KWARATA RETURN COMPLETE

KWARATA RETURN COMPLETE

     Mai gilashi da damuwa ta koma gida. Addu'arta ɗaya Allah yasa Sultana taje makaranta idan Allah ya kaimu gobe , yanzu dai tasan gidan Dikko bazai zuwu wurinta ba tunda ya dawo , itafa bawai tana gudun kar ayi ma Sultana abiyar zama bane ba , a , a , ita abinda Sharifa tayi mata kawai zata rama , kuma itama yadda ta sata ta kashe kuɗaɗenta wurin bin malamai dan ganin wancan daya fasa aurenta ta sameshi amma Sharifa tayi mata zagon ƙasa tou itama sai tayi gwale² da Sharifa da duk kuɗin data tara a bariki. Dariya tayi cikin farin ciki cewa an kunna. Yarinya da *MAI GILASHI* kike wasan , muje zuwa..........

   Saida na farka kamar yadda na saba a ko wane dare. Bayan nayo alwallah na fito na ɗauki wayata , missed calls na gani babu iyaka. Sai text in Dikko daya cemin inzo ɗakinshi yana kirana... Cike da fushi na fita na nufi ɗakinshi , da sallama na shiga ! Palo na sameshi kwance saman kujera yana cht , gitsi² nace gani. Ba tare daya kalleni ba ko ya daina abinda yakeyi a waya yace zo nan , wurinshi naje na tsaya ina fushi. Ɗago idonshi yayi ya kalleni cikin sigar zaman lafiya yace bacci kikeyi ne ? Ey na faɗa ina turo baki a tsiwace , to ? Sai yanzu kika ga text ina ? Ey , yayi kyau kije kawai. Bazar² na juyo , bayanta yabi da kallo saida ta fita ya maida hankalinshi a wayarshi yaci gaba da abinda yakeyi...

  Ina dawowa ɗaki na fara kiran wayar Mai gilashi , kuma a lokacin 2 saura. Bata ɗauka ba , saidai ta turomin text cewa tana ɗakin Alhaji waya bazai yiwu ba , amma in sani Dikko yana zuwa katsina , kuma yana tare da Sharifa , abinda take so ta sani shine. Bawai tana zargin shi bane ba , abu ɗaya take so inyi a daren nan in baibaita rayuwa kawai nayi mata ƙoƙari na kyautata a daren nan cht inshi da Sharifa takeso na cire kaf na turo mata dan Allah ! Kar in kirata kuma kar in maido mata reply kar ince a , a , tamin alƙawari zata bani labarin da bata faɗamin ba , idan ban turo ba kuma wallahi bazata faɗa ba. Kiyi ɗamara..... Ki tuɓe , kuma ki kife gidadanci , ai kin gane abinda nake nufi , kiyi tunani , ki tuna. Tuna׳... Ki tashi ƙura kuma kiyi ƙoƙori a yada dogon zango in jini...

    Shiru nayi bayan na gama karatanta saƙon Mai gilashi , wato nine zata latsa ? Tou wai meye ma matsalar ta da Sharifa ? Bata zargin Dikko kamar ya kuma ? Shi Alhajin ina iyalin tashi take ne a wannan dogon daren ne ? Ita Sharifar kuma wai me yasa ne kowa yakejin tsoronta ? Nima lallai ina san sanin abinda kowa yake tsoron ma Dikko Sharifa , ina san gani kuma nima ina san sani. Ajiye wayar nayi tare da ɗaukar ɗamara kamar yadda Mai gilashi tace , cire hijabi na nayi na ƙara mammatsa turare naɗan kakkaɓe dai bayan na tabbatar nayi na nufi ɗakin Dikko.....

   Da sallama na shiga , yana kwance a inda na barshi , amma yanzu ya juya baya yayi takurarriyar kwanciya mai nuni da gajiya. Itama sallamar a gajiye ya ansa ta. Saman hannun kujera na zauna tare da cewa sannu da zuwa. Ba tare da wani damuwa ko rashin jin daɗin da farko ban masa ba yace yawwa , shiru ya ziyarci palon har na tsawon mintuna 3. Nice na katse shirun da cewa ina Papi da Sharifa ? Shiru yayi baiyi magana ba , dakai nake. Juyo da kwanciyarshi yayi yana kallona amma baiyi magana ba , ɗan kauda kaina nayi gefe haka nan naji gabana yana faɗuwa. Ban sake magana ba na miƙe , riƙoni yayi tare da jawoni a hankali zuwa saman jikinshi yakai hannunshi yana shafo cikina.

 Kwantar da kaina nayi haka ta tsaye ba ta gefen fuska ba ina kalloshi cikin damuwa. Murmushi yayi kaɗan ya tsareni da ido , gyara kwanciyar fuskar tawa nayi zuwa gefe fuskata na fara wasa da gemunshi. Zame hannuna yayi daga wurin , sake maidawa nayi ya sake zameshi duk munyi haka yakai sau biyar , zuciya nayi na tashi da niyar fita , karki fita zo kiji , shiru nayi fuuu na wuce , An mata dake nake fa kizo nace , haka nan naji zuciyata tanamin tuƙuiƙi. Da ɓacin rai naje ɗakina , ina zuwa toilet na wuce na wanke hannuna ina cewa kuma bazan sake taɓa gemunka ka ba har abadan duniya , dan kaga ina taɓawa shine zaka ciremin hannu tou bazan sake taɓa maka ba tunda baka so Dikko...

    Cike da damuwa yabi bayan Sultana. Ita kuma a dai² lokacin data fito daga toilet. Rufe ɗakin yayi sannan ya matsa jikin bedsite ya ajiye tarkacen wayoyinshi bai mata magana ba ya wuce toilet shima. Gefen gado na zauna naci gaba da haɗe rai kamar an sace uwata , shima ranshi a haɗe ya fito kamar an kaiko mishi saƙon mutuwar uwa uba a lokaci ɗaya....

   Bedsite in kusa dani ya zauna tare da bani umarnin ni in matso kusa dashi , ƙin matsawa nayi na ɗauki wayata ina latse². Ki matso nan nace kuma ki ajiye wannan wayar tun kafin raina ya ɓaci , basar dashi nayi naci gaba da latsan waya cikin taurin kai da ƙaddarawa ma bashi a wurin. Miƙewa yayi ya ɗauki wayoyinshi ya tunkari hanyar fita , me yaji me ya gani ? Oho ya dawo , saida ya zauna ya ajiye wayoyinshi ya ɗan riƙoni jikinshi da soyayya , hannuna ɗaya ya riƙe tare da ɗorawa a saman fuskarshi yana shafawa a hankali harya gangaro saman gemunshi yana shafawa kuma ya tsareni da ido da kallonshi mai burgewa yanayin wasa da iskar bakinshi cikin salo mai yanke damuwa.

 A ɗan damuwance nace ai tunda baka so ina taɓa maka na daina , ina so yayi maganar yana rage girman idanuwanshi. Ai nayi fushi , na bari , ya faɗa yana min kallon rainin wayau. Ey dama dole zakace ka bari tunda ga Sultanar banza yanzu ne kasan amfani ta rashin kunya kawai. Da yanayin tsinkuwa ya kalleni yace wai me ke damun kanki ne ? Haba An mata ni banajin daɗin abinda kikemin haka ! Ey dama ai dole zakace bakajin daɗi tunda ka ɗaukeni Sultanar bayan fage.

 Tou waye ta bayyanannen fage An mata ? Kasan inda ka barta , ya za'ayi in sani tou ? Jakar da ta rakaka tafiya , taje ta rakoka Katsina tunda baka san hanya ba , ni danma ka ɗaukeni bansan abinda nakeyi ba ai baka faɗamin zakayi tafiyar ba saidai na tashi na gani zaka tafi , ko inda zakaje baka faɗamin ba sai wasu "yan iska karuwan banza , kuma bana sanka dama jira nake ka dawo Allah bazan sake zama dakai ba na ƙarasa maganar ina fara kuka , cikin kuka naci gaba da cewa da wata "yar iskar karuwa mai turo maka hoton tsiranci tunda dai yanzu ka daina so na kawai ka sallameni nayi gaba abuna , dan dana fita daga nan wallahi wani babban Alhaji zai kwasheni ya tafi dani can ya gina min sabuwar rayuwa mai inganci. Wacce babu firgici ko tashin hankali a cikinta. Ni ɗawisuwa ce kuma ai kasan babu yadda za'ayi abar ɗawisu sake yana yawo. Martabashi ake , ɗawisu baka rayuwa gidan matsiyata sai gidan kuɗi. Idan ba gidan kuɗi ba sai gidan sarauta , da rubibi za'a kamani kuma duk sai masu kamanin sunsha wahala duk sai sun bugu da wahala sannan mai rabo zai sameni dakel , a dakel inma sai mai tsanantaccen rabo gidan kuɗi nawa ka leƙa amma babu ɗawisu ? Kuma kaji kunya an girma ba'a san an girma ba mai gemun yaudara. Taƙaitaccen murmushi yayi ba tare da yace wani abu ba ya tsare Sultana da ido.

