KWARATA 89

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* ????
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ ????????
*ASMA’U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI’ATU AMINU MAMMAN DEE*
???? —— 87
*_Wallahi idan kunji haushi na da gangan , inaji dai kun manta yadda labarin nan yake tun farko , masu cewa na gaji na yanke labari kuma dai matsalarku , kamar yadda na faɗa yadda ta tsara abunta dole haka zanyi idan ya miki a haka kibi idan bai miki ba ki barshi babu lallai fa ba dole dan anyi ciwo an warke ai ba’a ba mutuwa haushi ba , nabi tsakar dare nabi rana nayi safiya nayi marece , naji daɗi ko ba daɗi nabi dai ina muku dan kuyi farin ciki amma jiya kawai dan rashin adalci ni hada masu gayamin kalami mara daɗi hmmm aiko idan har kukaimin haka ni baku kyauta min ba kuma ƙullu yaci amanar koko…._*
Inna ce ta shigo cikin ɗakin da sauri inda Sultana take taje ta riƙeta tana shafa mata ruwa take min magana cewa Jamila da Allah kiyi haƙuri da labarin nan haka nan ki tafi sai wani lokaci , Inna ki gafarceni don girman Allah ki barni takai min ƙarshe , Inna tace a , a kije kawai , zan sake magana ta dakatar dani ta hanyar ɗagamin hannu , jiki a sanyaye na fara ƙoƙarin sauka daga saman gadon a dai² lokacin da Sultana ta buɗe idonta dan dawowa daga sumar da tayi wanda ta dawo ta dalilin ruwan da Inna ta shafa mata , cikin kuka tace Inna barta na faɗa mata , Inna tace to karki sakemin wani koke² na faɗa miki , insha Allah Inna , fita Innar tayi ni kuma na koma na zauna ita kuma taci gaba……
Dikko bai mutu ba kuma bai sakeni ba , da na barshi rufe a palo ni bansan abinda ya faru dashi ba tunda ni banyi waya dashi ba kuma ban ganshi ido² ba.
Dikko na kira Inna kuma ta shiga amma bata ɗauka ba , da kyau , daga haka bai sake cewa wani abu ba , kaji , naji , tou kace wani abu mana , ai shine nace hakan da kyau , nidai baka so na , baka damuwa da abinda yake damuna , ni bansan abinda yasa kake min haka ba na faɗa cikin hayaniya ina kuka , duk saida na safke mai isata sannan yace tou yi haƙuri An mata gani nan zuwa zan miki abinda kike so ,
Abinda na fahimta ni a nawa tunanin shine , tunda yana da matsalar fushi da saurin hasala , idan yana fushi kuma baya iya murza kanshi , ban sani ba tunda bai faɗamin dalilinshi naƙin saurere na ba , kila shi zuciyarshi ta tabbatar mishi da cewa lallai ni munafukarshi ce kamar yadda ya faɗa , dole da mamaki ya za’ayi ace sai a mafarki zanga Mustapha , me yasa tunda yasan Dikko baije wurinshi kai tsaye ya faɗa masa damuwarshi ba sai yazo wurina kuma sai a yanayin bacci ? Miye nasabata ko alaƙa ta dashi ? Shi yasa ya warware gaba ɗayanshi ya kasa saita kanshi sai lalurarshi tayi mishi tasiri a dai² wannan lokaci ya alaƙanta abun akan ni dama na zubar da cikinshi dan ina so na ɗauki fansa , kuma na faɗa masa cewa zan ɗauki fansa komin daren daɗewa zansa masa baƙin ciki da damuwa mara gogewa , saiya kira zuwa na wurinYazeed shima yana cikin ɗaukar fansa wato kuma sai yake gani da ni aka haɗa kai akayi masa asiri tunda har nasan Mustapha kenan har yanzu ƙudirin fansa bai goge min daga rai ba , maganar gaskiya ne kenan tunda itama Suwaiba ta kira Mustapha kuma Sultana tasanshi amma sabon rainin hankali wai a mafarki , a ganinshi ina tare da Al ‘ Ameen bayan shi kuma ya rabu dashi ne saboda ni dan yakai gulmata a wurin Dadynsu Dikko tun lokacin dana zauna gidan Dikko na farko , shine dalilin daya haɗashi da Al ‘ Ameen ya rabu dashi ya dawo da Ashiru , wanda lokacin da zan koma makaranta a karo na biyu mukayi faɗa da Mardiyya a motar Dikko na dawo katsina su kuma suka wuce Abuja.
