KWARATA 88

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ ????????
*ASMA’U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI’ATU AMINU MAMMAN DEE*
???? —— 86
Ya za’ayi Al ‘ Ameen ni yayi min wani abu ? Tou me mutumin ya faɗa mata ? Ina yasan Al ‘ Ameen ? Me yasa ni kuma Al ‘ Ameen zai zama jagorar matsalata ne bayan dashi ake nemamin magani , mi yasa dole sa a mafarki zai bawa An mata labari ? Ƙarar wayarshi ya dakatar dashi daga tunanin daya tafi , Momy ya faɗa tare da ɗaukar wayar suka gaisa , Dikko kana ina ne ? Ina nan bisa titi , ina zakaje a safiyar nan ne ? Zanje gida , wane gidan ? G R A , daga ina kake ne ? Goruba , daina tambayar tayi cewa Dikko kazo ina neman ka yanzu²n nan , cike da damuwa yace me kuma akayi miki ne ? Dikko nidai tafiyata zanyi na gaji da zaman haƙuri , kuma fa bata iya tafiya ko ina ta bar Dady , Momy kiyi haƙuri dan Allah,
Ni bazanyi ba , tunda ka tafi da Al ‘ Ameen jiya Bilki ta hana gidan nan zaman lafiya ta turo “ya “yanta sai rashin kunya sukemin dan taga ba kowa cikin yara duk su Nabeela suna wurin Jiddah ko nice zan fita inyi faɗa da Yara ne ? Nidai nasan nafi ƙarfin Bilki daga ciki har waje wani iskanci saida tasa yara suyishi , cike da damuwa Dikko yace Momy dan girman Allah kiyi haƙuri , wallahi bazanyi ba saidai idan Bilki ta koma uwarka sai in ƙaleka dama kwanaki dana faɗa maka ta zageni kace zakayi mata magana bakayi mata ba sakaran banza mara kishin uwarshi tana faɗin haka ta tsinke kiran.
Innalillahi wa’inna ilahir raji’un ya faɗa tare da samun gefen titi yayi parking , wayar Ashiru ya fara kira , Ashiru kuwa yanaji yana gani yaƙi ɗauka dan Umar ya bashi labarin abinda mai gida yayi a jiya kuma dama yasan tunda ya ɗauko Al ‘ Ameen saiya fuskanci matsala tou shi ya za’ayi ma yace ma Dady baisan inda Al ‘ Ameen yake ba taya zaice kuma bazai ɗauko shi ba ?
Yana ajiye wayar zai tashi motar text in Ashiru ya shigo , kayi haƙuri mai gida Dady yasa na ɗaukoshi kuma na kira wayarka a kashe ka gafarceni nasan ban kyauta ba , tsoki Dikko yayi tare da ajiye wayar saida ya fara tafiya ya fara kiran wayar Dady.
Cike da fargaba ya ɗauki wayar yace Babana lafiya ? Dan shi a tunanin Dady ba lafiya shi yasa Dikko ya kirashi a safiyar nan , Dady wai me nayi maka ne ? Babana ba komai , tou me yasa za’a hanani na zauna lafiya ne ? Da sauri Dady ya tashi daga kwanciyar da yake yace me akayi maka ne ? Horn Dikko ya danne ɓiyyyyy , Dady yace a , a Babana , Dady kawai zan mutu na huta , yi haƙuri Babana² dan Allah tashi tsaye Dady yayi cikin tashin hankali yace wai ina damuwar take ne ? Me yasa kasa aka taho da Al ‘ Ameen ne ? Yadda sukayi da Bilki ya faɗa masa , kashe waya Dikko yayo bai sake magana ba ya ajiye a gefe , me ne ne tsakanin Al ‘ Ameen da matar uba wai ?