Ci gaba nayi da feƙa rashin mutunci , Dikko ya tsareni da ido cike da mamaki shi al'ajabi ma ya hanashi yayi magana yadai bita da kallo , kuma gidanka banza kaje ka ajiye duk jakar macen da zaka ajiye ni bana zama da kishiya , ai da daka dawo sai kaje can inda kake zama sai 3 na dare ka dawo gidan , a gajiye ya jawoni jikinshi ya rufe idonuwanshi cikin ɓacin rai yace ƙaramar yarinya. Daga haka bai sake magana ba ya fitar dani daga jikinshi yanayin fushi. Nayi kwanciyata naci gaba da bacci....

 Bayan Sultana tayi bacci Dikko ya tsareta ido yana sake² a zuciyarshi. A daren yau baiyi bacci ba , kuma ɓacin rai bai barshi yayi cht in dare ba , gyara mata kwanciya yayi tare da jan bargo dan lulluɓeta sai kuma ya tsaya yana kallon cikinta. Na tsawon wasu mintuna sannan ya tafi da bargon a hankali ya lulluɓeta cike da soyayyarta a zuciyarshi. Wayoyinshi ya ɗauka ya fita bayan ya kashe hasken ɗakin.

Ya so a daren nan yaɗan rage nauhi amma An mata ta ɓata mishi , a gaban idonshi take cewa wani babban Alhaji zai kwasheta ! Ashe idan ya mutu An mata mantawa datayi dashi ? Bara tayi mishi addu'a ba ? Papi da wani babyn zata zubar dasu taje tayi sabgar gabanta ? Tunani barkatai a ranshi. Ya saƙa ya warware baisan iyaka ba , ƙaramar yarinya ta zauna tai ta faɗo mishi maganganu na yarinta , mtsww wannan damuwa tasa kafin safiya ta waye Dikko ya kwanta rashin lafiya..... Fatarshi ya wuce kawai kar yaga wannan baƙar ranar wallahi..... 

   Ni bansan Dikko bashi da lafiya ba , gari yana wayewa na shirya nai tafiyata makaranta banje ta ɗakinshi ba. Papi kuma yana can wurin Momy dan Nabeela ta dawo da suka fara zuwa tacan shine ya liƙe wurinta......

 A makaranta. Yau ajin ba daɗi dan Mai gilashi bata zo ba , dana kirata na tambayeta abinda yasa bata zo ba , cemin tayi ina cht in da tace na turo mata ne ? Sai anjima zan turo miki , tou ya akayi kikaje  makaranta bayan kuma ance D ' K baida lafiya ? Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji , meya samu Dikko na tambayi kaina......? Meke damunshi har abun ya fita waje yabi duniya ni banda labari ? Tsinke kiran Mai gilashi nayi na fara kiran wayar Dikko , bai ɗauka ba , Ashiru na kira shima bai ɗauka ba , Umar na kira , tana shiga yana ɗauka , Umar kana ina ne ? Qerau , wai me yake faruwa a goruba ne ? Ba komai , kowa lafiyanshi qalau ? Lafiyan kowa qalau ya bani amsa... Kashe wayar nayi na sake kiran Mai gilashi. Tana shiga ta ɗauka , Mai gilashi waye yace miki Dikko bashi da lafiya ne...? Sharifa , ki duba a whatsapp na ajiye miki saƙo kiga cht inta da mijinki , gaskiya Sultana baki da wayo , duk kina ina wannan iskancin ke faruwa ne ? Waton shi mai wayau idan yayi magana sai ya goge maganarshi , na turo miki dai ki gani abinda na fahimta ni zanji da sauran aiki , saboda yaƙin yafi ƙarfinki nima nace na Dikko An mata , tana faɗin haka ta tsinke wayarta....

 Haka nan naji gabana yana halbawa ɗil׳ sai tashin hankali da nakeji gaba ɗaya wani ruɗu yazo min na kasa zama. Wurin Farisa nabar jakata na nufi gida cikin tashin hankali , a ƙofar shiga palon ƙasa nayi parking kuma gidan yana nan cike da mutane maza da mata kamar yadda yake kasancewa a ko wane rana. Kowa yana hidimar gabanshi da gudu na shiga ciki kai tsaye ɗakin Dikko na wuce ko takalmi na ban cire ba danni bana shiga ɗakinshi da takalmi komai sabuwarsu dana shiga palo zan tuɓesu......

  Zaune na sameshi gefen gado ya jingina bayanshi da kan gado ƙafafuwanshi miƙe ɗaya saman ɗaya ya rungume hannayenshi kanshi yana kallon ƙasa. A tsorace na isa wurin ina cewa Dikko me ya sameka ? Bai ɗago ba kuma baimin magana ba , kusa dashi na zauna na ɗago fuskarshi , kallona yayi. Kuka ? Na tambayeshi ? Gyara bakinshi yayi yana ci gaba da kallona , rumgemeshi nayi nima na fashe da kuka , cikin kuka nace me ya sameka kakeyin kuka ? Zuciyata , shine amsar daya bani , amma me yasa baka faɗamin baka da lafiya ? Na ƙarasa tambayar ina riƙe fuskarshi da duka hannayena biyu. Ba kinsan na kwana gidan ba ? Idan har ina da mutunci da daraja zaki tafi makaranta baki zo kika ce wannan banzan ka tashi lafiya ? 

  Kefa yarinya ce , ni kuma na tsufa inji ki fuskata ta fara squeezing. Kamar ƙaramin yaro yake cemin nima fa ɗan saurayi ne , duka²na a nawa nake hararata yayi cike da soyayya sannan yace , ni a haka nayi miki tsufa dai ko ? Idan dai ni tsoho ne kema tsohuwarce tunda daga ni harke kowa ɗanshi ɗaya da zaki wani kalli tsabar idona kicemin wani Alhaji zai kwasheki. An mata wannan mutunci ne ? Ke da , da ne lokacin ina Dikkona har kin isa ki faɗamin wannan iskanci ban kashe ki ba ? Kika mutu murus , babu wanda yaji ba kuma wanda yasan anyi saidai a nemeki a duniyar nan a rasaki. Ko yanzu ni ba iya dukanki ne banayi ba wallahi tausayinki nakeji saboda kina da ciki. Duk wannan iskarcin da kikeyi ba tsoro yasa na zuba miki ido ba , ko zan mutu idan bana tare dake ni banajin kaina ke nakeji. Duk a wahalce yake magana cikin shashsheka a sanyaye cikin laushin murya maisa natsuwa....

Ki kalleni tsaf daga samata har ƙasa na kinsan ni ba sakaran namiji bane ba , kuma kinma san na tsufar kikace kina so na ? Tou ni ba tsoho bane ba , duka² shekaruna nawa ma ? Tsoki yaja sosai , tare da nunani yana cewa a gabanki ma zan zauna ina kwancewa har nake da lokaci maida miki magana , tsohon ne yayi maganar yana min wasa da harshenshi cikin salo mai ɗaga hankali ya raka wasan da kallonshi maisa mutum yaji cikinshi na halbawa , a kasalace na matsa da fuskata kusa da nashi na ɗora bakina a bakinshi. Maida harshenshi yayi yana murmushin jin daɗi tare da lumshe idanuwanshi a hankali cike da shauƙi , yana nuna yanayin zaƙuwa kuma har yanzu idanuwanshi a rufe , baya nayo da fuskata ina kallon kyakkyawar fuskarshi , bai buɗe idonshi ba yana a rufe kenan yana jiran tsammani , jina shiru yasa ya laliboni tare da riƙo kaina da hannunshi jikinshi yana kyarma ya haɗe cikin soyayya , bayan wani lokaci ya cire “yar guntuwar hijabita ya kwantar dani gefenshi ya kwanto shima har yanzu idonshi a rufe cikin yanayin farin ciki. Battery low……

  Mai gilashi kuwa saida ta gama tuɓe kaf sirrin Sharifa sannan take tambayarta shin ko Dikko yana da wani logo ne ? Sharifa tace bashi da. Shi miskili ne kuma yana da wahalar sabo baya maganar data wuce biyu , baya dariya kuma baya murmushi idan kuma surutunki yayi mishi yawa zai tsareki da ido ne. Kinga taya kuwa za'a iya gano logon shi ? Amma da me kike da ibar mishi fili ? { abinda takeyi tana ɗaukar hankalinshi kenan } Sharifa ta faɗa mata , Mai gilashi tace tou ko ya taɓa faɗa miki aibun matarshi ne ? Da dalilin yasa zai aureki ne ? Sharifa tace gaskiya a , a , yadai cemin shi yana san matarshi sosai kuma yana tausayinta bai haɗata da kowa ba kuma yarinya ce ni na girmeta. Duk kuma wanda ya taɓota tou ba itace ba shine aka taɓo. Idan An mata tayi kuka shine idan tayi farin ciki shine. Wanda yaso mata farin ciki shine yaso , kuma duk yadda yake san mutum idan ya aibata ko munana mata tabbas zaija layi tsakanin shi da koma waye , shine kaɗai ya isa ya ɓata mata kuma shine farin cikinta duk duniya bata san kowa ba saishi , haka bata gane kowa saishi. Shi kuma itace rayuwarshi , lumfashi , bugun zuciyarshi , itace komanshi dan haka in kiyaye. Kuma shi abinda yasa zai aureni shi bawai ra'ayin shi bace ni , ba irin tsarinshi bace ba. Umarnin Dad inshi ne , Mai gilashi tace tou me ya kawo akayi maganar ne ? Ko haka kawai ya faɗa ? Sharifa tace nice dai naɗanyi maganarta , duk dalilin maganar nan kuwa matar Babanshi ce tayi wani aiki akan shi bansan ko na miye ba shine tace idan naje wurinshi naɗan aibata ita matar tashi kome yace nazo na faɗa mata ta nan zasu gane idan nasara ta samu karɓuwa...... Bayan ta gama jin duk abinda take so taji. Ta turawa Sultana saƙo duk abinda takeyi ranar yau tayi ƙoƙari tazo gidanta , bayan ta ajiye mata adireshi gidan....

