bashi haƙuri tare da cewa ya canja mai gadi kawai , mai gadi yanajin za’a canja shi ya fara wallahi ײ Dikko yace idan bakaimin shiru ba saina harbar maka baki da ƙafata , duk inajin hayaniyarsu na koma nayi kwanciyata na ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya ina ɗigawa bakina fura ina lashewa ,

      Motarshi ya koma yayi “yan dube² sannan ya rufeta bai ciro makullin ba yayo ɗakina , kwance ya sameni ina ta ɗiga fura a bakina hankalina kwance kuma ko inda yake ban kalla ba na ƙaddara ma babu shi kawai a wurin , An mata ina kikaje ? Ban kalleshi ba nace naje saman katifata ne kuma gaka ka ganni kwance ina shan fura ko zaka sha ne ? Bana san sakarci ina kikaje ? Tashi nayi zaune nace to ko nima mai gadin zaka maidai ni ne ?

       Rufe idonshi yayi yace ina kikaje nace ? Shiru nayi na koma na kwanta naci gaba da shan furata , har yanzu idonshi a rufe yake ya maimaita ina kikaje ? Ni nace maka babu inda naje sai tambayata kakeyi ina naje idan naje wani wuri zaka sameni ina kwance wai ?

       Shigowa yayi cikin ɗakin ya shaƙoni ya ɗagani tsaye yace zaki faɗamin inda kikaje ko saina buga miki kai da bango ? A tsorace nace babu inda naje ina nan tunda kace karki in fita na dawo na faɗa mishi duk yadda sukayi da mai gadi da lokacin da zai tafi sallah nace idan bana nan taya na san haka ? Naji kina nan amma dana tafi sallah ke kuma sai kika fita da mota ta , nace wai na fita naje ina ? Murmushi yayi tare da sakarmin wuya daga shaƙar da yayi mini yace Allah ya sawaƙe miki ganin ɓacin raina , wallahi dan ina tausayinki amma yau dasai kinsan kinmin gardama ,

     Fita yayi daga ɗakin yana magana ƙasa² , ajiyar zuciya na sauke daga tsaye na ida shanye furata na wuce nayi alwallah nayi sallah isha’e , ina gamawa nayi kwanciyata dan yanzu bana daɗewa banyi bacci saboda makaranta dan banda lokacin baccin safe kona rana !

      Yau da kanshi ya kaini makaranta kuma bai tambayeni wanda ya sani makarantar ba haka kuma bai tambayeni dalilin da yasa na koma makaranta ba , kawai dai tunda safe yazo dana fito zan tafi yace muje in saukeki , kuma daya saukeni yacemin zai dawo ya ɗaukeni , nace masa idan na gama zan kiraka saboda munayin lesson banza yayi yai tafiyarshi bai cemin komai ba ,

      Caf lallai ni zaka sakawa rayuwata ido ? Hmm idan kasan wata baka san wata ba malam Dikko , wallahi sainaje asibiti naga kishiyar kakata , yauma “yan ajinmu dariya sukemin hada wanda bama aji ɗaya dasu an gayyatosu suzo suka ƙatuwa a JS 1 , nima dariya abun ya bani dan haka basu bani haushi ba ,

     Ana tashi makaranta na fice saida naje fmc nayi waya da Dady nace masa yamai jiki ? Yace da sauƙi , nace kana asibitin ko kana office ? Yace idan ina asibitin miye ? Nace wai da ka haɗani da ita in mata sannu da jiki jiya da tunaninta na kwana ko da nayi sallah dare saida nayi mata addu’a Dady , murmushi yayi tare da godiya sannan yacemin yana Office ! Nace Allah ya sawaƙe ya bata lafiya yace am3n ya gode , mukayi sallama dashi ,

       Bayan mun gama waya da Dady nace ma mai napep muje , tada motar yayi muka isa ɗakin , da tambaya na gano ɗakin da take a nuste na shiga da sallama , suka amsa min cikin sakin fuska tare damin sannu da zuwa , wuri na samu na tsugunna na gaishesu cike da ladabi tare da tambayarsu ya mai jiki ? Sukacemin da sauƙi nace Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne , suka amsa da am3n , wurin tsohuwar na matsa nayi mata sannu ta ansa da yawwa nace ni ƙawar Hafsa ce , tace Allah sarki aiko yanzu ta tafi ita da ƙawayenta nace Allah sarki , 5k na bata cikin kuɗin da ɗanta ya bani nace ayi haƙuri daga makaranta nake , godiya sukayi tayi tare da tambayata idan Hafsa tazo wa za’ace mata , nace ace mata uwar ɗakinsu ce , sukace da ance haka shikenan nace Eh kuma ai zan sake dawowa sukace Allah ya yadda , godiya sukayi sosai ni kuma na fito abuna.

Kai tsaye makaranta na koma saidai nayi sallah na shiga aji kuma malam yamin faɗa kar na sake na sake makara nace insha Allah .