Zan faɗa in mutu , ai nine zan jefaki da kaina , da gudu na sauka nayi waje kafin yazo naja ƙofar , kai………….. Saina kashe kaina , da gudu na fita daga gidan jikina yana ƙyarma kuma har yanzu ban daina fitsari ba , gaba ɗaya na ruɗe na rasa abinda yake min daɗi , ina gudu ina waiwaye ko ya biyo ni ne ? Nabar wayata a gida kuma ban riƙe number Inna ba amma tunda har nake kiran wayar a da bana samu yau kuma na kira na samu tabbas zan samu Inna hakan ya tabbatarmin tana nan , kuma lokacin ban lafiya ai ta faɗawa Dikko itama zata dawo babu jimawa , ta dawo kenan shi yasa na samu kiran ya shiga , napep na tare na nufi barhim estate….
Kamar yadda nayi tunani kuwa haka ya tabbata , a buɗe na samu gidan na faɗa da gudu nabar mai napep a ƙofar gida , bedroom na samu Inna kwance tana baccin gajiya da gudu na hau saman gadon na riƙeta ina waiwayen bayana , a firgice ta farka tace ke lafiya ? Me ya faru ne ? Gaba ɗaya bana iya magana dan na firgice yadda tunani baya tunani , bayana na buɗe mata inda ya jefeni da wuƙa sai kuma wasu wurare danaji ciwo wurin guje² , sai gefen kafaɗa ta dake min ciwo saboda halbin da yayi min nayi ƙundunbala , mai napep kuwa mai gadi ya sallameshi ya kama gabanshi.
Meya faru dake ne ? Inna take tambayata , bana iya magana sai kuka , dan haka ta sauka ta ɗauki wayarta ta fara kiran wayar Dikko , amma duk kiran da tayi masa bai ɗauka ba , itace ta taimakamin nayi wanka ta bani kaya na saka , fita tayi ta samamin abinda zanci kamar baƙuwar abinci haka naci gaba da cin abincin a zalamance ina tsare Inna da kallo , kuma har zuwa wannan lokacin kiran Dikko takeyi , ina gama cin abinci na kwanta naci gaba da bacci wahlala.
Inna kuwa kiran Dikko da tayi bai ɗauka ba shine yasa ta fusata ta fara wallahi׳ wannan auren saina kashe shi ni har ya isa in kirashi bazai ɗaukamin waya ba , shiɗin banza shin ɗin wofi me akayi² shi ne ? Ɗan iskan yaro mara kunya daya raina mutane , nan fa ta fara kiraye²n ƙawayenta Dikko ya daki Sultana ya caccaka mata wuƙa yaji mata ciwo , yarinyarta ta lalace kunga yadda Sultana ta koma ? Aure sai kace auren bauta ? Waye Dikko ? Saboda tsabar ma shi ɗan iska ne ya zanemin ɗiya kuma nake kiranshi baya ɗaukar waya , to ni nafi shi kangara da taurin rai naga yadda za’ayi ta koma.
