KWARATA 91

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* ????
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ ????????
*ASMA’U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI’ATU AMINU MAMMAN DEE*
???? —— 89
*_YAHANASU YUSUF A Y RAƊƊA , {{ Mrs TANIMU MUSA QERAU }} yau gaisuwar taki ce ke ɗaya matar Yayana , ina miƙo saƙon dubun gaisuwa ta zuwa gareki tare da addu’ar fatan alkairi , kiyi farin ciki , cikin farin ciki kuma kyakkyawa…_*
Shiru Dikko yayi ya gagara cewa ummm ummm idonshi yana kallon ƙasa ya kwantar da gefen kanshi a gefen kujera kusa da inda Momy take zaune , ita tana sama kenan shi yana zaune a ƙasa , cikin sigar lallashi tace Dikko mace ta fini mutunci a idon ka ko ? Yanzun ma shiru yayi babu amsa , idona biyu ban mutu ba kenan , idan kuma na mutu ka gama da “yan uwanka har abadan duniya haka kayimin adalci kenan ? Yanzun ma a ɗauke yake baiyi magana ba , me yasa daga kai har matarka bakuje wurin zaman ta’aziyya ba…… ???
Ba tare daya ɗago ba yace ai ni naje , sau ɗaya tak kaje fa , ko kana tunanin ban sani ba ko bana ganewa iye….. ? Duk yaran gidan nan tunda akayi rasuwar nan suna gidan Rabiya suna tayata jimamin rashin ɗiyarta , duk wacce ke aure kuma mazansu duk dasu ake zaman ta’aziyya , sai kai zaka kawomin wata sabuwar aƙida a cikin zuri’ata ka warwaremin zaman lafiya ka jefa ƙiyayya a cikin kai da kuma “yan uwanka ? In banda kake ɗan iska yarinyarta ta kwanta ta mutu ba ciwon kai bare na jiki , kuma ba yarinya ba budurwa Dikko kace kaine ka hana matarka zuwa gidan ta’aziyya kuna cikin “yan uban suna nan suna kallonku kuma suna karantarku idan har kuka kuskusara suka ga wata ɓaraka ta fita a cikinku sai sun hanaku zaman lafiya ,
Zaiyi magana ta daka mishi tsawa tace rufemin baki mara kunya , baka san dama ƙufule nake dakai ba ? Ni bana san “yar iskar yarinyar nan bana santa ׳ ko zan mutu bazan so yarinyar nan ba , ƙaton banza ƙaramar yarinya ta maida kai susutancen namiji , har nawa take da zata juyaka sakaran banza marar tunani , tou ita ɗin da kake gani kana iya rabuwa damu saboda ita muɗin dai daka ɗauka ba’a bakin komai ba mune na gaskiyar , ita kana iya rabuwa da ita kuma wata zaka auro , mace ana canja ita amma ni da “yan uwanka baka iya canja mu har abadan duniya , ka saki gaibu ka kama zahiri idan ba haka ba sai kayi dana sani wata rana , da sauri ya ɗago ya kalli Momy cikin damuwa yace kar kiyi min baki Momy , ba baki nayi maka ba , gaskiya na faɗa maka , bani na faɗa ba kaima ka sani kuma kowa ya sani , karuwa har amana ne da ita ?
Karuwa bata zaman aure , sai ka gama gina rayuwarta zata zazzage ka tayi gaba abunta , badai yarinya ka auro ba ? Yarinyar ma karuwa , karuwar ma da bata fito daga tsatson mutunci ba ko ? Hmm addu’a ɗaya ma zakayi karta kashe ka , dan wannan yarinya daga ganin idonta babu Allah a lamarinta kana can ana barbaɗa maka kana tanɗewa , Allah kaɗai yasan iya ƙazantar da take baka kake ci a abinci , layu kuma baka san ta ina kake takasu ba , ka kwanta akansu ka tashi akansu gaba ɗaya ta ɗimauta ka , ka dawo wani sakarai , banajin daɗin ganin wannan ranar Dikko ka cuci rayuwata daka auri karuwa , ka rusa gidanka ka rusa rayuwarka da bayanka , dama mutuwa nayi banga zuwan wannan ranar ba , ta ƙarasa maganar kamar zatayi kuka.
Parpy dake tsaye bayan Momy saman kujera yana wasa da makullin motar Dikko yace , Culcana , shi Dikko ba wai duka yaren Papi yake ganewa ba dan hausarshi bata fita yana tsamin baki , Momy taci gaba da cewa , ina gudar maka irin abinda ya faru da mijin Safiya Ya’u ne , haka mijinta yaje ya auro karuwa , Papi ya juyo ya anshi labarin yana zaro ido cikin tsoro cine Culcana ta yankaci , ya ƙarasa maganar duk idonshi a waje yana nuna yankawa da hannunshi dai² wuyanshi , maimakon Momy tayi ma Papi faɗa tunda ita tana gane abinda yake cewa sai tace Ey mana haka zata yanke Yaya ya mutu shima , dariya Papi yayi yana kallon Dikko , ita kuma taci gaba da cewa hankalinta da natsuwarta bazata zauna lafiya ba harsai taga ya saki yarinyar nan , zata natsu.
