NOVELSUncategorized

KWARATA 61

???? —— 61
      Ina saka kayana ina mita cewa naga yanda za’ayi wani ƙaton banza ya hanamin nayi rayuwana yadda na tsara abuna , zanje daura dole saina san dalilin da yasa aka yankewa Aunty Suwaiba ƙafa , a madubi na kalli kaina kamar ina ma wani kashedi na nuna da ɗan yatsa duk wanda ya shigo da takura a rayuwata , abuna da nake fesawa na
bacci na ɗauko dan yana cikin jakar makaranta na tuni nake neman sa’a akan Dady dan ina da ƙudiri akan shi sosai a zuciyata , ta cikin madubi na fesashi fesss dariya nayi tare da cewa haka zan feshe ka kamar na watsawa sauro magani maimakon kai ka mutu sai kawai ka tafi duniya bacci…..

     Ina gama saka kayana na yafa gyalena na ɗauka jakana dan a lokacin har Yazeed yazo wayata na ɗauka da kwalbar abuna na fice daga cikin ɗakina dan ko Kaka ban faɗawa Daura zanje ba kuma ban leƙa mata ban kwana ba !

      A harabar gidan na samu hayaniya ya gauraye tsakanin Ashiru da Yazeed kowa sai ɗaga murya yakeyi kamar zasu buga , wurin Yazeed na nufa nace masa ya akayi ne ? Cikin ɓacin rai yace wannan jakin ne zai ɓatamin rai , wai me yace ne ? Nayi tambayar ina kallon Ashiru amma Yazeed na tambaya ,

     Yazeed yace cemin yayi ni ɗan iska ne ina leƙe² nazo zan leƙaki , ɗauke idona nayi daga kan Ashiru nace ma Yazeed miye leƙe² ? Duk shiru sukayi , murmushi nayi a raina na kalli Ashiru nace Dikko yace idan ka bari na fita zaka bini ko ? Yace Eh , nace idan Yazeed zai ɗaukeni fa ? Shima sai naje , kallon Ashiru nayi sosai ƙosashshen ƙato ne mai sigar “yan restyling ya ƙoshi sosai Dikko yayi mishi horon ƙarfi ko ina ya cika kamar anbi jikinshi an tsatstsaga mishi dutsina saboda cikarshi , 

     Ajiyar zuciya na sauke na kalli Yazeed nace wai miye leƙe² ? Kowa shiru yayi , to tunda baza kuyi magana ba kai Yazeed muje kafin rana yayi , juyawa Yazeed yayi da niyan tafiya Ashiru ya shaƙoshi ta baya , murmushi nayi a bayyane tare da cewa kai yaro sakar mishi wuyan riga kafin inci uwarka , na ƙarasa maganar ina nuna mishi da kaina ,

      Ni zaki ci ma uwa ? Ya tambayeni , nace ba kai kaɗai ba hada Dikko naci uwarka naci uwar wanda ya turoka ka zauna dani , gyara tsayuwata nayi sosai tare da nuna Ashiru da ɗan yatsa nace ai saboda so duk za’a sakawa rayuwata ido ko ? Shiru Ashiru yayi yana kallona a nutse baiyi magana ba , naci gaba da cewa ni dama inda na gode Allah ban taɓa cewa ina san Dikko ba , tou wai waye ma zai so mahaukaci ? 

Yanzu mutum anjima aljani , a haukan nashi yake tunanin zan iya aurenshi ? Bashi da aiki sai zafin kai da doke² idan har baka fita harkata ba saina tona maka asiri , ke ni zaki tona ma asiri…..? Tabbas nasan ahalinka kaf kuma nasan abinda ya raboka daga gidanku ka dawo rayuwa ƙarƙashin mahaukaci , { kuma ƙarya nakeyi bansan komai game da rayuwarshi ba , }

Ashiru yace ke yarinya bamu da sata bamu da maita kuma bamu gaji iskanci ba duk duniya wannan abu 3n dana faɗa ɗaya daga ciki mutum zai samu kanshi yaji takaici kuma shi ubana baya taushewa….

