NOVELSUncategorized

KWARATA 64

???? —— 64

          Lokacin dana isa sabon layi ban samu ganin matar da tacemin na dawo anjima ba , dana tambayi wacce ke bani ansar inda matar taje cemin tayi wai sun tafi wurin taron siyasa , kuɗi na fiddo a jakata saida na shaƙa mata su dai² hancinta na maidasu
a jakata nace zan tafi ni suna na Sultana , kuma ni ɗiyar Binna ce ai kin san Binna ba…..? Zaro ido tayi tare da cewa Binna….? Murmushi nayi da gefen bakina tare da shanye idona na dama nace Eh nice na gajeshi masu iya magana nacewa kyan ɗa ya gaji ubanshi na gaji Binna ban gaji uwata ba na ƙarasa maganar ina yatsina fuska , jinjina kai tayi tare da sake kallona ƙasa da sama tace Binna ? Nace tabbas.

         Dariya matar tayi ta zira hannunta cikin breziya ta fiddo sigari ta bata wuta , saida taja ta sosai ta miƙomin , ansa nayi ina murmushi na riƙeta a hannuna , ita kuma taci gaba da cewa lallai ai Binna namu ne , bara a kawo miki kofinshi kiyi mishi nayau tana faɗin haka tayi gaba , babu jimawa ta dawo riƙe da ƙofi a hannunta ta miƙomin cewa wannan da kike gani duk daren duniya Binna goma yake sha , kuma yabar wasiyya cewa duk daren duniya saboda san da yake ma giya koya mutu a zubar da kofin giya goma a saman ƙasa , ansar kofin nayi na riƙe a hannuna na ƙura mishi ido , hawaye naji ya cikamin ido bansan lokacin da suka fara gangarowa ba , ɗaga kofin nayi na kai bakina amma kafin in samu damar shanshi an ɓareshi , da sauri na ɗago kaina dan inga waye amma babu kowa kuma babu matar data bani kofin ,

       Da sauri na kalli hannuna saboda sigarin hannuna ta cinye wutar har ta taɓomin hannu , yadawa nayi na duba mutanen dake zaune suna wasan lido nace ina matar dake tsaye a gabana da Allah , wasu ne suka ɗauketa a mota , wannan shine ansar da suka bani kawai , da sauri na rufe idona na girgiza kaina gefe da gefe na kalla ba kowa dan haka na juya na tare napep saboda wurin bisa titi ne na nufi gidan cikin ɗimuwa wato har yanzu akwai sauran masu bibiyar min rayuwata ina da sauran lale.

        Kai……………Wayyo Allahna saina kasheta , shine kalmar da Dikko ke faɗa yayin da yaga hotunan “Yar matanshi ta riƙe sigari , watsi ya farayi da kaya yau sai ya koma nigeria , da sauri Dady ya dafe dai² zuciyar shi ya umarci a riƙe Dikko amma duk wanda yazo sai Dikko ya duƙe ya naɗa mishi hannu so ɗaya saiya koma da baya ya kwanta , wani irin gurnani yayi tare dayi ma Dady wani irin kallo kamar zaki ya ritsa mutum a dokar daji , cike da fargaba Dady yace ku kamamin shi , wani irin ihu Dikko yayi tare da halbin wanda yazo gaba shima ya kwanta , idon Dady cike da hawaye yace ku kwantar dashi mana gaba ɗayanku kuje , kai……… Saina kashe ku ya fara wannan zabure²n nashi taron mutane da yawa Dikko ya haukace gaba ɗaya yana saina kasheta….

      Dakel aka kaishi ƙasa yana wai… Wai Allahna …. Wayyo idonshi yana zubar da hawaye yake kallon Dady duk wanda ke wurin saida Dikko ya bashi tausayi har a ƙasa harbe² yake yana An mata ni zaki tonawa asiri me yasa kike min haka saina mutu tunda baki san Dikko saina mutu wallahi , shaƙe wuyanshi ya farayi tunda bazan kasheta ba ni zan mutu kawai Dady mutuwa zanyi An matana take taɓa kofin… Sai kuma yayi ihu sosai tare da watse mutane dasu ka danne shi , Dady yace karku barshi ya miƙe danne Dikko akeyi amma abun yana nema ya gagara ,