Jiddah ce ta shigo palon da sallama gaba ɗaya palon ya disashe duk wani ƙamshin turare da wani turaren wuta gaba ɗaya turarenta ne kaɗai ke tasiri , tafa wanku yadda hankali baya iya hasasowa dan Jiddah “yar gayu ce sosai , murmushi tayi tare da taɓo Perpy tana cewa dan Yaya yazo baza kamin Oyoyo ba ? Da sauri yayi baya yana goge inda ta taɓa mishi fuska , Momy ji abinda Perpy yakemin , Momy tace ai kun saba , Perpy kuma cewa yayi kuma baciyi cau ba , Jiddah tace kam lallai ma yaron nan aiko na haɗu kuma nayi kyau ka tambayi Yaya kaji , daga bayan Momy ya leƙo Dikko yace Yaya aije batayi cau ba , shiru Dikko yayi bai kalli Perpy ba kuma bai ɗago daga yadda yayi zamanshin tun farko ba , a yangance Jiddah tace Yaya barka da yini , yawwa ya faɗa tare da fiddo wayarshi daga aljihu yace Momy zan tafi , da sauri Papi ya sauko yayi gaba kar Dikko ya tafi ya barshi , Jiddah kuma ciki ta wuce tana wata irin tafiya mai ɗaukar hankali , da wutsiyar ido Dikko yabi bayanta da kallo , a ranshi yace hmm mata kenan……….
Momy kuwa taci gaba da cewa , ashe karuwar nan badan Allah ta auri mijin Safiya ba kuɗi aka bata akan ta kaso shi , shi yasa gabana yake faɗuwa kar haka ta kasance dakai , shima kamar kaine dai , da iyayenshi sun hanashi aurenta amma yayi kunnen uwar shegu dasu yaje ya aurota , ashe bai sani ba ajalinshi ya ɗauko , daya aureta dangi suka taso ta gaba saiya tsameta daga cikinsu dama tunda taje gidan bata ma wani yadda tayi ciki ba tunda tasan aiki ne ya kaita , Dikko ni nake faɗa maka wannan labarin dare tabi ta yankeshi ya mutu har lahira , da wuƙa nake faɗa maka , Allah ya jiƙanshi , saida Momy ta ƙara zage Dikko sosai tana farfaɗa mishi manyan illoli game da auren karuwa da kuma haɗarinta , sannan tace ya tashi ya bata wuri sakaran banza da mace ta gama dashi ,
Jiki a sanyaye tattare da damuwa Dikko ya fito daga palon , makullinshi ya ansa a hannun Papi ya faffalla mishi mari yace ya wuce ya bashi wuri idan ya sake biyoshi saiya ci ubanshi , riƙe Dikko yayi ya fashe da wani irin kuka mai tada hankali , danshi Dikko idan dai ranshi ya ɓaci tou saiya rarrabashi kowa ya samu , cikin hayaniya yace sakeni yayi maganar yana zazzaro mishi ido , kallon Dikko yakeyi kuma bai daina kukan ba yaƙi sakinshi , jin ihun Papi ne yasa Momy fitowa tace me yayi maka ne ? Ni babu inda zanje dashi , Momy tace sai kaje dashi , cikin ɓacin rai yace haka zan ɗauki yaro inta yawo dashi a gari kamar wani sakarai , ai sakaranne , shima ya san kai sakarai ne shi yasa yake ganin ka kamar wani abokinshi.
Ni gaskiya babu inda zanje dashi , Momy tace wallahi sai ka tafi dashi , Papi kallon Momy yayi yana shashshekar kuka bai saki Dikko ba , Momy tace sai yaje dakai daina kuka kaji ko…..? Har yanzu ita yake kallo sai kuma ya kalli Dikko bayan wani lokaci , Dikko baiyi magana ba ya buɗe mota ya shigar dashi suka tafi….
Momy kuwa palo ta koma cike da ɓacin rai , irin wannan ranar ce take gudun zuwanta kuma gata nan tazo , wannan dalilin yasa taso Yaya tayi haƙuri karta kashe auren Jiddah , gashi tun ba’ayi nisa ba Dikko ya hana kowa zuwa mishi gida , ya tsame matarshi tsam daga cikinsu bare in tazo su riƙa muzanta mata , gaba ɗaya Dikko ya canja hali kuma ya rage masifa ya zama wani ruwan sanyi saboda mace , ita dai Allah ya sani bata san Sultana kuma idan dai tana rayuwa saita raba Dikko da yarinyar nan , dan ta faɗawa wata ƙawarta abinda yake faruwa kuma tana nema ma Dikko auren “yarta amma tace matarshi ta katantane ko ina ta hana wata shiga , ɗiyar Yayarta ma da yake aure itace tayi mata asiri ta tashi hankali saida dai akayi saki Jiddah ta samu natsuwa , kuma saki 3 ne babu damar a koma , ita bata iya wannan ɓatar ba ta neman asiri amma idan zata iya ta fitsare ƙafafuwanta ta fitar da Sultana ita kuma zata sa Dikko ya auri ɗiyarta.
