KWARATA 72

???? —— 70
A rayuwarka babu abinda ka sani sai zafin kai , doke² , ɗaure fuska gaka mahaukaci ga aljannu kamar iccen tsamiya ni taurin kai , kai kuma zuciya talauci da arziƙi basa zama wuri ɗaya dole idan ɗaya yazo to ɗaya zai tafi , hawaye ne ya gangaro daga cikin idon Dikko bayan ya tuno maganganun da An mata ta jefeshi dasu , murmushi mai yagar zuciya yayi tare da kallon kanshi
a madubi yana mai sakeyin murmushi wanda har saida kyawawan haƙoransa suka bayyana.
Wai nine mahaukaci ? Duk dana faɗa miki lalurata amma shine kikemin gori wai aljannu kamar iccen tsamiya kwantar da fuskarshi yayi saman sitiyarin mota a bayyane yace bani ne na ɗorawa kaina ba ƙaddara ne kuma haka yazo rubuce a cikin ƙaddarar rayuwata , ɗago kanshi yayi yaci gaba da kallon gabanshi dan tuƙi yake kuma har yanzu baije inda zaije ba , yaci gaba da addu’a ya ubangiji ka bani lafiya ka yaye min wannan lalurar ka bani haƙurin rashin An mata , goge hawayen daya zobo mishi yayi yana ci gaba da cewa wai duk girmana ni nake kuka wa mace , macen ma An mata ashe dama bata so na , wani irin duka ya kaima sitiyari a hayaniyance yace ni kika yaudara ? Nidai kika yaudara bazan taɓa yafe miki ba An mata kuma Allah bazai barki ba saiya min sakkayya ya ƙarasa maganar hawaye na rigangato wurin fitowa daga cikin kwarin idanuwan shi.
Har ya isa goruba ranshi a ɓace addu’arshi ɗaya Allah yasa kada wani ya hawoshi a dai² wannan lokacin da yake cikin ɓacin rai dan duk wanda yazo yana cikin wannan yanayi zafa a samu matsala , aljannu kamar iccen tsamiya ya maimaita a dai² lokacin da yayi parking , yanayin parking Yazeed ya fara gani ,
Fita yayi daga motar cikin tsananin ɓacin rai fuskar nan a haɗe , Yazeed yana ganin Dikko ya taso cikin girmamawa ya miƙawa Dikko hannu , bai anshi hannu ba yace ya akayi ? Cikin rawar murya Yazeed yace DK don Allah wani abokina ne aka kama wata ƙawarshi ta gayyaceshi zuwa gidanta sai mijin ya dawo ya ritsatsu dan Allah kayi magana yana sabon gari police station ,
(pls mai yasa bakwa mana click akan ads) Wani irin munafikin kallo Dikko yayi ma Yazeed , a hanzar ce Yazeed yaja baya yana kallon Dikko , tsoki Dikkon yayi ya fara tafiya Yazeed yabi bayanshi Dikko kuma yana magana cewe , baku da aiki kullum an kamaku wurin neman mata , nima yau an kamani na kasa fitowa , banyi maganin damuwa na bare inyi ma wani nashi , ina cikin ɓacin rai ka kama gabanka tun kafin in fara ƙwallo dakai….
DK ka duba lamarin nan don girman Allah kayi wani abu akai matsalar babbace , da sauri ya juyo yace kai……….. Ka wuce fa , ganin idanuwan Dikko ba’a launin daya saba ganinsu ba yasashi juyowa da sauri ya dawo baya yana tunanin halin da abokinshi yake ciki.
Matsala ce ta neman duniya shi abokin nashi yana da wata buƙata akan wasu harkokin shi nayau da kullum shine malaminshi yace sai ya samo maniyin matar aure kuma saiya nemi matar a gidan aurenta a saman gadon da mijinta yake kwanciya da ita , a jikin hankicif kawai ake so a gogo sperm in shikenan zance ya ƙare , amma zai dawo zuwa anjima idan Dikko ya sauko , zuciyarshi tace a , a kawai kaje wurin Sultana a gabanka zatayi masa waya a wuce da damuwar nan , kai tsaye Yazeed gidansu Sultana ya nufo !
A halin yanzu zuciyata ta cika fal da Dikko , muradina shine naga na haɗu dashi maganar gaskiya so nake na kasance dashi domin inajin Dikko kamar wata runduna ta tsagin rayuwata idan har na bari Dikko ya tafi na shiga3 na tawa ta ƙare , fashewa nayi da wani irin kuka a toilet nace ina sanka ׳ mutumina…..