      Da ƙarfi ya miƙe ya watsar dasu ƙasa , Dady yace ku rufamin asiri ku maidashi ƙasa , ƙara kama Dikko akayi dakel aka sake kaishi ƙasa a karo na biyu cikin kuka yace idan har na mutu rayuwarki ta zama walawala duk wanda kike tunanin zaiso ki da gaske ƙarya ne nine nake sanki da gaskiya , nine kaɗai zan riƙeki da amana nine kaɗai bazan cuta rayuwarki ba haba “Yar matana karki kuskura ki bari Dikko ya fita a hannunki , birkicewa yayi yana kallon sama yace idan kina ganin munayin faɗa wannan tafiyar babu dawowa har abadan abada idan na tafi babu waiwaye ki natsu mana An mata gaki “yar yarinya ƙarama kina so ki ɓata rayuwarki wai meke damunki da Allah , surutunshi yayi yawa Dady yasa aka zuba mishi maganinshi a baki lokaci guda ya ɗauke ya tafi baccin wucin gadi…

      Ganin har yanzu Hafsa bata dawo ba yasa Dady ya shaƙi wuyan Bello yace ka tabbata idan har ɗiyata ta mutu wallahi saina kashe ka har lahira ya ƙarasa maganar yana tura Bello baya , murmushi Bello yayi tare da matsowa shima ya shaƙi wuyan Dady yace ni kuma idan har wannan tsinaninyar yarinyar ta rayu sai na tona maka asiri kuma saina kasheta dan uban daya ci uwarka….

     Kokowa ta rikice tsakanin Bello da Dady yayin da Dady ke cewa kai har ka isa kaci kwalar rigata kai waye ? Nan fa Dady ya ƙwance ya fara aman turanci yana zage mashayin giya ɗan wasan caca Bello ba’asan komai ba irin kan Sultana ne haka nan akai ta wanka ana zuwa makaranta , empty brain.

       Rabasu akayi dakel Dady yana kiran stupid , Bello yace kai kaima stupid olowa ƙwaira dakai shima dan dai ace wani shege ne , Dady ya sake shaƙo wuyan Bello saida yayi mishi lullusar fitar hayyaci sannan yace ina Sultana take dan uwarka ? Dariya Bello yayi hihihihihi kamar mahaukaci da bakinshi daya fashe jini yana binshi yace nima nemanta nakeyi , wani irin mari Dady yayi masa tare da cewa ina Sultana take ne ? Bello yace ai kana da numberta ka kirata mana , ganin Bello zai raina masa hankali yasa yayi waya polisawa suka zo suka tafi da Bello yayin da Bello kema Dady kallon idan na fito sai naga bayanka…

       Ana tafiya da Bello Dady ya fara kiran wayar Sultana , ni kuma a tsorace na shigo cikin gida gabana sai faɗuwa yakeyi kamar banda lafiya haka naji yanayin jikina suku² da sallama na shiga cikin palon gidan , Kaka tana zaune a palo tayi baƙi gaishesu nayi na wuce har zan shiga ciki Kaka tacemin “yan uwanki ne “ya “yan kawunki ne , murmushin ƙarfin hali nayi cewa sannunsu na wuce ciki da sauri.

      Ina shiga na fara cire kayana bayan na gama nayi ɗaurin ƙirji dan har yanzu kiran wayar Dady bai daina shigowa ba , saida nayo alwalla na ɗauki wayar Dady cewa barka dai alawar zuciyata , murmushi yayi maicin rai tare da jinjina kanshi yace Hajiyata kina ta ina haka…..? Cike da iskanci nace ka ganni ina nan hotel tun shekaran jiya wani Alhaji ya tafi dani ana wasan danbe dani…

      Shiru Dady yayi ni kuma naci gaba da cewa ko zaka zo ayi dakai ne kaga wata yazo ƙarshe , ciki² yace ummm nace tou kayi sauri ka sameni ina nan hanyar shinkafi a cikin fesra hotel ɗaki na 10 , gani nan zuwa , nace kai saurara ba zafin zuwa ba kazo da kuɗi ai zanzo dasu nace mintuna biyar na baka idan ka wuce babu kai a lissafi Dady yace to ina faɗin haka na katse kiranshi na fara kiran wayar Dikko , bai ɗauka ba kaima kayi fushi da yawa haka mutumina Allah ya sawaƙe , ina faɗin haka na ajiye wayar na kabra sallar magrib.

