KWARATA 90

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* ????
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ ????????
*ASMA’U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI’ATU AMINU MAMMAN DEE*
???? —— 88
*_Godiya mara iyaka zuwa gareku ,_* ????????
*_HADIZA MATAWALLE…_*
*_RUKY ” ” ” ” ” “_*
*_FATY ” ” ” ” ” “_*
*_ZEE ” ” ” ” “_*
Ngode sosai ku huta gajiya Allah ya daɗa zuminchie…
*_Gaisuwa marar iyaka zuwa gareki ZAINAB AHMAD KADUNA { Sheke } ina miki fatan alkairi tare da NA’IMA ABU KANKIYA…_*
Tabbas wannan zance haka yake , Allah ya bawa Dikko lafiya ya ƙara soyayya a tsakaninku ya kuma ƙaro irinsu Papi hada Junior Dikko muzo musha suna , murmushi Sultana tayi amma batayi magana ba , saukowa nayi daga saman gadon ina ɗan gyarawa cewa ni zan wuce zan tara ƙarshen labarin a takardar labarin rayuwarki , godiya tayi min sosai mukayi sallama cikin mutunci da mutuntawa , itama Inna munyi sallama cikin mutuntawa na barsu lafiya nima zan tara muga ƙarshen labarin tare daku masoyan Sultana & Dikko ,
Bayan Jamila ta tafi wanka na farayi tare da ɗoro alwallah dan magrib ya gabato , ina fitowa kayana na saka na shafa mai sama² da powder naci gaba da tattara kayan da Inna keyin parking zatayi tafiya zuwa Abuja ita da mijinta.
Inna ce ta shigo ɗakin tana cewa wai ga wani Abbakar can yana miki sallama a waje , ba tare dana kalleta ba nace wane Abbakar kuma ? Abokin ɗan iskan yaron nan mana , murmushin jin daɗi nayi a zuciyata a fili kuma na ɗan basar cewa Hajiya Inna kenan waye ɗan iskan yaro kuma ? Dikko , Inna wai me yasa kikejin zafin Dikko da yawa ? Bana san yaron ne kwata² gaba ɗaya ya siremin kamar tusar safe….
Saura kaɗan na fita na zageshi dan dai kar ace na haukace , ai bana nan ma dan ni bazanje ba , aiko sai kinje kodan ya ganki baki lalace ba ci gaba aka samu ba ci baya ba yaje ya bawa Dikko labari , nidai Inna gaskiya bazan wani je ba , aiko sai kinje kuma kin barbaɗa masa rashin mutunci yadda Dikko da uwarshi suka tozartaki kema sai kin tozartasu kuma sai ya baki sakinki tunda basu da mutunci….
Inna kenan na faɗa a raina , a zahiri kuma na bita da kallo , kin wani tasani kina kallo kamar niɗin baƙuwarki ce ki wuce kije ki dawo , banyi magana ba na ɗauki hijabi na fice , a harabar gidan naga wata irin lutsetsiyar mota ɓaka sai sheƙin sabinta take tunda na taho nake ganin kaina a jikinta bana iya ganin na cikin motar shima a gilashin kaina nake gani saboda yana da duhu , jikina ya bani ba Dikko bane a ciki amma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba duk inda wannan motar ta fito tashi ce kuma ban taɓa ganinta a cikin motocinshi ba ,
A jikin motar na tsaya na ciki ya sauke gilashin motar tare da cewa sannu , yawwa na faɗa rai a ɗan haɗe , ya gida ? Lfy , kin gane ni ? Ey a Bakori daka kawo katifa a motar ka ko ? Murmushi yayi tare da cewa ashe baki da mantuwa , ya akayi ne ? Gefenshi ya kalla ya ɗauko wata “yar leda bansan ko miye a ciki ba ya miƙomin ba tare dana ansa ba nace meye a ciki ne ? Ki ansa koma miye zaki gani , hannuna ɗaya a ƙugu ɗayan nake nunashi amma bada ɗan yasa ba kawai ka faɗa danni bazan karɓa ba , ki ansa An mata , ban sake magana ba na juya na wuce dan kar in ɓata lokaci Inna ta biyoni ta yabamin , sallah na samu Inna tanayi nima abin sallah na shimfiɗa na kabbara sallah.