 Hafsa da Amisty gurfane a gaban sabon malamin da ta samawa Hafsa kamar yadda ta faɗawa ita Hafsat in. Saida ya zana ƙasa ya goge , ya sake zanawa , ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama zane²n ƙasarshi sannan ya fara rattafo mata bayani kamar yana karantawa a rubuce. Ya kuma ɗora da cewa ta gode Allah da tazo wurinshi daga yau kuma damuwa ya ƙare. Aurenta da Dikko anyi an gama kuma a ƙarshen watan nan ne , yaci gaba da labarta mata rayuwarta ita kanta , Hafsa tayi na'am da wannan bayani sosai dan haka akayi ciniki bugun farko miliyan biyu ba tayi idan aka taya ko anyi aikin baya ci , za'a siya jajayen raƙuma da jajayen sanaye jajayen tumaki tattabaru jajaye da kaji suma ja kuma duk ko wane za'a siyo mata da mijinta guda biyu² , shanaye maza biyu mata biyu kenan huɗu² mace da namiji a cikin ko wace dabbar daya faɗo....

 Zatayi magana Amisty ta rufe mata baki tana cewa malam yi haƙuri zamuyi magana , jibi idan Allah ya kaimu za'a kawo kuɗin , tana faɗin haka taja Hafsa suka tafi. Bayan sunje gida ne Hafsa take cewa ita ina zata wani samo 2million ne ? Tada ma sigari wuta Amisty tayi saida ta ibi hayaƙi tace riba zaki ci ne , duk gidan da kika ga anyi zazafen abinci tou karki bincika ma'ajiyar abinci dalilin haka da sanin gaskiyar sirrin yana wurin mutanen gidan. Ki zuba kuɗi gona yarinya ko kin samu albarkatun gona , wannan malami da kika gani malamin "yan siyasa ne shi yasa kikaji aikin nashi da kuɗi sosai , ga tsada fa amma akwai biyan buƙata , gwamna kanshi wurinshi yake zuwa shine ya ɗaurewa gwamna ƙugu ya koma mulki , ai ya miki sauƙi ma ne saboda ni. Ai da banje ba aikin nan kila sai ya kai miliyan huɗu , ba nace miki shine yayi ma Sultana aiki ba? Kinga tana can ta shige abunta. Hafsa tace miliyan biyu fa Kaka ? Amisty tace miliyan biyun , miliyan har kuɗi ce da zaki tsaya kina wani jinjinata ? Hafsa tace ai inda zan samosu shine damuwata....

  Kashe sigari Amisty tayi sannan tace ke kuwa kike da miliyan biyu da wurin samunta. Idan baki dashi ai Babanki yana da. Kije kawai ki tattaro takaddar wani ƙaton gida ki siyar , idan aka ɗaura aure ƙarshen wata D ' K zai biya. Kinga basai mu siya ma Dady sabon gida ba a manyan anguwanni dake cikin garin nan ba ? Murmushi Amisty tayi tare da nuna Hafsa da ɗan yatsa manuni tana cewa anya ma mu D ' K zai barmu muje gidanshi......? Dariya Hafsa tayi cikin jin daɗi cewa sai kunje mana tunda yana aurena ai dole ma ne yaso duk abinda nake so. Amisty tace yawwa "yar gari yarinya ta gano hanya mai takaba ta buƙaci kwarto...

 Hafsa kuwa dariya tayi tare da warware hannunta taci gaba da cokalar ciwon tsakiyar hannunta , ihu take dan azaba amma cikin yanayin kafurci take ƙara faɗaɗa wurin dan bata so ya warke tunda malaminta yace idan hannun ya warke bata babu auren Dikko har abadan duniya , shi yasa ta hanama hannun nan zaman lafiya kullum sai ta kwareshi , sai rami hannun yake yana tafi , wani irin wari yake mara daɗi har ya kusa ɓulewa ta baya , dan dai karya warke ta rasa Muhammadu Dikko. Ba magani kuma ba'a buɗeshi yana shan iska kullum sai caɓewa yakeyi abunda zot takaici......

Mardiya tsakiyar dare ta firgice. Bayan an kaita maƙabarta a daren , ganin gari yana tafiya , shiru yana ƙara dosowa. Maƙabarta tana daɗa ɗinkewa duhu yana ƙara bayyana ta gigice , hmmm hausawa dai sunce komin hasken farin wata dare abun tsoro ne , ga dare ga matacci kwance a cikin ƙasa , wadda su duniyar da komai sun tattara sun ajiye badan sunso ba suka tafi suka kwanta. Duk kashedin da Aunty Suwaiba tayi mata bataji ba , saida dare ya kusa rabawa biyu taji sukuwa saman bedinan dake zagaye da inda aka ajiye ta a cikin mankara kukan tsuntsaye da duk wasu ƙwarina dake cikin maƙabarta ya ƙara yawa kasancewar duniyar tayi shiru. Dan haka ta yada likafanin da aka lulloɓota dashi ta tsallake katanga ta ibi hanya tsirara , hauka sabon kamu......

  Boka da Aunty Suwaiba basu san ba Mardiyya ba. Saida alfijir ya fito , bayan anyi da Mardiyya zata dawo alfijir yana ketowa , har 6 saura ba Mardiyya ba labarinta dan haka suka tunkari maƙabartar ba labarinta sadai mankarar da likafinin data yada ina ta tafi............???

    Kwance take cikin kujera , ba kwanciya irinta ta yadda ake kwanciya ba , zaune take tayi irin kwanciyar nan ta "yan gayu kujerar ta riƙeta dai² burgewa , wani fitsararren ɗinki ne jikinta , halittar jikinta tayo waje ta kashe ɗauri dai² da zamani , hoto tayi tare da turawa daga ƙasa ta ajiye mishi barka da dare... Tun kafin daren yayi har anyi an ajiye. Yusra... Bayan ta gama hotonta kuma ta fara tallar surar jikinta tana video , duk saida ta safke kayan jikinta tayi ma Dikko video ta nuna mishi muhimman wurare a jikinta tare da faɗa masa ta sadaukar mishi. Tana video tana faɗa mishi nashi ne fa duka ya gani ya daina kawaici , kuma me yasa baka kallona idan nazo wurinka ? Baka cewa nayi kyau ? Videon ma har yanzu baka cewa ka gode ? Ƙafarta ta ɗaga ta ɗora saman madubi tana ci gaba da ɗauka tanayi tana dai maganganu irin nasu na gogaggin karuwan da suka san hannunsu , saida ta gama tasharta da iskanci iri² ta yadda duk musulincin namiji da tsoron Allahn shi idan ya gani saiya ƙara kallo sannan ya fara istigifira ya goge , idan kuma sheɗan yayi galaba ya tafi ruwa , maida kayanta tayi sannan aka yi ma Dikko vye² aka wani ajiye mishi a whatsapp..... 

    Murmushi yayi a wahalce. Cikin jan hali da jarumta bawai dan yanajin daɗin yinshi ba , shi kaɗai yasan bala'en dake zungurar mishi zuciya , danben ma dakel ya maida naushi saboda baiyi shi cikin natsuwa ba , wallahi baida lafiya zuciyarshi tun jiya take zugewa. Dakel ya kalli Sultana dake kwance gefenshi tayi ruf da ciki tana kuka , a wahalce yace An mata ki rufamin asiri ki dawo nan ya nuna bayanshi yana cewa kuma ki gyara kwanciyarki. Bazan koma ba , da damuwa yace to² ba komai haka ma yayi , daga haka bai sake magana ba ya dafe ƙirjinshi yana yin bayyanan nen numfashi , jin bai sake magana ba kuma na gaji yasa na tashi na koma inda yace in koma in kwanta tun farko ina mita cewa kuma a saman cikin zan kwanta , shiru yayi yaƙi magana yana kallo bango da yanayin tunani. Jin zan mutu yasa na ɗauki wayata na nufi ɗakina... 