Mota Dady ya hau ya bata wuta ya ibi hanyar shinkafi gudu yakeyi sosai yanayi yana kallon agogo cikin ƙanƙanin lokaci ya isa dan bashi da nisa da wurin yana isa ya fara kirana a dai² lokacin dana sallame sallah na ɗauki wayar yace Hajiyata na iso , ina ka iso ? Fesra hotel ! Ina ne kuma Fesra ? Inda kika ce na sameki ? Ni ? Ni nace ka sameni a Fesra Dady ? Ashe manyan mutane ma suna ƙarya kai amma kaji kunya , da ciwo ya jinjina kanshi tare da cewa tou kina ina yanzu ? Ƙasa² da murya nayi cewa zaka ganni ne ko kaima zakayi wasan danben ne…..? Na ƙarasa maganar ina dariyar mugunta , Ey tou yi sauri ka sameni ina nan ƙofar ƙwaya mintuna shidda na baka , 

Mintuna 6 daga shinkafi zuwa ƙofar ƙwaya ? Idan ka shirya kawai ka taho idan kuma ka ƙoshi in kakkaɓe zani na in rufe abuna inyi gaba mabuƙata da yawa ai , kallon agogo yayi ya hasko tafiyar dake tsakanin shinkafi zuwa ƙofar ƙwaya yace kidai ƙara zuwa mintuna goma , bana jira , Dady yace aiko baki nemi mu haɗu ba Hajiyata , murmushi nayi tare da cewa tou shikenan indai tayin banza wulaƙanci ne albarka ma amsa ce , dariya Dady yayi mai ciwo cewa gani nan zuwa , yana faɗin haka na ajiye wayar banza na ɗauki wayata da nake kiran kowa da kowa da ita.

         Yazeed na kira har ta shiga ta fito bai ɗauka ba , wai meke faruwa ne haba da Allah , shi wannan sarkin zafin kan baya ɗaukar wayana , Yazeedu kuma me ya faru dashi kardai su Ashiru sun dafe shi ? Aiko idan har sun kamashi ni wallahi basuyi min adalci ba.

     Haka nan na zauna jigum ina tunanin duniya , gaskiya nima dai wasa² “yar iska ce mai lasisi , tabbas duk wanda ya ganni yasan karuwa ce ni amma har yanzu dai karuwanci bai huda jikina ba dan kunsan akwai karuwar da ka ganta kasan karuwa ce , akwai kuma wacce ko ance maka ita karuwa ce sai kace ƙarya ne nima dai yanayi na kawai zaka kalla farkon kallo zaka kirani karuwa amma sanin fili akayi min sirrin ɓoye kuma ni marowaciya ce ga mazan bariki , nayi danfara wa mazaje da dama na feshe na kwashe kuɗi na gudu , na ɗauki tsiraicin maza nayi amfani dashi wurin ansar kuɗaɗe a hannun su , naɗanyi dai suna kaɗan kasancewar shagon da muka so buɗewa na kafa ƙungiyar kwarata a halin yanzu Amisty ta fini suna a harkar bariki ni kuma nayi suna sanadin tarayyata da Dikko dan mutane gani sukeyi ni karuwarshi ce !

     Hmmm nifa na buɗewa Amisty hanyar zaman “yanci , ta daina zaman karuwanci a gidansu ta dawo zama tare dani har tayi gidan kanta amma wai ni zatafi suna a harkar bariki , kiran wayar Dady ne ya dawo dani daga duniyar tunanin dana lula , ina ɗauka yace Hajiyata nazo ƙofar ƙwayar , tsoki nayi tare da cewa wai kai Dady wace irin kwalwa gare ka ne ? Ba tare dana jira ya bani ansa ba naci gaba da cewa me kuma ya kaika ƙofar ƙwaya kai da nace maka ka sameni ƙofar ƙaura ? Jinjina kai Dady yayi cikin tsananin ɓacin rai tare da danne zuciyarshi yace Hajiyata ai tsakanin nan da ƙofar ƙaura na kusa zuwa ma ,

      Tou cewa nayi ka taho ? Ai nasan cewa zakiyi mu haɗu wurin shi yasa na taho yanzu haka na iso , Dady kenan nifa ina filin jirgi yanzu haka , me kikaje yi a filin jirgi ? Hoto naje ɗauka yanzu mun gama kawai mu haɗu Qerau , ina faɗin haka na tsinke wayata nayi kwanciyata.