Kai Ashiru ɗauki yaron nan ka maidashi gida fita zanyi , riƙe Dikko yaron yayi yana kuka cikin gwaranci yace bajan je ba tare da maƙale ƙafaɗarshi , Ashiru yace mai gida bazai zo ba , kai da Allah ɗaukarshi basai zaije ba ku tafi zanzo nima , ƙara riƙe Dikko Papi yayi yana kuka , kafin Dikko ya sake magana Abbakar ya shigo inda Dikko yake tsaye yayi parking tare da sauke glass yace DK bata ansa ba , ko tace maka wani abu ne ? Yadda sukayi da Sultana ya faɗa masa , babu damuwa An mata tana da matsala , ni bansa abinda ya faru ba tunda bana nan bazan iya ƙarda komai ba , kawai anje an kwaɓa abu duk sun jagwalgwale min komai , taya kai tsaye zan tunkari inda take bayan Momy taje ta ɗauko yaro ta taho dashi dole kowa zaiji babu daɗi , Momy Dady duk su ba’ayi musu dai² ba , itama Mamar kanta yayi zafi , kallon Ashiru yayi tare da cewa kiramin Umar yazo yanzu²n nan ya ƙarasa maganar yana kallon Papi daya duƙunƙune shi , isowarshi kenan su Nabeela suka zo dashi yi ma Dikko sannu da hanya da kuma dubashi da jiki , shi kuma sai wani bin Dikko yakeyi kamar yasanshi dan ko su Nabeela gajiya sukayi suka tafi suka barshi yaƙi binsu , iyakarshi gidanshi baije gidansu ba ,
Kai ka sanni ne ? Ya tambayi Papi fuska a haɗe , yadda yayi abun yasa Papi yayi dariya danshi a tunaninshi Dikko wasa yakeyi mishi , kai kasanni ne nace ? Ƙara ƙyalƙyalewa da dariya yayi yana kallon Dikko , tsoki yayi tare da buɗe mota ya sakashi a baya ya rufe yace ma Ashiru idan Umar yazo kace masa nace yaje wurin An mata haka kawai zakace masa , Ashiru yace to , zagayawa yayi ya shiga gaba suka fita da Abbakar ,
A palon Momy ya samu Jiddah tasha wanka na ɗaukar hankali da firgita tunani , Dikko ne a gaba Abbakar yana ɗauke da Papi da yayi bacci , suna shiga Momy ta ansheshi tana cewa Nabeela taje ta kwantar dashi , ansar shi tayi ta shiga ciki dashi su kuma suka samu wuri suka zauna , Yaya DK sannu da zuwa ya ƙarfin jiki ? Ko inda take bai kalla ba bare ta sa ran zaice yawwa , gaishe da Abbakar tayi shidai ya ansa saida ta rufe bakinta sannan Dikko ya gaishe da Momy , ta ansa cikin jin daɗi tana nuna yanayin farin ciki ɗanta ya dawo lafiya kana kallonta dai kasan tanajin daɗi ne a daren nan , labari marar ma’ana taita bashi akan Papi shidai shiru yayi baiyi magana ba kuma ko murmushi baiyi ba hankalinshi da kaf tunaninshi yana can wurin tunanin yadda zai taro matsalar da suka haifa da kansu , amma An mata ta bashi mamaki yayi tunanin ko bashi ne da ita suka haifi Papi ba zata iya riƙe mishi ɗanshi ko bayan baya nunfashi amma shine ta bada yaro da baiji bai gani ba da yana da ƙarar kwana daya mutu shikenan ya sake tashi a zero…..
Momy ce ta dawo dashi daga tunanin da yakeyi taci gaba da fanfo da ƙaga abinda bai faru ba kuma ba’ayi ba akan Sultana tayi mata rashin kunya ita da uwarta , yadda ta faɗawa Dady haka ta faɗawa Dikko ta kuma ƙara da cewa tuntuni suke aiken rashin mutunci akan ka sakar mata “yar ta , hankalin Dikko akan waya yace wa suka aiko ? Wata maƙociyarsu ce can Barhim , sai kuma kai tsaye aka barta ta shigo saboda an aikota daga gidansu An mata ? Ya ƙarasa maganar yana tsare Momy da ido , tou ƙarya nake Dikko , ah yi haƙuri ba nufi na kenan ba , daga haka bai sake magana ba sai ita taci gaba da farfaɗo maganganu marasa daɗi da ɓatanci , a ranshi kuma yace da na saki yarinyar nan gara na dawo da ita muci gaba da cakuɗawa daga inda aka tsaya har tayi hankali danshi kullum kallon Yarinya yake ma Sultana bai san ta ƙara girma ba , saida Momy ta tsiyaye mai isar ta tana faɗa tana kunnuwa ta tata rashin mutunci iyakar iyawarta , har tayi ta gama Dikko bai sake magana ba , ita ta gaji da kanta tace ya tashi ya bata wuri sakaran da baisan inda duniya ta nufa ba , miƙewa yayi ya fice Abbakar ya biyo bayanshi amma Jiddah Momy tana fara faɗa ta tashi….