     Nima ban gaji iskanci ba hayenshi nayi kamar yadda kaima baka gaji kwaraka ba kake rayuwa a ƙarƙashin wani , kuma idan ubana ya taushe kaima ai naka ya taushe saboda kunne ya girmi kaka yaro idan baka san asalinka ba yanki fili ka shiga siyasa , Sultana bata siyasa amma rayuwar kowa da labarin gidan kowa yana a tafin hannuna saboda ɓacin rana , kasan duk wanda baisan kanshi ba daya shiga siyasa duniya zata faɗa mishi koshi ɗin waye , nima siyasa ce duk wanda ya shigoni zan warware mishi dan nidai ubana bai taɓa murƙushe surikarshi da ɗiyar maƙocinshi ba , { kuma haka nan kawai na faɗa dan in ɓata mishi rai bansan komai game da rayuwarshi ba , } cikin ɗaga murya Ashiru yace ke…… Ki gyara kalamanki akaina tun kafin in ƙera miki rayuwa , a sanyaye nace malam Ashiru ai yanzu muka fara , zama fa tare dani zakayi anshi wannan kafin in dawo , kafin ya ankara na feshe banza ya ƙame a wurin , 

     Da taimakon masu aiki da kuma Yazeed aka sakashi a mota bayan na faɗa musu ciwon farfaɗiya yake , haka ciwon yake taso mishi lokaci² , ina ƙoƙarin rufe motar naji wayar Ashiru tana kuka a aljihunshi , Yazeed nasa ya cirota nace waye yake kira ? Yace mai gida , saida nayi dogon nazari sannan nacewa Yazeed ya maida mushi wayarshi a jikinshi muje ,

     Maida wayar yayi jikin Ashiru mu kuma muka shige mota mukai tafiyarmu , tunda muka kama hanya bana tunanin komai sai tunanin irin halin Dikko , ga zuciya kamar kumburƙuma , mema Dikko yayi min na rayuwa wanda ya kamata ace na so shi ? Bashi da aiki sai doke² so biyu yana dukana na farko saida na suma , na biyu dakel aka riƙeshi umm gaskiya bana san namiji da zuciya gashi bashi bada uziri ko kaɗan na rayuwa jiya daga ya kirani na fara bacci kawai ya hauni da masifa , na sake kiranshi ya kashe wayarshi gaba ɗaya..

      Dai² saitin zuciyata na dafa a bayyane nace kiyi haƙuri dan Allah dan annabi kiyi haƙuri ki goge wannan mutumin daga cikinki , a sirrance na sake cewa me ma Dikko yayi miki na rayuwa ? Mota ce kawai ya baki sai miliyan ɗayan kuma dan ƙaranta daci baya mahaifiyar shi ta ansa , gashi bata so na , kallon Yazeed nayi da wutsiyar idona , zuciyata tace kalli Yazeed shima dai lafiyayyen matashi ne jini yana motsawa ko ina ajikinshi , yana da ƙirar burge mace kuma shima dai ɗan kwalisa ne , me ake nema na rayuwa ? Idan dai namiji yana da “yan canjinshi kuma ya iya soyayya ai shikenan , kawai ki watsar da Dikko duk da dai badai wata makusa shima dai kyakkyawa ne gashi ɗan gayu uwa uba ya iya magana mai daɗi amma yanayin Dikko yafi na Yazeed nuna gogewa a wurin iya ɗagawa mace hankali ƙwayar idonshi ya nuna haka giraren shi kawai ka kalla kasan zaiyi jarabar masifa duk macen da Dikko ya damƙa zataji a jikinta bare kuma ni da yakeji ma haushi nayi imani da Allah irinsu Dikko sune masu horar da mace da azaba a wurin kwanciya matsawar tayi musu laifi , mace taita ƙarewa a rasa abinda ke damunta , ai dama yama taɓa faɗa min da bakinshi cewa idan harya aureni sai nasan shi ba abokin wasana bane ba bare ga Dikko da ƙeta , umm manta da Dikko kawai ki auri Yazeed na tabbata zakiyi rayuwa mai inganci dan shima jajirtaccen namiji ne tunda har baiji tsoron Dikko ba ya shiga soyayya dake wannan namiji yakai jarumi…