Bayan ta gama kiraye²n waya ta tasheni a bacci ina tashi na ganta da wata irin zuƙeƙiyar wuƙa , cikin magana mai kama da raɗa tacemin idan wani yace miki kina san Dikko dan ubanki kika ce kina sansa saina kashe ki idan mutane suka tafi , idona cike da hawaye na ɗaga mata kai , idan kuma kika kira Dikko ko ya kiraki ni kika ɗauka saina kasheki dan ubanki babu wanda yaji babu wanda ya gani , kaina na girgiza alamar to , sakarar banza Dikko baya sanki ya raina uwarki na kirashi ma bai ɗauki wayata ba , dama matar Babanshi ta faɗamin kullum dukanki yakeyi ga tsangwama ga gori ga masifar kishiya ki zubar da ɗan iska kwandon shara ki fuskanci sabuwar rayuwa , sake kaɗa mata kai nayi , Inna tace sai kin samu wanda yafi shi tunda ubangiji ya halicceki nagartacciyar mace , hawaye ne ya gangaromin daga cikin idanuwa nidai nasan wallahi ƙarya ne babu wani inda zan samu wanda yakai Dikko bare kuma wanda yafi shi…..
Inna kuma taci gaba da cewa idan kuma kika kuskura kika sake zaɓarshi kika koma zama dashi wulaƙancin da yayi miki a baya sai yafi wannan kina komawa gidanshi na cire hannuna a lamarinki , kuma duk ranar daya sake dukanki idan kika je wurin “yan uwana ko ahalin Babanki ko nan gidan da wannan wuƙar zan kashe ki in huta , yanzu ma da kai na bata ansa , saida ta ƙare duk mai isarta sannan ta ɗaukeni a mota muka tafi asibiti.
Tunda muka fita duk idan naga ɓakar mota ta wuce da gudu sai inji kamar Dikko ne a cikinta , tunanin Dikko kawai nakeyi ko yana a wane hali ? Ko ya zaiji idan ya tashi bana nan ? Me yasa nazo gida dama na tsaya a wurinshi gashi yanzu Inna ta ɗauka da zafi harta fara cewa wai ya sossokamin wuƙa , sossakawa fa , jifana yayi fa kawai , yanzu ya zanyi idan na tuna dashi a halin da nake yawan tunaninshi ina gidanshi , wace irin rayuwa zan fuskanta , dandai babu kyau zunubi mai girma ne tsallake maganar Iyaye da kawai saina koma amma ina iya komawa matsallar data fi wannan ta taso ina zanje a lokacin kuma…….? Waye zai ƙwaceni ? Allah sarki mutumina ko kana a wane hali , kana raye ko kuwa ka kashe kan naka kamar yadda ka faɗa……… ?
Har mukaje asibiti muka dawo tunanin Dikko nake , ya wani zo ya tsayamin a rai , ji nakeyi dama kawai zan buɗe idona naga mafarki nakeyi ina buɗe idona sai in ganni a gaban Dikko da nayi farin ciki , koda muka dawo gida bedroom na shiga naci gaba da tunanin da bashi da gaira bare dalili , shashshekar kukan Dikko nakeji a zuciyata yadda yakeyi idan yana kwance dani , yadda yakeyin wata ƙyarma yana wannan kukan nashi , bawai ɓare baki yakeyi yana ihu ba , a , a wani iri dai yakeyi mai riƙe zuciya dasa mutum tunaninshi a ko wane lokaci , nashi daban ne dan Alhaji mai gidan “yanci ba irin na Dikko yakeyi ba , kai na Dikko daban ne salon nashi ma yasha banban , uwa uba ya iya sumbatar mace cikin salon da bashi tafiya har abadan duniya , ko ina kike ko ina kikaje sai kinyi tunaninshi dole ,
Haka nake zaune a gidan Inna tunanin Dikko yasa gaba ɗaya na fita hayyaci na , na ƙara ramewa haske na ya rage ga rashin lafiya ta kunno min kai sai jarabar shan kankana idan na riƙe ƙwallo saina cinyeshi dukanshi , da safe ina tashi dashi zan fara , da rana haka idan zan kwanta bacci , Inna kuma dan na rage yawan tunani yasa ta samanin malami mai bani karatu na musamman a gidan , ina dai tunani sosai amma hakan bai hanani gane abinda ake koyamin ba , itace ta sakani a makaranta kuma ta siyamin motar da nake hawa , ina cikin wannan hali na shigar ƙaramin ciki Inna tabi mijinta sukayi tafiyarsu ta barni a gida dani da wata tsohuwa dan ina tunanin kila mijinta ya sake matarshi dan tafiya da Inna yayi yawa duk lokacin da zaje da Inna yake tafiya ,