Sai ihu nakeyi a toilet babu mai jina saboda gidanmu cike yake da mutane “yan kawo lefe , kuma gashi gobe idan Allah ya kaimu ɗaurin aurena wanda za’a ɗaura 2:00pm idan Allah ya kaimu , saida nasha kukana har na gode Allah na fito daga toilet ko mai ban shafa ba na saka kayana , wayata na ɗauka na fara kiran wayar Dikko ,
Ɗauka yayi amma baiyi magana ba , cikin kuka nace Dikko gobe ne fa ɗaurin aurena , Ey ai kin faɗamin jiya da daddare ko kin manta , a , a ban manta ba ƙara tuna maka nayi fa , ina sane ban manta ba , to baza kayi wani abu ba ? Wani abu kamar me ? Shiru nayi ina kuka na kasa magana , Dikko yace Allah yasa alkairi ya baku zaman lafiya ina tayaki murna sosai yana faɗin haka ya tsinke wayarshi….
Wani irin ihu nayi wanda ya jawo hankalin duk wanda ke cikin gidan sukayo ɗaki wurina kowa yana tambayata lafiya ? Kamar baƙuwar mutane haka naci gaba da kallon mutane ɗaya bayan ɗaya cewa ya akayi ne ? Munji kina kuka ne , murmushin ƙarfin hali nayi cewa ba komai ni ba kuka nake ba wani abu ne ya faɗamin a ido , kowa Allah ya sawaƙe yayimin sannan suka fita.
Hijabi na saka na fita wurin Sultan dana baro a mota yana zaman jirana , dakel na ƙaƙaro farin ciki na isa wurinshi amma yanzu ban shiga motar ba a waje na tsaya , ki shigo mana , a , a , haka yayimin , bawan Allah ko murmushi baya gajiya dashi yace kodai naje na barki ki huta ne ? Cike da zumuɗi nace Eh , tada motar yayi yana cewa zan anso miki kayanki kinsan jiya mukayi dasu , godiya nayi masa tare da mishi addu’a Allah ya tsare hanya dan na matsu ya tafi wurin Dikko nake so naje , ina tsaye a wuri harya fita daga gidan yana fita motar Yazeed yana shigowa .{{{}}}
Inda Sultan ya ɗauke motarshi a wurin Yazeed ya ajiye nashi tare da sauke gilashin gefenshi An mata wurinki nazo , ai na sani tunda na ganka gidan nan dama nasan saboda nine kazo , to dan Allah ki shigo wani wuri zamuje muyi magana naga gidanku cike da mutane , babu wani jayayya ko tambayar ina zamuje na zagaya na buɗe mota na kame a gaba Yazeed yaja muka bar gidanmu!
Iyalin Dady suna cikin tashin hankali da damuwa dan tun jiya suke neman Dady babu shi ba labarinshi kuma wayayonshi duk a kashe suke , saƙo da lungu nemanshi ake amma babu wanda yaji ko ɓirɓishin inda yake , cikin kuka Momy tace saika tafi ka saƙe duk ka tashi hankalinmu ? Ka tafi babu bankwana shin wai kana ina ne ?
Wani irin gumji Dady keyi bayan an ɓanɓare Dikko dakel daga jikinshi yace baza ku faɗamin gaskiya ba ko ? Bello da wahala tasashi ya koma wata siffa daban tsakanin ranar daya yayyanki Sultana da wuƙa zuwa yau yace ranka ya daɗe wallahi shine yasa ni , yayin da shi kuma Dadyn yake cewa ƙarya Bello ke masa shine Dikko ranshi ya ɓaci yacicci ubansu yana cewa bazasu faɗa masa gaskiya ba suna masa wasa daa hankali ko ? Ya ƙarasa maganar yana ƙara kaiwa Bello halbi a baki.
Cikin kuka Bello yace wallahi bani bane shine , Dady yace wallahi ƙarya yakemin shine tunda shi ka kama da wuƙa kuma shi idonka ya gani ya yayyaka mata a jiki ni misali idan ma har zanyi kisa zan faɗawa wani ne ? Koshi sakaraine baisan shari’a ba ? Me yasa da nace yaje ya kashe ta baije ya faɗawa hukuma ba ? Ko zan hura wuta nace masa ya shiga yaje ya faɗa ? Idan har ka duba wannan abun kasan duk ƙarya ne sharri kawai yake nemana dashi bansan abinda nayi masa ba !
Bello ganin Dikko yaɗan so karɓar uzirin Dady yasa yace to ranka ya daɗe tunda naga kanshi ya sani baisan nawa ba kuma naga yana ƙoƙarin fita ni ya barni a ruwa bara na buɗe maka gaskiyar abun yadda shike….
