NOVELSUncategorized

KWARATA 67


???? —— 66 Daga Bello har Dady duk tsoro ya kamasu kowa a ƙagare yake yaji abinda boka zai faɗa bayan sun kora masa bayani cewa sudai duk yadda za’ayi ya kashe Sultana har yanzu basu samu yarinyar ba , kuma a halin yanzu babu wanda yasan inda take , Dariya boka yayi sosai sannan yace nace bazan iya kasheta ba , Dady yace me yasa ? Boka yace aljannun da nake tsafi dasu basa san mutum mai cika

kamsus salawat dole sai yarinyar nan ta daina salloli biyar a rana kaɗai zasu iya kasheta , ba kuma zasu kasheta ba tana cikin jinin al’ada ba dole² sai ta daina sallah sannan kaɗai su iya kasheta. Dady yace zan baka miliyan ɗaya , girgiza kai boka yayi cewa bata ansuwa kuma bata ciwuwa kuje kawai kusan yadda zakuyi ku dakatar da ita daga sallolin dana faɗa idan ta daina ni kuma zansa aje a tsige mata wuya , cikin hayani ya ida maganar cewa ku tashi ku bani wuri…… Daga Dady har Bello da sauri² suka fito daga wurin boka bayan sun fito ne Dady ya kalli Bello yace duk yadda za’ayi ka samo mana yarinyar nan mu kasheta da kanmu idan har ka samota zan baka zunzurutun kuɗi har naira miliyan 20 , murmushi Bello yayi ya kalli Dady a ranshi yace haba ai kafin Sultana ta mutu kaine mutum na farko da zan fara kashewa , yadda ka wulaƙantani a ofishin “yan sanda kana tunanin ka wulaƙanta banza…..? Amma a fili sai yace zan iya Alhaji amma ba zanyi aiki bashi ba , Dady yace dama ka taɓamin aiki a bashi ne ? Bello yace har yanzu ina binka cikon kuɗin shiga rayuwar Binna da nayi tun muna matasa , ina binka kuɗin asirin da nayi masa ya shiga caca ya shiga harkar mata sannan kuma har yanzu kuɗin lalata rayuwar Sultana sisi ma baka bani ba , Dady yace to wannan zan baka dai , Bello yace tou idan ka haɗo kan kuɗaɗen saika kawomin ni kuma a ranar zan shafe lissafin sunan ta a cikin jerin sunayen masu lumfashi a duniya , Dady yace karka damu zuwa ƙarshen satin nan zan baka , haka dai suka shiga mota suna tattaunawa…. Auntyna ga wasu kayan mata na kawo miki suna da kyau sosai kuma zakiji daɗin amfani dasu masu kyau ne jarababbu ne , Mardiyya ce a gaban Jiddah take korata mata bayani akan kayan matan data haɗo take mata bayani cewa kinga wannan sunansa babu sauran kallo , wannan kuma rantse baki da kishiya , Jiddah tace ya rantse baki da kishiya…..? Murmushi Mardiyya tayi cikin kwantar dakai mai nuni da salon yaudara tace ai Aunty idan kikaje sayen maganin sai kinyi rantsuwa baki da kishiya ma sannan a siyar miki dashi , dan idan har kina da kishiya ba’a baki shi dan Yaya DK bazai sake zuwa wurin ta kullum yana tare dake manne kamar hanta da jini , dariya Jiddah tayi ta ɗauki maganin tace Mardiyya ina kika samominshi ne ? Mardiyya tace ni na samo miki shi a Banbaɗawa kuma Aunty da tsada na siyo shi fa , shi kuma babu sauran kallo Yaya baya sake kallon ko wace mace saike domin kece sarauniyar zuciyarshi , dariyar jin daɗi Jiddah tayi cewa kuma kamar kinsan aure zaiyi , wata irin faɗuwar gaba Mardiyya taji lokaci guda taji wutar ganinta ya ɗauke , Jiddah taci gaba da cewa ance ma Momy yana aiki gidanshi na goruba road wai acan zai ajiye matar , gidaje biyar ya siya ya haɗe yana tayi ma amarya gyara , amma Momy tace masa ko waye ya tsaya masa bazaiyi aure ba sai yace mata dama ai ba aure zaiyi ba , kuma da tace masa ance mata yana gyaran gida idan ba aure zaiyi ba me yasa yakeyi ? Shine yace mata masu gidajen ne kawai zasu siyar shine sukace da Allah ya siya shine fa ya siya…….! Amma ni wallahi inaji a jikina Yaya aure zaiyi , gyara zama Mardiyya tayi tare da cewa Aunty taya zaiyi aure bayan ya faɗawa Momy bazaiyi ba ? Murmushi mai ciwo Jiddah tayi sannan tace idan har Yaya yace zaiyi abu to wallahi duk duniya babu wanda ya isa ya dakatar dashi sai yayi , idan kuma yayi rantsuwa akan abu shima ko za’a mutu sai yayi , kaifi ɗaya ne shi kafin ya furta yake da wahala amma da zaran ya furta tofa ko kanshi baya saurara , Mardiyya tace amma me yasa baki faɗawa Momy auren nasa da gaske ne ba ? Jiddah tace Dady tayi ma magana akan ya dakatar da Dikko maganar aure ba zata yadda ayimin kishiya ba , sai Dady yace mata Babana zaiyi aure shine bai faɗamin ba yayi faɗa sosai sai Momy tace itama hasashe ne takeyi , sai Dady yace shirme kenan yama ɗauka gaske ne da yace me yayi ma Babansa aure haka babu shawara ? Cikin kwantar da murya da ladabin munafirci Mardiyya tace to aike ma Aunty ance ki samo sparm inshi kin gagara , Jiddah tace tunda bai bani ba wai ya zanyi ne ? Tayi maganar cikin hayani , ganin haka yasa Mardiyya ta sake kwantar da kanta tace akwai wani magani da zan samo miki a tea zaki zuba mishi ko a lemu amfanin maganin nan shine yana sa sha’awa na masifa kin gane ki bashi shi da safe zaiyi ta nemanki ya kwanta dake saiki ƙi yadda kiyi ta ja masa rai , zai kasa fita ke kuma kinayin abubuwa irin wanda zasu na tayar mishi da hankali kuma ba zaki kwanta dashi ba , zaiyi ta roƙonki idan kikaji nacin nasa yayi yawa sai kice zakiyi amma da sharaɗin zai baki…..? Zai ansa kai tsaye dan yana bisa matakin da bazai iya miki gaddama ba , haka dai sukaci gaba da tattaunawa taron wawayen… Ko da aka kawo abincin a mota mukaci saboda gidan akwai taron ma’aikata sosai sun wasu ta ko ina kowa yana aikin daya shafeshi , bayan mun gama cin abinci ya fita yacemin yana zuwa , nima ta cikin madubi na leƙa na gani an ɗaukeshi a mota sun fita daga gidan , ina ganin ya fita kuma ga mota nima na koma mazaunin matuƙi na fice daga gidan na nufi sabon layi , Lokacin danaje sabon layi ban fita daga cikin mota ba saboda banajin daɗin jikina , ina zauna na kira wata mata nake tambayar matar nan ko ta dawo ? Tacemin ta dawo amma yanzu bata nan taje Qerau , ni da kaina na buƙaci tayi min kwatance ina taje a Ƙerau tacemin gidan Kaka , nace wacece Kaka ? Tacemin baki san Kaka ba ? Nace ban santa ba , tacemin aiko kowa yasan Kaka garin nan , wayarta ta buɗe ta miƙomin bayan ta nunomin hoton Amisty tana cewa wannan itace Kaka , murmushi nayi tare dayi mata godiya na maida mata wayarta bayan na bata kuɗi na tunkari Qerau kai tsaye…. Ina tafiya ina tunanin Amisty har ta zama Kaka bama uwar karuwai ba Kakarsu fa ? Lallai Amity tana da sa’ar rayuwa , babu wani nisa tsakanin sabon layi da Qerau cikin ƙanƙanin lokaci na isa ƙofar gidan Amisty , taron karuwai da “yan daudu duk wata tsinana da bakin iyaye ya kama gata nan tana wurin karuwai