      A asibiti kuwa abinda yasa nace musu su faɗawa Hafsa uwar ɗakinsu ce dan kada a faɗa Dady yana nan idan yaji Sultana kila hankalinshi zaikai kaina , tou dukansu babu wanda yasan nasan kowa a cikinsu , Dady nasanshi ya sanni , Hafsa ta sanni na santa amma gaba ɗayansu babu wanda yasan ina tare da wani a cikinsu , Hafsa tasan ni ɗiyar Binna ce amma bata san ina da zuminchie da ita ba , Dady kuma bai sanni ba kuma baisan daga ina na fito ba yasan Binna amma baisan ni ɗiyarshi bace ba , su kuma asibiti basu san ko wace ce ni ba ni kaɗai nasan ko suɗin su waye.

     Yauma sai gab magrif na koma gida saboda naje islamiya , kuma Dikko yayi masifa sosai yace har makaranta bokon bazan sake zuwa ba duk abinda nake idan ban sani ba motsina ɗaya a waje wallahi saman tafin hannunshi yake kuma ya faɗamun naje asibiti saboda kin ɗauke ni bansan abinda nakeyi ba ni zaki gayamin idan kin gama zaki kirani , wallahi kallonki kawai nakeyi amma ki sani koda gira kikayi magana nasan ƙafar dake miki ɗingishi ,

      Na fiki hankali na fiki wayau nafi sanin rayuwa shekaruna da naki ba ɗaya ba gogewa ta da taki ba iri ɗaya ba duk wani wayau da kike tunanin kina dashi ni a wurina Xeyro , mu zuba dani dake tunda kin rainani zanyi miki maganin rashin kunya.

       Nace yi haƙuri don Allah kuma dama ai kasan zan faɗa maka kuma saida na faɗawa mai gadi nace nabi ƙawata zan gano kakarta ko Yayana yazo , ki rufemin baki ke ɗaya kika shiga napep sannan kuma kika fito daga cikin makaranta kina waige² yaushe kikayi magana da mai gadi ?

     Ba mai gadi ba malam na faɗa mawa , tou malam kika faɗa mawa koma dai waye na soke makaranta daga yanzu , dan girman Allah kayi haƙuri wallahi bazan sake ba , na gama magana yana faɗin haka ya wuce ɗakinshi , binshi nayi naci gaba da magiya ina bashi haƙuri , banza yayi dani ya wuce toilet yana alwallah , saida ya fito nace dan Allah kayi haƙuri Yaya Dikko , murmushi yayi yana maida agogonshi yace da kince Yaya cuta na zakiyi ya ƙarasa maganar yana kallona , nima murmushi nayi ina kallonshi cike da soyayya , shima cike tsantsar ƙauna yake kallona kowa ya kasa daina kallon kowa.

      Dafa kujera yayi yace An mata wai a haka baki so na ko ? Ɗan turo baki nayi banyi magana ba , yace Hmm irin wannan kallo haka idan kuma kika fara so na wane iri zakimin kenan ? Kunya naji dan haka na juya na fice da sauri daga ɗakin murmushi yayi tare da cewa Allah ka kamamin zuciyar yarinyar nan kasa mata tsantsar sona da tausayin rayuwata , ubangiji ka ƙaramin haƙuri akan duk abinda zatamin ka wadatani da tausayinta ka bani ikon riƙeta da gaskiya ka kauda sharrin shaiɗan tsakani na da ita dama duk ko wane namiji dake zuwa gidan nan har ta gama zaman ta a gidan nan , ya ubangiji ka ɗauke idon duk wani namiji akanta , ka janye mata tunanin ko wane irin namiji saini ,

       Ina shiga ɗaki saman katifa na faɗa tare da rufe idanuwana na kwantar da fuskata a saman bargo daɗi kawai nakeji Dikko yayimin murmushi kuma nasan wasa yake bazai hanani zuwa makaranta ba dan yaɗan latsani ne , wallahi Dikko ɗan gayene mai kyau na burgewa yanayin magana cikin salo mai ɗaukar hankali , ihu nayi tare da murginawa nace ina sanka mutumina , ina sanka ׳ , juyowa nayi na kwanta rigingine fuskata tana kallon sama na rungume hannaye na a ƙirji na lumshe idanuwana cikin yanayin jin daɗi nace kuma wallahi bazan sake tafiya na barka ba dan ina shan wahala idan bana tare dakai ,


(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


      Jiddah tsaye a gaban Al ‘ Ameen duk ta fita hayyacin tace ni wallahi na kasa , Al ‘ Ameen yace haba ranki ya daɗe kamar dai ba wayayya ba ? Saboda rashin wayau aiko ƙawarka mace bakya faɗa mata yadda kike kwanciya miji ba bare yaron mijinki , Jiddah tace ai idan ya kwanta dani baya sauka daga jikina sai bayan mintuna 15 , Al ‘ Ameen yace basai ki saukeshi da dabara ba ? Jiddah tace wallahi baya sauka , tsoki Al  ‘ Ameen yayi yace haba Aunty Jiddah karki bari kiyi wasa da wannan damar ki sake jarabawa a ƙaro na ƙarshe mu gani , Jiddah tace to saidai idan ya dawo ya tafi Abuja Al ‘ Ameen yace Allah yasa ya dawo lafiya ta ansa da am3n , 

     Haba Jiddah waye ya faɗa miki Dikko na Abuja…….?

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button