Da ɓacin rai ya dawo gidan , tunda naga yanayinshi banma shiga sabgar shi ba daga sannu da zuwa ban sake mishi magana ba , kuma bai ansa ba , tunda ya shiga ɗaki bai sake fitowa ba , da Papi yayi bacci text ya turomin inje in ɗaukoshi daga ɗakinshi , ko da naje ɗaukarshi faɗa yayi tamin wanda shi kanshi baisan dalilin faɗan ba , waishi yafi ƙarfin mace ta raina shi , haka kuma babu wata banzar macen da zata iya juyashi ko wacece ita , nidai ban masa magana ba na ɗauki Papi zan fita yace idan naje na kaishi inzo , a ɗan tsorace nace ina zan kaishi ne ? Saman kaina zaki kaishi ,
Allah ya baka haƙuri , na ɗauka zan kaishi wurin Ashiru ne ya maidashi , duk yadda kike so haka zakiyi , yadda dai kake so Dikko , to da kinsan wurin Ashirun zaki kaishi zaki tsaya kina tambayata saboda raini……? Tou ki sani jiya ba yau bane ba idan kuma kika ce zaki min yarinta yanzu zakiga yadda zan ruɗa miki rayuwa.
Ajiye mishi ɗanshi nayi zan fita , An mata zo nan , yi nayi kamar banajin shi , wallahi idan kika fita saina zaneki , zo nace , tsayawa nayi ban dawo ba , karki bari na sake miki magana , ɗaure fuska nayi na koma wurin shi , cikin ɓacin rai yace ke har kin isa ni zaki ma baƙin rai ? Wace ce ke ? Ɗaukarshi , ban sake magana ba na ɗauke shi na fita ,
Ina kaishi na dawo , ci gaba yayi da faɗa yana rufe idanuwanshi cikin rashin mutunci , waishi ya gaji da cin zarafin da ake masa akaina , ko aure kanshi farau saidai insan inda zanje danshi ya gaji , da wane rayuwa zaiji da Allah , gani nima mara kunya na raina shi harna faɗa masa , tou ya gaji wallahi saidai in tafi gidanmu , ƙyarma jikina ya farayi gaban ya faɗi , a raina nace na shiga3 Inna ta koreni kaima ka koreni ? Abinda Inna tace tunda na zaɓi Dikko ko zai kasheni karna zo mata gida ta yafe mishi ni duniya da lahaira , cikin rawar murya nace Dikko me kuma nayi maka yanzu……. ? Ba abinda ya dameni ki barmin gidana ni na gaji bana iyawa , kayi haƙuri idan nayi maka wani abu insha Allah bazan sake ba , cikin ɓacin rai ya juyo tare da nunani yace ke………… Ki barmin gida nace ,
Fashewa nayi da kuka nace kayi haƙuri don Allah , bazanyi ba………. Sai kin tafi daga gidan nan , yau akanki zagi nawa Momy tayi min ? Tacemin sakarai har take cemin Perpy ma yasan ni sakarai ne , ance kin shanyeni tou yau sai kin barmin gidana dan kowa yasan ni ba shanyeyyen namiji bane ba , ya ƙarasa maganar yana ciro bero daga gaban aljihun rigarshi….
Cikin kuka nace haba Dikko me kakeyi haka don Allah ? Ke ni ba mahaukaci bane ba nasan abinda nakeyi ya nuna saman ƙoƙon kanshi , ita Mamar taki kinsan me tacemin akanki ? Ta muzantani ta tozartani me nayi mata ne ? Kayi haƙuri Dikko , naƙi inyi haƙuri tunda kika shigo rayuwata farin ciki yayi bankwana da zuciyata , matsalar yau daban ta gobe daban in fita waje a ɓatamin rai in dawo gida dan na samu natsuwa kimin rashin kunya , ba tattalin miji kwata² baki san darajata ba , kina ƙasa na amma kina nuna ke wata isashshiya ce , wace ce ke ? Wanda kinsan ko a gado nine a samanki duk ta inda aka juya , na bari , hararata yayi cikin fushi yaci gaba da cewa , wane fi’ili zakimin duk wani feleƙenki a tafin hannu a yake , me ma kika iya ? Me kika sani akan namijin……. ?
Shiru nayi ina kallon ƙasa , yaci gaba , kullum ɗaurin zanin ki iri ɗaya ne , tafiyar ma tun wacce na sani , kullum kina nan dunkume ba ranar da zaki buɗe idonki kisan wace irin rayuwa akeyi , babu ilimin zama da miji sai rashin kunya shi kaɗai kika iya mutum ya taɓaki ki ɓare baki kiyi ta wani kukan munafinci , { idan yana kwanciya dani } me kika nema kika rasa ne ? Ni wallahi bana san kidahumar mace , bana san jakar mace bana san ƙazamar mace , idan na faɗa miki yadda nake so kiyi rayuwa dani sai kicemin ina miki cin fuska , me Jiddah tafi ki ne ? Babu abinda takai ki a cikin mata dubu baki kasuwa ba’a fini mata ba amma an fiki sanin zamani , cikin ɓacin rai nace niba kidahuma bace ba , kuma kai kanka kasan ni ba ƙazamiya bace ba , dan kaga ina baka haƙuri kake ganin kamar inajin tsoron rabuwa dakai ne ? Banda ilimin zaman mijin kuma bazan koya ba , idan ka rabani da kanka zan mutu ne ?