burjik , hada wasu daga cikin “yan gidanmu suma dai duk anyi musu sign in karuwanci , Hamida na gani naga Fa’iza naga Farida naga Zainab ni da yake dai ban san sunansu ba amma duk fuskokin “yan gidanmu na gansu sunkai su goma sha wani abu ashsha… Inayin parking na sauke glass Hamida ta fara gani na ta rugo wurina cikin farin ciki tana Sultana kece ? Murmushi nayi kaɗan tare da cewa ya gda ? Lafiya qalau me kukeyi anan naga an taraku ? Kallon taron mutanen tayi sannan ta kalleni tace ƙuru’a akeyi , wace irin ƙuru’a ne ? Gasa za’a tafi ta wasan danbe ? Idona naji ya cika da hawaye na kalli Hamida sosai nace kema hada ke a zuwa gasar ne ? Dariya tayi mai nuni da nama raina ta , murmushin ƙarfin hali nayi cewa uhum ? Tace ai nima ina jagorantar team guda ne bayan anyi ƙuru’a idan mutum yaci sai ayi masa interview idan yaci sai ayi training. Ina ne zakuje gasar ? Na tambayeta , tacemin a gabi za’a gabatar da gasar , bin taron matan nayi da kallo na hango Safiyya yarinyar Baba Ƙarmi itama ta samu isowa Maman Affan da Maman Sadiq kallon Hamida nayi na tambayeta suma wa’ancan hadasu za’aje ne ? Tace suma suna da yaransu , amma ba matan aure bane ba ? Murmushi Hamida tayi cewa ai matan aure ma sunyi kowa yawa a ciki , to me yasa suka shiga harkar danbe bayan suna da mazajen su ? Hamida tace kowa da matsalar data kawoshi kedai bar kowa yayi rayuwarshi , jinjina kaina nayi a lokacin dana hango matar da nake nema dan haka nacema Hamida ta kiramin ita. Tafiya tayi dan kiramin ita yayin da ni kuma nabi taron dandazon mutanen ina kallo , hankalin duk wanda yake wurin akan motar da nake yake amma tunanin kowa dai Dikko ne shi yasa babu wanda yazo , turomin matar tayi ita bata dawo ba , bayan mun gaisa nace mata kin kuwa gane ni ? Murmushi tayi cewa ya kuwa za’ayi na manta Binna ? Nace yawwa , tou wai ya akayi ranar muna tsaye sai kawai kika ɓace abunki ? Cikin damuwa tacemin wallahi yaran Dikko ne suka ɗaukeni sukaje dani sukamin tambayoyi akan abinda na sani game da Binna da rayuwar ahalinshi , abinda yasa ya shiga harkar caca da kuma bincike akan mutuwarshi , yana da wasu abokan hamayya wanda suke takon saƙa nace musu babu , sundai bincike sosai kamar an bajewa uwar san banza dilar gwanjo. Kallonta nayi sosai sannan nace to me yasa baki dawo ba ? Riƙeni sukayi a wurinsu har sai da DK yazo da kanshi , da yazo , shi me yace miki ne ? Shima dai tambayoyi yaimin , a tambayar me ya tambayeki ? Hankalinta yana wurin taron su dan haka tacemin ki bari kawai zamuyi magana daga baya , nace a , a ki saurareni mana , dan Allah kiyi haƙuri ko kuma ki bani number wayarki idan na gama abinda nakeyi zan kiraki , wayata na miƙa mata tare da cewa kisa taki a ciki sai ki kira dan kiga nawa , haka tayi bayan ta gama ta miƙomin ta wuce , Fita nima nayi daga cikin motar ina tunani kafin Dikko ya gama yin bincikenshi insha Allah ni na gama da matsalata , domin ni nasan abokan takon saƙar Babana, babu wanda ya sani saini ɗaya kuma saina kwatarwa kaf ahalina kuɗin gadonsu sannan kuma da hannuna zan ɗauki fansar mutuwarshi , nayi maganar ina kallon tafukan hannaye na , Fitowata daga mota yasa wurin ya ɗauki ihu mutane sukayo wurina