Labari tiryan² Bello ya zayyanawa Dikko kuma ya ƙara da cewa kuma kwalbar da ita matar taje ta ɗauko yanzu haka tana hannun shi , wani irin ihu Dikko yayi yace saina kashe ku………….. Wayyo , wai…… Wai , wai Allahna , kai……….. Wai , saina kashe ku wallahi kaine ka mayar min da matata daƙiƙiya ko ? Zai fara duka su Ashiru suka danneshi ƙasa dakel saboda ai har yanzu akwai munafirci a maganarsu abinda su suka fahimta kenan , ya akayi kwalbar ta dawo hannun Bello bayan shi yace wata tazo ta ɗauki kwalbar kuma an bada ita wa wani malami ? Shi malamin ya akayi yasan Bello kuma ya bashi kwalba ? Dole bazasu bar akashe su Bello ba Sultana ya kamata a nemo kuma a nemo inda matar data ɗauko kwalba take , bayan ankai Dikko ƙasa Ashiru ya koma mota da gudu ya ɗauko magani har yanzu Dikko zubar da yaranshi yake duk girmansu duk ƙarfinsu tuni tsoro yasa Dady suma shiko Bello yayi fitsari baisan adadi ba , sunga bala’e da masifar daya girmi nasu , dakel aka sake kai Dikko ƙasa aka zuba mishi magani dole tasa ya ɗauke….
Fiddoshi sukayi suka kaishi mota aka sake kulle su Bello sai mai gida ya dawo , Bello kuma maimaita kalmar matata kawai yakeyi , har yaushe Dikko ya auri uwar masu gida ? Lallai akwai bala’e ɗiyar Binna zata zama matar ɗan gwamna ? Surukar gwamna ? Sam wallahi abinda bazai yuwu ba kenan an ɗaura auren ko kuwa ? Wannan ansar ita ya kamata na fara sani farko kenan ,
Kwance zariyar wandon shi yayi ya matsa kusa Dady yayi masa fitsari a fuska , nan take ya farko , ɗaure wando yayi yana cewa zaune fa bata ƙare ba matarka ba ƙawar matar gwamna bace ba ? Cikin jin haushi Dady ya tashi ya kama Bello da kokowa yana cewa ni zaka zubawa fitsari ? Bello yace kai da Allah dan ka farfarɗo akwai sauran rina a kaba fa , saida suka caku suka rabu da kansu , cikin wahaltuwa Bello yace kaji wani aikin kuma ko ? Tou idan baka sani ba ɗiyar Binna ta zama matar ɗan gwamna ,
Da sauri Dady yasa hannunwan shi biyu ya goge fuskarshi tare da yarfarwa , yace aure ? Ta auri Dikko ? Yayi maganar yana fiddo duk girman idanuwanshi , Bello yace ba kana can ka suma ba yace matata kuka mayar min daƙiƙiya yace duk saiya kashe mu , Dady yace sam ba’ayi aure ba , Bello yace idan ba’ayi ba kenan ai zaice budurwarshi , tunda kuma anyi sai yace matata , Dady yace idan anyi auren nan saina rabashi idan kuma ba’a ɗaurashi ba babu ubanda ya isa ya daurashi duk cikar faɗin birnin garin katsina….
An mata kin fito da wayarki ? Yazeed ne yake tambayar Sultana ko wayarta yana hannunta bayan ya samu ƙofar wani gida yayi parking , E na fito da wayata na bashi amsa , An mata dan Allah ki kira DK kice masa yayi waya a sakar min abokina , daga ina za’a sakeshi ne ? Yana sabon gari police station kamashi akayi , laifin me yayi aka kamashi ? Gonar wani ya aura kuma ya samu damar tattare kaf amfanin gona , to ya akayi harya tsaya aka kamashi ? Yankin ya shiga ba ita matar tazo nashi yankin , kaima Yazeed wannan ai ganganci ne , Eh An mata amma dan Allah kiyi ma DK magana yasa a sakeshi , murmushi nayi mai ciwo nace Yazeed zanyi masa amma me yasa wai suke san fasiƙanci da matan aure ne ?
Mafi yawancin matan auren sune suke miƙa kansu wa mazajen waje ta hanyar ɓoye kawunansu su masu aure ne , kowa da irin matsalar dake shigar da ita bariki da aurenta , wasu rashi ne na talaucin abinda zasu ci ko sha , wasu kuma rashin basa samun gamsuwa ne wurin mazajensu , wata kuma tana da komai babu abinda ta nema ta rasa kawai ra’ayi ne ,
Tou su mazan me yake sa suna neman matan waje bayan ga nasu matayen a gida , gyara zama Yazeed yayi cewa mafi yawan mazan waje masu neman matan aure suna nemansu ne saboda matsalolin matansu na gida , wasu kuma suna neman matan aure ne saboda neman wani abu na samun duniya , me yasa dole sai a matan aure ake san samu ne ? Duba girman aure kuma ki tuno daraja wacce Allah yayi masa duk wanda ya ɓata matsayi da darajar aure ya halaka , nidai kira DK a fiddoshi , kayi haƙuri Yazeed gaskiya ni halin yanzu bana tare da Dikko , me yasa ? Haka nan na fita daga rayuwarshi ne dan ina so nima ya fita tawa rayuwar , wai miye tsakaninku ne ? Murmushi nayi a zuciyata nace anzo wurin , kallon Yazeed nayi cewa to kai a naka tunanin meye tsakaninmu ?