Bai fita ba saida ya haɗu da sauran “yan uwanshi suka gaisa suna mishi sannu da addu’ar Allah ya tsare gaba ya bashi lafiya mai ɗorewa , suma dai sunyi mishi labarin Papi wai ya tambayi Papi ina Mamanshi yaji me yake cewa , murmushi kaɗan Dikko yayi wanda iyakarshi kawai a saman fuskarshi ya tsaya baizo baki ba , bai wani daɗe ba ya wuce saboda Dady baya nan ,
Abinda yasa ya tura Abbakar wurin Sultana waya ce ya bada yakai mata zasuyi magana dan tabar wayarta a goruba road ta gudu tou yaso ta ansa wayar suyi magana yaji ita kuma Mama ko tayi fushi ? Wai me yasa wasu iyayen miji suke tsanantawa akan matan “ya “yansu ne ? Suke nuna ƙiyayya tsana da kuma hantara ne ?
Matar ɗa abun so ce kuma itama ɗiyarki ce inda mutunci , abin tausayi ce ta wuce wulaƙanci , baki san yadda take zaune da ɗanki ba , tanajin daɗin sa ne ? Ko kuwa wahalarshi take sha ? Idan kinsan ɗanki yana da kyawawan hali kila ita matarshi munana yake mata , idan ke yana da haƙuri a wurinki kila ita rashin haƙuri yake mata Koma dai wane irin baƙin hali ɗanki yake da tadai yi haƙuri ta zauna dashi , waye yasan ni ina dukan An mata ne ? Duk wanda ya ganta idan dai mai hankali ne da ilimin karantar rayuwar ɗan adam yasan An mata bata da kwanciyar hankali , na doketa na zageta mari rashin haƙuri akanta gashi kuma sam² baya mata uzuri akan komai ƙanƙantar laifi idan tayi mishi , gaskiya iyayen miji ku daina tsanantawa wa matan “ya “yanku a gidan aure dan baku san yadda su matan suke haƙuri da “ya “yan naku ba ,
An mata tayi haƙuri da halinshi tuni ba tun yau ba kuma a hakan dai tana sonshi bata daina ba , ko a yaddar mishi ko kar a yaddar mishi , ko aji daɗi ko kishirya hakan shidai ba yaro bane yasan abinda yake shine yake auren matarshi dalilin wani bazaisa ya sake aurenshi ba , dan haka babu wani abinda ya dameshi dasai an yadda ya dawo da ita kawai zaije ya taho da matarshi ,
Umar ne zaune a palon Inna yaci abinci yasha lemu ya wani mimmiƙe yana kallo , dan ita Inna bata san Umar ko daga ta ina ya fito ba kawai dai tana gani na dashi data tambayeni waye shi nace mata a can gidan Babana lokacin bata nan ne yake min mutunci tou shine take cewa ya shigo idan yazo ,
A zahiri kallo yakeyi amma a baɗinance wallahi rahotanni kawai yake iba , danshi Allah yasa mishi bakinshi bashi da saiti akan magana duk abinda ya gani ko yaji kamar mai aljanun surutu saiya faɗa , ya daɗe sosai daya tashi tafiya Inna ta bashi kuɗi wai yasha mai ,
Ƙarfe 8:21pm yabar gidanmu misalin 8:41pm Dikko ya bayyana a gidan , kuma kai tsaye ya shigo har palo ba tare daya bari an bashi izinin ya shigo ba , da sallama ya shigo daga ni har Inna muna ciki ina tayata tattara kayanta , jin muryar Dikko yasa na sauko daga saman gado da gudu Inna tana cewa ina zakije ne ? Banyi mata magana ba na bayyana a cikin palon a dai² lokacin da itama Inna ta fito , gefe na koma ina maida numfashi Inna da Dikko suna fuskantar juna kan Dikko a ƙasa ni kuma duk su nake kallo saina kalli wannan na kalli wancan ,
Mama barka da yi….. Fizgoni Inna tayi muka koma ciki gefen gado ta zaunar dani ta durƙusa gabana ta riƙe hannayena , cikin lallashi tace karki manta da yadda kikayi kuka Dikko ya turo aka ɓanɓare miki yaro daga aihuwarshi yace a anso mishi ɗanshi baya so yasha nonon karuwa , kinaji kina kallo suka anshe ɗan suka tafi dashi , a gaban idonki nayi ta kiranshi a waya yaƙi ya ɗauka daga baya ma ya rufe wayoyinshi gaba ɗaya kuma har zuwa yau bai kirani ba , wannan shine ya dace ya zama siriki na ? Mijin da bashi mutunta mahaifiyarki ? Mijin da baya so ɗan sa yasha nononki yace miki karuwa ? Kar ɗansa yasha nononki shima ya zama karuwi ? Wannan shine mijin daya dace ya zama siriki a gareni ? A , a , tou sakinki zai baki maza nawa kika sani suna jiranki ? Me zakiyi da Dikko daya fara tsofewa ? Nan zai tsofe ya barki ki shiga tararrabin rayuwa , sakinki kawai nake so ki anso zakiga mijin da zaki aura yafi Dikko duk abinda kike tunani kiyi ƙoƙari ki more rayuwarki tun kafin duniyarki ta ƙare.