suna ta runguma ta , yayin da wasu ke tambayata inda na shige , Amisty Hafsa da duk wanda na sani babu wanda bai rumgumeni ba haka nayi ta gaisawa da mutane cikin riƙe aji da kamewa sosai yayin da wasu kuma suke tambayata inda nake zama , babu wanda naba ansa saidai nayi murmushi kaɗan , A wayance Amisty ta fara gabatarmin da sabbin karuwai da irin jajircewar su a harkar bariki , saidai in jinjina kai , su Nana da A ` i Karima da Saude har Asma’u babu wanda babu a wurin domin naga suma sun ƙwace da yawa , Amisty ta zama gogagga sosai a bariki ta anshi takaddun gaba da degree a wurin karuwanci taci bilicin an saka haƙorin makka ƙasa da sama , anyi hujen hanci duk dai inda kake neman karuwar data ansa sunanta a harkar karuwanci kana ganin Amisty ka tsaya , domin kallonta kanshi shima abin burgewa ne , tadai zama Kakar da gaske. Kallon Hafsa nayi nace ke kuma kinje wurin Dikkon ne ? A sakace tace ni naje wurin daga nan bansan yadda akayi ba , nace kamar ya ? Wasu suka saceni suka kaini wani gida sukayi danbe dani , keda baki san yadda akayi ba ya akayi kika san anyi dambe dake ? Na faɗi maganar ina dafa kafaɗarta muka fara tafiya muna fita daga cikin mutane ina mata tambayoyi kamar haka , su waye suka kamaki ? Ni bansu ba kawai napep yana sauki ni a fesra suka cakumeni , me yasa bakiyi ihu ba ? Nayi ihu dan a kawomin ɗauki daga baya sai suka toshemin bakina , me yasa baki ƙwaci kanki da karfi ba ? Bana iyawa saboda suna da yawa , da suka ɗaukeki ina suka kaiki ne ? A mota suka sakani suka tafi dani wani gida , da sukaje dake ko kinji suna cewa wani abu ? Eh bana iya tunawa dai amma naji mutumin dai yana ta maganganu kuma sunanki yake kira kawai dai na manta abinda yake cewa , Kiyi tunani mai kyau idan har kika tuno ni da kaina zan ɗaukeki a mota na kaiki wurin Dikko kuma tsaya ki gani , wayata na fiddo na fara kiran wayar Dikko , ashe Dikko harya koma gida ya samu bana nan , ƙin ɗaukar wayar yayi na sake kiranshi tuni Dikko ya gune yana jira in dawo ya saukemin rashin mutunci. Ganin Dikko bazai ɗauki wayar ba nace yawwa kin gane ki tuno idan har kikamin gamsashen bayani wallahi sai na kaiki wurin Dikko , murmushin jin daɗi Hafsa tayi cewa , bara in tuno muji , dafe kanta tayi tare da ƙurawa wuri ɗaya ido , tunda taji maganar zan haɗata da Dikko dole nasan zatace wani abu. Bayan wani lokaci tace yawwa , ni kuma nace dana kiraki kince min kina Qerau , nayi maganar niƙaf da hijabi nace Dikko yana jiranki a fesra ki fara tunani tun daga lokacin da kika hau napep. Hafsa tace bayan na sauka a napep na fiddo wayata na fara kiran wayar Dikko sai akacemin a kashe yake , ina tsaye a wurin ban tafi ba ina ta kiran wayar kawai naji an nannaɗeni ta baya , nace su waye haka ? Ina zakuje dani ? Sai wani ya mareni yace wurin ubanki zamu kaiki , na nemi a kawomin ɗauki sai suka shakeni da niƙaf suka sakani a mota , Sun kaini wani gida bansan ko ina ne ba , wani ne ya fara zuwa a kaina yana danbe dani , sunyi maganganu dai , tayi shiru , ƙara dafeta nayi sosai nace waccan motar kinsan ko ta waye ne ? Hafsa tace ta DK ce , nace tunda har nahau motarshi ai kinsan kusanci yakai ko ? Tacemin Eh tana kallona , nace