        Ajiyar zuciya na sauke na sake kallon Yazeed da wutsiyar idona , kallon siffarshi nayi sosai domin Allah Dikko yafi shi zarrar cika cikakken namiji nesa ba kusa ba , duk baƙar hassadar ka babu yadda ka isa ka kushe Dikko wallahi , domin cikakken namijine jajirtacce yana da zarrar da duk macen data ganshi mai lafiya da sanin duk wasu qualitative na namiji tasan Dikko yakai kuma wallahi babu yadda za’ayi yaba kanshi kunya wurin mace a gado , mutum ɗan tara ne bai cika goma ba , ni gaskiya na haƙura da Dikko dan bansan ranar da zai samu lafiya , idona ya cika da hawaye gaskiya ina san Dikko sosai wallahi idan har nace bana sansa nayi ƙarya , domin duk yadda zan faɗa muku Dikko gani nake baza ku gane ba ,

      Da wata irin ƙara ya farfaɗo wayyo Allahna mai gida karka kasheni kayi haƙuri na bari , wayyo Allah ku taimakamin zai kashe ni wayyo…………. Wani irin ihu ya sakeyi wanda ya jawo duk hankalin wanda ke cikin asibitin yana cewa gashi nan ku riƙeshi wayyo kakkafawa Al ‘ Ameen ya sakeyi yana fizge² idonshi a rufe saboda tsabar tsoro , dole tasa akayi mishi allurar bacci dan ya cikawa mutane asibiti da ihu kuma ga marasa lafiya sosai masu buƙatar natsuwa.

       Me wannan yaron yake nufi zanyi ta kiranshi baya ɗaukarmin waya ne ? Ƙaton banza kila ma yaje ya miƙa mata fuskar tayi mishi feshi , shi uzirinshi idan ya kiraka so ɗaya baka ɗauki waya ba zai maka uziri har zuwa lokacin dakai zaka nemeshi da kanka , akan Sultana kaɗai yake maimaita kira dan idan ya kirata bata ɗauka ba duk bayan mintuna saiya sake kira yaji ko zata ɗauka , hardai ya samu sa’ar barin nigeria Ashiru bai kira ba bare yasan a ina aka kwana….!

           Duk wani shiri daya kamata tayi , tayi ta tattara duk wani abu da tasan idan taje tayi zata tafi da imanin Dikko , duk wani tsafe² saida ta haɗo kanshi , turarenta da man shafawarta da powder har kwallin da zata shafa a idonta duk anbisu an barbaɗesu da asiri , kaya masu azabar² ɗauka hankali ta ɗauka , wai ita zataje jinyar ƙanin mahaifiyarta wato Al ‘ Ameen , shiri tayo mai kyau da makaman yaƙinta tayo garin katsina bata san sunyi hannun riga da Dikko ba…..

         Ni yanzu ina zansa kaina komai ya fara warwaremin kayi wani abu haka nan mana ai bana tunanin akwai abinda ya gagareka , ya ina neman mafita kuma ɗan gwamna zai shigo rayuwarta , yaron nan ɗan iska ne ya raina mutane duk garin nan babu wanda baisan halinshi ba baida mutunci kuma ya raina mutane dan baya ganin girman kowa a garin nan , dan gaskiya idan aka aike ka neman tantirin ɗan iska daka ga Dikko ka tsaya ka samu saboda wannan dalilin ne yasa nasa kayimin aiki akan ya lalatawa ɗiyar Binna rayuwa dan nasan idan har Binna yace zaiyi wani abu Dikko kawai zai iya bi ta kanshi da mota ya wuce , dan na tabbata daba Dikko ne ya farke yarinyar nan ba da har yanzu zaune bai ƙare ba.