      Saida yaje airport sannan ya nufi Qerau ɗan wahalar , duk inda ya duba bai ga Sultana ba , haka ya haƙura ya tafi station yasa akayi Bello jakin duka yace duk a ɓare mishi haƙoran bakin Bello na gaba idan dai har bai faɗa masa inda Sultana take ba , Bello yace shi wallahi baisan inda Sultana take ba , Dady yace suyi ta dukanshi harsai yaje maƙabarta ya dawo… Haka akai ta dukan Bello harsai daya suma kuma basu daina dukanshi ba har ya farfaɗowa , Dady yace ka tuno inda take ? Cikin kuka Bello yace a , a , Dady yace kuci gaba saiya koma ya ɗauko kwalwar inda ya ajiyeta , haka akayi ta ma Bello gwalagwala yana zuwa duniyar suma da duka kuma yana farfaɗowa saboda azabar duka…

         Su Ashiru sune suka ɗauki matar data bawa Sultana kofin giya , sune suka tafi da ita bayan sunci ubanta sosai suka ɗauki bayanai a wurinta kamar yadda da suka faɗawa Dikko ya umarcesu , bayan sun gama kuma ba sakinta sukayi ba umarni daga Dikko aka ajiyeta a wurin daya basu umarni , bayan sun gama ne suka tura mishi hotunan da sukayi ma Sultana wanda shine yace duk inda suka ganta da abinda takeyi su ɗauko mishi ita su tura mishi , 

          Su Jiddah an samu abinda ake so ana wurin Momy kuma sai ƙara tunzura Momy takeyi yayin da ita kuma Momyn take ta daɗa hawa kamar kashin safe ,

       Dady kuwa bayan ƙura ta lafa ya fara doke²n waya cewa a ƙara saka shi da addu’a lamarin Dikko fa gaba yakeyi , yanzu banda furunci zai kashe , shi da kanshi yake cewa zai kashe kanshi kuma yana shaƙe wuyanshi , itama Momy haka ya faɗa mata itama dai tasha kuka kamar zata mutu , kuma haka itama tayi ta doke²n waya tana faɗawa “ya “yanta mata Yayun Dikko su biyu ne wanda suke ma’auri tace su saka ɗan uwansu a addu’a.

      Bayan Dady ya gama yake tambayar Dikko meya ɓata mishi rai ? Cikin kuka Dikko ya rungume Dady yace Dady nidai ka yafemin badan halina ba kayi haƙuri kabarni aure zanyi idan kana san farin ciki na da kwanciyar hankali na , Dady yace haba Babana kana ɗan yaronka zaka fara taretaren mata ? Nidai Dady a haka dan Allah , Dady yace Babana kayi haƙuri kar kayi aure yanzu lalurar mata biyu kanka baya ɗauka gaka baka da lafiya ka bari ka samu sauƙi mana , 

        Ɗagowa yayi ya kalli Dady cewa amma ka manta fa lokacin Sadiyya kafin ta rasu aka fara maganar auren Jiddah nidai Dady gaskiya aure zanyi kuma saura wata ɗaya kawai na faɗa maka dan in fita haƙƙinka , Dady yace ba umarni na kake bi ba ? Kayi min addu’a dan Allah Dady kuma bana so ka faɗawa Momy tace saidai in mutu bazanyi kishiya wa Jiddah ba ,

       Shiru Dady yayi yana kallon ɗanshi daya ɗauki soyayyar duniya ya tattara akanshi , kyakkyawan murmushi Dikko yayi ma Dady tare da ciro cingom a aljihun wandon shi ya cireshi a takardarshi ya rabashi gida biyu yasa rabi a bakinshi rabi a bakin Dady yana ma mahaifinshi kallo mai tattare da tsantsar ƙauna yace ai nasan ka yadda Dady shi yasa nake alfahari dake ya ƙarasa maganar yana ƙara rumgume shi , murmushi Dady yayi cikin yanayin damuwa ya fara tauna cingom in da Dikko yasa mishi a bakinshi yace ina bayanka Babana , tafawa Dikko yayi da duka hannayen shi biyu yace na gode Dady.