Ai saika rubutu abinda zaka rubuta ga biron nan a hannunka , ni ba abinda zan rubuta da biro ajiyeta zanyi saidai in zaneki kikaimin rashin kunya , murus zan kasheki babu wanda yaji babu wanda ya gani , amma yau sai kin tafi gidanku na faɗa miki , bazan tafi gidanmun ba , wallahi babu inda zanje , cire kayanshi yayi ya nufi toilet yana cewa shi yasa duk namijin da yasan abinda yakeyi wallahi bai auren yarinya , kullum kaida mace faɗa cikin gida , ai kasan inda ake auro manyan mata kaje ka auro mana , shigewa yayi bai sake magana ba , ni kuma naci gaba , banyi shiru ba har yayi wanka ya fito.
Yana fitowa yaci gaba , ina ma amfanin mace ba soyayya , kije cikin matan gidanmu su koya miki yadda ake tattalin miji , ki koyo yadda ake rainon miji , a koya miki kissa su koya miki wanka da saka sutura tunda ni kin raina ni , Nabeela zata koya miki yadda ake tafiya a gaban miji je kiga yadda suka wayar da Jiddah suka buɗe mata ido baki ajiye komai ba sai girman kai , da raina miji , kin ɗauki miji kamar wani sa’arki ina magana kina ɗaga min murya sama sai kace kece kike aure na.
A daren yau saida ya tabbatar ya ɓatamin rai harsai da nayi kuka ya jagulamin lissafi tas , sannan yayi shirinshi yana gama shiryawa ya wurgamin kuɗi a saman gado shi ya tafi Abuja kuma kar in sake zuwa makaranta saiya dawo , binshi nayi ina kuka , kila tausayi na bashi ya tsaya ya rungumeni yace An mata bakijin magana wallahi , cikin kuka nace Dikko dan Allah na bari , na faɗa ina kallon idonshi , riƙeni yayi sosai a jikinshi , a hankali ya duƙo saitin fuskata cikin magana mai saukar da kasala yace yi shiru , ya ƙarasa maganar yana tsareni da kyawawan idanuwanshi , rufe bakina nayi ina kallonshi , buɗe bakinshi yayi , yayi wani iri da harshenshi kaɗan yana wasa dashi sannan ya kirani da harshen nashi ,
Saida na sauke ajiyar zuciya cikin shashshekar kuka na riƙe jikinshi tare da shiga bakinshi da nawa , kullum idan zaimin wani abu yakan canja min sabon salo ne , nayau daban , na gobe ma zaizo da baƙon salo , ya ɗauki wasu “yan ƙalilan mintuna sannan ya sakeni daga jikinshi , ƙara riƙeshi nayi ina kuka nace dan Allah karka tafi , ba tare daya kalleni ba yace ki bari sai kin iyo riƙe namiji a gida sai ki riƙeni in zauna , inaji ina gani yayi tafiyarshi….
Ɗakinshi na koma na faɗa saman gado ina kuka , nidai Allah ya sani banda wannan idon tsakiyar kai irin na gogaggin mata , ko a can baya dana riƙa iskancin nan ba’a hayaccina nayi ba , ina naje ina aka sanni ne ? Wa na gani waya ganni ? Ban taɓa haura Katsina ba daga Daura sai Katsina iyakata nan , kenan tunda akayi min sauka aka sauke duk wani sheɗanci dake saman kaina , tou me Jiddah tayi wanda yasa Dikko yake faɗamin ita a magana harso 2 ? Duk yadda akayi kila yaga Jiddah ta burgeshi ne , shidai Dikko yana san gogaggiyar mace , mai tafiya da zamani , wacce ta waye sosai idonta ya buɗe da duniyanci amma a gidan aure , ƙwanƙwasashshiyar mace a fagen tarairayar miji , “yar duniya da tasan logon maza , wacce ta shahara ta kuma ƙware a wurin iya wasan danbe ,
Tou ba Dikko kaɗai ba duk mazan zamani mata haka suke , gadai Jiddah an saketa amma tunda tasan yadda yake san mace ta kasance ta kasa sanya , kullum a riƙe take , irin su Jiddah ne matan da idan namiji ya sakesu zasu kashe shi da bariki shi kuma yaci gaba da zagayawa kina gida kwance kamar asara ana can ana hidimar duniya babu ke , yanzu zamanin nan duk inda kika nufa mazan sun zama iri ɗaya ko wane baya san afi matarshi kuma basasan baƙauya ko ƙazamiya , wallahi duk kyanki duk tsarinki duk iya haɗuwarki duk irin sigarki da nagarta da kike da , idan dai baki da gayu baki da wayewa baki iya girki ba tsafta da ilimin zaman aure ke hoto ce , hoton ma elajiment da zaran an liƙaki a bango an gama dake , tou haka macen da bata san damarta ba take wurin mazan zamani , baki da wani amfani saidai ki share gida kici abinci , idan kuma kikayi sa’a da ɗan duniyan namiji kina nan sake da baki kina ta rashin wayanki yana can shi kuma yana miƙa kuɗinshi ana sashi a ɗaki , duk hidimar da miji yake miki zata ragu tunda masu ci sun ƙaru , gaki ke matar gida ga matan bariki , yake “yar uwata me akafi ? Wane duhun kai kika tsaya ? Tou rayuwa ta canja , zamani ya juya keda mijinki kina ji kina kallo makwaɗaitan matan bariki zasu ɓanɓare miki miji ta ƙarfi da yaji ,
Dan wallahi wasu mazan basu iya ba koya musu akeyi , wasu kuma dama can jarabar a jininsu take , wasu abokai ne suke kaisu su barosu , wasu kuma matan nasu ne da kansu suke yanka musu tikitin shiga bariki, idan kikayi masa magana ya daina kwanciya dake in kinci sa’a ya faɗa miki illolinki idan kina da rabo saiki gyara , idan kuma kin samu namiji mai zafi ya buɗe miki ita tsaye yace ake ƙazamiya ce ba wanka ba gayu ba shafa turare haka zai dosoki kina ƙarnin hayaƙi ko zufa ko zarni fitsarin yara , ke kuma sai kiji haushi an faɗa miki gaskiya ki masa rashin kunya , idan akaci sa’a da irinsu Dikko su zaneki a barki da kunburaren jiki , ke kuma fuuu kinyi yaji daga nan matsala ta samu hanyar shigowa , mata mace ƙwalisa ce ita , fulawa ce bata rayuwa saida gyara , zamanin ga ya lalace idan kuma kika kwanta tou fa lallai kinji a salansa , bawai ina nufin ki tashi ki nemi asiri ba , a , a ki tashi ki gyara domin zamanin yazo da sabon salo.
