KWARATA 6

Murmushi yayi kad’an da gefen bakinshi sannan ya kuncemin hannu na, mik’ewa nayi da sauri na d’auka hijabina na saka, sannan nayi hanyar fita da gudu,
Dukan k’ofar d’akin na farayi tare da kwarara ihu a kawomin d’auki, Dikko bai sake bi takaina ba ya tashi ya shige ciki, dan yasan inda nake ihuna banza ne kururuwata wofi…
Alwallah yayi bayan ya shiga yai kwanciyar shi, duk abinda Dikko zaiyi bayayin shi kai tsaye zai dad’e yana tunani idan yayi abun bayan wani lokaci me zai haifar mishi ? Yana duba duk abinda zaije ya dawo kafin ya aikata…..
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Ni kuma gajiya nayi da doke doken k’ofa na zauna a wurin saboda har muryata ta shak’e tama daina fita sosai, a wurin na zauna har asuba banyi bacci ba ina zaune,
Koda asuba a gabana Dikko ya fito da jallabiya brown a jikinshi da hula fara wacce ake cema tashi da kwakwa hannun shi d’aya a aljihu d’ayan kuma rik’e da makulli, bud’e k’ofar yayi da makullin ya fita, kuma yana fita yasa makulli ya rufe ta waje,
Nima tashi nayi na shiga ta hanyar dana ga Dikko yake bi yana tafiya, hanyace doguwa sosai ta tafi d’od’arar tasha tayils sai kyalli yakeyi mai d’aukar ido, sai tukwanen shukoki da suka sakani tsakiya, wato wasu a gefen damata wasu a haggu na,
Ina zuwa k’arshe naga hanya ta rabu biyu, daidai bangon da hanyoyin suka rabu kuma anyi rubutu wanda bansan abinda aka rubuta ba, saidai zuciyata ta gargad’eni da na tsaya karna fad’a inda zan kashe kaina.
Dole naja na tsaya daga nan, zama nayi a wurin, ban wani dad’e da zama ba Dikko ya dawo, a daidai inda nake zaune yace taso muje ya fad’i maganar ba tare daya tsaya ba,
Da sauri na tashi nabi bayanshi dan zuwa wannan lokacin zuciyata ta tabbatar min babu abinda Dikko zaimin, yanayin shi abinda na lura yanayin abu na mutuntaka, yana da ruwan mutanen kirki kila zai tausaya min.
Allah ka azurtamu shine abinda na fad’a a zuciyata yayin da na shiga d’akin Dikko, banda cikakkiyar natsuwa a wannan lokaci shi yasa ban wani damu da abinda d’akin yake ciki ba, saman kujera ya zauna tare da cewa ga wurin wanka can ya nunamin da hannunshi,
Ki fara wanka sannan kiyi alwalla, zaki ga ruwa yana nan na zuba miki dan karki je kiyiwa mutane kauyanci, a inda ruwan yake anan akeyin wanka kuma karki sake kimin fitsari a ciki,
Banza nayi na kyale d’an iska na shige, saida nayi fitsari na a inda yace baya so sannan nayi wanka nayo alwallah na fito, wurin da zanyi sallah ya nunamin ina kabbara sallah ya shiga toilet in,
Jinjina kanshi yayi sannan ya fito ranshi a matuk’ar b’ace , ko ya akayi ya gane nayi fitsarin oho ! Rashin sani ashe ya gwada ni ne yaga idan ya kyaleni bazan sake mishi rashin kunya ba, idan ya tabbatar banyi fitsarin ba zai fitar dani na tafi gida,
A fili yace shawar dare zan d’auka kawai, ledar da Bello ya ajiye mishi jiya itace ya d’auka ya fita, ashe maganin maza ne a ciki, Bello yace masa duk wanda yayi masa a ciko tou shi zaisha guda d’aya, shi kuma a nashi tunanin ko wanne zaisha guda d’aya a ciki,