      Shi kuma Dady shiru yayi amma bai tambayi Dikko dalilinshi na abinda yasa yake so ya ƙara aure ba , yadai ansa kuma har a zuciyarshi ya yadda amma dake bayahude ne Dadyn na bugawa a jarida babu abinda ya dameshi da wani auren Dikko kawai dai yana ganin wani ra’ayi ne nashi na daban tunda bai faɗa ba shima kuma bazai tambayeshi dalili ba , kuma bazai hana Dikkon yayi aure ba , dan sanin da yayi ma Dikko a baya babu abinda yake ɓoye mishi kamar aboki da aboki haka suke faɗawa juna damuwar junansu sakamakon Dikko yanzu daya fara zurfin ciki , ajiyar zuciya Dady ya sauke yabi Dikko da kallo shi baya gajiya da kallon Dikko saboda soyayyar da yake mishi ,


    Bayan sati 4,


      Abubuwa da dama sun faru , kuma duk cikin kwanakin nan babu ranar da bana fita kullum rana saina fita kuma kullum sai anyi hotuna an turawa Dikko , kuma ni ina kiranshi kullum baya ɗaukar waya , nadaiji babu daɗi kuma inayi tunani sosai nakan tuno masu abubu sai inyi murmushi.

      Inna har yanzu basu dawo ba , tana can ita da mijinta sunma bar Dubai sun ƙara gaba abunsu , kullum sai sunyi waya da kaka ni kuma sai lokaci² nake kiiranta mu gaisa dan idan ban kirata ba bata kira tana daiyin kara haka ta fulani saidai ta kira mahaifiyarta kuma idan ta kira bata cewa ina Sultana ,

     Al ‘ Ameen ya samu sauƙi sosai an sallameshi daga asibiti ya dawo gidan gwamnati da ƙudurika da dama a zuciyarshi , kuma har yanzu Mardiyya tana nan bata tafi ba ,

     Jiddah ma tana wurin Momy har yanzu bata koma gidanta ba , kuma tuni Umar ya biga waya ya faɗawa Dikko Jiddah tayo yaji tana nan gidan gwamnati , 

      Hafsa ma ta samu sauƙi babu laifi an sallamota amma dake kanta irin na Sultana ne ta gagara gane yadda abun ya faru kwata² , Bello kuwa har yanzu yana can ana gana mishi azaba yanki² , Dady kuwa ido rufe neman Sultana yakeyi kuma har gidansu taje wurin mahaifiyar Dady wato kakarsu Hafsa ,

     Yau tunda gari ya waye da faɗuwar gaba na tashi , idan abu na ɗauka saidai ya kubcemin ya faɗi ƙasa , ko magana akayi sai in firgita , da sauri na fito wanka zanje wurin Yazeed ne dan ya daina zuwa gidanmu saidai muyi waya kuma duk yawan kwanakin nan bamu haɗu ba dan shima yaje tafiya jiya ya dawo shine yau yayi min waya cewa na sameshi company ,

Saida nayi sallah isha’e na fara shiri , Yazeed sai kirana yakeyi kila na ɓata mishi lokaci , ɗauka nayi yacemin kin taho ne ? Nace a , a yace ni nabar company yanzu ina tafiya zuwa G R A mu haɗu dake a wurin , idan kin hau napep wurin wanki motoci na cikin G R A za’a ajiyeki , nace sai nazo ina faɗin haka na ajiye waya naci gaba da shiri ,

     Ina gamawa na fice babu wanda ma yaga fita ta a gidan ina fitowa na samu napep na faɗa mishi inda zanje mukayi ciniki na faɗa yaja muka tafi ,

      Da sauri ya sauko daga saman gado jin wayarshi tana ringing kuma ya ajiyeta nesa dashi , kafin ya isa inda wayar yake harta tsinke yana isa wurin a dai² lokacin da wani kiran ya sake shigowa , ɗauka yayi tare da kara wayar a kunnenshi mai gida tana nan cikin G R A , baiyi magana ba ya tsinke wayar , makulin mota ya ɗauka ya fita daga ɗakin cikin tsananin ɓacin rai….