A makarantar da nake zuwa a nan na haɗu da Umar bansan abinda yakai shi ba , naji daɗin ganinshi sosai wallahi sai naga kamar zanga Dikko ko zaicemin gashi mai gida zaiyi waya dani , bayan mun gaisa nace masa ko yana koyarwa ne anan ? Yace min a , a wurin wani yazo , ina taso yayi min maganar Dikko ya ƙiya , nace tou ko yanzu ka daina zama Qerau ne ? Nayi haka nidai dan inji an kamo tashar Dikko amma ya ƙiya , tou ina mai gidan naku ne ? Abinda kin guji mai gida sai kuma kice wani ina mai gida? Kamar ya na guje shi ? Ey ai haka kikayi ma Momy rashin kunya dan tazo tafiya dake , Dady yace aje a taho dake kije kiyi jinyar mijinki shine kika ce bakya san mahaukaci sai an sake ki , ai kinsan da rashin lafiyar nashi kika gudu kika barshi , tou haka akayi ? Na faɗa a zuciyata , Umar kuma yaci gaba da cewa mai gida yasha wahala kema Hajiya baki kyauta ba da kika faɗawa mahaifiyarshi baki san mahaukaci , yanzu yana ina ne ? Waye ma yasan a ina yake ? Yana can Dady ya tafi dashi itama kanta uwarshi bata san inda yake ba , a nan yake faɗamin mai gida Dikko yamin halakci da bai kamata koma miye na baɗa masa ƙasa a ido , shine ya faɗamin Dikko yasa anmin sauka da ragunan da aka yayyanka ya ƙara da cewa wallahi da nasan matsayina da yadda mai gida yake so na yake ƙoƙarin kyautatamin da ban saka mishi da muguwar sakayya ba , nasan mutum nawa Dikko ya rabu dashi saboda kawai nayi farin ciki ? Me yasa na tsananta ? Me yayi zafi haka ? Miye dalilin saka sharri akan alkairi , naji dai babu daɗi amma koma dai miye nasan Dikko zai dawo kuma tabbas zaizo , nice na faɗawa Umar inda nake na kuma yi masa kwatancen gidanmu….
Mai ƙwaƙwale ido kuwa na sake mafarki dashi , abinda Al ‘ Ameen yayi min ni na yadda dashi 100% shi yasa a gidana banyi mishi shamaki dashi ba , ko ina nan ko bana nan zai shiga gidana kamar gidanshi , tunda na fara neman matar da zan aura na faɗa mata cewa Al ‘ Ameen Yayana ne , tana ganin girmanshi kuma tana girmamashi a matsayin shi na Yayana , idan bana gari ko wani abu matata ke so Al ‘ Ameen nake turawa yaje yayi mata ,
Hmmm , da Al ‘ Ameen ya samu sake nidai banda wani ƙarfi kuma iyayena basu dashi tunda na faɗa miki daga ni har iyayena duk a ƙasan baban Dikko muka tashi , Al ‘ Ameen kuma a wancan lokacin shi yayi ƙutu² ya fitar damu a gidan yaje ya haɗo bala’en dashi kaɗai yasan iyakar irin makircin daya shirya akayi mana rashin mutunci a lokacin Dikko baya nan ya raka Dady ganin likita , amma a cikin rashin mutunci babu Momy a ciki dan ita bata cika surutu ba kawai dai idan tana sanka tana sanka idan batayinka ko sabgar ka bata shiga , matan Dady sune sukayi wulaƙancinsu suka koramu kafin dawowar Dady kinga bamu san abinda mukayi ba kuma Al ‘ Ameen bai nuna mana komai ba duk dashi muka sha jimamin abun har kuka yayi tare da cewa shima zai bar aikin gidan , Babana ne ya bashi haƙuri yace kada abinda akayi mana ya shafeshi a taƙaice dai ya bawa Al ‘ Ameen baki akan zai haƙura yaci gaba da aiki.