Inna waye zan aura ? Wayarta ta ɗauko ta nunomin hoton wasu matasa har 4 wai idan bana san wannan ga wannan kuma duk shekarunsu kamar na Dikko ne , bayan na gama gani nace umm umm suma dai duk sun tsofen tunda naga zasu kai shekarun Dikko , amma aisu basu ciccika fuska da gashi ba , gemu take nufi da ƙasimba , taci gaba da cewa ya sakeki ki auri zaɓina ko kuma dani dake kowa yaja tashi da’irar danni gaskiya bana san Dikko a matsayin siriki , me yasa Inna ? Saboda yaron baida kunya ko kaɗan , to me yasa kika yaddarmin na aure shi tun farin fari ne ? Wancan karon ra’ayi ne yanzu kuma muradi ne shin Dikko kika ɗauka ko ni………….???
Haba harma sai an tambaya ? Ai ke na zaɓa Inna , idan ni kika zaɓa ta faɗa tana bani biro da takarda a hannuna anan ciki zaki dawomin da ansar , ansa nayi na fito jiki a sanyaye ban samu Dikko a palo ba , dan haka na fito harabar gidan , a mota na sameshi zaune yana waya , tsayuwa nayi ina jira ya gama , buɗe murfin motar yayi ya fito da duka ƙafafuwanshi waje sannan ya kirani da hannunshi ɗaya wanda bai riƙe waya dashi ba , matsawa nayi ya riƙeni jikinshi ni kuma na dafa kafaɗarshi ina wasa da gemunshi da ɗayan hannuna , murmushi yayi ya kalleni amma bai daina magana a waya ba ni kuma baiyi min magana ba yadai tsareni da ido yana kallona.
Ɗauke idona nayi gefe ɗaya na janye hannuna daga gemunshi , kamo hannun yayi ya maidashi a dai² lokacin daya ajiye waya , riƙo ƙuguna yayi da duka hannayenshi ya jinjina shi tare da ɗan girgiza jikina sannan ya ansa biron hannuna da takaddar ya ajiye a gefe , jawoni yayi jikinshi yace me ne ne zakiyi da ? Ya nuna inda ya ajiye , Inna tace ka sakeni , wane irin saki haka babu daɗin ji ? Shiru nayi banyi magana ba , yana nan dai da halinshi na faɗa , yace ina miki magana kinmin shiru kuma kinaji , yanzun ma banyi magana ba , turani yayi baya daga jikinshi yana cewa wuce ki bani wuri , da sauri na sake komawa , dakamin tsawa yayi karki sake ki taɓani ya ƙarasa maganar yana gyara zamanshi zai rufe mota ,
Ƙara matsawa nayi da sauri na riƙe murfin motar cikin rawar murya nace yi haƙuri na bari , cikin fushi yace ni duk abinda kika min banji fushi a kanki ba saike mai Mama zaki wani cemin wai tace miki na sakeki ? Me nayi miki ? Ƙiyayyar harya kai fagen saki ? To me yayi zafi haka ne ? Ke ko kunya ma bakij…. Nima irin abinda ya taɓayi min can² baya nayi mishi nima na kulle bakunan mu wuri ɗaya , da sauri ya sauke ajiyar zuciya ya riƙeni jikinshi sosai yanayin lunfashi da yanayin gajiya , riƙe fuskarshi nayi da duka hannayena gefe da gefen fuskarshi na lumshe idanuwa na nima inayin irin yadda yakeyi idan yana kwance dani , murmushi yayi mai sauti amma bai raba bakunanmu ba kuma ba magana yayi ba yana dai ci gaba da fitar da numfashin kamar wanda yakeyin mura , miƙa yayi a kasalance da niyar ƙara jawoni jikinshi najiyo muryar Inna tana ta kwararamin kira cikin ɓacin rai , ƙoƙarin raba jikina da nashi na farayi amma ya wani riƙeni sosai , ƙyarma jikina ya farayi har yanzu bai saki bakina ba , nace Dikko Inna ke kirana kar tayi faɗa fa , fita yayi daga bakina yace shigo , Inna kuma ƙara kira takeyi Sultana……..
Ƙoƙarin kwace hannuna na farayi daga riƙon da yayi min dan tafiya wurin Inna , shi kuma yacemin shigo , Inna fa ke kirana , Innar , shigo nace , ah ni gaskiya bazan shiga ba , shigo nace , haba Dikko wai meye haka ne ? Nima bansan koma miye ba , Sultana………. Na rantse da Allah idan nazo wurin nan saina zaneki , Inna ta ƙara² faɗa , cikin kwantacciyar murya yace karki tafi ki barni , ko kina so inyi rashin lafiya ne ? Ya ƙarasa maganar yana yimin yaudararren kallonshi fuskarshi ɗauke da kyakkyawan murmushin shi mai ɗaukar hankali , girgiza kaina nayi alamar a , a , tou zo muje kinji jarumata yayi maganar cikin sigar lallashi , ita kuma Inna zuwa wannan lokacin ta ƙufule ta daina kirana , ni kuma Dikko ya ɗaukeni a mota muka bar gidan……. Shin Inna laɓewa tayi ta gani abinda mukeyi ? Me yasa ta kirani , Allah kaɗai ya sani.