        Hajiya nifa na kasa gane inda zan ajiyeki wurin wanki motocin biyu ne ke baki san sunan companyn ba ne ? Kiran Yazeed nayi cewa nifa ban gane ba gashi ina tare da mai napep muna ta yawo , cewa yayi in ba mai napep in waya na bashi ya faɗa mishi inda zai kawoni ,

        Baya muka koma muka sha wata kwana mai napep sai masifa yakemin wai tun farko ban iya kwatance ba , da tuni nace masa majalissar Yazeed ai da baisha wahala ba , banza nayi dashi dan bana cikin yanayin fitina yau gabana faɗuwa yakeyi har yanzu , 

      Mai gida yanzu napep yayi parking da ita a majalisa , kashe waya yayi har yanzu baiyi magana ba , ya tafi wurin kai tsaye zuciyarshi tana ƙara ruruwa da zafin masifa ,

       A gaban wani irin makeken wuri yayi parking an ƙayata wurin da wasu irin fitilu masu ɗan bara’un haske , anyi parking motoci masu zafin bala’e daga waje har cikin wurin da aka zagaye shi da wata irin waya mai kyau amma kana ganin wanda ke waje shima na waje yana ganin na ciki , wurin ya haɗu duk matasa ne zaune a saman fararen kujerun rober wasu da ƙananan ƙofinan nan irin wanda ake shan shayin nan na maza duk shekarunsu bazai wuce kamar su Yazeedu ba , duk wanda ubanshi ya tara wasu manyan kuɗi na tashin hankali gashi ya hallara a wurin.

     Mai napep na sallama na tun kari wurin kai tsaye , wurin bashi da banbanci da rana kowa yana ganin kowa haka zaka iya gane duk wanda kuka sake haɗuwa a wani wurin daban , can gefe ɗaya kuma ga “yan mata zafafa suma an parkersu sai sheƙi sukeyi dan ubansu gayunsu irin ɗaya babu wacce tafi wata haɗu suma dai cikakkin “yan iska ne kowa tasha karuwanci ta ƙoshi duk “yan yara ² ne sunsha atach sunci bilicing har sunce wayyo Allah sai jin kansu sukeyi , 

     Amma ina shigowa wurin wallahi duk macen dake wurin saida ta shiga taitayinta , gaba ɗaya wurin ya anshi ƙamshina ya fara yawo zuwa cikin ƙoƙofin hanci duk wanda ke wurin , ba mazan ba suma kansu matan na zama abun kallo a wurinsu , wurin Yazeed na nufa amma kafin in ida isa tuni ya shigo a haukace wurin da mota , motocinsu Ashiru a bayan tashi ,

       Gaba ɗaya wurin ya karaɗe da hayani haba DK kowa DK yake faɗa yana magana da turanci , ɗan duniya uban Yazeed zaici amma sai yayi murmushi a dai² lokacin dasu Ashiru suka fito daga cikin motocinsu fuskar kowa babu imani , 

         Da sauri na juya zan fita amma Dikko yace Ashiru riƙemin An mata karka barta ta fita wurin nan , da gudu na wuce Ashiru cikin hayani Dikko yace na rantse da girman Allah idan har ka barta ta fita zakaji ni da ɗaci , tsoro ya kamani a dai² lokacin da Dikko ya taɓa Yazeed amma ba dukanshi yayi ba yanayin dana ganshi na firgita matuƙa , ga Ashiru ya ɗaure fuska kamar bai sanni ba dole na kama kaina na tsaya nabi Dikko da kallo.