Ko dan yace zaice ya kama Al ‘ Ameen a ɗakinta ne ? Tou kodai ? Karka yi zargi zuciyarshi ta faɗa masa , to me ya shafeta da lamarin Al ‘ Ameen haka da yawa ? Dama kwanaki daya dokeshi itace tayi video ta turawa Dady , yanzu kuma shine tasa akaje aka taho dashi ko ? Maganar Sadiyya ta dawo mishi a zuciyarshi an haɗa kai dashi da matan uba an maidakai lusarin namiji , ni kuma yayi nasara akaina yakai min rayuwata ƙarshe , ka tattaro kaf yaranka har wanda suka daina maka aiki ka kawosu idan na ganshi zan ganeshi { Suwaiba } , wallahi mai gida ba abinda ya haɗani da ita kawai dai tana aike na ne na samo mata asiri tana san ganin bayanka , { Al ‘ Ameen } , a , a Dikko da gaske ne wallahi , { An mata } , banda ƙaryar bacci to me ya kawo Al ‘ Ameen a mafarkinki ? Dady kuwa sai kiran wayar Dikko yakeyi amma yaƙi ɗauka dan haka ya kira Momy yace mata yasan itace ta ɓatawa Babanshi rai har so nawa yace su daina saka “ya “ya a damuwarsu basa bari , me yasa suke san ɓata mishi gida ? Kullum yana ƙoƙarin haɗawa su kuma suna rusawa ? Wai me yasa sukeyin abu na rashin tunani haka ? Tou wallahi tayi kuka da kanta dan zai mata rashin mutunci idan wani abu ya sami Babanshi.
Da wani irin ihu ya shiga inda ƙannen shi suke kaf dan duk irin wannan lokacin basa bacci zasu zauna sai bayan 6:45 su tashi idan da makaranta kenan haka wannan tsarin yake ko bakya sallah duk idan akayi sallah kaf “yan gidan sai sun haɗu a wurin amma “ya “ya ƙananansu da manyansu idan dai ɗan da Dady ya haifa ne harshi Dikkon , kuma ko aure kikayi idan dai kika zo gida sai kinyi wannan zaman tunin duniya haka suke haɗuwa kuma ba addu’a akeyi ba , ba karatu akeyi ba zasu haɗu dai kawai su zauna a wurin suyi fira ne , idan kuma ranar da babu makaranta sai 7 suke tashi , saida ya zane kowa a cikinsu duka bana wasa ba amma ƙannenshi bai daki yayyenshi ba kuma babu wanda baiji ma ciwo a cikinsu ba ya ɗora da cewa daga yau idan wata ta sake shiga cikin faɗan iyaye saiyabi ta kanta da mota ya wuce “yan iska marasa kunya , dakel aka fito dashi daga wurin yana cewa suma su Nabeelar duk saiya ci mutuncinsu wallahi ba babba ba yaro duk wani ɗan daya sake shigar ma uwarshi faɗa a gidan nan shine zan kawo ƙarshen rayuwarshi…………
Sai kuka sukeyi , shi kuma ƙwacewa yayi ya nufi ɗakinsu , a falo ya samu Momy ta kashe saman kujera ta murza wani irin ɗaurin kallabi mai burgewa dan fita zatayi zuwa wurin Dady parking in da Dikko yayi yasa ta koma ta zauna tana ta gunewa , kusa da ita ya zauna ya riƙe duka hannayenta yace Momy dan Allah ki daina damuwa , nuna kanshi yayi da hannu ɗaya ɗayan kuma yana riƙe da hannuwanta yaci gaba da cewa idan ina nunfashi babu wanda zai isa yasa miki damuwa kuma babu inda zakije mu muna tare dake nima ina tare dake Mamana Dady nawa ne shima yana tare da duk abinda nake so kiyi haƙuri baza a sake miki abinda zaisa kiji damuwa ba , cikin sanyin murya tace Dikko ya za’ayi yara su riƙamin rashin kunya idan nayi magana sai ace banda haƙuri , ba tun jiya na faɗawa Dadyn naku ba yace wai bana san zaman lafiya , yi haƙuri Momy fushi yasa ya faɗi haka , me yasa baiyi fushi ya faɗawa Bilki ba saini mareniyar wayanshi ɓacin rai yasa Momy taita maganganu Dikko dai tsareta yayi da ido bai sake magana ba , wato ita dai mace duk shekarunta idan tayi wani abun saidai ace Allah ya sawaƙe ,
A mota ya ɗauketa suka tafi wurin Dady , shima ranshi yayi mishi zafi sai faɗa yakeyi yana kuma ƙara ɗora laifin a wurin Momy itace ta fara koyawa yaranta rashin mutunci kuma ai itace ta fara nuna rashin san zaman lafiya a matsayinta na babba , murmushin ƙasaita tayi tace ma Dikko yaje ya jirata falonta tana zuwa , saida ya gaisa da ya fita , Dady kuwa yabi Dikko da kallon soyayya harya fita , ×××××××.