  Saida nayi wanka na gyara jikina sannan na ɗauki wayata na buɗe data nake duba saƙon da Mai gilashi tace ta ajiyemin , ganin cht in da yawa yasa na kasa binshi na tattara na ajiye , amma na duba saƙonta da tace ni duk yadda za'ayi inzo gidanta , kuma zanje , saida nayi azahar na shirya dan zuwa gidan Mai gilashi , komawa da nayi ɗakinshi ɗaukar makullin mota yasa yasan fita zanyi , duk da baida lafiya ya balbaleni da masifa waini wace irin mahaukaciya ce ? Baya faɗamin baida lafiya ba shine zan fita ? Tou inje in fitar idan na dawo zan samu ya mutu sai in zuba ruwa ƙasa insha. Wuri na samu na zauna ina kallon ƙasa , yaci gaba da cewa zaki ga kamar ina takura miki ne duk girman duniyar nan wanda kike ganin yafi ni ko yafini sanki yaudararki yakeyi , niɗin dai da kika raina nine zan faɗa miki ko zai miki zafi , ai baka san abinda zanyo ba. Koma me zakiyo bazaki fita ba , kuma na rantse da girman Allah idan dai kika fita yau wallahi idan kika dawo saina zaneki ki fitar wawiya dake. Ƙasa² nace dole kacemin wawiya tunda ka samu abinda kake so har ka samu bakin magana , tsaf ya jini yace kije duk inda kike so , in Allah ya yadda zan zuba miki ido kuma saina ƙara aure ke kije kiyi yawo tunda shi kike so , yadda kika san katsina ko ni kaina bansan garin nan ba , lungu da saƙo sai ance Dikko naga matarka kullum kina bisa titi ke da kikafi ƙarfin mijinki. Idan na ƙara auren ta zauna ta kula dani , ta dafamin abinci ta bani inci da soyayya bata bari yunwa ta kamata , abinci akan lokaci kalami masu daɗin sauraro bata barin kunne na yaji magana mara daɗi saboda soyayya bare taimin gori na kwanta da ita , kullum ma nema na zatayi ko bana so sai ta bani tana ƙaramin cikin san kasancewa da tsari. Taimin wanka ko ɗakina an gyaramin , idan banda lafiya ta riƙa bani magani insha tanamin sannu. Ta faɗa da launin so. Kije can kita haukarki ta kwaceni miki ni sai gani na yayi miki wahala. Ina can inda ake riritani kamar yaron goyo , da nace uhum za'ace ina ne ....? Ya faɗa a shagawaɓe yana wasa da idanuwanshi. Kallonshi nayi ina kuka , yace ey aure ba fashi tunda ke kinajin yarinya ce kije kita rashin wayonki , duk kyan ɗawisu idan baida ado ai komai kuɗi yai maka banza bara ka siya ba , magana ce ya faɗa mata a kaikaice ta zancen da tayi mishi a daren jiya...

  A tsiwace nace zan gyara maka ɗakin , bana so zan gyara abuna. Yi haƙuri , ki naɗa gammo ki ɗauka keda za'ayi ma abiyar zama , ƙara kallonshi nayi yace daina kallona kar in cake miki ido ya ƙarasa maganar yana fiddo duk girman idanuwanshi , ƙara fashewa nayi kuka na tashi na fara gyara ɗakin ina kuka. Murmushi Dikko yayi tare da bin Sultana da kallo cike da tsantsar so , yanzu ya gano ciwonta , a ranshi yace kaji yarinya da baƙin ciki zata hanani zaman lafiya ta firgice ta tafi Mama tace ta gama aurena , da gaskiyarta fa , wallahi An mata babbar ƙaddara ce sai mai rabo zai sameta , tabbas idan ta tafin a tsautsayi labari zaisha ban² , ki rufemin baki bana san kuka kin sani ko ? Bazanyi shirun ba , tou kiyi zanzo in kamaki. Amma ai kasan mai ciki batayin aikin wahala kace inyi , ni nace kiyi aiki ne ? Amarya nace ko kece amarya ? Allah yana kallon ka na faɗa a dai² lokacin dana zo ina goge gado kuma har yanzu banyi shiru ba... 

  Da amaryar da zan auro ce idan tazo kusa dani sai ta sumbaceni a nan ya nuna yana min kallon ƙasan ido , cikin fushi na sumbaci inda ya nunamin , riƙeni yayi yana wannan kukan yaudarar nashi da bana so , a gajiye na kwanta saman jikinshi. Murmushi yayi sannan yayi magana da yaudararriyyar muryarshi ya faɗa a wahalce An mata daina kuka yayi maganar yana hawo dani saman gadon , kalli , kallonshi nayi ina fushi , kwantar da idonshi yayi yanamin kallon rainin wayau , yi haƙuri ya bada haƙurin yana rufeni a bargo....

Kwaɗo…
A gajiye ya shigo gidanshi ya ɗibo gajiyar makaranta , yunwace yake dan ya fita baiyi kalaci ba haka ko wanka baiyi ba , saboda da ya dawo masallaci tuni Hadiza tazo gidan har ta shiga toilet in tanayin wanka , haka nan ya fita waje ya ɗan wanke jikinshi ya goge bakinshi da omon wanke baki ya fice daga gidan. Yanzu ya dawo palon kuma cike yake da mutane , hada Mai gilashi data gangaro kwaɗo itama dan rage rana take zaman jiran kiran Sultana amma shiru kakeji , ita kuma tana tsoro ta kirata ace Dikko yana nan… Mijin Halima yana shigowa Mai gilashi ta gaishe ta fice da damuwar rashin kiran wayar Sultana….

 Gaishe shi kowa yayi tare da mishi sannu , ansawa yayi da yanayin anshi karka rasa ya wuce ciki. Shiru² Halimatu ta shigo amma taƙi ta shigo , ga yunwa yanaji kuma a matse yake yana san ya fita yaje toilet amma yana jin nauhin ratsasu suna zaune a palo ya shiga ya kuma ratsotso ya fito yanajin kunya gaskiya...

Matarshi ya fara kira a waya , amma sai bata ɗauka ba daga palon tace ya akayi ne kake kirana ? Bayan kasan ina gidan , baiyi magana ba ya tura mata text tazo yana kiranta , duk saida ta nunawa ƙawayenta wai kiranta yakeyi , shewa akayi gaba ɗaya aka dunƙule kawuna wuri ɗaya ana zance maganin data sha shine haɗarin , ashe ba dare kaɗai yake aiki ba harda rana , saida ta ballabaɗashi tayi bedroom..

 Halimatu dan Allah kuɗan koma daga tsakar gida zan shiga toilet , cike da rashin kunya tace mu koma waje duk iska da ƙura ta barbaɗemu muyi datti ? Da yanayin san zaman lafiya yace duka mintuna nawa zanyi in fito in bar muku gidan , gaskiya bazamu fita kaje kayi abinda zakayi ai su basa kallonka , haba Halimatu sai in ratsa matan aure da gajeren wando in tafi toilet tsabar ɗan iska ne ni ? Tou meya damesu da kai ? Kaje kayi huɗɗoɗin ka , Halimatu wai me yasa haka ne ? Tou taramin mutane kai mai gida , dama tun jiya naga kakejin masifa , kace buhun shinkafa bai kai maka yadda kake so , maganar jiya ya wuce kiyi haƙuri.....






*Jinin Katsinawa ce....* ????????

JAMILA MUSA….
BRILLIANT WRITERS ASSO ????
-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-

           *KWARATA RETURN...*
  _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

Rubutawa…
JAMILA MUSA…

   *SAI NA AURI D ' K*

???? —— 5

  Ai ba maganar inyi haƙuri bane ba. Idan dai na fahimce ka kawai dai kana mana kora da hali ne. Ah² yi haƙuri ba haka nake nufi ba , yayi maganar yana nunawa da hannunshi da yanayin ladabi. Inda ya ajiye rigarshi daya cire ya matsa ya ɗauka yana cewa ai duk abun bai kai haka ba , nayi wankan ma da daddare idan sun tafi , da ka rufawa kanka asiri. Ɗan shafa gefen fuskarta yayi yana murmushi tare da cewa idan akwai sauran abincin ki bani sai in tafi can shagon Salihu inci....

 A tsiwace tace na ajiye maka sai naga bai ishemu ba. Kawai dai mun cinye nasan ka siya can waje idan ka fita. Da kinɗan silalamin ko taliya tunda akwai miya wallahi yunwa nakeji sosai , abincin sayen nan ina ci zuciyata tanamin ba daɗi , tsoki tayi ta fice tana gunguni har palo ba tare data bashi amsa ba. Tana isa wurinsu Hadiza taci gaba da cewa wallahi babu wanda zaisani tsira wata girki yanzu danni ba jakace ba , gidajen abinci nawa a garin nan ? Dan dai kawai kar ya fita ya isa. A shi a dole sai yazo gida yaci shi mai mata....!

 Hadiza tace ya akayi ne ? Shi mana , shi waye ? Abdul mana , meya faru ? A dai² lokacin daya fito dan fita ita kuma tana cewa wai in dafa mishi abinci. Ko tausayi na ba'ayi a gidan nan , tun safe nake hidima da mutane a ya kamata na riƙa hutawa. Cike da ladabin ɗan ƙunama Hadiza tace haba dan ɗan wannan ? Ai komu kika ce a cikin mu wani yayi zamuyi , ba komai ki huta bara a dafa maka tayi maganar tana miƙewa , Halimatu tace ai da kin barshi tunda fita zaiyi ai yace zai siya a waje. Hadiza tace ah yi haƙuri Oga a girka babu jimawa , tayi maganar tana shiga kicin... Salam² ya koma bedroom.