tou duk cikar faɗin birnin katsina Dikko baida aminiyar daya wuce ni , idan nace yayi zaiyi idan nace ya daina zai daina ya yadda dani fiye da lissafinki , me kike so na roƙar miki a wurin Dikko ? Cike da zumuɗi tace ni ya aureni kawai , nace Dikko ya aureki ya gama idan har kika bani labarin komai baki ɓoyemin ba saina sadaki da Dikko faɗa ina saurarenki , saida ta sake tunani taci gaba da cewa ! Tabbas naji wani yace nine Bello aminin ubanki , kiji da kyau yadda kikamin video tsirara haka zanyi miki kema , ni na koyama ubanki iskanci amma ɗan iskan ya lashemin mata a daren farko , yace na ɗana masa tarko amma ɗan banzan ya tsallake , idan baki sani ba nine nayi asiri wa Babanki kuma nine na haɗashi yake tarayya da ahalinshi , Kuma yace nine nayi asiri wa Babanki ya sakaki a wasan caca nine na mayar dake kidahumar ƙarfi da yaji na sakaki kika antaya a ruɗun duniya , bayan ya gama magana yace ni Bello zanyi iskanci da “yar ka idan ka isa ka dawo daga duniyar mutuwa ka ƙwaci “yar ka a hannuna , Ya kira Binna daga baya kuma yadai yi maganganu sosai kuma Dadyna yana wurin , kuma mai maganar yace yayi asiri ahali ɗaya sunyi gauragauraya suna iskanci badai zan iya ganewa ba domin ina cikin wani hali a dai² wannan lokacin. Sakin Hafsa nayi tare da juyawa nace wane irin hali kike ciki ? Juyowa nayi na shaƙe wuyan Hafsa ina cewa wane irin hali kike ciki ? Wane irin haline wannan ? Me Dadyn naki yake faɗa……? Me yace ? Nayi maganar cikin hayani sosai tare da cewa na rantse da Allah idan dai harni ɗiyar Binna ce ɗaya daga cikinsu idan ya sakeyin rayuwa mai daɗi ni ba ɗiyar Babana bace , sakin Hafsa nayi tare da turata baya da ƙarfin bala’e ta kusa faɗuwa Amisty ta riƙeta tana lafiya Mother , idona cike da hawaye nace dake da Hafsa dani gaba ɗayanmu ahali ɗaya ne , Gaba ɗayansu babu wanda baiji faɗuwar gaba ba , cikin tashin hankali Amisty ta cire gilashin dake saman fuskarta tana kallona , saida na goge hawaye sannan nayi murmushi mai ciwo nace kunji wani iri ko ? To nima haka naji lokacin da aka faɗamin ku “yan uwana ne , nayi kuka kuma nayi baƙin ciki kasancewa ta a cikin gurɓataccen ahali , cikin ɗaga murya sosai nace tou ku sani ni ɗin ɗiyar Binna ce kuma nima jikar gidan su Hafsa ce dani da “yan uwana da kowa na nuna Hafsa cewa tou idan baki sani ba Kakarki itace silar roshe komai , duniya ya ruɗeta yasa ta kora “ya “yan kishiyarta saboda san duniya wanda basu ji basu gani ba , ni ɗaya tak nake a wurin uwata kuma soyayyata a zuciyar Babana ba ƙarama bace ba , fashewa nayi da kuka ina cewa amma shine suka kashe Babanan, me yayi musu ne ? Cikin musulmar murya na sake cewa me yayi muku ? Mu kuma me mukayi musu suka mayar damu marayun ƙarfi da yaji ? Inda taron “yan gidanmu suke na kalla tare da nunasu nace su kuma wa’ancan me sukayi muku ne ? Me suka tsare muku ? Shine kukayi silar maida ahalina karuwai……..? Cikin ɗaga murya na cire gyalena na wurga saman mota ina cewa na rantse da Allah , na daki kaina , dai² zuciyata nakai ma duka cewa na rantse da soyayyar mahaifina idan nabar ubanki da kakarki sun huta Hafsa kice ni ba MARYAM ALIYU MUHAMMAD BINNA nake ba , ni ba ɗiyar BINNA bace ba. Cikin tashin hankali