Tunda Dikko ya fita Hafsa ke kiran wayata naƙi ɗauka ta dameni sosai dan haka na ɗauka bayan mun gaisa tacemin wai na fasa zuwa ne ? Ina ne na fasa zuwa ? DK bai faɗa miki rasuwa ba ? Waye ya rasu ne ? Kakar Babanku duk “yan gidanku suna can yau ake addu’ar 3 muma yau zamuje , wace ce kuma Kakar Babanmu ? Wacce ta haifi Maman Babanku , ke ina kika santa ne ? Kaka Sahura ta faɗa man inda take ni naje na gano wurin nakai “yan gidanku , ranar da mukaje na dawo na barosu can a ranar ta rasu , dan lokacin da zamu tafi na kiraki DK ya ɗauka yace baki lafiya sai muka tafi data rasu kuma na kirashi yace idan kin samu sauƙi zai kawoki , tou Allah ya jiƙanta na faɗa a tsiwace , dan Allah kiyi ƙoƙari kuje yau kuma duk “yan uwa sun haɗu kiga dangi kema , shi yasan wurin ne ? Ey nayi masa kwatance ranar dana kirashi na faɗa masa rasuwar , { wato ranar da aka sallamoni daga asibiti kenan } tou me yasa bai faɗamin ba , zan gani ina faɗin haka na tsinke kiran ,
Gaskiya fa ya kamata naje ko dan nuna soyayya wa kabarin Babana , Allah ya jiƙanka Babana yasa ka huta nayi rashin ka a duniyar nan shi kenan ka tafi inda bazan sake ganinka ba har abadan duniya , ka tafi tafiyar da babu dawowa shikenan ka tafi ka barni…….., dole naje wurin ahalinka ko dan jaddada soyayya a gareka Baba na gari , kai sarkin fushi zakaje ko bazaka ba ne ni naje ? A dai² lokacin dana fara kiranshi , saida ta tsinke bai ɗauka ba , sake kiranshi nayi itama saida ta kusa tsinkewa ya ɗauka da abinda bana so wai ya akayi ne ? Dikko koma ya akayi ai zakaji yanzu , dan yadda akayin ne yasa na kiraka , ke karki min rashin kunya kinji , ba wannan ba ni zakaje ko ka fasa zuwa ne ? Ina ? Ba Hafsa ta faɗa maka rasuwa ba shine sai kace saina samu sauƙi bayan ni lafiyata qalau , ni bazanje ba sai kin dawo , tou babu damuwa ngode , ina faɗin haka na tsinke kiran , wayar Inna na kira , cikin hukuncin ubangiji kuma ta shiga amma bata ɗauka ba , ci gaba nayi da kira taƙi ɗauka ,
Dikko na sake kira , bayan ya ɗauka yace ya akayi ne ? Dikko na kira Inna kuma ta shiga amma bata ɗauka ba , da kyau , daga haka bai sake cewa wani abu ba , kaji , naji , tou kace wani abu mana , ai shine nace nace hakan da kyau , nidai baka so na , baka damuwa da abinda yake damuna , ni bansan abinda yasa kake min haka ba na faɗa cikin hayaniya ina kuka , duk saida na safke mai isata sannan yace tou yi haƙuri An mata gani nan zuwa zan miki abinda kike so , tou me yasa ni kake min haka ko ka daina so na ne ? Ina sanki mana tayama zaki fara wannan tunanin ? Bana fata kuma bana tunanin akwai ranar da zanji sanki ya ragu a zuciyata , kiyi haƙuri ki bini da addu’a har ubangiji ya yaye min damuwata dana tuno da abinda yake damuna sai inji raina yana ɓaci shi yasa a ko wane lokaci nake miki magana hayaniya² , kana ina yanzu ? Ina nan inajiran Momy data sallameni zanzo wurinki ai haka yayi miki ko ? Ey , to baki ce kin gode ba , murmushi nayi tare da cewa godiya nake mutumina , yawwa jarumata ngode yana faɗin haka ya tsinke kiran , bin wayarshi yayi da kallo yace mata kenan , ita ba abinda ya dameta shin ina lafiya ? Ko ina cikin yanayin fushi me ya sameni bayan na fito babu ya hanya ba komai itadai burinta ayi mata dai² , zan faɗa mata ba’a kiran miji kai tsaye a faɗa masa damuwa sai an tabbatar da yana cikin natsuwa.