 Ita kuma Halimatu ta zauna a palo cikin ƙawayenta akaci gaba da maida yadda akai ana shewa.... {{ Kina aikin me "yar uwata...? Ƙawar banza ƙawar wofi...? Wace ce ita ? Me kike nema a wurinta da har zaki fi²ta ta akan miji ? Wacce yau tana iya canja ki , shifa miji ? Ko kun rabu idan da zuri'a an zama "yan uwa. Hmmm ki kiyayi kanki da duniya kinji ko....??? Murmushi , kuma bawai nace kici ƙaniyar ƙawarki ba , a , a adai riƙa abun da lissafi... Karki canja ma ƙawarki fuska tace ƙawata lafiya ? Kice Jamila Musa tace a sakeku a riƙe miji , ba haka nake nufi ba , kudai fahimci inda na dosa. }} cikin ƙan²nin lokaci ta gama dafo abincin ta kawo mata , da farko tace Hadizar ta miƙa mishi , Zainab tace a , a ki kai mishi mana... Wai ita a dole nan tayi fushi wai wallahi bara takai mishi ba tunda jiya yace ana cinye abinci da wuri , {{ ba dole yayi miki faɗa ba ? Kin san wahalar daya sha ya samo ? Wace ce ke da baraya yi miki magana ba ? Ke kaɗai ya ɗauki alƙawari zai ciyar , yasharwa , tufatarwa , ilimantar magani idan baki lafiya wurin zama da kuma kyautatawa a gaban magabatanki haka ya ɗauko alƙawari , baice dake da ƙawayenki ba , ke kaɗai ya biya sadaki aka bashi kuma yayi alƙawari ya ɗauko ki. Duk abinda yayi ko ya bari kikayi da dukiyarshi ko abincinshi da komai nashi tou wannan shine kyautatarwa. Idan kuma bai fita haƙƙin naki ba zai haɗu da sakayya. Akan me zaisa ya samo abunshi ki wulaƙanta mishi ne ? Ko kece kike nemo mishi kuɗin ? Ba kuma nace ki riƙa yiwa mutane rowa ba , idan kinji maƙota ki noƙe risho. Ba rowa zakiyi ba , abinda ka bada shine naka. Kar kuma kina cin abinci idan wasu suna zuwa ki ɓoye kiƙi basu. Ko ki daina fita haƙƙin masu haƙƙin ku basu ba , kar abun duniya ya rufe miki ido. Ki bada , wanda kika bashi zaiji daɗi. Kuma zaiyi godiya da addu'a wa mijinki Allah ya ƙara buɗi da rufin asiri. Bana nufin kiyi rowa wa mutane a , a , ba haka ba , ina nufi dai abun komai kiyi shi dakai... Bawai duka "yan anguwar ku zaki ciyar ba , sai ki duba dai² ƙarfin mijin naki , wani yana da ikon ciyar da jaha ɗaya ma , amma mugun marowaci ne , tou karki almubazzarar masa amma a hankali ki riƙa nuna masa matsayin kyauta da kuma kyautata ma wanda baya da ƙarfi sai kiga a hankali yau da gobe ya rage , wani kuma yana san ya ciyar amma baida ƙarfi , kawai dai duk abinda za'ayi a riƙa sa nazari tunani da kuma lissafi... }} shine take fushi dan yace abinci yana saurin ƙarewa. Shin tasan dalilinshi nayi magana ne ? Ga nauhi yayi mishi yawa , gidansu shine yake riƙe dashi , ga Allah suka dogara shine sukayi ma zuru , itama gidansu Halimar ana aika musu da kasafi duk watan duniya , tou ke zaki nuna masa yadda zai kyautata a rayuwa ? Wace ce ke ? Daga "yar karo baki kau ba fa..... Sai wani kumburin banza take tana cika fuska tunda taga gareta ya miƙa wuyanshi. Mai abun hana miji idan ya buƙata , waye yace miki hana miji haƙƙi shine zai siya miki mutunci ? Tou idan dai wannan shine mafita a gareki zero.......

  Dakel Zainab tasa Halimatu takai ma mijinta abinci , tana zuwa ta dungura mishi tayo waje. Shi kuma yaso taɗan zauna yana ci ana ɗan tattaunawa irin nasu na ma'aurata , amma ita ba ruwanta tunda dai ta samu ya ɗaure mata ƙugu zataci tasha tayi gulma tou an biyata , sai idan an kawo kayan mata ta loda ta riƙa mishi ƙarya yana bata kuɗi , ita kuma taita loda ma cikinta kamar akuyar mahaukaciya.....

 Yau babu abinda na girka dan tunda na kwanta bacci sai bayan la'asar na farka , bai kuma wani tasheni ba saida na gaji na tashi dan kaina. Babu inda ya fita yaje saboda bayajin daɗi kuma ma ai dama shi ba ma'abocin fitar rana ba ne. Ganin na kasa tashi ne yasa aka kawo mishi abinci daga gidansu , na nashin dandai ina da cikin amman da ko ba abinda zanyi mishi saiya tasheni dan dai ya ɓatamin rai. Ba abinda naci tun kalacin safe sai bayan sallah isha'e na jiƙa garin rogo { garin kwaki } kuma Dikkon nasa da kanshi a siyomin , dan bana ra'ayin abincin da aka kawo. Shine yasa aka kawo buhu ɗaya. Bayan yayi faɗa wai salan inje inba babynshi wahala zanci wani gari bana daijin magana , nace baby ne zaici garin ai bani ba , wai babu wani ya faɗa yana hararata nace da gaske shine yasa aka kawo.

 Bedroom na sameshi zaune saman gado da irin zaman ɗazu yana kallon ƙwallo. Kusa dashi na zauna , ina zama ya gyara min zamana tare da matsowa ya kwanta ya ɗora kanshi a jikina ya riƙe ƙuguna da duka hannayenshi yana kallona , nima kallonshi nayi tare da cewa tashi muci , ɗauke idonshi yayi daga kallona yana kallon tv yace me ye ? Gari , murmushi yayi me sauti yana cewa Allah ya sawaƙe , garin ne Allah ya sawaƙe ? Ah ni bana iya cin garin gaskiya sai kace inyamuri....? Aini inyamurar ce shi yasa zanci , shiru yayi bai sake magana ba , ya ɗauki wayarshi yana duba dokuna.... Shikenan tunda bara kaci ba bari in tafi nayi maganar ina ƙoƙarin tashi , riƙeni yayi sosai yaci gaba da abinda yakeyi a waya....

 Ni tafiya zanyi , ba tare daya kalleni ba yace kinyi fushi ? Ey , tou ina ci kawo min cokali , ai bada cokali akeci ba , da me akeci ne ? Da hannu , tou bani ya ƙarasa maganar yana buɗe bakinshi ba tare daya kalleni ba... Ai haka kayimin haggunce , ya zanyi ? Ka tashi.... Tashi yayi zaune amma har yanzu hankalinshi yana kan wayarshi saidai bakinshi a buɗe yake , bashi nayi , riƙeshi yayi a bakinshi tare da ɓata fuska ya taɓe baki yana juyashi , ƙara ibowa nayi. Da garin a bakinshi yayi magana cewa dan Allah An mata ki kyaleni kinga banda lafiya..... Dan Allah kaci , kallona yayi a sakace yace baya tafiya , jeka dashi kawai ka kora da ruwa..... Idan banci ba zakiyi kuka ? Dariya nayi dan yadda yayi maganar kamar ƙaramin yaro wallahi. Shagwaɓa tana mishi bala'en kyau kuma yana burgewa idan yayi , hada hawaye. Na faɗa ina kallonshi da irin kallon da yakemin. Ɗan kauda kanshi yayi gefe tare da shafa kanshi yaci dakel , yace ngode. Hahahaha bawan Allah , yau da Jiddah tana nan da nace mata Dikkon ma da kowa da kowa yake taƙa dashi ni nasa ma yaci garin kwaki dan ubanta....

Aimu dama mun saba , kuma ni ban manta ba har yanzu nasan martabar gari , duk irin matsayin da nake a yanzu baisa na manta da rayuwar baya ba. Ai gari yayi mana kuma mu bama wulaƙanta shi duk matsayin da mukaje muna tare da gari gaskiya , kuma ina ƙara godiya da Allah yasa nake a wannan matsayin , haka nan naji ina sha'awar garin. Na ɗan haɗo rayuwar baya da yanzu ! Nayi tunanin nima bazan iya ci ba , ashe dai zan iya ? Allah ya ƙara yalwata arziƙin Dikko amin.... Da gefen ido yake kallona har na gama ci. Saida na gama ya kalleni ta gaba yace sannu , yawwa na faɗa tare da tashi dan fitar da filet in , idan kin jiye kizo , ni bazan dawo ba , ki dawo nace miki , ban sake magana ba na nayi gaba , tana fita ya tashi dakel yaje ya ɗauki cingom yabi bayanta.....

Ɗakina na sameshi kwance yana waya , ɓata rai nayi tare da samun can gefe na zauna na ɗauki wayata , text in Mai gilashi ne kaɗai , ban zo ba , me yasa ? Idan naga D ‘ K baya nan in kirata dan Allah , yau D ‘ K bai fito ba lafiya ? Ko har yanzu baida lafiya ne ? Inyi ƙoƙari in riƙeshi gida na kwana 3 kar in barshi ya fito in rufa mata asiri don girman Allah za tayi wani aiki , kuma inzo makaranta duk yadda za’ayi idan Allah ya kaimu inzo makaranta dan Allah…..