Saida muka fita daga barhim na matsa na riƙe Dikko , murmushi yayi cikin izza sannan ya riƙeni da ɗayan hannunshi ɗayan kuma ya riƙe sitiyari amma baiyi magana ba , kwantar da kaina nayi a jikinshi fuskata tana kallon kyakkyawar fuskarshi saida naja gemunshi nace ina kaje ne ? Ba da fuskarshi ya kalleni ba da idonshi ya kalloni kaɗan sannan yace nima bansan ina naje ba , ba kin gudu kin barni ba ? Baki san ɗana ko An mata ? Hmmm ba komai ni ina sanki a haka ,
Sauka nayi daga jikinshi cikin hayaniya nace bana san² , ai basai kin faɗa da yanayin fushi ba nasan yadda abun yake , ai nima na sani , karki min rashin kunya ƙaramar yarinya , Dikko nayi , ai baki da lissafi mai gotacciyar kwalwa dake kuma saina ƙara aure tunda har yanzu baki da lissafi , kaje ka ƙara mana ba kaji abinda Inna tace ba , shiru yayi bai sake magana ba saini nayi ta rattafa ɗimi kamar wacce ta lashi wuta , kafin muje G R A harna ratto mishi yadda Momy tazo ta ƙwacemin ɗa , har yanzu bai sake magana ba , bayan yayi parking bai fita ba kashe motar yayi ya ɗauki wayarshi yana latse² , ni kuma har zuwa wannan lokacin abin faɗawa Dikko bai ƙare a wurina ba , saida na gaji na ɗauke da kaina , cire makullin motar yayi tare da cewa muje yayi maganar ne a dai² lokacin daya fita daga motar , nima fita nayi nabi bayanshi ina cewa kuma ai ni banajin tsoron kishiyar ko an faɗa maka ni ɗin lusarar mace ce mai ma auren miji kuka , jinjina kai yayi cikin ɓacin rai , saida muka raba palon 2 ya juyo yace nidai kika raina ko ? Yadda yayi maganar cikin ɗaure fuska yasa na koma baya ina kallonshi , jinjina kai yayi cewa muje yayi gaba nabi bayanshi har ɗakinshi….
Yau da kanshi ya rufe ƙofa , kuma bai wani bani wannan maganin nashi da yake bani idan zai kwanta dani ba , na yau wani iri ne daban saida nasha akaje wasa , kamar dai na daren farkonmu yauma saida ya tabbatar ya gama gigitani yace tunda na raina shi saida in tashi in tafi gida , kamar sakara haka naita kuka ina bashi haƙuri amma sam Dikko ya kifa kanshi wai bayajin yaren da nake mishi magana dashi , nayi kuka kamar raina zai fita ina cewa bana san hakan wai kai me yasa mugu ne da Allah ? Ba kin rainani ba ? Tou yi haƙuri , cewa zakiyi kin bari bazaki ƙara ba , na bari bazan ƙara ba , ɗan gajeren tsoki yayi cewa kawai kije idan kinyi hankali sai kizo inyi wasan danbe , riƙeshi nayi ina kuka yace min na fita jikinshi karya kasheni , ƙin fita nayi naci gaba da kuka ina kallonshi , dariyar mugunta yayi min sosai yana min video , kuma ban daina mishi magiya ba , haka yaita gwalgwala ni , yana dariya wai saina faɗa yadda ake cewa wasan danbe da indianci idan ba haka ba shi bayaji da hausa , cikin ɓacin rai nace ban iya ba buɗemin ƙofar na tafi , anƙi a buɗe ba makullin a hannuna yake ba ? Idan kece kika kulle ai sai kinga dama kike buɗewa , sai kin faɗa , kuma ko kin faɗa sai Dikko yaga dama zai danbace ƙaramar yarinya ya ƙarasa yanamin gwalo , da nazo nayi shiru sai inji bana iyawa , kamar wata zararra haka ya haukatani a ɗaki naita hauka yana min dariya , saida ya gaji da ranfa ni sannan ya kwanta dani da wani irin baƙon salo , daga farko naji daɗin yadda yayi min daga ƙarshe saida yayi ɗabi’ar tashi dan idan baiyi mugunta ba ji yake bai haɗu ba , da naji azaba nayi magana sai ya nunamin vidion yace kefa kika roƙa , saida ya tabbatar ya wahalar dani sosai sannan yace gobe ma ki sake raina ni kindai ga amfani na…
Tare mukayi wanka , kuma kayan da nazo dasu sune na maida , saida na gode masa kamar yadda ya koyamin , shine da kanshi ya maidani gida , bayan yayi parking yace kin yafemin ? Saida nayi shashshekar kuka nace na yafe maka , rumgumeni yayi a jikinshi yace Allah yayi miki albarka , nace amin , kuma wasa nakeyi miki bazanyi wani aure ba , ai babu mai iya haƙuri da halina saike , ina sanki sosai “yar matana Allah ya ƙara miki haƙuri da halina , banyi magana ba ina kallonshi dai , murmushi yayi tare da sumbatar saman bakina , yace yi haƙuri don Allah , banyi magana ba har yanzu , da , da ne nake masa wannan kallon daya zazzaromin ido yace daina kallo , kinyi haƙuri ko ? Ey , tou jeki , kuma ki huta gajiya ngode , yawwa nima ngode na faɗa a dai² lokacin dana fita na rufe ƙofar bam ,
Ajiyar zuciya ya sauke bayan Sultana ta shige , vidion da yayi mata ya kalla sannan ya ƙyalƙyale da dariya yace baiwar Allah An mata , cike da tausayin Sultana da soyayyarta mai girma ya ɗaga mota yabar gidan.