Duka magungunan nan babu wanda Dikko baisha ba, bayan ya gama sha ya shigo, a lokacin na gama sallah ina zaune wurin da nayi sallah, gyara labuleye ya farayi lokaci guda duhu ya fara bayyana a d’akin, kashe hasken fitilar dakin yayi lokaci guda yanayin d’akin ya koma kamar dare,
Bansan ya taho ba saidai naji an rik’oni cikin duhu, saida ya rik’eni sannan ya mik’ar dani tsaye amma baiyi magana ba, fitilar wayarsa ya kunna sannan ya sakata a aljihun gabar rigarshi,
Kamo fuskata yayi a bakina ya cuccusa min wani abu sannan ya nad’e bakin da salitaf, hijabina da zanin jikina ya cire ya zubar awurin, ganin da gaske yake yasa naji wani irin k’arfi yazo min na kwace na fara kai duka ba tare da nasan inda yake ba saboda duhun da d’akin yayi,
So d’aya na sameshi kawai ya rik’e hannuwana duka yace ni kika daka ? Waye yace miki ana dukana ? Murd’e min hannu yayi saida yayi k’ara sannan yace ko a gidanmu ba’a tab’a dukana ba kuma babu mai min kallon banza kowa so yake ya kyautata min dan insan dashi. Ke kuma kimma samu Dikko a arha har wani kai mishi duka kike ? Zanyi maganin rashin kunyarki yanzu nan.
Hannun daya murd’e shine ya jani dashi har zuwa bakin gado, jefani yayi saman gadon zuwa wannan lokacin ko motsin kirki bana iyawa saboda murd’ewar da yayi ma hannu na, shima jallabiyar shi ya cire tare da hawowa saman gadon.
Gaba d’aya Dikko ya zare hankalinshi da tunaninshi ya fita daga jikinshi, babu wani sauk’i bare tausayi ya nufi hanyar masar ba tare da tunanin komai ba,
Wata irin gumza nayi a lokacin da Dikko ya shigeni, jikina yana kyarma saboda azaba nasa hannu na mai lafiya na kware abinda ya rufemin baki, nace kaji tsoron Allah karka b’atamin rayuwa ka rufamin asiri dan girman Allah, ko saurare na baiyi ba, da hannu na mai lafiya dashi na fara yagushin Dikko tare da cizo, nayi kuka na bashi hak’uri amma kamar an watsa ruwa a k’asa, dan gaba d’aya tunanin Dikko ya b’ace saboda duk abinda nake masa bayaji, cizo da yagin ma kamar ina yagin karfe kwata kwata bayaji.
Tun ina iya Allah ya isa, cizo yagi har k’arfina ya k’are na gaji na daina bai barni ba, wata irin azabtuwa nake sha wadda tunda nake a duniya ban tab’a jin irinta ba, haka kuma bazan iya musulta girman azabar ba, wai yau nice akayi ma fyad’e, wannan bala’in ne Zainab ke zuwa ai mata a bata kud’i ?…….
Wurin kamar kimanin 12:45pm dukan k’ofar d’akin Dikko akeyi babu sauk’i, kuma har zuwa wannan lokacin Dikko bai kyaleni ba, na suma na dawo bansan adadi ba, baida niyar bud’e k’ofar kwata kwata, magana mai dukan k’ofar ya farayi cewa wai har me kakeyi ne baza ka bud’e k’ofar ba.
Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, yai ta maimaitawa, tare da sauka daga saman gadon, ta jikin tagar d’akinshi ya lek’a a bayyane yace Dady……
Gajeran wando ya saka sannan ya kunna fitila, jawoni yayi daga saman gadon ya sauko ni k’asa sannan ya bud’e loka na bedsite ya d’auko gishiri, saida ya cikamin bakina da gishiri sannan ya zubamin ruwa a baki na hakan ya bawa gishirin damar narkewa yaci gaba da gangarawa cikin mak’oshina.