Momy ta daɗe bata dawo ba , har Ashiru ya iso gidan danshi zai maida Maman Jiddah tunda Al ‘ Ameen bashi nan kuma tsarin nan Momy ce ta tsarashi shi kwata² Ashiru baisan Dikko yana nan ba , ita kuma Maman Jiddah tana gama shirinta ta fito falo dan Momy tayi mata waya cewa wanda zai kaita ya iso itama tana zuwa yanzu , shine tayo parking ta bayyana a falon , cikin girmamawa da mutuntawa Dikko ya gaishe da surukarshi….
Ba yabo ba fallasa ta ansa tana ta riƙe fuska , ko inda take bai sake kallo ba , ita kuma taci gaba da cunkusawa cikinta abinda ta samu an ajiye mata dan karin safe tunda zata ibi hanya ko kunyar sarakuta babu , Dikko kuma fita yayi ya koma mota yana jiran Momy , yana zama yaga Ashiru yasha ta baya da gudu , tsoki yayi tare da kallon agogon jikin waya 8:39am kuma har yanzu Momy bata fito ba shawara ya yanke kawai ya fara ganin Jiddah kuma suma su Nabeela ya zanesu kamar yadda ya zane “yan uwansu zaije ya dawo kafin ta gama ta fito , tashin mota yayi ya nufi gidanshi….
Yana fita Momy ta iso taga babu Dikko kawai ya wani ɓace abunshi , Momy kuwa tana shiga wuri ta samu ta zauna tana ma “yar uwarta magana , amma ke dake gidanki idan kin tanka tou Maman Jiddah tayi magana sai wani cika take tana batsewa , Momy taji ba daɗi amma ta haƙura ta kanne dan abu na “yan uwan taka dole sai an haɗa da haƙuri da kuma kai zuciya nesa , data tashi tafiya duk abinda Momy ta bata cewa tayi ita ba baƙuwar arziƙi bace ba tafi ƙarfin ita ta bata wani abu ta ansa ta riƙe kila zasuyi mata amfani wurin nemawa Dikko rubutun danga na , Momy tace wane irin rubutun dangana kuma ? Maryam gaskiya ni na kashe wannan auren , cikin tashin hankali Momy tace Yaya don girman Allah kiyi haƙuri wai miye matsalar ne ? Kuɗi , banbancin kuɗi ne ke naki ɗan gwamna ne ni kuma gwamnan zata aura gaba ɗaya , zaɓe yana tunkarowa bana tunanin ku zaku sake zarcewa siyasa zata wurgar daku a can tsohon gidanku gidan gwamnati kuwa zai zama na masu rabo ,
Momy tace mu kenan masu rabo ni inaji a jikina munci kuma sai mun sake wannan zaman darajar manzan Allah S. A. W gidan gwamnati sai mun maimaitashi , maganar kuɗi kuma ba damuwar Dikko bane ba saboda shi basu ne gaban shi ba yana dasu yadda tunaninki da ƙwalwarki basu ɗaukar misali dan dayabi izzar kuɗi da mulki wallahi Jiddah bata kai mace ba a wurinshi , Maman Jiddah tace aiko ke kinsan Jiddah mace ce hada gyara gwamna da kanshi yake santa gwamna fa ? Shin ke kin raina gwamnati ko ? Ban raina gwamnati ba amma nima na san nawan tunda ya fara saiya taka matakin da bakya tunani , da haukan zai taka matakin da har ni bana tunani ? Momy tace ba mahaukaci kuma ba hauka Dikko duniya , zamani ɗaya tak a ƙarni matashi mai sa’ar rayuwa , yaro da kuɗi abokin tafiyar manya , mahaukaci da kuɗi kuma mai maihankali babu , gwamnan da kike tunanin kashe auren Jiddah saboda shi tun kafin na ganshi nasan waye shi na tabbata duk kuɗinshi shi 30 baya Dikko ɗaya , yadda baki tunani Dikko ya kafu shi kanshi ubanshi alfahari yakeyi dashi yace yasan ko bayan baya raye zai tallafi “yan uwanshi shi yasa ya dage saida ya tabbatar ya gina Dikko sosai , amma duk da haka shi kuɗi basu ne gabanshi ba shi yasa yake rabar dasu kamar hauka , abinda yasa na kafe sai Dikko ya auri Jiddah dan naga wasu sunci ma bare nawa bana san ya baku² shi yasa na haɗa auren Jiddah dashi , dan nasan Dikko bashi da mutunci idan nice yau gobe bana nan na gina ku ne ku “yan uwana ko bayan bana raye arziƙin Dikko bazai muku wahalar ci ba saboda akwai Jiddah , amma idan har kika kashe auren nan kuka bar bare kuka hana zuminci wallahi gidan Dikko raɓe zaku zama , kuna iya zuwa ma tace muku baya nan kuma yana nan ta hanaku ganinshi , kallon banza ko magana mara daɗi kukayi ma matarshi tabbas nasan saiya ya taka muku burki ko kuma ya ɗauki matakin hanaku zuwa gidanshi ba abu bane mai wahala a wurinshi , ni bana miki hassada kuma bana miki baƙin ciki dan “yarki zata zama matar gwamna shawara na baki dai dan kece ya kamata tun yanzu ki daina tunanin kashe auren , a sanyaye tace kuma kece zaki anshi kuɗin nan ki fara nemawa “yarki rubutun dangana tun yanzu , ɗa ɗaya tak ragamar mata idan dai harya kafa soyayyarshi a zuciyar Jiddah tou sorryn ku ina jajanta muku domin ni kaina bansan a ina Dikko ya gaji zuciya ba , da zaran ya yanke hukunci tou fa ko kanshi baya saurara , karki raba domin yadda mukayi zaman nan zamu sake maimaitashi idan har kika tafi da Jiddah wallahi kuma Dikko yasan dalili tou fa tabbas yadda kika ga kiyi sabon rubutu a saman allo bai bushe ba ki tsomashi ruwa ba tare da kin murza ba rubutun zai sauka to haka Jiddah zata wanke a cikin zuciyarshi ko matalwa batayi , shawara ya rage naki neman rubutun dangana da mafita yana wurinki…..
Tana faɗin haka ta wuce ciki abunta , Maman Jiddah kuwa fita tayi dan Ashiru ya fitar da duk wani abu nata , haka ta fita waje taita tata ruwan rashin mutunci wai Maryam tana mata hassada mai takarar gwamna yana san “yarta take jin zafi , kurar Momy ta riga tayi kuka shi yasa kowa yake ganin Momy bata kyauta ba abu har ga “yan uwanta ashe ba’a kishi ba har “yan uwanta bata raga musu ba , saida ta gaji da tonon sililinta tayi ta tona musu asiri dan wasu basu iya riƙe ɓacin rai ba idan suna fushi sai su manta da abinda gaba zaiyi su kulle idanuwa suyi ta wulaƙanci na rashin lissafi , ko a mota haka ta ci gaba wulaƙanci su “yan gadon rashin mutunci , duk yadda Ashiru yaso ya nuna mata waye Dikko idonta ya rufe ita mai takarar gwamna kawai kuma saita kashe auren , da ɓacin rai suka isa G R A lokacin Dikko harya zane su Nabeela suma ya farfasa musu jiki ya wuce wurinsu Al ‘ Ameen.
Haka ta tisa ƙeyar Jiddah hada Mardiyya suka kama hanyar Kaduna , Dikko baisan wainar da ake toyawa ba , Momy kuwa tayi kukan baƙin ciki bata nunanin idan bata raye wannan karuwar zata bar Dikko yayi zuminci da “yan uwanshi , dole a sake nema ma Dikko wani auren a cikin familyn Dadynshi……
Lokacin da Dikko ya isa Al ‘ Ameen ya dawo kuma ya shaƙe Suwaiba tana ta halbe²n mutuwa , halbi ɗaya Dikko yayi mishi a haƙarƙari ya sake somewa , dakel Suwaiba ta nuna Al ‘ Ameen tace shine , idan baka yadda ba kuma ka tambayi Mustapha zai maka bayanin komai , wane Mustapha ? Mustaphan daka sani kuma saida ya zalinceshi ya munafurce shi yaci zalinshi sos…. Daga haka ta ɗauke Dikko yasa aka tafi da ita asibiti kuma a tsareta , Al ‘ Ameen kuma bazai dakeshi ba saiya dawo…..