Hafsa ta rugo da gudu ta riƙeni tana cewa Uwar ɗaki me yayi zafi haka ? Ki goge ƙudirin ɗaukar fansa a zuciyarki , cikin hayagaga nace ke ji nan kije ki tambayi wannan ruɓaɓɓiyar tsohuwar meye dalilin da yasa ta kora Binna da ɗan uwanshi daga cikin gidan ubansu , murmushi nayi mai kyau ina kallon Hafsa cikin tsananin ɓacin rai nace to ki sani nice na shirya komai ta yadda aka saceki akaje akayi wasan danbe dake , nina shirya komai kaidina da sharrina yafi alkairi na yawa , idan har kina so na goge babanki daga siraɗin ɗaukar fansa na baki daga yanzu zuwa gobe da safe kije wurin kakarki ki tambayota dalilinta na kora iyayena daga cikisu kizo kuma ki faɗamin idan kuwa ba haka ba kema zaki zama marainiya kamar yadda mu “ya “yan Binna muka zama marayu , ina faɗin haka na wuce na shiga mota nabar wurin cikin ƙunar rai….. Daga Hafsa har Amisty sun gagara gane abinda Sultana ke nufi saboda toshewar tunani , Amisty tace taya ma zamu zama ahalinta ne wai ? Hafsa kuma tace kinji wata sabuwar barazana wai itace tasa aka saceni akayi danbe dani bayan babu abinda ta sani nice fa na bata labari yanzu bata san komai ba , tana ganin dan na bata labari zatayi amfani da wannan damar ta tayar min da hankali , can ita ta sani da ita dasu wannan ba damuwa na bane ba , Ina fita bakin titi wuri na samu nayi parking a gefen titi na fara kiran wayar Dady da wayar da Dikko ya bani ba tashi wacce ya bani ba , babu ɓata lokaci ya ɗauka , cikin wata murya daban nace bawan Allah sannu Allah ya ƙetare “yar ka daga hannun azzalimai , ai dama nace duk yadda za’ayi saina samu number ka na faɗa maka gadar zaren da ake gina maka na ƙarasa maganar ina fashewa da kuka , Dady yace wace ce ke ? Cikin kuka nace masoyiyar ka ce , wata ce take neman ganin bayan ka shine ni kuma zan tona mata asiri , dani da ita duk a bariki muka haɗu ƙawata ce kuma itama karuwa ce ana ce mata Sultana ko ka santa ? Murmushi Dady yayi yana cewa tana ina ne ? Tana ɓoye a halin yanzu domin tana nan tana nemanka ta kashe ka shine na sace numberka daga cikin wayarta dan in faɗa maka cewa ka ankare dai dan yarinya bata sanka da yawa , cikin rashin lissafi kawai Dady yace ai har yanzu Binna baida ɗiyar da zata ga bayana ke wace ce ? Nace zan bayyana amma sai ƙura ya lafa kuma karka faɗawa kowa domin da wani abokinka ta haɗa kai suke san ganin bayanka , Dady yace waye abokin nawa ? Nace bansan sunanshi ba saina siffanta masa kamanin Bello na ɗora da cewa wata rana kayi ma Sultana waya zaku haɗu a fesra hotel ita kuma ta kirashi ta faɗa mishi shine shi kuma ya bugama “yarka waya yace su haɗu a wurin dan yana jin haushinka sosai shine yasa yakai “yar ka sukayi danbe da ita kuma kaima yaso sai kayi danbe kaga “yar kace , wata irin ashariya Dady ya dandanƙara cikin jin haushi yace ni Bello zai cuta ? Amanata zaici ? Tabbas biri yayi kama da mutum domin idan ban manta ba ita Sultana tace min wai na ɗan ɓoye mota ta daga ciki dan wani ne zai sauketa , wato tayi haka ne dan kar Hafsa tazo taga mota ta ne , amma a cikinsu waye ya gayyato Hafsa , tsakanin Sultana da Bello……..? Bello ne domin shine ya shirya komai yana jin haushinka fiye da yadda baka tunani , amma