NOVELSUncategorized

KWARATA 72

      Cikin ƙanƙanin lokaci Dikko ya iso Inna tayi  masa jagora har ɗakina , Dikko yana da raini tsabar rainin shi duk mutanen dake palon ko ɗaya babu wadda Dikko ya gaishe da , haka ya wuto su yana musu kallon ƙyankyanmi fuskar nan haɗe kamar hadarin tsakar dare har ɗakina , ina kwance saman gado ina ta kuka dan na gaji da bugun ƙofa har na koma na kwanta.

      Bayan sun shigo ne naji Inna tace ina zuwa ta fita , shi kuma ya shigo cikin ɗakin har bakin gadona kuma bai cire takalmin ƙafarshi , kallo ɗaya nayi masa na juya mishi baya naci gaba da kuka , jawoni yayi daga saman gadon na fizge na koma na kwanta , cikin rarrashi yace zo inji waye ya taɓamin An matana ? Taho ya miƙo hannunshi , saukowa nayi daga saman gado naje kusa dashi na tsaya , kallona yayi sosai sannan ya kamo hannuna na dama ya ɗora saman kafaɗarshi ya riƙe tsakiyar bayana yace kallarni yayi maganar yana murmushi , kallonshi nayi ina kuka , wai me ne ne ? Dikko ya tambayeni , kwanciya nayi saman ƙirjinshi nace bana sansa , ke yar raini bana so kinaji na ? Kinga zaki tayar da hankalin Mama kiyi haƙuri kinji jaruma ta ?

     Dikko nidai bana sansa don Allah nayi maganar cikin kuka sosai ina mai ɗagowa na kalleshi , ƙarya kikeyi da bakinki kika faɗamin kina sansa kuma na tambayeki yayi miki kika ce min yayi sai yanzu kice kin fasa ? Baya yuwuwa wallahi duk wanda ya tsaya miki sai an ɗaura auren nan kuma babu gudu babu ja da baya , wallahi ko na tafi kika sake cewa bakiyin auren nan zanzo in tafi dake goruba jawoni yayi a jikinshi sosai sannan ya shafa bayana da lallausar hannushi yana cewa zakiji a jikinki , da sauri ya ɗagani jikinshi jin ana shigowa.

      A dai² lokacin da Inna ta shigo tana ta faɗa cewa ai dama nasan duk yadda akayi Sultana tana da maziga ashe wai wani tsinan yaro ne ɗan mara mutunci take tare dashi , kusa dani ta matso ta yayyanka min mari tana cewa meya haɗaki da Dikko ɗan iska yaron da baya ganin kowa da mutunci garin nan , ke banda kike jaka marar tunani duk wulaƙanci da tozarcin da Dikko yayi muku kin manta ? Tou idan kin manta ki tuna saida Dikko ya haramta muku mazaunin gida , gararin rayuwa wane ne bakuyi ba sanadin shi ? Ki rasa abokin tarayya sai mutumin da silarshi kika yanki tikitin shiga karuwanci , sassauta murya tayi cewa ban san Dikko na tsaneshi matsashi mai ɗagawa da baisan darajar kowa ba , yau da zanga Dikko dasai na ɗauki wuƙa na soka mishi a ciki ya mutu tsabar wutar ƙiyayyar shi dake ci a cikin zuciyata ,

     Kin samu za’a rufa miki asiri wawiyar banza a aureki amma da yake ke jakace har kike tunanin zaki ce kin fasa idan banda ma Allah yasa Sultan ɗin mai imani ne an faɗa miki zai iya aurenki ne ? Tou Allah ya rufa miki asiri ma yaso ki a haka da duk katsina kin rasa mijin aure , wayata taje ta ɗauko ta kawo ma Dikko tace ka duba cikin wayar ka ganomin lambar ɗan gwamnan ka kirashi yanzu²n nan ka rabashi da Sultana…

      Daga ni har Dikko kallan kallo muke ma juna , cikin jarumta Dikko yace Mama ke baki san Dikko ba ? Ina fa zanso sanin lalataccen yaron nan , to amma waye yace miki yana tare da ya nuna ni , Sultan yake faɗamin yanzu yace ko rashin lafiyar da tayi Dikko shine yake kwana da ita kirawoshi….

      Kallona Dikko yayi sannan ya kalli Inna yace ai ba buƙatar kiran shi , me yasa ne ? Inji Inna , saboda Dikko tuni yazo , yana ina ne ? Nine *DIKKO* kuma nine *DIKKOn* da kike nema……….. Gani nazo!


CLICK ON THE ADS PLS

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button