Fitarmu a gidan yasa muka fuskanci sabuwar rayuwar babu , talauci ya tiso ƙeyarmu gaba , na kira wayar Dikko bayayi danni a lokacin bansan akwai number ƙasar waje ba , kawai na ɗauka duk ɗaya ce , na kira Dikko har na gode Allah wayarshi bata tafiya dan nayi imani da Allah ko kisan kai nayi idan na zaunar dashi nayi mishi kuka zaiji tausayi kuma ko za’a mutu idan yace mu zauna gidan wallahi koshi Dadyn bazai koremu ba dan idan har Dikko yace masa kaza za’ayi tou sai anyi shi , idan Dikko baya san abu Dady duk yadda yake sanshi saiya fita sabgarshi , Dady yana ma Dikko soyayyar da tunda nake ni ban taɓa ganin irin soyayyar ba , amma saboda sharri da makircin Al ‘ Ameen saida yasa Dady yayi ma Dikko faɗa karon farko a rayuwarshi zuwanki a rayuwarshi kenan…..
Ba’a zagin Dikko ba’a daka mishi tsawa ba’a mishi kallon banza , amma yadda duk baki tunani Dikko yana da tarbiyya dan duk wannan soyayyar baisa ya zama sakaran namiji ba yasa abinda yake kuma Dikko ba ɗan iska bane yana da tausayi amma bashi da mutinci duk yadda baki tunani dan shima ya gaji baƙin hali wurin uwarshi kaifi ɗaya ne idan zaiyi² kawai , idan bayayi babu gudu babu ja da baya bazaiyi ba , yana da halin ko oho kuma yana da mantawa da duk abinda zai ɓata mishi lokaci yana da kafiya ko zai mutu saidai ya mutu ya yadda wani irin hali dai shi kaɗai yasan irin abunshi.
Ban wani ɓoyewa mata ta halin da muke ciki ba , ta tausaya min sosai , Al ‘ Ameen kuwa shine ya samamin uban gida aka bani mota na riƙa aikin mota ina ɗaukar fasinja zuwa jahohi daban² , da nace bana so yacemin na riƙe motar kafin mai gida Dikko ya dawo sai asan abunyi , haka na haƙura na anshi motar idan na tafi sai inyi wata ɗaya bana nan , idan iyalita tana san wani abu zan aiko direbobi masu yo wa katsina sai a bawa Al ‘ Ameen yakai ma matata…..
Ina can su suna nan bansan wane irin ɗan wanke suke jefawa ba , matata mace ce mai mutunci mai biyayya mai kawaici da kauda ido akan abun duniya , amma kinsan yawancin mata suna “yar ciwa²r nan tasu ta idan aka baka kuɗin cefane ka ɗan maƙale wani abu , tou haka matata take idan na aiko mata da kuɗi zata ɓoye batayin abinda ya kamata kuma bata cin abinci mai mahimmanci saita maƙale haka kuma ko ruwan da zatayi amfani dashi bata siya saidai idan an dawo da fanfo taje tabi layin ruwa acan ƙofar gidan wani tsohon attajiri da yake fito da tiyo waje mata suke ibar ruwa.
Al ‘ Ameen kuwa gani yakeyi kamar nine kasashshe wurin kula da iyalita , saiya fara wanketa da ruwan naira dan idan dai kana tare da Dikko tabbas kaima zaka samu bakin gwargwado kayi hidima da rayuwarka cikin rufin asiri kamar dai kaima mai halin ne , haka yake cikamin gida da abokanshi ni ban sani ba yakai cefane yakai abinda za’a dafa tayi girki suci a zauna min a gida har dare ana fira da matata , idan zan dawo gari ya sani dan ina faɗa masa bana ɓoye masa komai , matata kuma bata taɓa faɗamin Al ‘ Ameen yana zuwa shida abokanshi ba tunda dai na faɗa mata Yayana ne ta yadda a hakan kawai.
