KWARATA 56

???? —— 56
MAIMOUNATH O . G {{ Mahnoor }} ni bansan da irin kalaman da zanyi amfani dasu wurin miƙa saƙon godiya ta a gareki ba , idan zanyi ta rubuta ngode² sai cajin wayana ya ƙare ban gama cewa ngode ba , duk da haka dai ngode sosai Allah ya saka da alkairi ubangiji ya ƙara arziƙi ya ƙara zaman lafiya tsakaninki da naki master ya kawo
zuri’a masu albarka…
Ummu Farhana ta sake zagayo muku da wani sabon salon labari nata mai taken FANNAH {{ marainiya }} hanzarta ki samu naki karki sake ki bari a baki labari , ina miki barka da fara sabon littafinki Allah ya taimaka yasa yadda kika fara lafiya ki kammala lafiya…!
Saida Al ‘ Ameen ya tafi sannan Jiddah ta koma ɗakinta cikin tashin hankali , ta zagaya ƙaton palon ta bata san adadi ba , mafita ta farko da zuciyarta ta yanke mata shine duk yadda za’ayi kawai a fara kamo mata Sultana , shawarata ta biyu kuma sai gata ga Dikko…
Wayarta ta ɗauka ta fara kiran Momy bayan ta ɗauka suka gaisa tun kafin a gama gaisuwar Jiddah tace Momy har yanzu dai kin kasa wani abu akan yarinyar nan , Momy tace waye yace miki na kasa…..?
Jiddah tace to ai naji shiru har yanzu babu wani ci gaba , murmushi Momy tayi tare da cewa kwantar da hankalin ki an gano komai nata tana shiga makaranta kullum da ƙarfe 7 da wani abu na safe ,
Tana fita daga makaranta kullum karfe 4 , daga nan tana wucewa islamiyya , tana zuwa a napep idan aka tashi kuma ta shiga motar makaranta ta sauka islamiya , yau ba’a napep taje ba ance wani yakaita kuma basu san ko waye ba ,
Momy tou mi yasa basu kamata ba ? Kinsan komai yana san bin diddiƙi kuma har yanzu sun kasa gano gidan da take zaune , saboda sunce daga Islamiya kullum take ɓace musu saboda tana amfani da abun rufe fuska { niƙaf } mafiya yawan ɗalibai dashi suke amfani , Momy basai an gano gidan da take zama ba nidai burina kawai a kamota idan ba haka ba zata iya sake sulɓewa , Momy tace babu damuwa ,
Sun dai daɗe suna saƙawa yadda zasu ci mutuncin Sultana idan aka kamota daga baya sukayi sallama , Jiddah kuwa taci alwashi idan har aka kamo Sultana tunda dai har take tarayya da mijinta tou tayi alƙawari sai tayi mata tsarki da ruwan tsidagu bayan ta jajjaga attaruhu ta zuba abonaki a cikin ruwa zafi zata zaunar da ita a ciki , sai taci ƙaniyarta yadda gobe ko ance tayi iskanci da Dikko sai tace ta tuba….
Kamar yadda na saba fita daga gida yauma haka na fito sanye cikin kayan makaranta na , a palo na samu Dikko zaune saman abin sallah ya jingina da kujera ya miƙe kafafuwanshi ɗaya saman ɗaya yana karantun al’qur’ani mai girma ,
Kallona yayi amma baiyi min magana ba , hannu na ɗaga mishi alamar saina dawo nayi gaba , gab da zan fita daga palon yace An mata nace karki je makarantar nan ko , cikin muryar lallashi nace haba Yayana na ƙarasa maganar ina kwantar da kaina nayi kalar ban tausayi , rufe al’qur’anin yayi yace nidai banajin daɗi , jikina yana min wani iri inajin kamar wani abu zai faru dake wallahi , nidai dan Allah kiyi haƙuri da makarantar nan !