        Bello ne zaune a gaban bokanshi duk ya koro wannan sharfin tare da fashe mishi da kuka cewa tuni kasa ni nabar sallah azahar da asuba da isha’e amma ka kasa wani abu ? Wata irin dariya bokan yayi cewa akwai sauran mafita ɗaya , jikinshi na kyarma yace wace mafita ce ? Saura la’asar da magrib zaka dakatar , Bello yace na ajiye 3 biyun kake tunanin zai gagareni ne ? Na daina sallah dama ai ba kullum nakeyi ba ni koma miye zanyi amma duk yadda za’ayi nidai a raba yarinyar nan da Dikko ko kuma in aureta kawai kaga sai in ida cika burina tana gidana , hahahahaha bokanshi yayi dariya tare da cewa idan dai kana san ganin burinka ya cika na auren yarinyar nan yanzu sai ka auri mahaifiyar , zaro idanuwa Bello yayi tare da cewa kamar ya in auri mahaifiyata kuma boka ? 

       Wata irin dariya yayi mai ansa kuwwa gaba ɗaya dajin ya karaɗe da ƙarar dariyarshi bayan ya samu natsuwa yace yarinyar tana da ibada tana sallah akan lokaci kuma tana da karatun littafin Allah babu dare ba rana , kuma kasan munyi² mu rabata da sallah abun ya gagara idan har zaka iya auren uwarka duk daren duniya zaka kwanta da ita ne ka riƙa samun natsuwa daga gareta shikenan Sultana zata aure ka kuma duk duniya babu wanda ya isa ya hana auren , saboda sai mahaifiyar taka tayi bacci zaka kwanta da ita , tou yadda ka sadu da ita tana bacci bataji bata gani ba haka za’ayi aurenka da Sultana mutane bazasu ankara ba bare ayi ta surutu….

      Shiru Bello yayi bayan wani lokaci yace wannan kauce hanya tayi yawa da wane idon zan tsaya a gaban Allah uwata fa…….? An zan samu rahama ranar gobe ƙiyama ?  Boka yace wanda yayi kisa me ya rage mishi daga rahamar Allah a duniya da lahira ? Bello ga kisan kai ga zinace ² ga caca kawai kayi sai ka tuba idan ka kusa mutuwa tunda kana san rahamar , Bello yace to a rabata da Dikko basai na aureta ba , Boka yace ko ka aureta ko a rabata da Dikko saika auri uwarka , idan haka baiyi ba tou kisanta shine mafita kawai…. Bello yace shikenan zanyi shawara….

       Har muka isa Daura ni banyi magana da Yazeed ba sai shi daya kunna wata waƙa ta “yan siyasa yakebi , wannan ta shiga ta fita , nidai hankalina da zuciyata ya tafi yayin da nake jinjina auren Yazeed sai kuma tunanin yadda zanyi ma in cire Dikko daga raina tun farko ma kenan. Haka nan naji gabana ya yanke ya faɗi ina tunano lokacin da Dikko ya sumbaceni a ƙofar gidanmu ranar dazai rabu dani , tashi tsikar jikina tayi yayin dana tuno yadda na kasance a jikinshi da maganarshi da yake cewa zamuyi aure bada daɗewa ba ,

       Haukanshi na tuno yadda yake fizge² yana zabura kamar anba doki ƙwaya idan an riƙeshi , kai gaskiya ina san Dikko amma idan har na aureshi ranar da nayi mishi lafiya waye zai riƙeshi idan zai dakeni….? Murmushin Dikko na tuno a ranar da mukayi faɗa dashi hanyar tafiya bakori lokacin da muka tafi da Mardiyya maganar da yayi na tuno ,

       Haba yarinya Dikko ne fa ! Kin manta nine na koya miki ? Nine nayi kuma nine na fara baki idan daɗi kikaji ko zafi duk nine dai , ruwa idan da rabon ka a ciki ko ka zubashi a kwando bai maka yoyo , ni ba abin farautarki bane zaki duk jarumtatai yana ganin ƙimar mafarauci a wancan karon suma kikayi wannan karon ma haka zata sake faruwa dake ba suma ba har jinya sai kinyi idan kika dawo ɗaukar fansa zaki gane Dikko ba sa’arki wasanki bane domin saina baki azabar da sai kinyi fitsarin wahala , bayan kin dawo daga duniyar suma tsorona zai shigeki a duk lokacin da kika kasance dani a shimfiɗa ɗaya ,

     Wallahi jarumi ɗaya akeyi a ƙarni nine jarumin wannan lokaci , Dikko jarumin maza ne kuma keda kanki zaki faɗa kije ki dawo ina nan ina jiranki , murmushi nayi a bayyane nace wannan gaskiya ne mutumina Allah ya baka lafiya…..