Bansan yadda akayi ba ya ɓatamin mata ba idan ina nan nine miji idan kuma bana nan Al ‘ Ameen shine mai gida , haka maƙota sukayi ta bugomin waya suna faɗamin abokina fa yana zagayawa idan bana nan , da farko ban yadda ba sai naga tou idan sharri ne me yasa mutane da yawa zasu faɗa ? Ashe neman da yake mata akwai gejin da zai kai yana amfani da ita an bashi kuɗi ana neman idon matar aure amma sai anyi fasiƙanci da ita so adadin kwanakin da suka faɗa mishi sai a zuba mata maganin a idonta ana zubawa shi kuma tsafin zai cire idonta , ni kuma ranar da zan dawo katsina sai ban faɗawa kowa zan dawo ba , da farin ciki na shiga cikin gidana amma saina samu matata ba ido tana ta kakarin mutuwa , dana tambayeta sai tacemin Yayana ne yake nemanta shine ya cire idonta , daga haka ta mutu.
Nasan banda wani Yaya wanda ya wuce Al ‘ Ameen kai tsaye nayi ƙararshi amma sai ya samu ɗaurin ƙugu wurin manyan da yayi musu aiki sukaje suka baza kuɗi aka kori shari’ar kuma har lokacin Dikko bai dawo ba , haka na ƙara ɗage ƙara duk inda mukaje kuɗi ne suke magana , maimakon inyi haƙuri saina biye sharrin zuciya nima na nemi hanyar tsafi dan nayi alƙawari sainayi kuɗi da gasken gaske , zuciya ta ingizani nima na faɗa sana’ar ƙwaƙwale idanuwa , wanda Al ‘ Ameen ya haɗani dashi ya bani mota shine aka kaiwa idon matata , dan haka na koma wurinshi nima na shiga ƙungiya kuma da idon nashi matar na fara , na lashi takobin duk matar auren da ta zama makwaɗaiciya saina ƙwaƙwale idonta kamar yadda aka ƙwaƙwale na matata ,
Ƙungiyar ashe tana da wani tsari wanda ni ban sani ba , su zasu baka magani kayi amfani dashi ido kawai zai fita kai zaka zuba magani su kuma zasu turo tsafunsu ya zama maciji kana zuba maganin a idon mace macijin zai tsotse idon ya kuma shanye jinin jikin mace , idan yasha jinin saiya zuba wani a cikin ƙwarin idon daya cire kafin tsafin ya gama tsafinshi shine jini zai riƙa ɗiga a idon mutum da zaran an gama shikenan mutum ya tafi kai kuma sai a baka kuɗinka , tsarinsu shine shekara 3 sai kaima su tafi dakai ,
Mu mune ƙanana su kuma sune manya , mu zasu tura muje mu nemo musu matan aure muyi iskanci dasu sai mu zuba magani , kashe duk yaransu sukeyi bayan shekaru 3 sai suyi sabbin zubi , bansan da wannan tsari ba na faɗa ƙungiya kai tsaye saboda wani muradi nawa , ba wurin gudu babu wurin tsira mutuwa tazo min kuma shima Al ‘ Ameen zai mutu idan dai kayi musu aiki saika tafi saidai a wayi gari ba’asan abinda ya kashe ka ba , to me yasa sai matan aure suke so ne ?
Wannan tsarin tsafinsu ne shi ya faɗa musu irin wanda yake so bashi ya basu kuɗi , wasu zasu ce “yan mata , wasu matan aure , wasu zawarawa wasu mahaukata wasu jarirai wani tsafin kuma zaice mace mai ciki yake so , wasu makafi wasu guragu ko “yan maɗigo ko mazina ci , mai wasa da sallah ko wacce ta raina iyayenta , tou su nasu wacce ta raina aure suke buƙata , kinga ke ni ban kwanta dake ba amma kinci kuɗi dana tabbatar ke ba matar aure bace ba suka sa na koraki , amma sun matsa akan mutuwarki dan record in da kikayi sun takura sosai akan ki mutu , amma basu samu galaba dake tsafi yace kinyi kusanci da sallah yawan karatun al ƙur’ani da addu’a lokacin kwanciya bacci , cire hular saman kanshi yayi ya duƙar da kanshi gabana yace kin gani bani da sumar kai bansan ranar da aka cireta ba sun bugamin lamba , shima kuma tabbas nayi imani sun bugawa Al ‘ Ameen irinta gaba ɗayanmu zakiji labarin mutuwarmu.