Nidai zanje a haka , a kasalance ya lumshe idanuwan shi yace a , a , nace dan Allah , kallona yayi tare da cewa kiyi shiru zanyi fushi , zama nayi saman hannun kujera ina magana ƙasa² cewa kayi fushin mana ko an faɗa maka nima banda zuciyar ne ? Na ƙarasa maganar ina hararar bango ,
Ɗan kintsa bakinsa yayi ya kallo inda nake yace banji abinda kika ce ba , ai dama bana so kaji , saboda kinajin tsorona ko ? Sallamar Ashiru ya hana na bawa Dikko ansa , gaishe shi nayi bayan na ansa sallamar da ina kwana , maidomin gaisuwar yayi da ina kwana ranki ya daɗe , kunya naji dan haka na kwantar da kaina jikin kujera banyi magana ba ,
Daga inda yake tsaya ya haɗa hannayen shi ta baya tare da rusunawa cikin girmamawa yace mai gida barka da safiya , yawwa Dikko ya faɗa a taƙaice ,
Matsawa yayi ya duƙa kusa da Dikko yana magana , ya daɗe sosai kuma banajin abinda suke faɗa amma duk yadda akayi gulma sukeyi , bayan ya gama maganar ya fita , shima Dikkon tashi yayi ya maida al’qur’an inda yake ajiyewa ya fita , nima na tashi nabi bayanshi…
A ƙofar fita mukaci karo , shi yana ƙoƙarin dawowa ni kuma ina ƙoƙarin fita , cikin faɗa yace ina zaki je ne wai ? Komawa nayi na zauna banyi magana ba , ciki ya koma bai wani daɗe ba ya fito , yana fita yace jeka kawai zanzo bayan la’asar in Allah ya kaimu ,
Saida Ashiru ya tafi Dikko ya dawo , ba tare daya tsaya ba ko ya kallo inda nake yace fita zanyi idan kina zuwa ki cire uniform in sai in tafi dake , kaje bazan je ba , sai kinje ya faɗa a dai² lokacin daya shige ciki….
Tunda naga ya daɗe bai fito ba raina ya bani wanka yakeyi zaman toilet sai kace mai jego , tashi nayi na ɗauki jikkar makaranta ina na koma ɗaki ,
Wayoyina na ɗauko na fara dubawa , tarin miss calls a wayar da Dady ya bani ya kira sau adadin da bazan iya ɓata lokacina wurin faɗar su ba , Alaji ya kira Aunty Suwaiba , Malam Ɗayyu da baƙin numbers wanda banda su a cikin wayana !
Cikin baƙin numbobin na fara kira , ana ɗauka naji ya fara babbaka min ashariya tare da cewa duk inda kike a faɗin duniyar nan idan na kamoki kwanakin rayuwarki ya ƙare , Lahaula wala kquwwata illa billahil aliyyul azeem , waye kai …? Tsoro , tsoro ne , ni tsoro ne mai ban tsoro kuma na duƙufa akan cewa saina ɗan ɗana miki ɗanɗano tsoro sannan na kasheki ,
Na ganki nasan inda kike ƙoƙarinki ya ƙare kuma na tiso rayuwarki gaba saina ga kin shaƙe kinbi iska hankalina zai kwanta wuƙa zan caccaka miki a zuciya a wurin zaki mutu ko harbawa bazakiyi ba yau zan kashe ki……. Yanzu ne ? Ko anjima koma dai yaushe ne kici abincin bankwana gani nan tahowa…..
A firgice na juyo zufa ta tsatsanfomin dan ya faɗi kalaman nashi da kaushi , a wahalce nake fitar da lumfashi dan wanda baya cikin ɗakin yana iya jin sautin fitar numfashi na , zufar goshina na goge da sauri na juyo Dikko na gani tsaye yace me ya sameki ne ?
Mutuwa zanyi….. Na bashi ansa kai tsaye , cikin rashin fahimta yace wace irin mutuwa kuma ? Cikin kuka nace nima zasu kasheni kamar yadda suka kashe Babana kuma suka kashe Aunty Mamy suka kashe wata Auntyn wacce ma bata samu damar isowa wurina ba suka shafe labarinta ,
Tsoki Dikko yayi ya juya yana aike kanki rawa yakeyi kullum baki gajiya da sakin layi kamar zararriya , yadda yayi min sai abun ya tunomin ranar da za’a kashe Babana daya faɗamin nace masa shirmen mafarki ne ni kuma yau gashi na faɗa amma ni an danganta ni da mai rawar kai.
A tsorace na sake lalubo wata baƙuwar lambar na sake kira , itama wata murya ce daban ta tabbatar min da mutuwa ta yau babu gudu babu ja da baya , kashewa nayi na kira wayar Dady bayan ya ɗauka muka gaisa na tambayeshi mai jiki yace da sauƙi , ya akayi baki je makaranta ba yau ? Ya tambayeni ,
Cikin faɗuwar gaba da dakiya nace naje mana , abinda naje makarantar ban sameki ba , nace da wane lokaci kaje ne ? Tunda safe ina bakin get in makarantar ban ganki ba , jinjina kaina nayi tare da cewa amma me yasa kaje kai tsaye bayan baka saba zuwa ba saika faɗamin zaka zo , yau shawara na sake shi yasa naso yi miki bazata kawai , yanzu kina ina ne ?