Alhaji ina ganin shawara ɗaya me zai hana kawai kasa a kashe Sultana kafin ita taga bayan ka , Dady yace haka muke ta ƙoƙari mun faɗawa bokanmu amma yace sai ta daina sallah kaɗai zata iya mutuwa , shin ko zaki iya dakatar mana ita daga sallah ? Wannan ba abu mai wahala bane kauda ita daga duniya ni kaina idan ka bani izini zan iya shafe maka labarinta daga duniya guba kawai zan zuba mata a abinci taci ta mutu amma sai ka farayin wani abu akan Bello , Dady yace bari in fita daga Office sai muyi magana , godiya nayi masa tare da kashe wayata , bayan na gama na cire layin da Dikko ya siyamin na ciro layin da Dady ya bani na saka a cikin wayar da Dikko ya bani na fara kiran wayar Bello da layin da Dady ya bani , wato number da ake kirana ana cewa za’a kasheni , dan ina so nayi recording ita wayar da Dady ya bani ƙarama ce. Tana shiga ya ɗauka sai yayi shiru dan abinda na fuskanta number da yake kiran nawa kila daban yasai layin , nace ka gudu daga inda kake ni ina san tseratar maka da rayuwar ka ne , cikin muryar shi dana sanshi da ita yace wace ce ke ? Sanin ko wace ce ni ba shine ba ina san tseratar da rayuwarka ne domin a halin yanzu suna san ganin bayanka , su waye ? Kamanun Dady na faɗa nace shine yake san cin amanarka , kun haɗa kai akan zaku kashe wata yarinya amma shine naji yana cewa sai ya kashe ka , dariya Bello yayi ni kuma na dannan record bayan nayi shiru shima cikin rashin lissafi yace wannan shine ƙudirna da ko wane wata da ko wane sati ko wane yini da ko wace awa kowace daƙiƙa saƙo da lungu rana da dare neman sa’ar mutuwarsa nake , saina kashe shi. Yana faɗin haka na tsine kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya na nufi goruba road , zuciyar Dady tana ɗauke da gudirin ganin bayan Bello , danshi a ganinshi idan ya kashe Sultana sai ya kashe Bello sune damuwarshi kuma sune suka san komai , idan ya kashe su gaba ɗaya babu wata sauran barazana a dukiyarshi , yayin da Bello shima yake ƙudirin ganin bayan Dady zaisa Dady ya kawo kuɗin da zai kashe Sultana yana bashi kuɗin zai burma ma Dady wuƙa a ciki ya mutu shi kuma saiya ɗauki kuɗin yaje ya kashe Sultana shikenan ya rufe wannan matsala…. Tunda na shiga gidan wani irin kallo Dikko kemin fuskar nan a haɗe yana zaune saman bayan motar abokinshi , su Ashiru suna tsaye kusa dashi , jikina yana kyarma nayi parking na fito da sauri na nufi wurinshi , abokinshi na gaida sannan na matsa kusa dashi ina bashi makullin motar , bai ko kalli inda nake ba dan haka na ajiye makullin kusa dashi na koma gefe nima na tsaya kamar yadda naga kowa yayi , Hmmm yayi tare da ƙuramin idanuwa yana kallona cikin ɓacin rai , yakai kusan minti 3 yana kallona kuma ko ƙyabtawa bayayi dole na shiga taitayina jikina ya fara tsimama da ƙyarma tuni na sauke kaina ƙasa dan kallo ya firgitani , bayan wani lokaci na sake ɗagowa har yanzu ni yake kallo , da sauri na sake sauke kaina banma yi gigin sake kallon inda yake ba dan bana iya haɗa fuska dashi , tafiya na farayi dan komawa bayanshi ya daina ganina ta gabanshi saboda banajin daɗin kallon , Robar ruwa ya ɗauka a gefenshi da magani yace zo ki ansa , ban koma ta gabanshi ba na tsaya daga bayanshi na miƙa