Saida ya sake komawa ta gidansu ya tafi da abinda zasuyi kalaci kuma baije wurin Momy ba , sai 10:15am ya isa gida , lokacin harna shirya , bafa inda zakije yarinya , haba ? Ummm , to me yasa ? Bai sake magana ya zauna a gefen gado sannan yace An mata wai me mutumin cikin bacci yake ce miki ne ? Nima bana san wannan tatsuniyar , to wane iri ne ? Na manta , ke………….. Bana san iskanci ni zaki faɗamin kin manta…………….. Cikin ɗaga murya da hayaniya ya faɗa , a tsorace nace kamarshi biyu ce duk na faɗa masa sifofinshi dana sani , tashi yayi tare da kwantar dani saman gado yace me yace miki Al ‘ Ameen yayi mishi ne ? Bai faɗamin ba ka tashe ni daga bacci , danne ni yayi ta ƙarfi yace koma bacci ki tambayoshi abinda Al ‘ Ameen yayi mishi……………… , kyarma jikina ya farayi cikin kuka nace ai bazaizo ba ranakun zuwanshi daban ne a sati sau biyu yake zuwamin kuma ni bansan wace rana da wace rana bace ba , ke…………… Kiyi bacci ko in kashe ki…….. Fashewa nayi da kuka nace Dikko ka ƙyaleni don Allah , zaro ido yayi cikin ɓacin rai yace bazan ƙyaleki ba aradu sai kinyi bacci.
Dikko dan Allah , An mata dan Allah , mintuna 30 na baki kiyi bacci kizomin da duk wannan ansoshin , me yasa baya zuwa sai a bacci ? Me yasa baizo wurina ba sai wurinki ? Me Al ‘ Ameen yayi mishi zai tona masa asiri ? Me yasa yake san ki goge recording ? Me yasa yake kwakwale ido ? Me yasa basu cire naki ba ya kuma nuna miki hanya ta yadda zaki gane zuwa inda kika ce sun binne tsafinsu , me ne ne tsakanin Al ‘ Ameen da Aunty a cikin mintuna 30 idan kuma kika tashi babu wani bayani zan kashe ki kema kin zama munafukata kenan gawarki zan jefar da ita a cikin ruwa kadojina su cinyeki banza kawai dake , kafin in irga 10 kinyi bacci kafin na irga 200 kin tashi kuma zaki bani ansar duk wannan tambayoyin dana aikeki a wurinshi ki samomin……
Fara kiran nombobi ya farayi tuni har na saki fitsari dan nasan wallahi bazai zo ba , wani irin firgitaccen mari ya yankamin har kin isa kiyimin fitsari a saman gado ? Ni zaki ɓatawa ɗaki ? Da duka hannayena na riƙe kumatuna na runtse idona dan bana san kallon Dikko a irin wannan yanayin , shaƙemin wuya yayi yace me yasa kikayi min fitsari a saman gado ? Saina kashe ki na gano ki kema munafuka ta ce ashe , dama kince min saikin ɗauki fansa akaina shine kika zubar da ciki dama ko ? Duk yana cikin ɗaukar fansa , zuwa wurin Yazeed shima ɗaukar fansa ne , yanzu kuma kin ɗaukeni mahaukaci dake za’a haɗa kai ayi min asiri shine zaki rainamin wayau wai a cikin bacci kike gani dan kin ɗaukeni kidahumi ko ? Tou saina kashe ki…………..
Ihu na farayi amma ya riƙemin maƙoshi na fara kakari ina halbe² Dikko yana cewa saina kashe ki tunda kema munafuka ce na tsaneki Sultanar banza Sultanar wofi , faɗowa nayi daga saman gado ni na rigashi zuwa ƙasa daga saman gadon ya ziro hannunshi ya riƙeni Allah ya bani sa’a na tashi da gudu nayi waje ya biyoni yana ihu mai tada hankali , sulɓewa nayi a ƙofar fita falo , wata irin zamiya ya kawo ya riƙeni na tashi da gudu , wuƙa ya ɗauka a saman firij ya jefeni da ita saida ta caki bayana ta sauka ƙasa , hannuna na miƙa ta baya na riƙe wurin , da gudu na gangare falon ƙasa kamar biri ya sauko ta sama ya rigani bayyana a cikin palon , sai ihu yakeyi yana faɗin saina kashe ki……….. Da gudu na koma sama ya sake biyoni yana cewa bana sanki na tsaneki kuma saina kashe ki , tunanin yadda zanyi na fita na rufeshi nakeyi dan idan harna fita waje haka zai bini yana ihu , tausayin Dikko ya kamani sosai kuma na rasa yadda zanyi na fita dan ta ko ina ya riƙe hanya , tsayawa nayi tare da durƙusawa na duƙar da kaina ƙasa na rufe idona cikin kuka nace tou gani na tsaya idan dai har mutuwata zaisa kayi farin ciki na baka fansar raina ka kashe ni ,
Wani irin halbi yakai min saida nayi baya suuuuuu nayi ƙundunbala ina birkitowa na tashi da gudu ashe dai da gasken kashe ni zaiyi , saman benen na koma nace zan faɗa in mutu , ai nine zan jefaki da kaina , da gudu na sauka nayi waje kafin yazo naja ƙofar kai…………. Saina kashe kaina , nidai bansan yadda akayi ba daga haka……..