Kai kana ina haka ? Har yanzu ina bakin get in makarantar ku ? Ka jirani gani nan zuwa , ina faɗin haka na kashe waya , lambar Alaji na kira bayan na gama waya da Dady , tana shiga ya ɗauka ko gaisawa bamuyi ba yace Sultana kina ina ne ? Ina Lokoja na bashi ansa kai tsaye , wace irin Lokoja kuma ? Nace lokoja nawa ka sani ? Tou ke meya kaiki lokoja ? Idan aka ga kuɗi katsina aka gansu a lokoja abin mamaki ne ? Ai kuɗi yawo sukeyi babu inda basa iya zuwa a cikin ƙanƙa lokaci , nace to karkayi mamaki domin karuwa da kuɗi duk ɗaya suke yanzu nan zaka ganni anan zuwa anjima kuma in ɓace , nabar katsina ina lokoja , zai sake magana na katse kiranshi na kira Aunty Suwaiba , bayan ta ɗauka muka gaisa nayi mata sannu da jiki ta ansa cikin kulawa tare da cewa Sultana kina ina ne ? Aunty ina kaduna , yaushe kika tafi ne ? Tunda muka rabu da malam ɗayyu a katsina ranar nabar katsina da daddare !
Amma me yasa baki faɗamin ba , murmushi nayi sannan nace kiyi haƙuri Aunty , tsoki tayi tare da kashe wayar bata sake magana ba , tana kashewa na kira malam ɗayyu shima mun gaisa muka ɗan taɓa fira sannan yace min kina katsina kuwa ? Nace masa kana san gani ne ? Yace Eh nace ina Abuja , yaushe kika tafi ? Nace jiya da daddare , yaushe zaki dawo ? Sai bayan wata ɗaya ina faɗin haka na katse kiran malam ɗayyu.
Lallai kawai abinda zai faru , tabbas akwai masu farautar ruhi na , mutum ya bashi da tabbas kuma yakan iya canjawa a cikin ƙanƙanin lokaci , kuɗi sunkan canja mutum tsoro yana canja mutum , nacewa Alaji ina Lokoja , Aunty Suwaiba nace mata ina Kaduna , na faɗawa Malam Ɗayyu ina Abuja , Dady kuwa na faɗa masa ina Katsina……. Murmushi nayi tare da ajiye wayoyi na a gefen katifa dani daku mu zuba lumfashina yana hannun ubangiji idan mutuwa ta yazo wayau ko tsimi da dubara bazai hanani ansa kiran mahalicci ba , fatana Allah yasa inyi kyakkyawan ƙarshe.
Amisty da Bello zaune a mota , bayan ya kora mata wani birkitaccen sharhi ya ɗora mata da cewa yayi tarayya da Sultana ne ta ɗauki hoton videon abinda mukayi tana ta bazashi a social media gashi yanzu ta durƙusar dashi a harkar wasan caca idan Amisty zata iya tou da Allah ta kawo mishi Sultana ko ta faɗa mishi wurin da Sultana ke zama idan kuma bata sani ba ta binkico mishi inda Sultana take a cikin sa’o’e 24 zan bata naira dubu ɗari ,
Su Amisty anji zancen kuɗi dan haka tace ai sanin inda take ba abu bane mai wahala dan nima haƙe nake da ita saboda ta ɗauki tsiraicin mahaifina ta turomin , naso na ɗauki na ubanta nima na tura mata dan kai kanka kasan nidai Binna Allah kaɗai yasan iyakar abinda ke tsakaninmu , ina san Binna tunda nake ban taɓa huɗɗa da wani namiji ba sai akan Binna , shine ya koyamin ya gogar dani tun ban iya ba har na ƙware dan Binna aharkar mata yai zarra , na jaraba bin wasu mazan amma banji daɗinsu ba nayi niyar ɗaukar videon tsiraicin shi sai nayi tunani idan har ya sani nice nayi masa zai rabu dani ni kuma idan ya barni bansa ya zanyi rayuwata ba , kwatsam kuma sai ga mutuwarshi dan da na lashi takobin auren Binna dan in dasawa Sultana baƙin dafi mai wahalar amayarwa amma sam Binna yace bazai aureni ba.