     Fita nayi daga cikin motar ina fita da Yayar Aunty Suwaiba na fara haɗuwa muka gaisa da ita take cemin yanzu nan aka tafi da Suwaiba Zaria wai sunje zasuyo wasu aune² , cikin rashin jin daɗi nace yaushe zasu dawo ne ? Tace insha Allah barasu wuce kwana biyu ba , nace tou dan Allah akwai wata waya a hannunta wacce aka bata a asbiti shin ko zan samu wayar ne da Allah ko kuma ta tafi da ita…..?

       Shiru tayi irin na masu nazari tace me zakiyi da wayar ne , murmushi nayi ba tare dana bata ansa ba na buɗe jakata na ɗauko kuɗi na bata tare da cewa bani wayar ke kuma ki riƙe wannan , cike da farin ciki ta anshi kuɗi tare da cewa ina zuwa , mota na koma ita kuma ta shiga gidan Aunty , bata wani daɗe ba ta dawo da wayar ta bani , godiya nayi mata sosai tare da cewa zan sake dawowa godiya tayimin sosai har muka tafi tana godiya tare da ɗaga mana hannu har saida muka ɓace…

     Har yanzu banyi magana da Yazeed ba amma na fahimci wasu ɗabi’u nashi , ina wani tunanin ne wayar da Dady ya bani ta fara kuka da sauri na fiddo wayar daga jakata na ɗauka tare da cewa Dady barka da wannan lokacin , na nunawa Yazeed yayi parking , yana yin parking na fice daga mota…

     Barka dai kin wani manta dani ko ? Haka kin kyauta kenan ? Haba taya zan manta dakai bayan kullum kana raina kamar kuɗin haya kayi haƙuri ban manta dakai ba kullum tunanin ka nake yanzu haka ma tunaninka nake kawai sai ka kirani , dariya yayi cewa tou yanzu kina ina ? Kallon titi nayi tare da cewa ina gida , ina ne gidan naku wai ? Zaka zo ne ? Saidai ke kizo , kana ina ne ? Ina nan Ambasada kinsan wurin ne ? Nace Eh hanyar Shinkafi ko ? Yace Eh kizo to , gani nan zuwa amma zanzo sanye da niƙaf da hijabi wurin ina kake ne ? Kinsan Fesra hotel ? Eh na san wurin tou ina a wajen da Allah karki ɓatamin lokaci , baka da damuwa ina faɗin haka na katse kiran !

         Kwanan wata na kalla a wayata nai murmushi cewa hawan ruwan ciki na fa sai mutum ya shirya baka da zarrar da zan miƙa maka linzamina rayuwata , wahalar banza zansha bayan ka haɗamin da “yan dabaru kayan maza , tsoki nayi tare da cewa anya ma muradin kake nema ? Ko kuwa dai……?

      Kiran dana ansa a baya da baƙuwar number da akace za’a kashe ni na fara kira a kaina nake cewa zan gane yanayin iskan inda ake magana dani dan ranar dasu Al ‘ Ameen suka bini da gudu har muka haɗu da Bello naga motar Dady a ƙofar get in makarantarmu , kila Dady ya ganni Bello yana bina daga baya zasu haɗu sai yace meya haɗaka da wannan yarinyar da kake binta ? Kawai zaice ai ɗiyar BINNA ce… , ko kuma sunyi magana na shi yasa na ansa wayoyi daga mutane daban² kowa yana so yasan inda nake , tou idan wani abu bai faru ba taya akayi Bello ya kasance a wurin bayan Dady kaɗai yasan zanzo makaranta tunda shine kaɗai na faɗawa ina katsina ? Kuma wurin baiyi hanya ɗaya da majalissar su ba kwata² gidan Bello ba’a hanyar yake ba ? Murmushi nayi tare da cewa haba tsofaffi na gano makircinku amma idan ma nemana kukeyi yanzu zan gane ta hanya mafi sauƙi , a dai² lokacin da aka ɗauki wayar , ba mai maganar nake saurare ba yanayin iskan wurin nake so na fahimci ko a inda Dady yayi waya dani ne yake magana…..? Shi kuma cewa yakeyi ,