Taya zan riƙe Dikko a gida in hanashi fita ? Abinda ma baya yuwuwa ne gaskiya. Wane aiki ne zatayi ? Koma dai miye Dikko bai zama , yanzu ma jira yake dare yayi ya lallaɓa ya fece abunshi , zuciyata kuwa cewa tayi ai saidai ki jashi kuyi faɗa kawai tunda dai yace bazai dakeki ba tunda kina da ciki. Ci gaba nayi da cika fuska ina ɓata rai , bayan ya gama waya yace An matana miye ? Dikko wai mema yasa kaje kayi ma karuwa liƙi ? Da yanayin rashin jin daɗi yace ba karuwa bace ba , Mamanta fa ƙanwar Dady ne. Ni bana san sanin wani dangantaka ko alaƙa , amma me yasa baya bakimin magana ba sai yanzu ? A lokacin abun bai shafeni kamar yanzu ba , yanzu kinajin fitina kenan ko ? Ey fitinar nakeji , tou ai ba ƙyaleki zanyi ba , zaneki zanyi. Fashewa nayi da kuka sai abun yaci gaba da zungurar min zuciya kamar yanzu ne akeyin abun wani irin azababen kishi yaci gaba da ƙwal²rmin zuciya. Da videon da Yusra ta turo mishi gaba ɗaya na ƙwace na fara ɗuɗɗurma ma Sharifa da Yusra zagi , da sauri ya taso yazo kusa dani yace haba An mata meye haka ? Cikin kuka nace dama ai dole zakace zaka dakeni tunda na taɓo karuwowin ka , kiyi a hankali kinsan bamu kaɗai ba a gida , so kike ace kin rainani ne An mata ? Ace na rainanka kaima ai raini yasa kaje kayi mata liƙin a gabana , da Jiddah ce ka isa ? Saini duk wani shararka da komai akan An mata. Saina faɗar da ƙarfin dandai kar asirinka ya tonu asan kana da karuwowi , salati Dikko yayi tare da cewa idan dai kika kasheni hankalinki ya kwanta... Nine ma nake da karuwowin ko ? Ni An mata ? Ya ƙarasa maganar yana riƙoni jikinshi , fizgewa nayi na miƙe naci gaba da kuka ina zagin su Sharifa.

 Riƙeni yayi da ƙarfi. Ya rumgumeni jikinshi , bayan wani lokaci ya sassauta riƙon zuwa riƙo da tako mai kyau ya fara maida lumfashi da salon da yasan zaisa na ɗauke wuta da wuri , ƙasa² na farayi da murya cikin shashshekar kuka ina cewa amma ai kasan baka kyauta ba , yi haƙuri yarinya na yake faɗa yana ƙara sautin. Kasala ta fara zuwa. Dakel na sake furta kuma na ɓata dakai , ai bamu ɓatawa An mata yayi maganar yana fara kukan kissarshi , wani ɗan iskan kuka yakeyi cikin kurman sauti maisai jiki ya mutu da sauri , sai ya riƙayin wani jaririyar ƙara "yar ƙararrama yana numfashi , shidai yasan yadda yake abunshi amma dole dai idan kikaji sautin sai tsikar jikinki ya tashi , kasala da san kasancewa dashi ya tattaru ya lulluɓeki a lokaci guda dan da shagawaɓe yake fitar da sautin sai kuma ya ƙadaddabe ki da raunanannen riƙo , hmmm Dikko ? Bayajin magana kona misali. Saida ya gama sinsineni ya fara lasar bakina , muƙus nayi shiru , a gajiye yaja ni ya ɗora saman tsakiyar gado dakel. Yana maida numfashin wahala da yanayin rashin lafiya cewa bakijin magana kuma tunda kika ɓatamin rai naushin mai ƙarfi zanyi , riƙeshi nayi ina kuka , kallona yayi a shagwaɓe yace me ye kuma ? Yayi tambayar yana ɗaure fuska , na bari , a , a ya faɗa badai bakijin magana ba ? Yi haƙuri. A wahalce ya gyara kwanciyarshi yana cewa tou zoki bani haƙuri ya ƙarasa maganar yana min dogon kallo ranshi a haɗe........ Matsawa nayi kusa dashi nace yi haƙuri , kallona yakeyi har yanzu , bayan kamar mintuna biyu yayi murmushi tare da ɗan tattauna cingom da salon jan rai sannan ya huroshi irin abun nan kwai ya kuma riƙe kwan. Da kanshi ya nunamin in sauka muje , sauka nayi. Shima ya sauka ya biyo bayana har ɗakinshi , inda aka ajiye kayan da ya dawo dasu daga tafiya yace in buɗe inyi ta sakawa yana gani. Ya ƙarasa maganar yana kwanciya saman gado, 

 Wasu irin riguna ne masu kyau da tsada , bawai baƙaƙe bane ba dukansu kaloli ne masu kyau launin "yan gayu , takalma masu kyau haɗaɗi suma , sai sarƙa da "yan kunne "yan hannu da zobe kala biyar kuma duk na zinari ne masu masifar tsada. Manya² bawai "yan kucilaye ba kamar na wasan yara. Jakunkuna turaruka masu ƙamshin gaske da dai duk abinda yasan zai haɗani ya siyo , haka naita gwadawa ina saka takalmi ina bada step yana daga kwance yana kallona , idan bai burgeshi ba sai ya gyaramin , idan na burge shi da yawa yana daga inda yake zaice inzo , idan naje saiya sumbace ni yace An mata mai kyau. Ko kuma yace bara in miki hoto Yarinya....

   Mai gilashi yau ta kasa fita zuwa wurin Alhaji. Sai zagaye takeyi tsakanin ɗakinta da ɗan madaidaicin tsakar filin BQ insu , meke faruwa ne ? Sultana ba reply kuma ba fita ba kira ? Kardai zuwa tayi taje ta nunawa Dikko cht in ? Kila ana can ma ana faɗa , ta shiga 3nta , ɗaki ta koma ta ɗauki wayarta ta fara kiran Sharifa.....

  Babu wani daɗewa ta ɗauka , ko gaisuwa babu Mai gilashi tace alherin Allah dai ya kaimu wannan rana amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida , ni Mai gilashi ? Oh , naga Nana Ade a gidan amarya , ashe ina da rabon ganin wannan rana..........? Hmmmm , ׳ Sharifa tayi dariya cike da izza ita amaryar Dikko , Mai gilashi taci gaba da cewa ni ina nan na duƙa addu'a Allah dai yasa karya haɗaki da matarshi. A yatsine Sharifa tace ni wannan ai ban ɗauketa a mace ba. Kinsan da haɗemu zaiyi sai nayi wani nazari nace masa bana so kowa ya raba mata gidan ta , yanzu ke ina ne zai ajiyeki ? Cike da kwarin guiwa tace G R A , wannan gidan duk ke ɗaya Sharifa ? Cass ni ɗaya abuna daga ni sai bataliyata ga kuma Dikko nawa abuna , kai zanfa zuba tasha danni wannan banzar matar tashi banajinta wallahi. Dan bata da ban²nci ita da kashin da nayi a toilet ruwa kawai zan sheƙa tabi 5v abunta.... A hankali dai Mai gilashi taci gaba da zungurar mata ciki , daga ƙarshe tace ko tayi magana da Dikko ne ? Tace ai zasu haɗu 1:00am a G R A , Mai gilashi tace idan sauran kishiyoyin naki sun bar miki shi ya samu zuwa wurinki ko ? Sharifa tace waye su ? Bana ce komai ba , amma ni na faɗa miki yau gobe da kuma jibi Dikko ba naki bane ba , na waye......? Murmushi Mai gilashi tayi tare da cewa na wata gogaggar ce , tana can ta ɗaukeshi sai sun dawo.......... Tana faɗin haka ta tsinke kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya....

  Ya Yazeed ni wallahi na kasa gane wannan farashi da kake magana. Jiddah da Yazeed zaune a mota kuma a gidan Rabiya ake zancen , dan jiya da Dikko ya dawo daga tafiya da Papi ya maƙale yace shi zai zauna wurin Nabeela sai Momy tace ita Jiddah ta tafi can gidan Rabiya ta zauna , kora ce da hali akayi mata amma ta kasa ganewa jakar. Shiru Yazeed yayi yana kallon sitiyari , Jiddah tace Ya Yazeed kayi shiru baka ce komai ba.....!!!