Wata “yar munafikar dariya yayi yana cewa muje kawai na maida ke gida yanzu banda lokacin magana dan hankalina baya kwance amma zamuyi magana daga baya , yayi maganar yana taka motar muka tafi , saida muka isa gida sannan mukayi magana dukanmu , Yazeed yace zai kawomin wata ƙawarshi matar aure ce amma tana wasan danbe , kinsan miye danbe ? Ya tambayeni ? Nace masa a , a , Yazeed yace aiko yadda kike hakan nan kika shiga harkar danbe abin zai miki daɗi zaki taka matakai masu girma zaki fito duniya zata sanki kuma sai kinfi ƙarfi DK wallahi ,
Murmushi nayi tare da cewa in banda abinka taya zan iya raba fili inyi wasan danbe da ƙatti majiya ƙarfi ne ? Murmushi Yazeed yayi cewa ba irin waccan danben ba , kawai kidai kije zan turota tayi miki bayanin yadda danben yake , fita nayi daga motar ina cewa Allah yasa tazo lafiya , da amin ya ansa ya fita gidan da gudu lallai yana tare da damuwa , bin bayan motar Yazeed nayi da kallo nace ɗan raini kenan kamar yadda nake kallon kaina a madubi haka nake kallon inda ka nufa , murmushi nayi tare da tinkarar hanyar shiga cikin gida da sauri.
Ina shiga palo Inna na fara gani ta kame saman kujera an wani waye an goge ta fito cikakkiyar hajiya ga haƙorin makka tasha kuma wallahi yayi mata kyau sosai , da gudu na ruga na rungumeta na fashe da kuka , cikin jin kunya take ƙoƙarin rabani da jikinta tana kallon idanuwan mutane ita a dole sai tayi alkunya irin tasu ta fulani , ke saukar min a jiki cikin kuka na sauka ina kamo hannunta cewa Inna zo kiji , da yanayin tausayi ta kalleni ta taso kuma ta biyoni , ɗakina muka shiga muna shiga na rufe ƙofa na sake ɓarkewa da kuka nace Inna nidai tsakani da Allah bana san auren nan…..
Cikin tashin hankali ta kalleni tace Sultana ki rufamin asiri wannan maganar ma ki barta tun farko , ni gaskiya bazan barta kawai kice wani abu na rantse da Allah bana aurenshi nidai bana sansa kawai biyayya nayi ma Kawu nayi tunanin zaicemin ko ina da wani da nakeso amma sai bai tambayeni ba , Inna tace aiko dai ko zaki mutu wallahi auren nan babu fashi ni zaki tona ma asiri dan ubanki , kinsan bakya sansa uban wa yace tun farko kika amsa musu , bakisan halin mutanen ba kina wasa da sha’aninsu ko ?
Cikin hayani nace nima kina wasa da nawa sha’anin bari in fita na faɗa musu bana san Sultan , Sultan in banza Sultan in wofi , wani irin wawan mari Inna tayimin , kamar zan hau bori nace wallahi bana auren Sultan saidai ki kasheni , to na yadda saidai ko ki mutun , aiko bana mutuwa zanje na faɗa musu bana san Sultan tunda ni ba tsoronsu nakeji ba na tunkari hanyar fita zan buɗe ƙofar ɗakin , fizgoni tayi ta maidani saman gado ita kuma cikin damuwa ta buɗe ɗakin ta fita ta kulle da makulli ta waje , da gudu na sauka daga gado naje jikin ƙofar naci gaba duka ina cewa bana so ׳ wallahi ,
Inna kuwa palo ta koma ta ɗauki wayarta ta kira Dikko , yana ɗauka ta fita waje bayan sun gaisa tace da Allah na dawo kazo ina san ganinka idan baka komai , lafiya dai Mama ? Ya tambayeta , gaskiya ba lafiya Sultana tana so ta sake tado min wata fitina da “yan uwana , bayan an tsayar da ranar aurenta duk kwanakin da suka wuce batace ta fasa ba saboda Allah saida taga gobe²n nan ɗaurin aurenta Dikko tace ta fasa ? Na rasa ya zanyi duniya Allah yayi ma Sultana taurin kai , murmushi Dikko yayi tare da cewa me ne ne matsalar ? Nidai kazo yanzu²n , zanzo idan anyi isha’e , a , a Dikko yanzu dai , gani nan zuwa……..