Tunda Dikko suka ibi hanya saidai yayi tsoki , Sultana fa ga mace har mace komai yaji , ga kyau , ga siga , nagartacciyar mace gata tayi dai ko ta ina baka isa ka kusheta ba inba hassada ba , ga ƙugu An mata , ƙaramar yarinya da ita amma Allah yayi mata zubin bodi irin na manya mata , saidai ɗanyen kai ya hanata ta fuskanci damuwarshi , wace ce Jiddah ? Wace ce ita idan An mata tana nan ? Gaskiya An mata kyakkyawa ce , mace ce ta tsara , fitacciyar mace mai kyakkyawar halitta , bakinta mai kyau , tana da tsarin haƙora masu burgewa kuma tsaftatacci , tayi sosai gaskiya saidai matsalarta yarinta , zuciyarshi ce ta bashi haƙuri cewa shekarun Jiddah da Sultana ba ɗaya ba , inda Jiddah taje Sultana bata je ba , ƙawayen da Jiddah keda su ba irinsu An mata take da , ba wani , yaran ƙauye ai basu kai An mata ba ake musu aure kuma lumi suka riƙe miji babu mai ji , saishi ko kwanciya zaiyi da ita saida “yan dabaru , zuciyarshi dai haƙuri take ta bashi akan cewa idan Sultana ta goge wallahi shi kanshi saiya zama swry ya kwantar da hankalinshi da sannu za,azo wurin……
Wayarshi ya ɗauka tare da tura mata text , taje makaranta , sai kuma adireshin { address } in gidan Rabiya taje mata ta’aziyya , sai izinin hawa mota da inda zata ɗauki makullin saboda Ashiru bashi nan , hada lambar { number } Momy ta kirata tayi mata gaisuwa , kuma daga makaranta gidan Rabiya karta je ko ina……
Saida safe naga saƙon Dikko bayan nayi sallah asubahi zan koma bacci na gani dana ɗauki wayar , ban ce masa na gani ba kuma ban kirashi ba nima na basar da lamarinshi , da ya tafi saida yayi wata ɗaya da sati biyu kuma har yaje ya dawo banyi waya dashi ba , koya kirani ma bana ɗauka kuma banje gaisuwar ba , kuma kuɗinshi a inda ya wurgasu a gado ban taɓasu ba banma ko kalli inda suke ba , yadda yabar ɗakin haka ya dawo ya sameshi , ya cancara ruwan rashin mutunci a daren nan saida yasa ni na gyara ɗakin na goge ko ina da ina yace kuma tunda banda wayau kar in sake zuwa mishi ɗaki , ni kuma abinda ya ɓatamin rai dashi da yace wai me Jiddah tafi ni ne ? Ashe ma kallonta yakeyi , sai kuma abun ci baya waini zanje Nabeela ta koyamin yadda ake tafiya a gaban miji , inje inga yadda suka wayar da Jiddah suka buɗe mata ido , wato ni ban iya komai ba ? Shine abinda ya ƙonamin rai nake zuciya tunda ya tafi har ya dawo kuma ban huce ba.
Fita nayi daga ɗakin ya biyoni yana cewa ko zaki mutu saina faɗa miki gaskiya duk duniya baki da wanda ya isa ya faɗa miki iskan nan mai kaɗawa saini , ko yayi miki daɗi ko yai miki zafi saina faɗa , ke ni har zaki nunamin fushi ? In banda iskanci ni zaki barma ɗaki har inje in dawo yadda na barshi haka zanzo in sameshi , nace kije ma Rabiya gaisuwa shine baki je ba kuma bazaki ba inyi duk abinda zanyi , zama nayi a gefen gadona nidai na rasa abinda yakemin daɗin duk an jagulamin lissafi , wayata na ɗauka ya fizge wayar ya bugata a bango duk ta tarwatse yace ina miki magana zaki latsa waya , nace kije ki koyo zamantakewar aure idan kinji fushi ki koyo saiki zauna lafiya.