Murmushi Amisty tayi mai cin rai tare da cewa Hmmm Allah ya jiƙan “yan maza a ƙiyama , Binna namijin duniya jajirtaccen namiji mai kafawa mace soyayyar shi a zuciyarta mai wahalar goguwa ya tafi ya barni da maraicinsa , na tsine kuma bazan daina tsinewa wanda yayi sanadiyar mutuwar Binna ba , amma a tsaye nake saman ƙafafuwana saina wulaƙanta rayuwar Sultana idan dai har ina numfashi a duniya…
Ta ƙarasa maganar tare da fara kiran wayar Sultana , ni kuma lokacin da kiran wayar Amisty ya shigo cikin wayata a lokacin muna gidan abokin Dikko su suna saman tebirin cin abinci sunayin kalaci dan tunda Ashiru ya kawo abin kalaci Dikko bai fito dashi daga mota ba yace idan yazo nan zamuyi kalacin tunda jiranshi akeyi wai wasu dokuna ne aka kawo mishi zai gansu , shi kuma abokin nashi ya uzira mishi wai zai tafi ɗauko matarshi ,
Ko ina zai ɗaukota Oho mishi , ɗaukar wayar nayi muka gaisa , bayan gaisuwa Amisty tace uwar room gaba ɗaya kin manta damu , miye duniya dake abu baya wucewa wurinki ? Da Allah kiyi haƙuri idan dai akan abinda ya faru baya ne muyi haƙuri abinda ya wuce ya zama labari muyi haƙuri dukanmu mu fuskanci sabuwar rayuwa ,
Labarin Babana ne ya dawo min a kaina da yace bayan nayi fushi da Bello saida yayi yadda ya yaudareni ya sake dawowa dani cikin rayuwarshi ya jagwalgwalamin rayuwa , murmushi nayi cewa ba komai Amisty ya wuce , to kina ina ne yanzu dan ina so inzo har gabanki in durƙusa a saman guyawuna in baki haƙuri , ina kano aiko yanzu ma sa’a kikayi kika sameni gab nake da kashe waya kiranki ya shigo ,
Amisty tace me kikaje yi kano uwar ɗaki ? Zanje Lagos ne kuma a jirgi zan tafi , tou yaushe zaki dawo ? Ƙarshen wata ina faɗin haka na kashe wayata murus ,
Shiru Bello yayi bayan ya gama jin wayar Sultana da Amisty , bayan wani lokaci yace ma Amisty jeki kawai zan dawo anjima , fita Amisty tayi daga cikin motar tana mishi addu’a Allah ya dawo dashi lafiya ta wuce ,
Fitar Amisty Bello ya dunƙula uwar ashariya yace lallai yarinyar nan ta ɗauki mutane “yan iska , dan duk wanda sukayi waya da Sultana banda Dady a gaban Bello akayi ta , saboda Bello yaje gidan Baba Ƙarami ya tambayeshi inda Sultana take a matsayinshi na aminin mahaifinta , Baba Ƙarami yace baisan inda Sultana take ba tunda shi Baba baisan baƙin halin Bello ,
Bello yace masa ko kasan mutanen da take huɗɗa dasu ? Kai tsaye Baba ya faɗi Alaji da malam ɗayyu , kuma duka mutanen nan babu wanda yasan Bello sunansa kawai sukeji , kuma babu wanda yasan akwai tsama tsakanin Bello da Baba , koda yaje wurin malam ɗayyu cewa yayi shi aminin Baban Sultana ne kuma yana nemanta dan ta tattaro mishi kan “yan gidansu ya taimake su , kuma ya kira wayar Sultana bata ɗauka kila bata ɗaukar baƙuwar number , shine yace malam ɗayyu ya kira Sultana suji ko tana ina ? Tunda shi tana da number shi ,
Da malam ɗayyu ya kira bata ɗauka ba shine ya kira Aunty Suwaiba , kuma duk da suka samu damar yin waya da Sultana ta rarraba musu , tacewa Alaji tana lokoja , ta cewa Aunty Suwaiba tana Kaduna , ta kuma faɗawa malam ɗayyu tana Abuja da sukayi waya da Amisty kuma tace tana filin jirgin kano a cikin jirgi zasu tashi yanzu zuwa Lagos ,
Itama Momy da aka faɗa mata cewa Sultana bataje makaranta ba cewa tayi karsu sake su dawo sai sunganta ,
Shi kuma Bello bokanshi yace dole sai an kashe Sultana idan ba haka ba masifa da balbalin bala’e tsutsar magana zata cizar mishi harshe zai tonawa kanshi asiri duk abinda yayi zai faɗa da bakinshi makarin wannan masifa shine kisan Sultana….