Har yanzu Inna batayi bacci ba , a palo na sameta zaune tayi takurarren zama , Inna har yanzu bakiyi bacci ba ? Na tambayeta , ummmm ta bani amsa ba tare data kalleni ba , kuma cikin yanayin jin kunya dai ta bani ansar , zan wuce ciki ta kirani har yanzu bani take kallo ba ta kasa haɗa ido dani kwata² , ɗazu bakiji ina kiranki ba ? Yi haƙuri Inna banji ba , dama taya zakiji tunda kina so kibi Dikko , shiru nayi ban sake magana ba , tou tsaya kiji ina tsaye wurin ganin na nemo miki mutuncin ki da martabarki harni zan kiraki kiyi kunnen uwar shegu dani kibi namiji a gaban idona ke mara kunya ko ? Yanzun ma shiru nayi mata , idan wani abu ya faru ke kin isa kice Dikko ne ? Munafikin Allah ya saɗaɗo ya biyo dare ya ɗaukeki to ina kukaje ? Kaina na kallon ƙasa nace kiyi haƙuri don Allah ,
Wallahi bazanyi haƙuri ba saidai ki tattara kayanki ki koma wurin Dikko danni babu mai jamin dogon zance da karkata kai ina wallahi² , tunda kina san Dikko kawai kije ki koma amma ki sani idan har shi yayi miki wani abu ko “yan uwanshi karma ki sake kizo min gida na faɗa miki , tunda kika zaɓi Dikko wallahi na bar mishi ke duka , dama ai nace miki idan kika zaɓi Dikko a kaina saidai dani dake kowa yaja tashi da’irar , kin bishi kuma kin dawomin babu takaddar sakin ki , zanyi magana ta dakatar dani ta hanyar dakamin tsawa tana ci gaba da cewa jaka ya ɗaukeki sakarar banza da baki da kyakkyawan tunani , tunda kin bari ya rainaki ya ɗauke matattara sauke buƙatunshi , yazo yayi miki daɗin baki kin kwashi jiki kin bishi amfaninki kawai ya samu natsuwa dake ya samu kuma ya maidoki hoto kawai dake , to sai kije idan wahala ta kasheki kece kika huta idan sun barki kin zauna ɗangin nashi kiyi ta haihuwa suna ɓanɓare “ya “yan ta ƙarfi da yaji , shi kenan kin zama jaka saidai kullum kisha wahalar ɗaukan ciki ki haihu a barki da shan ruwan zafi , In , ki rufemin baki ko inci mutuncinki a daren nan , kuma sai kin barmin gida tunda kin zaɓi Dikko akaina , I , ki rufemin baki wallahi kika sake kamo suna na saina wulaƙantaki , simi² na wuce ciki ita kuma tana cewa ki tattara kayanki yazo ya tafi dake , tunda kinƙi ya sakeki ki aure wanda nake so a cikin maza 4n dana nuna miki………
Da safe Inna haka ta barbaɗomin kayana a tsakar gida ta rufe ɗakunanta , duk haƙurin dana bata² saurareni ba bayan ta cemin kar na sake naje inda duk wani ɗan uwanta yake , duk saboda ta kirani Dikko yace nazo muje akan me zan bishi ? Kuma itama ai tasan kiran wanda yake gaba tsakanin miji da uwa , kawai dai tana so ta kashe min aure ta auranmin wanda ranta yake so , a cikin mazan da tace na zaɓa su tana da tabbacin daga su har iyayen nasu dashi kanshi wanda zan aurar bazasu wulaƙantani ba ?