Cike dajin haushi yace tunda bakya ganewa a daina maganar ko dole sai anyi auren ne wai...? Haƙuri ta bashi tare da cewa bara in kira Nabeela. Tayi maganar tana danna wayarta dan neman lambar Nabeela , anshe wayar Yazeed yayi daga hannunta yana cewa kema kanki zawara baki fahimta ba taya ita Nabeela zata sani ? Shiru tayi tana saurarenshi , Yazeed yace waye zai saci kayan wani tou inba ɓarawo ba ? Jiddah tace gaskiya , shi kuma yaci gaba da cewa ni sakarai sai in biya sadaki lefe wurin zama abincin da zakici har na tsawon sati biyu da kuɗin hidima sai su tashi a banza bayan kwana biyu in sakoki alhalin ban gama gurje kuɗin ba....? Tou ya akeyin abun ne ? Yadda akeyin abun tsarin da komai kawai ki bada miliyan 5 zanji da komai , Ya Yazeed yanzu banda kuɗi duka² fa a account ina baifi miliyan ɗaya ba , 

 Kallon rainin wayau yayi mata yana cewa karki ɗauki Yazeed sakarai mana ? Wallahi kuwa Yaya ta faɗa kamar zatayi kuka , kina nufin duk zaman da kikayi da D ' K haka nan kika fito fayau ba wasu manyan kuɗi a account ? Yaranshi ma sunyi kuɗi bare kuma ke matarshi ? D ' K da macen zai bari kiyi talauci ? Nafa san D ' K fiye da yadda ke kika sanshi. Halinshi da komai na rayuwarshi ni ina iya rubuta littafi Jiddah , ai bana tunanin nan da shekaru biyar miliyan biyar za tayi miki wahala wurin bayar da ita a matsayin kyauta. Bare kuma wannan ba kyauta zaki bayar ba kece za'ayi ma hidimar dasu , ina gwala²i ? Ina kuɗi Jiddah......? Wallahi duk na siyar na ba malamai , sakaran kallo yayi mata , taci gaba da farfaɗo mishi irin manyan malaman data bi amma har yanzu shiru kuma kullum idan ma Ya D ' K ya ganta kamar zaici ƙaniyarta ne. Yazeed yace tunda kinbi malamai ba'a dace ba ki zubo hannun jari a asusun banki na , zaki sha mamaki , Yaya banda kuɗi wallahi , Yazeed yace idan ba kuɗi ba aure karta sake kiranshi idan bata samu ba , daga haka fira ya tsaya. Yazeed ya tafi ita kuma ta koma ciki da tashin hankali , ita dake so suyi aure ya sakota ta koma gidan Dikko ? Ya kuma Yazeed zai rusa mata bajet haka ? Dole ma a samu kuɗin a daren nan...

      Tunda ta shiga take tunanin inda zata samu kuɗi. Ta juya ta zaga ta rasa yadda zatayi , tayi waya wa ƙawayenta ko zata samu duk kowa yace babu , Ashiru ta kira yace shi baima san yadda miliyan take ba bare kuma miliyan 5 , tambayarshi tayi idan ta tambayi Dikko zai bata ne ? Ashiru yace tou shidai bai sani ba amma ta jaraba kila ta dace tunda su ɗin "yan uwane. Bayan Ashiru ya gama waya da Jiddah ya kira Dikko yake faɗa mishi. Tun kafin Jiddah ta kira Dikko ya tura mata miliyan goma , shi a ganinshi idan ta nema bata samu ba zataje tayi iskanci ne , shi kuma dudduniya abinda ya tsana yaga mace tana barbaɗewa..... Shi kuma Ashiru wallahi da yasan Dikko zai bata kuɗin da bazai faɗa mishi ba , dan koshi yana iya bata kuɗin amma haushinta yakeji kamar ya babbakata da wuta tunda taba Papi fiyaya². Dan yasan bata iya tunkararshi da zancen ya bata wani abu saboda abinda tayi ma ɗanshi. Shi kuma Dikko ba haka yake ba , idan dai ta haɗoku zaiyi hayaniyar shi yayi bobbotanshi tare da rufe idanuwanshi ya zazzaga ma mutum rashin mutunci dai² iyawarshi , kuma wani dalilinshi bazai hana shi ya kyautata maka ba , haka ta faru dashi da Yazeed ai. Lokacin da yake tarayya da Sultana akace ya korashi daga company yace su  ƙyaleshi , yanzun ma bashi ne ya koreshi ba. Ashiru ne kuma ya kawo Abbakar ya ɗora , da Dikkon yayi magana yace Mai gida haka za'ayi , kuma shikena ya wuce wurin......

 Wani irin ihun farin ciki Jiddah ta kwarara , lokacin da taga kuɗin da ya shigo account inta kuma daga Dikko ne , tayi murna sosai ta fara kiran wayarshi , a kashe yake , ita kuma a tunaninta na neman biko ne , dan haka ta zauna ta tsara yaudararrin kalamai ta aika dasu ta whatsapp tasan komai dare zai hau kuma zai gani , kila yana jin kishi ne Yazeed zai aureta shi yasa ya fara neman shiri , ita kuma batayi tunanin Ashiru ya faɗa mishi ba a ganinta kai tsaye ya bata dan kyautatawa , ai tasan wannan sharar fage ne idan manyan suka taho account inta baya ɗauka. Kai Yaya D ' K mahaukaci ne , aiko bayan kwana biyu zatace ya bata 20 tasan zai bada 40 ne kaɗan ne daka aikinshi , kai ai dole ma ta koma a ci duniyar nan da ita , tayi murna har ta rasa irin wacce zatayi , gaskiya Dikko baisan darajar kuɗi ba haka nan yake nemansu mutane na cinyewa , a nata tunanin kenan...........

  Bakajin komai sai ƙarar ragonshi dake fita { munshari kenan } kwar , kwar , kir² kwar² , da sanɗo ta shiga ɗakin bayan ta tabbatar da babu mai ganinta har jikin wadrof, a hankali ta buɗe wadrof ƙiyyyy , ƙarar buɗewa , a ɗan tsorace ta cije haƙoranta tare da yaƙewa cikin yanayin tsorata ta kallo inda Dady yake kwance yana jan rago. Maida hankalinta tayi wurin neman takaddun gidajenshi , saida ta sabko kayan tass sannan ta taka tayi sama bayan wani lokaci ta sauko da wani fayil , a ƙasa ta ajiye ta dudduba tsadajjin gidaje da Dady yake taƙama dasu a cikin anguwannin "yan gayu da akeji dasu ta ɗauko har 3 ta ajiye ƙasa sannan ta maida sauran ta mayar da kayan yadda suke , ta rufe weldrop in ta fice yana nan kwance kamar asarar safe yana bacci....

  Itama a wurin Sultana haka ta kasance , tana kwance gefen mijinta kamar asarar itama shi kuma yana cht. Murmushi yayi kaɗan tare da juyawa ya ɗauko bluetooth wurin dawowa ne ya bugeta , da sauri ya ajiye wayarshi yana rirrigata irin yadda akeyi ma yaro idan ya farka , riƙeshi tayi taci gaba da bacci , ajiyar zuciya ya sauke. Cikin jin daɗi ya lumshe idanuwanshi a gajiye yana numfashi kaɗan. Saida ya tabbatar ta koma bacci ya cireta daga jikinshi ya gyara mata kwanciya ya lulluɓeta , a hankali ya sauka daga saman gadon ya ɗauki wayarshi ya koma palo..... { kunga bai iya gani ba , amma yau da gobe tasa zaije ya kalla , tou a hankali suke raka mana mazaje suna dawowa , idan abun ya ɗaure haka tun tana mishi tayin kanta yana a , a , a hankali zata labbaceshi ta nuna mishi ai ba wani abu bane ba. Da kaɗan take ɗorawa idan kuma tafiya tayi nisa haka zata rufta miki miji , daga nan sai ta Allah , karuwa ba.... }}

  Kashe fitila yayi bayan ya shiga palo , ƙasa ya kwanta saman kafet ya sargafa bluetooth a kunnenshi sannan ya buɗe cht in da Yusra ta turo mishi. Hotunan ya fara kallo da yanayin mayata , bayan ya gani ya kunno voice note ya saurara a kasallance ya furta mata yana ci gaba da kallon hoton Yusra , a voice note kuwa lallausar magana ce da manyan kalaman irin na "yan tasha wanda yaji sunyi mishi dai² da sauron kunnuwanshi , daya kai ƙarshe sai ya sake kunnuwo , taɓe bakinshi yayi tare da fara kallon video , da sauri ya rufe idanuwanshi yana murmushi , amma yanajin maganar da takeyi lokacin tana video , buɗe idonshi yayi ya sake kallo yana murmushi , bayan wani lokaci ya sake rufewa yana dariya..... Gyara kwanciyarshi yayi yana miƙa alamun saƙo ya fara shiga jikinshi. Dariya ya sakeyi mara sauti sannan yagoge ya kifa kanshi saman pilown da yake kwance yanajin wani baƙon yanayi yana shigarshi. Bayan wani lokaci ya ɗago yaci gaba da dubawa bai bawa Yusra amsa ba , ya duba saƙon Sharifa itama baice mata umm² ba ya wuce wurin na Jiddah , kallon hotonta yayi data turo tayi kyau sosai wai ga Jiddah tana godiya Yaya , itama bai bata amsa ba , ya duba saƙon da wata number ke turo mishi hotuna , gani yayi ya wuce yana duba na abokanshi , zuciyarshi kuwa sai san ƙara jin labarin Yusra takeyi , komawa yayi ya gogeshi da hotunan yasan idan An mata ta gani kuka zatayi.... Ɗayar wayarshi ya ɗauka ya fara kallon hotunan da yayi mata ɗazu , da wanda itace tayi musu tare , bayan ya gama gani yace An matan Dikko......