Dikko kuwa bayan sun gama kalacinsu da kanshi ya tattara komai ya bani yace in mayar a mota , ansa nayi naje nakai mota na dawo na samesu a inda suke ta tattaumawa , maganar dokunan kawai akeyi a hankali abokansu suka fara cika gidan sai an zakuɗa doki yayi sama yana haniniya sai ayi mishi hoto , hanayi kawai ke tashi ganin inda muke tsaye mutane sun fara yawa Dikko yace in koma mota in jirashi yana jiran Umar yazo ne , dan abinda na lura shima gidan babu mata a ciki,
Wurin mota nazo na tsaya ina neman sa’a inyi waje , ina tsaye ina neman sa’a nake ganin rashin aikinyi na maza ko kuwa rashin sanin darajar kuɗi ne , dan naji wai duk doki ɗaya ana maganar miliyoyi gaskiya Dikko baisan darajar kuɗi ba , wato rayuwarshi zata ƙare a mota ne da dokuna sai yawon tsiya kamar kuɗi , na daɗe a wurin sannan Umar yazo.
Umar na shigowa na samu nasarar fecewa daga cikin gidan , da gudu na fita ina gudu ina ɗaura niƙaf ina ,gidan baya da nisa da titi saidai kawai ace anguwar gayu ba’a samun abin hawa tunda mafiyan su kowa da mota yake amfani ,
Wayar da Dady ya bani na ciro na kirashi yafi a irga amma bai ɗauka ba , na kirashi har na gaji yaƙi ɗauka , ganin bai ɗauka ba kawai nahau napep na nufi makaranta dan a tunanina yayi fushi na ɓata mishi lokaci ,
Ina fitowa napep da Al ‘ Ameen na fara cin karo ina ganinshi na nufi napep da gudu da zumar komawa , dan tunda Dikko yacemin Al ‘ Ameen baya so na yana biye da rayuwata dan ya ɓatamin suna yasa ina ganinshi na nufi hanyar komawa dan karya bawa Dikko labari ya ganni tare da wani , yawwa gata can ku kamota , inajin ance a kamoni ai banma yi gigin komawa napep ba na ibi santa nabi ta lunguna na yanki fili naci gaba da gudu , ai kamar kura taga kare haka suka biyoni da gudu , ganin da gaske ni suke bi yasa na sake tattarewa naci gaba da gudu kamar raina zai fita.
Dikko kuwa bayan Umar yazo ya dawo mota bai samu Sultana ba , idan hankalinshi yayi dubu ya tashi da guda² cikin palon ya koma dan a tunaninshi ko ta gaji da tsayuwa ta koma ciki , ya duba bai ganta ba ya dawo ya duba iya inda yasan mutum zai iya lafewa a gidan babu Sultana babu ma mai irin siffar mata a gidan kawata² ,
Wayarshi ya ciro daga cikin aljihu ya fara kiran wayarta amma a kashe , dan tunda ta gama waya da Amisty ta kashe wayar , cikin tashin hankali Dikko ya shiga mota ya fita daga gidan da gudu wallahi kai tsaye makarantar su Sultana ya nufa dan a iya fahimtar da yayi mata tana da taurin kai da kafiya abinda tasa kanta shi zatayi bata jin bari kuma bata san yi haƙuri ba , tunda tasawa ranta zuwa makaranta yasan sai taje can wallahi.
Shi kuma yau yayi alƙawari idan harya kamata sai taji babu daɗi saiya jagula mata rai yadda ko baya nan idan yace mata kar tayi abu zataji tsoron fushinshi ,
Ta wata ƙatuwar santa na ɓullo ina ta raba idanuwa kamar nayi ma sarki ƙarya , ina ta murna na samu wurin ɓoyo , duƙawa nayi tare da cire niƙaf ɗina ina fita da hijabina dan nasha gudu zafi ya tasomin , ɗan lumfashe idona nayi ina maida numfashi bayan na sarara buɗe idon da nakeyi mukayi ido huɗu da Bello , kamar a mafarki da sauri na ƙara buɗe idanuwana wata irin harara ya zabgagamin bara’uban nan wani irin tsalle nayi na haura wata katanga na tsula da gudu Bello ya biyoni , tashin hankali abinda na ambata kenan yayin dana juya naga rundunar da suka biyo bayana , ga masifar yunwa da nakeji duk yau babu abinda naci gashi juwa ta fara ibana , har bana ganin gabana sosai saboda wahala……
Dikko kuwa bayan yaje makaranta yayi bincike ce masa akayi Sultana bata zo ba , jinjina kai yayi cikin tsananin ɓacin rai wallahi idan har An mata ta bari ya kamata yana cikin fushin nan kashin ta ya bushe ,
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Bello kuwa cewa ya farayi wayyo jama’a ku tare ku taremin ɗiyata ku agazamin don Allah , dariyar mugunta nayi tare da addu’ar Allah yasa masu bin bayana su riƙe Bello suce tunda shine ubana su bashi azaba mai tsanani………