Dikko baice baya so na ba , bai wulaƙanta ni ba , tou wai me ma yayi min ne ? Ko sai in kashe auren nawa inzo in zama na Jiddah nima in tashi biyu babu , idan kuma nabi irin nata ra’ayin ita Inna kenan itama ba wannan mijin aka ce ta aura tun farkon farko taƙi aurensa taje ta auri Babana , saini zance Dikko ya sakeni inje inma kashe auren Allah ya jarabeni da fitinar duniya , zawarci ai shima ɗaure yake da ƙugunshi ,
Saida nayi musu rakiya har wurin mota duk addu’ar sauka lafiya da nayi mijinta kaɗai ya ansa ita kuma ko kallona batayi ba , addu’a ta dai su sauka lafiya kuma su dawo lafiya.
Haka na yini a filin gidan Inna har kicin inta ta rufe abinta , ina zaune a ƙofar ɗakinta data rufe kamar asara duk abinda zanyi a bayin tsakar gida nake huɗɗoɗina amma har dare babu abinda naci saboda banda ko si² a hannuna. A ranar yau Dikko bai zo ba , kuma a maƙotan gidan Inna na kwana ganin zan kwana da mai gadi , a gidan ne suka bani abinci naci ,
Washe garin tafiyar Inna ma Dikko baizo ba , kuma ranar ma a maƙota na kwana , saida akayi sati biyu da tafiyar Inna Dikko yazo , ina maƙota mai gadin gidan Inna ya kirani , yauma babu driver ba ɗan rakiya a mota na sameshi zaune daga shi sai wani ɗan kyakkyawan yaro anci mishi gayu cikin wata irin zuƙeƙiyar shadda { getzner } hutu ya zauna a jikinshi sosai , kallo ɗaya zakayi ma yaron kasan gidan kuɗi ya fito daga shiyar manyan mata gogaggi wanda suka san darajar wanka da gayu sai kuka yakeyi , Yaya mu cafi jida ya cire hular da aka ɗora mishi a kai ya riƙe a hannu sam ya hana Dikko yayi min magana ,
Kai ni bazan tafi ba waye yace ka biyoni ? Ni a nan zan kwana , ƙara fashewa yayi da kuka yana ta maimaita suje jida , kashe motar yayi yana cewa muje ciki , taya zan iya faɗa masa Inna ta kulle ko ina ne ? Ah kawai mu zauna a mota shi kuma harya fito da yaron daya zo dashi yasa na ɗaukeshi sai yagushin fuskata yakeyi yana kuka baya co , ƙafarshi ɗaya a waje ɗayar a ciki yake miƙomin wayoyinshi da hular da yaron ya jefar , daka mishi tsawa Dikko yayi yana cewa kai bana san iskanci kaji , shiru yayi yana kallon Dikko yana kuka kaɗan² , saukeshi ya tafi da ƙafafuwanshi , da sauri na sauke shi nima ina kallon Dikko kamar yadda yaron keyi tare da cewa wurin fa a rufe yake….
Tou kije ki buɗe yayi maganar hankalinshi nakan wata leda da yake dubawa , shiru nayi na rasa abin cewa , da faɗa ya juyo kunzo kunmin tsaye nace kuje ciki zanzo , babu makulli a hannuna , sai a hannuna nake da ? A , a ina nufin bana nan Inna ta fita bata dawo ba , daga Abujar ? Kai tsaye nace masa Ey , da ɗan yanayin damuwa yace shikenan ku shigo mu tafi ba tare daya kalleni ba yayi maganar yana gyara zamanshi ya rufe ,
Zagayawa nayi zan shiga motar yaron nan ya fara kuka bana shiga musu mota , Dikko yace kai zan zaneka wallahi , fashewa yayi da kuka yana turani baya , juyawa Dikko yayi bayanshi ya ɗauko dorina yace masa gafara daga nan , cikin kuka yace bata ciga ya matsa baya ya riƙemin hijabi wai basu zuwa dani , da bulalar ya kawo duka yaron ya matsa yana kuka bai sameshi ba sai cewa yakeyi bacu zuwa dani , Dikko yace An mata shigo muje mu barshi a nan , ɗaukarshi nayi na sakashi ciki nima na shiga na rufe , tunda muka ibi hanya Dikko yake faɗamin Mama ta kirashi ta tozartashi iyakar iyawarta , abun bai mishi daɗi ba dan saida tasashi ya sameta har Abuja ta wulaƙantashi hmmmm , cika idonshi yayi da hawaye yace ta faɗi maganganu masu muni a kaina marasa daɗin ji , nayi mata uzirin ɓacin rai nasan duk fushin abinda ya faru ne ta tattara ta sauke a kaina da bansan abinda ya faru ba , ina can ina jinya banma san ina nake ba , ina nan zan barki kizo ki zauna gida har banzo ba ? Da nasan inda kaina yake ko a waya ai zan kiraki tunda gashi ranar dana dawo ai ranar nazo wurinki , kuma ita Mamar da tace ta kirani ban ɗauka ba idan naga kiranta zan basar ne ? Haka nan ma nake kiranta na gaisheta babu ranar da bana kiranta na gaisheta tunda na aureki , tou idan baki saki ba ranar da kika kulleni a ɗaki kika gudu kinsan yadda na kasance a wannan ranar ?