        Yazeed har so nawa nace bana so kana tara mun mata a wurin nan ne wai ? Shima kanshi Yazeed zufa ke zobo mishi kanshi ƙasa ya kasa magana , murmushi Dikko yayi tare da cewa ba abinda zan maka idan har nayi faɗa dakai akan mace ni na zama sokon namiji , salon soyayyata a zuciyarta baya buƙatar dukan abokin takara wurin lashe zuciyarta , gani gaka ga An mata macece ita kuma zuciyarta tana da rauni na baka dama dani dakai kowa yaje yayi fira da ita ta bani lokaci naje kaima ta fitar maka da lokaci kaje na baka nan da wata ɗaya idan har ka samu ƙarɓuwa a zuciyarta na baka ita duniya da lahira amma karka sake fiddota waje , yana faɗin haka ya ciro hula daga saman kanshi irin tashi da kwakwar nan ya goge ma Yazeed zufar dake saman fuskarshi bayan ya goge mishi ya kamo hannunshi ya ɗora mishi hular a hannunshi , Yazeed yabi Dikko da kallo , duk saida yabi abokansu ya gaisa dasu sannan yaja hannuna ya sakani a mota yana cewa muje in baki tsaraba..

      Ya faɗi tsaraba yana min kallo mai nuni da kasheki kaɗaine bazanyi ba , zagayawa yayi ya shigo cikin motar ni kuma na fashe da kuka , murmushi yayi tare da cewa baki farin ciki na dawo lafiya ? A dai² lokacin daya fara tafiya da mota , ni kuma naci gaba da kuka yace wallahi ki rufemin baki yayi maganar yana kallon madubi ko su Ashiru shi suka biyo , tsayawa yayi ya sauke gilashi yace Ashiru kuje kawai zamuyi waya , banji abinda Ashirun yace masa ba naji yace a , a barshi kawai amma dai goruba zanje yanzu ,

      Yana faɗin haka ya ɗage gilashin yana cewa An mata kinsan bugun rabani da yaro ? Kuka nakeyi har yanzu banyi magana ba , Dikko yace wallahi yau mai ƙwaceki a hannun majnun { mahaukaci } sai Allah kawai miƙomin wayata inga waye yake kirana , ɗauka nayi na miƙa mishi , Jiddah ya faɗa tare da cewa lafiya ita kuma wannan ? Yayi maganar yana ɗaukar wayar yace inajinki , banji abinda tace ba yace Ey naje zance yana faɗin haka ya ajiye wayar yana cewa wallahi An mata yau na raina miki wayau , aini ko mace ce banga ranar da zanbi namiji ba ,

      Namijin mi Allah na tuba ina mace ? Namiji ma ya biyoni yana so ai sai yaga yanga da kisisina , macen da aka santa da kwarkwasa da ƙwalisa aji da ɗauka kai ke kuma gaki nan sake dan wawanci kin taho kin biyo namiji sakarar banza dake da baki san namijin so ba , wallahi ni da macece ni dana ba maza azaba ko zance namiji yaje wurina dan ubanshi saina daɗe ban fito ba dan yasan yes wannan tasha banban da sauran mata a cikin mata dubu sai yasan ni ɗin ta daban ne , kuma in fito ina isa ina riƙe aji , namiji yayi magana goma ansa ɗaya zan bashi , nidai a tsarina ina mace ko driver bana yadda Yazeed yayi min bare dan ubanshi harya ɗaukar min jakata , ashe hakanan nake tun ƙaho “Yar mata tana da class nan ma ashe zero kin ban kunya kuma kinci baya , saboda Yazeedun banza da wofi kika hau napep ƙarshe ya wulaƙantaki yayi miki masauki inda suke ajiye karuwai nan yace ki sameshi ke kuma wawiyar kika kama hanya kika taho wallahi ji nake kamar in wurgaki waje in take ki da mota ki mutu in huta da takaici , mtsww haba inama amfanin mace ba aji ?

      Gunguni nayi mishi yace me kika ce ne ? Shiru nayi ban sake magana ɗaure fuska yayi cewa bari haushinki nakeji da yawa wallahi , tsoki nayi cewa to ai sai ka kasheni nayi maganar ina miƙa mishi jikina wani irin mari yayi min wanda yasa na ɗauke lunfashina lokaci guda…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button