Dakel na bud’a idona na kalli Dikko, tsoki yayi tare da cewa munafikar Allah bari kallona dan uwarki….. A hankali na maida idona na rufe, k’asa yajani har muka fito daga d’akin kuma har yanzu ba’a daina dukan k’ofar d’akin ba,
Wani d’aki daban ya kaini ya ajiyeni, sannan ya kulle da makulli, saida ya goge inda jini ya b’ata daya jawoni sannan ya koma d’akin daya b’atamin rayuwa, zanin gadon ya cire ya tafi toilet dashi,
Bai wani dad’e ba yayo wanka ya fito, saka kayanshi sannan ya bud’e k’ofar, hannu Dady ya mik’a wa Dikko suka gaisa yace masa Babana baka tashi ba ? Na tashi…, tou lafiya baka shigo ciki ba ? Me yake damunka ne ? Ba komai Dady, sosai Dady ya sake kallon Dikko sannan yace mu shiga ciki,
Duk yanayin fuskar Dady ya canja zuwa na damuwa, jan Dikko yayi suka zauna har yanzu yana rik’e dashi a jikinshi yace Babana fad’amin abinda yake damunka, Dady nace babu, to miya hanaka shiga ka gaisheni, ba komai, tab’a jikin Dikko yayi cikin damuwa yace tou mi yake maka ciwo ? Kanka ne ? Ko bacci kake ji ?
Shiru Dikko yayi duk abun duniya ya dameshi, Dady kad’ai yaketa ma Dikko sannu, yana san Dikko fiye da yanda kowa yake san d’anshi, yana tattalin Dikko ko ina Dady baya san Dikko yana zuwa dan duk fitar da Dikko keyi Dady baisan yana fita waje ba, yana lallab’a Dikko sosai gani yakeyi kamar Dikko zai mutu ya barshi, kullum addu’ar shi Allah ya k’ara kare mishi Dikko ya shirya shi ya albarkaci rayuwarshi, saboda d’a d’aya tsotsai gareshi. Yana da “ya “ya sunkai sha biyar amma duk mata ne Dikko ne kadai na namiji a gidanshi.
Taso muje, Dady ya fad’a tare da dafa kafad’ar Dikko suka fita, cikin gida suka shiga, tunda suka shiga k’annen shi suka fara cewa Yaya munce ma Dady lafiyar ka qalau yace saiya ganka zai fita, kallonsu kawai yayi amma baima kowa magana ba, suma basu damu ba tunda halinsa ne shariya, sai kayi ta mishi magana ya kyaleka kamar bayajin ka.
Gishirin da Dikko ya zubamin a baki nake ta tofarwa amma rabi ya riga ya gama shigewa cikin cikina, kuka nakeyi mara sauti, duk ilahirin jikina ciwo yakemin, ga kaina kamar zai fashe saboda rashin bacci da kukan da nayi.
Haka na yini zubur babu Dikko ba labarinshi, ga ciwo da nakeji a k’asana kamar zai fita saboda azaba, kuma d’akin da nake babu toilet a ciki duk sallolin da akayi na yinin ranar nan inajinsu amma tun sallah asuba ban k’ara wata sallah ba.