      Zaki mutu mutuwa irin ta karnuwa wallahi saina kashe , dariya nayi tare da cewa baka iyawa , yace zaki mutu fa , nace ƙarya ne , sai na kasheki wallahi , wallahi kana iya kasheni ? Na tambaye shi , yace Eyyy , nace tou idan ka isa kai jarumin ne a harkar kisa ka kashe ni a Ambasada zanzo wurin Fesra hotel yanzu sanye da niƙa da hijabi bana kasuwa fa , sai kin mutu kuma kafin mu kasheshi sai kowa ya zagaya ki , gani nan ka kasheni in gani , ina faɗin haka na katse kiran na fara kiran wayar Hafsa…

     Ba ɓata lokaci ta ɗauka muka gaisa da ita , nace Hafsa kina ina ne yanzu ? Cikin muryarta ta sakarkari tace ina Qerau gidan Amisty , nace kina da hijabi da niƙaf ? Me za’ayi dasu ne ? Nace Dikko ne naji yana maganarki yanzu yace baiji daɗin abinda yayi miki ba da zai ganki da zai baki haƙuri amma sai ya ganki cikin niƙaf da hijabi dan ranar nan ma abinda yasa ya dakeki wai saboda kinzo ko gyale babu shi yasa kika ɓata mishi rai dan kishinki yakeyi sosai ,

      Hafsa tace muna da niƙaf mana wanda muke amfani dashi idan zamu shiga wurin da bama so asan mune , nace to ki saka niƙaf da ƙatuwar hijabi ki shiga napep karki tafi da wani ya rakaki kinsan su “yan siyasa basa san surutu shi yasa sukeyin komai nasu cikin sirri , kicewa mai napep ya kaiki Fesra hotel dake hanyar shinkafi idan kinzo wurin ki kira wayar Dikko kinji ko ? Tace to , nace yawwa kiyi sauri kinsan baya san jira , tace yanzu fa , tana faɗin haka na kashe wayata na sake kiran Dady ,

      Bayan ya ɗauka nace ya kamata kaɗan sirrinta motarka a cikin hotel in dan wani ne zai ajiyeni a mota ban sani ba ko ya sanka , Dady yace ai dama ba’a mota nake ba ina zaune a ƙarƙashin wata bishiya ne ba da mota ta nazo ba , kashe kiran nayi tare da cewa lallai ka shiryamin zagon ƙasa da yawa ,

      Wayar mai cewa saiya kasheni na sake kira bayan ya ɗauka nace wallahi ku dukanku baza ku iyamin fyaɗe ba , na rantse da Allah duk yawanmu sai munyi wasan danbe dake wallahi ׳ sannan mu kashe ki , idan kuma kinyi sa’a kin mutu kafin mu gama kin huta , dariya nayi tare da cewa aiko rijiya ta ƙafe da zaran anyi yasa wasu ruwan ne zasu sake ɓulɓulowa ƙananan kwartaye daku nice uwarku gani nan zuwa…

     Kashe wayar nayi na koma cikin mota inda Yazeed keta jirana , ina shiga yaja muka nufo cikin babban birnin garin katsina ta Dikko ɗakin kara , kunya gareku badai tsoro ba ,

     A motar Yazeed na saka cajin wayar dana anso a wurin Yayar Aunty dan wayar a kashe take ba caji , bayan na saka naci gaba da sauraren waƙar da Yazeed kebi ta mai girma gwamna , 