Fashewa Sultana tayi da wani irin kuka mai tada hankali da gudu mahaifiyarta ta shigo tace kin fara ibadar taki ko ? Cikin kuka tace har abadan duniya bazan daina kukan rashin Dikko ba , ina sanshi ׳ ina ƙaunarka mutumina , saida tasha ihunta harta gode Allah sannan tace Dikko zamani mai zaman kanshi inji Inna , ɗan gayun namiji wayayye ajin farko , mai buɗewar ido da gogewar rayuwa , bazan gaji ba kuma baxan daina kukan rabuwa dakai ba har abadan duniya , saida ta samu natsuwa nace tou ina Jiddah take……… ? Ina Al ‘ Ameen ? Ina Bello ina Dady ina su Amisty ina labarin sahura , kinyi karatun boko ko kuwa a , a , kin haihu da Dikko ko ah ah ? Dan naji a labarin naki baki min zancen karatu da haihu ba , da kika gudu kika zo gidanku “yan gidan su Dikko sunzo ko kuwa……..? Ina Suwaiba ? Ina matar da Mami ta haɗaki da ita wacce ta bawa Suwaiba kwalba ? Ina Mardiyya ? Ina Alajinki ? Ina mutumin dake ƙwaƙwale ido ? An cire asirin ko a , a , Goge hawaye Sultana tayi sannan taci gaba da cewa……..
*JAMILA MUSA…*
Mai karatu ina fatan dai ka gane ? Domin farkon labarin zaku kamoshi idan kuka duba ai kunga labari ne bani ce nake faɗa muku ba Sultana ce take bada labarin rayuwatar da Dikko ne , Allah dai yasa kun gane…….
*SULTANA….*
Maman Jiddah suna isa Kaduna da asibiti suka fara saida aka wanke cikin Jiddah tas dan tana ɗauke da ƙaramin cikin Dikko wata3 , Maman Jiddah kuwa bayan ta tabbatar da ciki ya fita ta buga waya ta faɗawa Momy ta zubar da cikin dake jikin Jiddah , hankalin Momy idan yayi dubu ya tashi tayi kuka kamar zatayi hauka taso ace ko cikin ta bari dan idan ka haihu da namiji duk matsayin da yakai da matakin daya taka idan dai kuna da zuri’a ka more mishi , dan duk ranar da aka wayi gari idan Dikko ya ida kicimewa tace ta auri Dikko saima an bata kashin bala’e dan tace tanaji a jikinta Dikko wani babban sa’a ne kuma shi ɗin hatimin nasara ne , idan ta bar cikin ta haihu itace haihuwar zatayi ma rana ba Dikko ba , amma abinda ya faru ya riga da ya faru ,
Dikko kuwa data faɗa masa bai jahilci lamarin ba cewa yayi Allah yasa hakan da tayi shine alkairi a rayuwarshi , kuma ta faɗa masa Maman Jiddah ta tafi da ita akan zata kashe auren shi ta aura mata mai takarar gwamna yace ai wannan ba komai bane ba , idan ita rabonshi ce dasu sake zama idan kuma babu rabo shikenan kawai.
Bayan wani lokaci kuma Maman Jiddah tazo tayi wulaƙancin na ƙarshe saida ta zazzage auren Jiddah hankalinta ya kwanta , da Momy ta kira Dikko akan ya saki Jiddah cewa yayi ai itace ta auro Jiddah , sai kuma ya saketa tazo daga baya idan wani abu ya haɗota da “yan uwanta tace shine yaje ya saketa , ya yadda zai saki Jiddah amma rubutunta ya zama a sama zai saka hannunshi daga ƙasa….