Tou ta ina ne zanbi nazo inda aka binne tsafin da akayi ma Dikko ne ? Labarin tsafinshi ya goge idan ya dawo zai baki labarin komai banda sauran lokaci wanda aka bani ya ƙare , hankalina kuma ya kwanta tunda shima Al ‘ Ameen zai mutu , yana faɗin haka ya zama maciji suuuuuu ya gudu da wuce , da tashin hankali na farka kuma tun daga wannan ranar ban sake ganinshi a bacci na ba har yau ,
Inna ta daɗe a tafiya lokacin data dawo cikina ya shiga wata 7 bata sake komawa ba har na haihu , dana aihu ni na faɗawa Umar na haihu ita kuma Momy tazo har asibitin da muke ta anshe jariri wai ba zaisha nonon karuwa ba yazo shima ya zama karuwi , ta tata rashin mutunci dai² iyawarta tayi gori tace kuma tunda bata san zamana da Dikko duk wanda ya tsayamin a garin nan zata ga wanda ya isa yasa na sake zama da Dikko , zai dawo saki 3 zai bani babu sauƙi , idan kuma ina tunani Dadynsu zai tsayamin kamar na aurenmu da Dikko yaƙiji ya aureni Dady ya goya mishi baya yanzu haka bazai goyu ba , shi da kanshi zaisa Dikko ya sakeni , ban santa ba labarinta na keji , nayi kuka nasha hauka bansan iyaka ba , kuma da suka tafi da jaririn Umar yazo ya faɗamin wai Momy tace ma Dady nice nayi waya wai azo a ɗauki jaririn nan yadda bana san Dikko haka bana san jaririn kuma duk jinin da Dikko ya haɗo dashi bana sanshi , idan basuje sun ɗauki yaron nan ba komai zai iya faruwa tunda tun cikin naso na zubar bai fita ba zan kashe yaron , ta dai haɗa da ɗan makircita.
Abinda yasa nake kuka har na tafi shine , Umar yacemin Dady yake faɗa da yana tausayina kuma yana so na tunda Babanshi yana so na , ashe bani da mutunci har na danganta mishi ɗa da mahaukaci kuma nice zan kashe mishi jika daga wurin Babanshi dama na zubar da ciki a farko tunda nice nasa Rabiya tayimin allura , Allah yaba Babanshi lafiya ya dawo saiya sakeni………
Dana tuna zan rabu da Dikko sai inji dama mutuwa nayi kawai na huta da baƙin cikin rayuwa…………..!!! Ga Dikko yace baya zuwa bikon mace , iyayenshi sun ɗauki zafi , nima Inna ta gune akan rashin ɗaukar wayar da Dikko baiyi ba kuma har yanzu bai kirata ba , kuma tace idan har na koma gidan Dikko babu ita babu ni har abadan duniya saidai idan Dikko zai zama uwata , tasa kullum ina kiran wayar Dikko akan ya bani takaddar sakina naje nayi aure , wayoyinshi gaba ɗaya basa zuwa , shin yana ina ? Yana nigeria ? Ko yana ina ?
Me Dikko zaice idan ya dawo ? Wane hukunci zai ɗauka ? Ya zaiji idan iyayenshi suka ce nice na maida musu ɗanshi nace bana riƙewa saboda bana sanhi , shin zai sakeni ko kuwa zai zauna dani ? Ya zanyi ׳……………… ??? Yadda zanyi da mafita da rabuwa , gaba ɗaya na tattara lamarina wurin ubangiji duk abinda ya zartar a kaina dama haka yazo a rubuce kuma bawa bai isa ya goge ƙaddara shi ba ,
07/12/2019 ????????
*JAMILA MUSA….* ????????