Ke in kina da hankali ma har ni zakiyi gaba dani ? Nine nake aurenki ko kece ? Ni zan kiraki a waya ke a dole kinyi fushi , tou ƙarya na faɗa ne ? Ba komai cikin wannan sakaran kan sai wauta da yarinta , idan kinga dama ki shirya zamu fita , yana faɗin haka ya fita abunshi.
Goge hawaye nayi cikin ɓacin rai , duk duniya babu wanda ya cuceni sai Inna , ko waya na kirata ta daina ɗauka , gata a raye Dikko yake iƙirari shine kaɗai zai faɗamin gaskiya , tabbas shine zai faɗamin , zanji fushin na iya zamantakewar zama dashi dan mu zauna lafiyar…..
Ya daɗe sosai sannan ya dawo ɗakina , yasha gayu cikin sigarsu ta “yan gayu , nima nayi wanka na shirya amma daya shigo saida ya gyaramin diresin , yana cewa saura in munje ki saki baki kita surutu ko yawan murmushi , daga ina yini Allah ya jiƙanta kika sake ko kallon wani muka dawo zan kulleki a ɗaki.
Shine a gaba ni nake bayanshi bayan ya gyaramin tafiyata muka fita , 9:32pm a palon Rabiya tayi mana , kafin ta fito saida tasa aka fara tara mana “yan abubuwan taɓawa , Dikko ya nunamin ko ruwa nasha muka koma gida saiya ɓatamin rai , yana tsaye wurin ganin ya siyomin mutunci amma ni bahaguwar kwanya gareni ,
Bayan wani lokaci ta dosa , ƙarar takalminta kakeji a saman tayils ƙwas׳ , ƙamshi yayo gaba ta bayyana a palon sai isa takeyi mijinta na biye da ita , saman kujera mai zaman mutu 3 { 3sieter } suka zauna , mu kuma muna saman 2sieter , gaisawa aka farayi nima na gaisheta tare dayi mata ta’aziyya , ta amsa dai cikin sakin fuska , daga haka ban sake magana ba , sukaci gaba da firarsu , bamu wani daɗe ba muka tafi , kuma Rabiya tace ko ruwa musha Dikko yace an gode , tace tana zuwa kila wani abu zata bayar yace ai zamu dawo ,
A mota ne yake cewa kaje wuri ana marmarinka ka tafi kafin ka fita ran mutane , kin gani dai ko ? Dare ne muka je amma kallarta shirye , tsakanin palo da bedroom sai an saka takalmi masu kyau , kana doso miji yasan ka taho , amma ke duk babu wannan takalmin ma “yan maraɗi kike yawo dasu babu wani notice saidai kawai mutum ya ganki , har muka isa gidan gwamnati Dikko faɗa yakemin , kuma saura idan munje canma inyi surutu ko inci wani abu Jiddah tana nan idan ta barbaɗeni ba abinda ya dameshi ,
Daga gidan Rabiya har gidansu babu abinda na kalla kar yacemin na cika ƙauyanci , a kame nake dan nima ba sakara bace ba , amma a raina inajin daɗi , tunda Dikko yayi parking su Nabeela suka yo waje har Papi shima baiyi bacci , duk sannu sukayi mana , Papi kuma ya tafi wurin Dikko yana oyoyo , hannunshi ya kama sukayi gaba Papi yana bashi labari shidai baya gane yarenshi.
Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji lokacin da idona ya sauka akan Momy , kai uwar Dikko “yar gayu ce , ta haɗu ׳ , Allah yayi mata kyau sai kuma ya haɗu da hutu uwa uba kuma gayu , kamar yadda Dikko yayi nima a ƙasa na zauna jiki a sanyaye sai mulki Momy ke zubawa , kai Momy tayi wallahi ta haɗu “yar gaye ce first class kuma ko a ajin ma itace ta gaban benci , bayan sun gama gaisawa da Dikko nima na gaisheta , saida ta mula tasha iska bayan ta gama kalleni tas sannan tace lafiya qalau , ƙannenshi suka shigo wanda muke karatu dasu makaranta ɗaya , wai me yasa kwana biyu banje sch ba ? Saida na kalli Dikko sannan nace musu ba komai , su jina suke kamar wata ƙawarsu dan haka sukace inzo muje ɗakinsu suma ,
Momy tace bazata je ku koya mata kilbibi ba , Dikko yace Momy ki barta suje , kasan yaran gidan nan munafukai ne basu aje komai ba sai kilbibi da gulma idan suka ɓata maka mata da tsigudidi ka huta , Nabeela tace matar Yaya zo kiji , ta leƙo daga ciki tana kirana , kallon Dikko nayi , da girarshi ya nunamin inje wurin Nabeela , tare da sauran masu cewa naje ɗakinsu duk muka runguɗa ciki , muna shiga suka ciremin kallabi suna ganin gashina , Nabeela ta ɗauko abin taje kai ta fara tsigarmin kai , wai ince ma Yaya zan kwana , nidai banyi magana ba , sune sukayi ta surutu nima ina so ince wani abu amma Dikko ya hanani magana dole nayi shiru , Jiddah kuwa yanzu ta shigo ta fara masifa wai anzo ana ciccira musu datti a gado , ganin babu wanda yabi ta kanta ta koma palo ta faɗawa Momy amma sai Momy tace idan mun gama an gyara ,
Nan Dikko ya barni yace zaije ya dawo , Momy ma ciki ta dawo bayan fitar Dikko , kuma bata wani ji ƙanƙamina ba , ganin Dikko ya tafi yasa ta kora duk wanda ba itace ta haifesu ba , tana satar kallona lokaci² irin kallon nan na gefen ido , itace ma tayi ma Nabeela faɗa ta rufemin kaina saboda dare , shine Nabeelar tace muje ɗakinta , Momy tace bazanje ba ,
Har 11:46pm Dikko bai dawo ba , ni kuma na gaji ni bana san irin kallon da Momy kemin kila kuma karatu na takeyi , kallon Nabeela nayi tare da riƙe hannunta nace nidai muje ɗakinki , Momy tace muyi zamanmu , sai kuma take tambayata bayan gidan Rabiya sai ina Dikko ya kaini , nace sai nan , zai kaini gidan Yayarshi wacce yake bi itama inje in mata ta’aziyya nace to , wai kuma duk abinda akayi in riƙa zuwa idan ba haka ba babu wanda zai sanni nace tou ,
Sai 1 saura Dikko ya dawo kuma Nabeela tace masa in kwana yace a , a , itace ta anshi Papi ni kuma muka wuce gida , tun daga wannan ranar ina zuwa gidansu Dikko amma tare dashi , idan kuma anyi wani abu biki ko suna Nabeela take zuwa ta tafi dani ko Dikko baya gari , basa dai min wani gani² ko habaici , amma Jiddah idan muka haɗu sai tacemin ga irin asiri wai na mallake dangi miji , bana tanka mata tunda dai Dikko ya gargaɗeni da baya san inje in zama ɗaya dasu na riƙa kama kaina banda yawan surutu banda yawan dariya , ba ruwana da sabgar kowa , kuma kar in kuskura na riƙa shiga sabgar Jiddah.
Shigata cikin familynsu Dikko yasa na gane banbanci tsakanin “yan geto area da boti sayit , na gane matsayin wanka kuma na gane shima kanshi wankan iri² ne , na gane matsayin gayu kuma nasan nawa gayun an daina yayin irinshi , na zubar da gayun rayuwar baya dan na ɗauki sabon darasin wanka a wurin wayayyin mata , lokaci guda kaina ya fara hayaƙi nima na fara fizge² , idona ya fara wayewa , akwai banbanci tsakanin wayewar talauci arziƙi da kuma rayuwar lingu , ko a karuwanci ashe iri² ne nawa da nayi a baya wahalallen karuwanci ne , Nabeela tana taimako na tana shiga dani wuraren da tunda nake ma bansan akwai su a cikin garin Katsina ba sai su masu kuɗi , kai talaka ya rayuwar haƙuri ? Talaka bawa alere dangin jakki ka mutu gobe a sake sabo , da nasan zanzo irin wannan rayuwa da ban ɓatawa kaina lokaci ba wurin shirmen da nayi a baya , wanda bai haifa min komai ba sai ɓacin suna , karuwancin wahala ya bugamin tambari mara goguwa , kai kuɗi na inda suke gayu wayewa da buɗewar ido na gidan gwamnati , idan taƙamarki wanka sai kin gama wankuwa har kin gaji , idan kika tunkari ahalin Dikko sai kin raina kanki ,
Nidai ban sani ba , shin Dikko yayi magana da “yan gidansu dan su ɗago rayuwata ko kuwa sune suka ga ya kamata su wayar dani oho musu , nidai dama can gaskiya bawai wata kidahuma bace ba saidai kunsan wayewar kuɗi da talauci ba iri ɗaya bane ba , kawai dai ciwona rashin ganewa a boko shine ciwo na tou yanzu ina ganewa kuma na iya , rabon da muyi faɗa da Dikko harna manta , shidai burinshi ya samu natsuwa cikin kulawa da soyayya kuma kullum nazo masa da baƙon salo , na jiya ba irin na yau ba , na yanzu daban na anjima ma yazo a baƙo , kuma karna gajiya da sauri shine dalilin yasa yake bani magunguna dan na ɗauki buƙatarshi har ya samu gamsuwa ba tare dana gaji ba , na zama jajirtacciya mai juriya a fagen tsakiyar filin wasan danbe , sai kuma biyayya shi mutum ne mai san ka bashi girma , yana san girma sosai kuma yana so ka girmamashi , saboda san girmanshi yasa Rabiya ke zaulayarshi cewa saida tayi aure ma yazo duniya , kuma shi mutum ne mai san godiya , yana san godiya akan duk abinda yayi maka , sannu da zuwa idan ya dawo cikin soyayya rakiya idan zai fita da addu’ar Allah ya dafa mishi akan duk abinda yasa gaba na alkairi , yawan damuwa da rayuwarshi ta hanyar yi masa waya idan baya nan , sai kuma idan yana gari bana zuwa ko ina sai makaranta shikenan matsalarshi.