Ba abinda ya dameni da yadda ka kasance har ni kake cema kayi ma Inna uziri idan bakayi uzirin ba me zakayi ? Ko itama haukar zakayi mata ne ? Cikin ɓacin rai yace aike yarinya ce uzirin ne hauka ? Ni nasan darajar duk wanda ya haifi ɗiya ya bani , bawai rashin kunya ko rashin ɗa’a yasa nace nayi mata uziri ba , ina nufin nasan taji fushi da ɓacin rai akan abinda akayi miki na ɗauke Papi ya nuna yaron yana ci gaba da cewa shi yasa kirkina dubu wannan dalilin ya gogeshi na dawo mara mutunci a idonta , to kici gaba da kiran hauka zamu haɗu anjima , shiru nayi ban sake magana ba har muka iso G R A , haka na taho ba abinda na ɗauko daga gidan Inna , kuma bansa yadda sukayi ita da Dikko ba amma tabbas nasan zai faɗamin yadda sukayi da ita har yaje ya taho dani , da yadda ya kasance bayan na kulleshi na gudu , da yadda suka ƙare da Yazeed da Aunty Suwaiba Al ‘ Ameen da kuma labarin Mardiyya.
Saida Parpy yayi bacci Dikko yasa Ashiru ya maidashi , kuma yau da ya bani maganinshi ban ma yadda nasha ba dan abinda na fahimta ta cikin maganin nan yake haukatamin lissafi , yayi lallashi nace bafa zansha ba , haba An matana dan Allah kisha , Allah bazan sha ba , kar Allah yasa kisha “yar rainin hankali , oho maka dai……
A ranar wasan ba magani akayi shi , kuma ran Dikko ya ɓaci , tunda naƙishan maganin banzarshi , har gari ya waye bai min magana ba sai fushi yakeyi , daya tashi fita ma nayi masa a dawo lafiya bai ansa ba , daya dawo ma sannu da zuwa na ma bai karɓa ba.
Haka dai mukaci gaba da dafa rayuwar , Momy tayi ruwan wulaƙanci da taji labarin na dawo kuma tazo ta zabgaga rashin mutuncin ta iya ƙarfinta , kuma Dikko yaji babu daɗi sosai ya bani haƙuri kuma nayi , Dady kuwa Dikko ya zauna ya warware masa komai kuma Dady yayi ma Momy faɗa yace bataji dai daɗin halinta ba , ɗiyar ɗanta da girmanta ta zauna tana mata ƙarya bata kyauta ba , kuma ya ƙara maimaita mata batayi hali mai kyau ba data raba uwa da ɗanta ta guji ranar da sakayya ta waiwayota , shi dama bai wani ɗauki zafi da Sultana ba Momy ce takaishi ta baroshi kuma yanzu ya gane gaskiya dan haka ya dawo daga rakiyarta.
Gaba ɗaya Dikko ya tsameni daga sabgar “yan uwanshi , biki suna jaje ko mutuwa bana zuwa , yace tunda basa so na kawai inyi rayuwata na manta da sabgar duk wanda baya sabga na , hankalina kwance banda wata damuwa dan Dikko ya hana duk wannan gayyar “yan gidansu zuwa gidanshi , kuma makaranta ɗaya muke da sauran ƙannenshi amma ba wanda suke ɗaki ɗaya ba , ban koma SS a tsohuwar makarantar da Inna ta kaini ba , Ashiru ke kaini yana ɗaukoni , idan kuma Dikko yana gari shine yake kaini yana dawo dani ,
Muna cikin haka ne babbar ɗiyar Rabiya ta kwanta ta mutu , kuma banje gaisuwa ba , mutuwar ta tashi rankatakaf hankalin ahalinsu Dikko , saboda babu wata jinya da tayi lafiyarta lumi tana cin abinci maka’ikan mutuwa ya zare ranta , koda akaje asibiti likitoci sunce tuni ta mutu saima a wurin wankan gawa aka kwakwale sauran abincin daya maƙale a bakinta.
Rashin shigata cikinsu yana musu ciwo Dikko kuwa ya zuƙeni daga cikinsu kwata² , tou rashin zuwa gaisuwar ne ya ƙara basu mamaki , abin ya damesu , koda Momy tace ma Dikko meya hana matar ka zuwa gidan gaisuwa ? Cewa yayi shine ya hanani , dalili Momy ta tambaya………
Kuyi haƙuri wallahi wayar lumshewa takeyi bata doguwar tafiya yau dasai na ƙarƙare labarin nan amma ku bari mu ƙara ko feji biyu ne ,
18/12/2019 ????????
*JAMILA MUSA…* ????????