Momy itace ta rubuta saki3 kai tsaye ba tare da tunanin komai ba , ta kuma ɗora da cewa saboda Maman Jiddah ta buƙaci sakin Jiddaah dan zata aura mata mai takarar gwamna , bayan ta gama ta miƙawa Dikko ya saka hannu tare da rubutawa.
_Ni Dikko Umar Dikko na saki matata Jiddah saki 3 , ina mata addu’a Allah ya bata miji na gari wanda yafi ni…._
Tunda Jiddah taga takaddar saki tayi kuka , kamar ranta zai fita dan ita kwata² bata san haka za’ayi ba , uwarta ke cin kuɗin mai takara kuma itace ta tabbatar mishi da zata kaso auren Jiddah ta bashi ita , ita dai Jiddah tasan tana sanshi a da amma tunda aka zo da zance Dikko ta jingineshi a site , bayan auren Jiddah da Dikko ita kuma Maman Jiddah taci gaba da cin kuɗinshi akan zata bashi auren Jiddah ta ci gaba da aske mishi aljihu ta kuma tabbatar mishi da saita kaso auren Jiddah ta bashi ita , shi kuma yaji baƙin cikin kasashi Jiddah da akayi dan haka ya buɗe bakin A T M ya riƙa yayyafa mata ruwan kuɗin , saida aka kaso auren yace baya aurenta shima idan ta ga wani haka zata kashe nashi ta bashi aurenta , kuma ya ƙara da cewa shi babu wata takarar gwamna daya fito yayi haka ne kawai saboda yaga ita mayyar duniya ce ,
Ita kuwa Jiddah haka tayi ta guduwa tana zuwa wurin Dikko kuma haka take tarashi a Abuja , shine ya taka mata burki yace ta daina binshi karta ja mishi sharri , taƙiji taci gaba da binshi yace tou duk ranar daya sake ganinta wurinshi zai kashe ta ne kawai kuma ya kashe banza……
Mardiyya kuwa tana tare da Jiddah amma ba’a gidansu ba itama ta koma gidansu da zama amma suna ƙulle dai tunda ana gari ɗaya , Mardiyya itace take raka Jiddah wurin boka ana ci gaba da neman asiri akan Dikko ya shiga tashin hankali yaji idan baiga Jiddah ba yaji kamar zai mutuwa , idan ta haɗo tsibbunta haka zata zo wurin Momy idan taji Dikko yana gari aita barbaɗe² , Momy kuwa bataji wani komai ba dan ita Allah yasa tana san “yan uwanta , Dikko kuwa ko a ƙwalar rigarshi , itama dai Mardiyya tana ta ƙara gyara nata ƙaimun , amma har yanzu kamar suna tura agwagwa ruwa ne dan Dikko bayajinsu wannan jagwalgwalon sihirin nasu bai zo ba ,
Banda labarin Al ‘ Ameen haka kuma banda labarin Suwaiba kowa banda labarinshi dan a gidanmu nayi haihuwar farko , na haifi namiji kuma “yan gidansu Dikko sunajin labarin haihuwa suka zo suka ƙwace ɗan wai bazaisha nonon karuwa ba , sunan Dady suka sa mishi { UMAR FARUK } suna kiranshi da Papi , haka Umar ya faɗamin , kuma shine ya bani labarin saukar da Dikko yasa akayimin , ina zuwa makaranta yanzu nayi JSCE kuma tunda naje ban ɗauki position sama da 5 ba , dake kafin na koma saida Inna tayi tsayuwar arfa wurin bani taimako da karatu na musamman a gida , ina js2 nayi jarabawa da “yan js3 , Inna ta siyamin mota nake zuwa makaranta da ita ,
Sahura ta rasu , kuma dani da Inna munje gaisuwa , kuma naje wurin ahalin Babana a can ƙauye dani da Inna , kuɗin gado basu bani ba sun haɗa gaba ɗaya sun cinye , Dady dai shima rayuwar sai a hankali , Bello kuwa yana can yana fama da rashin lafiya ni banje ba kuma bansan abinda yake damunshi ba ,
Tou yanzu ina Dikko ya mutu ko yana raye…………….?
Wani irin ihu Sultana ta darkaka daga haka ta ɗauke ashe ba’a tambayarta Dikko ni kuma na tambayeta…….!!!
06/12/2019 ????????
*JAMILA MUSA…* ????????