hannuna na ansa , robar ruwan ya bani maganin kuma ɓallomin yayi ya miƙamin , ansa nayi nasha bayan na gama na maida mishi robar da sauran ruwan dana rage , ansa yayi ya maida ita a inda ya ɗauka yace tafi Ashiru ya maidake gida , kwantar da kaina nayi saman motar nace ngode , baiyi magana ba Ashiru ya ɗauki makullin yace muje , Bin bayanshi nayi ya buɗemin gidan baya na zauna ya rufe ya zagaya ya shiga mazaunin matuƙi yaja muka fita daga gidan , tunda muka fita Ashiru kemin nasiha yana cewa wallahi yau Allah ya tsareki irin dukan da yaso yayi miki Allah kaɗai yayi iyaka dashi haƙuri mukayi ta bashi kafin ki dawo , dan Umar ya kirashi waya yace ya ganki Qerau , mai gida yace ya barki goruba saida ya turo mishi hotunanki sheda ya gani ya yadda kuma ya dawo bai sameki ba , lokacin da kike kiranshi waya tou lokacin ya hau muna ta ƙoƙoarin saukeshi , wai kema ranki ya daɗe dole sai kin fitar wai ? Murmushi nayi amma banyi magana ba , har muka iso gida nasiha Ashiru yakemin , fita nayi tare dayi masa godiya kawai na wuce ciki…. Wasu irin motoci ne parke a harabar gidanmu masu kyau da tsada , kila ɗan uwan Inna ne ya dawo , tunda na tunkaro hanyar da zai sadani da palon naji maganar shi yana cewa ƙaddara babu wanda ya gagara yahau , ni banga abin ƙin wannan yarinya ba , matar ɗazu take cewa wallahi nidai jinina idan dai ni na haifeshi bazai auri yarinyar nan ba , idan kuwa ba uwarshi bace ni tou yaje ya aureta nayi bare duniya dashi ko lahira kada Allah ya haɗani dashi , yarinya karuwa kowa yasan karuwace a garin nan gata ɓarauniya kuma daƙiƙiya kidahuma gata bata fito daga tsatso mai kyau ba , haba duk iyayen mutunci sun haɗa ɗiyansu aure da ita ? Ɗan uwan Inna yace tunda duk kowa ya hana ɗanshi ya aureta ni zan bada ita , cikin hassada tace ai kasan ɗan tsiya bai gaji arziƙi ba kana tunanin ka haɗa ta da ko driver n ka ko mai gadinka ai ƙarshe watsa maka ƙasa zatayi a ido tace bata sansa kaga kuwa ai ba haka kaso ba , ni ba cikin su zan bata ba , Sultan ɗana zan haɗasu aure a cikin satin biyu masu zuwa , Sultan kowa ya faɗa ɗanka mai mutunci da daraja shi zaka aurawa karuwa ? Gaba ɗaya palon ya gaurare da hayani har bakajin abinda wani yake cewa , Hawaye naji ya ɗigomin daga cikin idanuwa na , wayyo Allahna , kila sunyi tunanin zai haɗani da mai gadinshi ko driver ko wani dai mara galihu , ɓarauniya , karuwa , daƙiƙiya , kidahuma ban fito a tsatso mai kyau ba , yace yaji kuma ya gani ɗanshi zai aureni , ya zanyi da Dikko ? Idan har kuma ban amince da maganar ɗan uwan Inna ba ance dama zan watsa mishi ƙasa a idanuwa saboda ban gaji arziƙi ba ni ɗiyar tsiya ce , jinjina soyayyar Dikko nayi a zuciyata gaskiya Dikko yana min soyayya mai girma , a bayyane nace tabbas haƙuri zanyi dakai kodan in nunawa ɗan uwar Inna na fito daga ahalin masu mutunci zanyi haƙuri da soyayyar Dikko in anshi Sultan ko baimin ba , tou tayama zan iya rabuwa da Dikkon wai ? Tun ma farko kenan wayyo Allahna…… Ji nayi gidan yana juyamin yayin da zuciyata kece cewa *DIKKO KO SULTAN…?* cikinsu wa zan zaɓa……?

PLS CLICK ON ADS
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


Related Articles

Leave a Reply

Back to top button