Sai dare sosai Dikko ya bud’eni, shigowa yayi yana waya, wallahi dawowa ta kenan naje Abuja kwata kwata na manta da yarinyar nan saida nayi alwalla zanyi sallah magrib ta fad’omin a rai, ko Dady basai na dawo ba kuma ina ajiyeta zan koma , ……. A , a, 06:30am ne, ai bana so Dady yaji ban tafi ba kasan yanzu sai ya shiga damuwa, bada driver nake ba, tou kudai ku sakani addu’a , yana gama wayar yace ke da Allah tashi muje, munafika kinja min tafiyar dare, daka min tsawa yayi tare da cewa ki wuce mu tafi kina b’atamin lokaci dare yana karuwa,
K’iri k’iri na kasa tashi, kaina sai juyawa yake ga wani irin amai dake kai kawo tsakanin zuciyata da cikin cikina, jiki na yana kyarma nace masa bana iya tashi….. Na k’arasa maganar hawaye na zubomin daga cikin ido na,
Zan tafi idan kin tashi kin basu labarin abinda ya kawo gidan nan ni kinga tafiyata, ya juya zai tafi nace dan Allah zan tashi, juyowa yayi ya kalleni sannan yace tou taso ya fad’a cikin sigar lallashi,
Dakel na iya tashi amma a duk’e nake na kasa mik’ewa tsaye, yanayin fuskar shi ya nuna tausayi, akwai zafi ? Ya tambayeni, banza nayi dashi bance masa komai ba, murmushi yayi tare da cewa ki sameni ta baya, kuma kiyi hankali karda a ganki,
Dakel nake tafiya har nafito, a lokacin harya d’auko motar daga inda ya ajiyeta, ina k’ok’arin shiga yace in tsaya kar in b’ata motar, ciki ya koma ya sake gyaggyara inda na b’ata sannan ya d’auko wani k’aton zani ya taho dashi, inda zan zauna ya shimfid’a sannan yace shiga,
Shiga nayi na zauna ya rufe k’ofar tare da zagayawa shima ya shiga, waya ya kira yace gani nan zan fito bud’e min get in, yana fad’a ya ajiye wayar ba tare daya kashe ba,
Da gudu yaja motar kamar zamu tashi sama muka tun kari hanyar fita, a daidai get ya tsaya sukayi ta masa addu’a da fatan alkairi ya amsa da amin sannan muka fice, hanyar filin gidanmu ya nufa, babu mota ko d’aya a hanya bare machine haka ya tabbatar min da dare yayi sosai,
Lokaci lokaci nakan goge hawaye, tare da Allah ya isa zuciyata, saida ya kusa zuwa gidanmu ya tsaya yace ke sauka haka nan, kama murfin motar nayi sannan na kalli Dikko nace Allah ya isa ban yafe maka ba mugu azzalimi d’an isa mai bakin mata, murmushi Dikko yayi sannan yace ngode,
Kuma ko zaka mutu bazan tab’a yafe maka ba, Dikko yace tou, in Allah ya yadda saika had’u da tashin hankali a hanya, bazan had’u dashi ba in Allah ya yadda, tsoki nayi tare da bud’e motar na fita, tillomin zanin dana zauna akai yayi a daidai lokacin da nace kuma wallahi sainayi k’arar ka, babu damuwa ina jiranki, azzalimi , murmushi yayi tare da cewa naji ba komai duk abinda zaki ce ki fad’a nidai nasan na more miki har abadan duniya, gwallo yayi min tare da jan motarshi ya barbad’eni da k’ura…..
Wani irin bak’in ciki ya kamani nayi wani irin ihu daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba saidai na farka na ganni kwance a gadon asibiti, an d’aure hannuna wanda yaji min ciwo, anmin dinkuna a k’ark’ashi na,
Zainab itace ta zauna tare dani a asibiti dan Inna tunda taji abinda ya faru tayi tafiyarta tace ta gama auren Baba har abadan duniya,
Sati na d’aya a asibiti aka sallame mu muka dawo gida, Babana kuma kunya tace ta koreshi babu wanda yasan inda ya tafi, tunda na dawo na samu labarin Inna ta tafi ban wani ji sha’awar binta ba, na hak’ura na zauna cikin “yan uwana.
Naje nayi k’arar Dikko wurin “yan sanda abinda ma na fahimta sumo so suke suyi irin abinda Dikko yayi dani, dan haka na hak’ura na dawo gida.
Babu ranar da zata zo ta koma ga Allah ban fad’owa Dikko a rai ba, ya shiga damuwa da tashin hankalin abinda yayi min, yaji bak’in ciki tare da tambayar kansa mi yasa yayi zina ? Mi yasa nayi ? Mi yasa,…..????