Inna kuwa har yanzu babu ruwanta dani , ko gidanta mukaje dani da Dikko haka zata watsar damu sai mun gaji da zama mu tafi , dan dama Dikko shi komai rayuwarshi na dare ne yakeyi kamar mara gaskiya , shi yasa ko gidan Innar sai dare muke zuwa.
Ita dai yanzu Momy bata da sauran ja tunda tayi karatu na kuma ta fahimci rayuwata , kawai dai tayi ma Dikko addu’ar mu zauna lafiya , ɗiyar ƙawarta kuma da taso ta aurawa Dikko ashe itace karuwar bata sani ba , can wata ƙawarta ta faɗa mata yarinyar nan da take nemawa Dikko fa batajin magana har ciki aka zubar mata kwanan nan , sai ta zauna tayi karatun ta natsu tare dayi ma Dikko addu’ar su zauna lafiya da Sultana , sai kuma tayi hangen idan Sultana ta tafi bata san wace surukar zatayi ba , shine suke lallaɓa Sultana a jone , a taƙaice dai kawai ta gane idan bata share masallaci ba aradu kasuwa zata share hada mofin ,
Amma duk da haka nan dai yana nunamin nesa² dai , danshi yasan “yan gidansu yanzu sukeyin ka anjima su sauke ka ƙasa , Dikko dai yana tsaye kullum yana ta kwatanci yana ɗorani hanya , idan yaga na lauye nan zai ɗagoni ba faɗa ba ɗaga murya , zaice wannan da kikayi ba haka akeyi ba , haka zakiyi , zama dai nayau da gobe idan kuma yayi min wani abu nayi fushi , zaicemin ba’ayin fushi da miji kuma ko nayi miki abu ya ɓata miki rai ki riƙa haƙuri ba komai ne zakiyi fushi akanshi ba , rayuwa juyawa takeyi ba kullum akeyin farin ciki ba , kuma shima kanshi ba kullum zan sameshi yanajin haƙuri ba idan na hawoshi yana ɓacin rai ba abinda ya dameshi kawai zai zaneni ne kuma inyi masa godiya idan ya gama , wannan shine ake cema yau da gobe…
Ina shiga ahalin Inna sosai , duk abinda akayi ina zuwa , idan Dikko yana nan Ashiru ke kaini , idan basa nan ni zanje da kaina , idan yana Katsina da abokinshi Abbakar suke fita ni kuma a barni da Ashiru , idan kuma zai bar gari tare suke tafiya gaba ɗayansu , masu gadi da sauran masu hidimar gida ake bari , dan yanzu Dikko baida lokacin kaini wani wuri kuma ko yana gari nima kaina wahalar gani yakemin suna can wurin siyasarsu zaɓe yazo sunƙi haƙura su fita wasu su shiga , itama Momy bata zama suna can basa nan basa can hada Jiddah ake zuwa , niko banma ga fuska ba bare ince ko so ɗaya naje naga yadda akeyi , hmmmm Dikko ? ׳ halinshi saishi.
Gidan Sultan ma duk abinda akayi ina zuwa , amma ni Dikko baya bari na zama wuri , mintuna 15 shine nawa idan na fita , idan yaji dani 25 ne , makaranta kaɗai nake zuwa na daɗe , nidai bansan dalilinshi na wannan tsarin ba , ko gidan Inna idan naje shima haka ne , ni idan tana gari ina zuwa dan wallahi shi yanzu ya daina zuwa gidan kwata² , haka zamuje yaita gaisheta tanaji tana kallonmu tai mana banza , shi kuma tsakani da Allah ya bita² harya gaji idan kuma zamu tafi taita zagin Dikko tana aibatashi , shi yasa ya daina zuwa , tun kana da mutunci a idon siriki yana jin nauhinka har kazo kayi abinda zaka fita ranshi haba ina ma amfani da Allah…………..?
Sati biyu rabon da nasashi idona sai yau a asibiti , yazo ganin Kaka nima Ashiru ya kawoni muka haɗe , kuma shine ya iskeni , yana shigowa nasa takalmina nayi gaba ina jirashi waje , koda ya gama abinda yakeyi bansan ta ina aka ɗaukeshi ba kawai ya ɓacemin saida na ga an hau motoci babu shi , na koma ko an barshi ban ganshi ba , nima sallama nayi musu na wuce gida raina ɓace , kuma shi ba waya yakeyi ba saida ya turo text.
Duk yadda na kasa na tsare a ranar ban ganshi a gida ba , washe garin ranar ma baya nan , wata washe garin sai naji shi kawai ya halba Abuja bansan abinda yajeyi ba , kwanashi biyu ya dawo , ina makaranta ya dawo kafin in dawo harya bar gidan , naji babu daɗi dan haka na zauna na zuƙa mishi zuƙeƙen text nace kana can kana yawon kamfen ka manta da yankin iyalinka , waini waye ya faɗamin shi yawon kamfen yakeyi ? To nidai koma me kakeyi ina san ganinka , gani nan zuwa……… !
22/12/2019 ????????
*JAMILA MUSA…* ????????