      A zahiri nake sauraren waƙar amma a baɗinance ina tunanin yadda zan ƙare da masifar da nake san haɗawa dariya nayi a bayyane a zuciyata nace ai basu iyawa dan basu da shedar da zasuyi shara’a dani harkar karuwanci dai kowa yasan anayi ko sunkai ni ƙara kawai zancewa alƙali ni karuwa ce kuma kawaliya ce , inayin karuwanci ne saishi Dady ya kirani yace inzo , sai ince ya mai girma mai shari’a da ya kirani to dama wayata ta kwana biyu kashe babu caji , shine ina buɗewa kiranshi Dady ya shigo bayan na gama waya dashi akan yana da muradi munyi ciniki nace na sallama , bayan na gama waya dashi sai na fara bin kiran miss calls in da aka ajiyemin a wayata bayan ya ɗauka shima dai muradin ne sai naji shi wannan zai bani kuɗi da yawa to kaga tunda ina kawalci kawai saina tura Hafsa taje wurin Dady nace mu raba ƙafa taje can ni inje wurin masu yawan dan danbe zasuyi tunda ni nafita kuzari da kuma daɗewa ana ɓarin wuta a gado ,

     Sai Dady yace ya mai girma mai shari’a ai Hafsa ɗiyata ce , sai Alƙali yace ke Sultana me yasa kika haɗa uba da ɗiya sai ince ai ranka ya daɗe ni badashi na haɗa ta ba a tambayeta Dikko nace mata , wata zufa naji ta ketomin duk da a c dake cikin motar , yayin dana hasko har an kirawo Dikko ya fara wannan ihun nashi ana riƙeshi yana wannan zaburar yana saiya kashe kowa… Wayyo Allah ba Dikko ba kai ba ,

      Ajiyar zuciya na sauke tare da sake tunanin Alƙali zaice kince Dikko to ya akayi kikace bashi ba kuma ? Shikenan sai inyi shiru inta mazurai banda mafita dan idan an tambayi Hafsa zatace ai cewa tayi Dikko yace in sameshi a Fesra hotel , na shiga 3 , ina cikin wannan jimamin sai Alƙali yace to ya akayi kika samu miss call na wasu kwanaki , sai in nuna mishi miss call in wanda aka taramin ranar da akace za’a kasheni , bayan alƙali ya gani sai kuma yaga nabi kiran babu daɗewa , da sauri na goge wancan tsohon kiran , sai Alƙali yace ya akayi duk kwanakin baki bi kiran ba sai yau ? Kuma kinga miss call , sai ince yamai girma mai shari’a ai nazo zan ɗauki wayar ta mutu saboda rashin caji , idan alƙali ya irga kwanaki sai yace har kwana kaza bakiyi caji wa wayarki ba ? Shafa kaina nayi tare da cewa ai cewa sukayi zasu kashe ni…..? Meye shedar ki kin shigo da wani zance a wani , kai aiko ubana zanci.
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
      A , a bazanci ba tsautsayi sai yasa suce ai ranka ya daɗe ta kirani bayan na kirata , dama ina da record in kiran sai in faɗawa alƙali sai yace in kunno aji , zufa nagoge lokacin dana kunno amma ba m card a wayar an cireshi wani irin ihu nayi tare da cewa Dikko me yasa ka ciremin abuna ? Wallahi Dikko ya cireshi da sauri na zura ƙafata na taka burki tare da kaɗa kan sitiyarin motar kamar sakarai haka Yazeed ya sakar min motar dan mun shigo cikin gari kallo Yazeed yabini dashi tuni na juya kan sitiyari na tun kari goruba road Yazeed ya zuƙe gefe ɗaya dan rabi na a saman jikinshi nake shi tuni ya ɗauke kamar an ɗora kura saman kare , banma san yanayi ba , ina tuƙin nake tunani anya ma Dikko yana garin nan gaskiya baya nan dan daya nan bazai turo min Ashiru ba , 

     Ai banma tsaya ba dana isa goruba yadda naga duk an watse gidan ana rusashi aiki ake mishi kuma baya zama , cikin hayaniya nace Yazeed ina Dikko yake zama banda nan ? Banza yayi dani dan baya iya magana , kai tsaye gidanmu na nufa a wurin Ashiru zan samu wannan ansar ,…..

          Ilimi ake nema baiwa kuma samunta dace ne

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button