Wani lokaci haka zai zauna yayi ta kuka yana mai jin bak’in ciki da nadamar aikata abunda yayi, ya tambayi kanshi so babu adadi wai miye amfanin abinda yayi ? Yin hakan meya haifar ? Dadin me yaji ? Wane rayuwa yarinyar mutane zata shiga? Mi yasa saishi ne Bello ya zab’a ya farkewa Sultana mutunci ? Tabbas ya yadda ya zama babban mahauci iliminshi baida wani amfani baida banbanci da jahili,
Kullum addu’a Dikko yakeyi Allah ya yafe mishi akan abinda yayi min,zuwa wannan lokaci ya fara tunanin ko ya sanar da Dady abinda ya faru kila zai bashi shawara tunda babu abinda suke b’oyewa juna,
Ko isashshen bacci Dikko baya samu, daya kwanta shashkar kukana yake tashin shi daga bacci, a fili yayi magana cewa baiwar Allah kiyi hak’uri ni wannan na d’auke shi matsayin k’addara tunda nake a rayuwata Allah ma ya kulle min idona da zuciyata akan mata,
Wallahi ko labarin mata bana so anayi a gabana, ban tab’a zina ba kuma wallahi ban tab’a jin sha’awarta a zuciyata ba, Allah yayi min kyankyami da tsoron sab’a masa , amma ya akayi banji kyamar yarinyar nan ba, na sab’awa Allah mi yasa na kasa control in zuciyata mi yasa wai……….? Dan Allah ki fita daga rayuwata ki barni, kiyi rayuwarki inyi tawa, hawaye ne suka sake tsirarowa daga cikon idonshi, cikin kuka yace ya Allah na rok’eka dan arzik’in annabi Muhammad S. A. W ka mantar min da lamarin yarinyar nan daga zuciyata, ka hanata zuwa man cikin bacci ta daina min wobuwa idan ina cikin mutane wallahi ina iya haukacewa,
A b’angare na kuwa, zuwa yanzu na shafe babin Dikko a rayuwata, akwai wani d’an uwanmu da yake so na, kuma yayi alk’awarin aurena dama tunda ya fara zuwa Baba yace mishi ya bashi ni amma babu maganar zance kawai dai idan na isa aure zai aura mishi ni.
Shima yaji labarin abinda ya faru dani, kuma yazo wurina, ya tambaye ni da gaske ne ko wasa ? Da farko naso na b’oye masa, amma daga baya kawai na fad’a masa gaskiya, yacemin tou shi gaskiya bazai iya aurena ba inyi hak’uri, ban wani damu ba nace Allah yasa haka shi yafi min alkairi a rayuwata.
A hankali magana ta fara zaga gari, anyi min fyad’e kuma wanda yayi min fyad’e d’in ba’asan ko waye ba, amma asibiti sunce ina da cutar H I V, duk abinda na tab’a a gidanmu babu mai k’ara amfani dashi, duk wacce na zauna kusa dashi sai ya tashi, idan na fito mutane da sun ganni sai su dare….
Ko a familyn mu kowa baya shiga sabgata, kyara da tsana ake nunamin kamar mayya, ga mahaifiyata tayi tafiyarta garinsu, Baba bansan inda ya tafi ba, na rasa abinda yake min dad’i a duniya, banda mai bani abincin da zanci duk wanda naje wurinshi saiya koreni, azaba ta isheni na fara sana’a babu mai siye,
Koda naje na fad’awa Amisty abinda rayuwata take ciki da fyad’en da aka min amma ban fad’a mata Dikko bane ba, shawara d’aya ta bani, shawarar kuwa itace, sana’a d’aya zanyi inyi arzik’i ba H I V gareni ba ko kabari ce ni sai an shigeni,
Wace sana’ace ? Murmushi Amisty tayi tare da cewa zan kaiyi wurin uwar d’akina in yankar miki form zata baki lectures, lokaci guda zaki goge idonki ya bud’e zaki ga yanda maza zasu rik’a layi akanki,…..
Idan sunyi layin me zan basu ? Abinda kika bawa wanda yai miki fyad’e,……………