Yauma shirye na fito cikin kayan makaranta amma Dikko ya rufe ido wai babu inda zanje , ai da kwata² na daina zuwa makaratar. Dan naga ya dawo daga tafiya yana huta gaji shine zance makaranta , kuka na farayi tunda yanzu na lura kukan shine ƙarfina a wurinshi , shikenan muje in kaiki ya faɗa yana cewa jirani , 

kiyi ƙoƙari ki riƙeshi gida na kwana3 karki barshi ya fito…. maganar Mai gilashi ta dawomin da turomin a saƙo jiya , binshi nayi ciki ina ƙara yawan kukana nidai bazanje dakai ba , idan dai ba tare dani ba saidai ki fasa zuwa , zama nayi gefen gado nace tou naji na fasa ina cire takalmina. Kallona yayi cikin ɓacin rai yace wato ni ban isa in jera dake mu fita tare ba ko ? Ko kuma karki tafi dani ace kinzo da tsoho ? Tou sai kinje makarantar wallahi , kuma nine da kaina zan kai daga yau ma idan ina nan nine zan riƙa kaiki ko ina tunda na lura so kike ki ɗaukeni wani bansan abinda nake ba , nine ma tsohon ? Yayi maganar yana shafa gefenmu , to idan dai dan wannan na zama tsoho yau saina kwasheshi , da sauri nayi wurin nace yi haƙuri dan Allah , rufe idanuwanshi yayi da yanayin haukarshi yace ke…….. Saina cireshi duka wai shekarata nawa ne ? Ke baki da lissafi ne ? Ko dan kinji ina ce miki yarinya ne ? Tou nima bara in dawo yaron tunda kin rainani dani dake duk mu haɗu muyi yarintar , ya ƙarasa maganar yana nufa hanyar toilet , da gudu nasha gabanshi cikin kuka na haɗa hannayena ina cewa na roƙeka da girman Allah kar kayi min haka , daka min tsawa yayi tare da cewa matsa ki bani wuri ya janyeni ya shiga toilet in , binshi nayi ina ƙara yawan kukana dan Allah Dikko kar kayi , so kake idan na fita naga masu gemu in riƙa kallonsu ? Nayi maganar cikin sanyi , tou me yasa kikemin abinda bana so ne ? Bazan ƙara ba , nunani yayi da ɗan yatsa yana cewa daga yau ko me kikayimin zan cireshi kuma banajin yi haƙuri , goge hawaye na nayi tare da jinjina kai nace na yadda , maimatawa yayi a karo na biyu cewa ko me kikayimin. Zan , ya nuna da hannunshi yana fitar da sauti mai kamar fito , kenan zai cireshi. Nace na yadda , tou wuce muje yayi maganar yana murmushi , fitowa mukayi saida ya tsaya gaban madubi ya sake gyarashi kalar fizgar hankali sannan yace muje yayi gaba…..

   Binshi nayi ina sauke ajiyar zuciya. Gaskiya yana da kyau maza ku san abinda yake ɗaukar hankalin matayenku daga gareku , kuma ku ɗan riƙa cancaɗewa kuna yin kalar burgewa a gaban matayenku , ita fa mace abu kaɗan ke ɗaukar mata hankali , idan dai bakayi ma matar ka gayu ba tou gaskiya baka haɗu ba , wallahi wasu mazan ko ɗaki ɗaya baka iya haɗawa dasu , ba wanka bare kuma kasa ran samun ƙamshi a jikinsu , yadda yaje kasuwa ya dawo haka zai dawo ba wanka ba wanke baki duk ƙurar kasuwa ta gama barbaɗeka , ita kuma matarka tasha wanka taɗauki fili da gayu kamar zataje gasar wanka , ta haɗu tana ta zuba ƙamshi kamar matar sarki sai kace a haka zaka zo ka wani rungumeta , tsakanin ka da Allah kayi mata adalci kenan ? Gaskiya duk mu haɗu mu gyara gaba ɗaya sai a zauna lafiya. Idan kuwa ba haka ba ta sauke ka daga saman gadonta har sai ka koyo wanka wanke baki da kuma shafa turare.... {{ ba cewa nayi ki saukeshi ƙasa ba , ah kidai ɗan gyara mishi dan kema zakiji daɗin tafiyar idan da ƙamshi , ai kindai gane ba , kinsan wasa bai tafiya idan ba abokin wasa haka kuma baya daɗi idan babu abun wasar , kenan wancan hikimar da nake magana tafi daɗi idan da gyaran fili }}  haba kuma kuyi koyi da Dikko mana. Ku zama "yan gayen mazaje shalelen matayenku.

  Da sauri Ashiru ya fito yana cewa Mai gida bari in kaita , bai mishi magana ba ya wuce wurin mota ina bin bayanshi , da kanshi ya buɗemin na shiga ya rufe , wurinsu Ashiru ya koma suna gaisawa , duk banajin me suke cewa bayan ya gama ya dawo yana ɓata rai , juyar da kaina nayi nima ina fushi har muka fita daga gidan.....

  Har mukaje makaranta baimin magana ba , nima banyi mishi ba. Tuƙinshi ya jawo hankalin mutanen dake kusa dan baya tuƙi da natsuwa kwata² , fita. Yace bayan yayi parking , matsawa nayi na shafa fuskarshi nace amana nayi maganar idona cike da hawaye , naji jeki , saida na sumbaci gemunshi sannan nace ina sanka na faɗa ina kallon idonshi , murmushi jin daɗi yayi yace Allah yasa da gaske kike , da gaske nake Dikko , riƙeni yayi tare da cewa zanzo in ɗaukeki idan kun tashi , kuma ki daina ɓatamin rai An mata kinga banajin daɗin abinda kikemin , wallahi maganar da kikamin shekaran jiya bakiji yadda naji ba har yanzu zuciyata ciwo takemin , ki daina haka babu kyau , to , ngode ya faɗa yana ɗan gyarawa. Nima godiya nayi mishi tare da fita , addu'ar Allah ya tsare yaimin nima nayi masa Allah ya tsare hanya , saida ya tafi na wuce......

  A aji kuwa Mai gilashi ta tambayeni yadda aka ƙare jiya , kai tsaye nace mata janshi nayi mukayi faɗa duk dai abinda ya faru na faɗa mata. Cewa nayi kuyi faɗa ? Ta tambayeni ? Waike baki iya irin ɗan karuwancin nan ba ? Waye yace miki da faɗa ake hukunta namiji ne ? Ai namiji bakiyi mishi hauka , da sannu kike latsashi , kuma da kinja kika ga yaja sakar mishi ki kuma bishi da swry My President. Shiru nayi bayan wani lokaci nace nima yadda kika ganki a da haka nake , wani abokin Babana ne yayi min asiri naɗan firgice bayan kuma an samu nasara lalatawa na zama sai a hankali , tunda kinga abinda nakeyi dama bani ce nakeyi da kaina ba , tsoki Mai gilashi tayi. A hankali ta ɗan fara labarta min halin Sharifa tare da cewa kuma idan ta faɗamin na daina zuciya ina aikawa Dikko da saƙon zagi , in kwantar da hankali in bata haɗin kai yauma inyi ƙoƙarin riƙe Dikko karya fita domin tana shirya ma Sharifa gadar zare ne , so take ta rifto cikin rami ita kuma sai ta bita da ƙasa ta rufe , tana min maganar taga wani malami ya wuce , miƙewa tayi tare da cewa bari inje wurin wancan mai zanzaron inji me yasa zai ɗauro mana ƙugu yana tayar mana da hankali , tana faɗin haka ta fice daga ajin.

  Har aka tashi makaranta Mai gilashi bata dawo ba , Dikko ne yazo ya tafi dani gida , ina ta tunanin yadda zanyi in hanashi fita a daren yau , dan nayi imani yadda ya samu sauƙin nan tou fa lallai babu abinda zai hanashi fita.........

JAMILA MUSA…. ce.
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ BRILLIANT WRITERS ASSO ????
-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-

           *KWARATA RETURN...*
  _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

Rubutawa…
JAMILA MUSA…

   *SAI NA AURI D ' K*

???? —— 6

Gareku ????????

UMMIEE ZARIA
UMMU FATIMA
&
ZAINAB MUSTAPHA MUSA { Mmn Sadig }

  Wata irin zufa ce ta ratato ma Dady. Da sauri ya cire hular saman kanshi ya fara firfita da ita , itama wayar tashi ya sauke daga saman kunnenshi. Miƙewa tsaye yayi bayan ya ajiye wayar da hular a saman tebirin gabanshi ya cire babbar rigarshi ya ajiye cikin tashin hankali , kamar wani zararre ya dafa tebirin yana furzar da hayaƙin ɓacin rai , ganin banza bata kai zomo kasuwa yasa ya ɗauki makullin mota da waya ya fita.... Da irin tuƙin Mai gida Dikko ya fita kuma dashi ne yaje har gidanshi......

  Ba kowa gidan. Dan haka kai tsaye ɗakinshi ya wuce. Inda yake ajiye takaddar ko wane ƙaddara nashi ya nufi wurin ya fara ɓaro kaya harya sauko da kaf kayan ya ɗauko fiyel in. Salati ya farayi jikinshi yana kyarma , a hankali yake ɗagawa yana salati harya gama dubawa amma babu takaddun gidajen da akace masa anga Hafsa tana takai dillah² , da gaske kenan ? Wata irin luƙeƙiyar ashariya ya atura yana fizge² ya ɗauki wayarshi.....

  Matarshi ya fara kira , amma harya ƙari kiranta ya gama bata ɗauka ba dan bata da lokacinshi. Hafsa ya fara kira itama tanaji tana kallo ta watsar da kiran nashi wanda Amisty ce ta hanata ɗaukar kiran , fita yayi da sauri yabar sauran takardun watse a tsakar ɗaki , har ya fita me ya tuno ? Oho ya dawo ya tattara su ya ƙanƙame a jikinshi kana kuka kamar gawar jaririn mahaukaciya......

  Hello......... Ta faɗa cikin irin yanayin da mata keyi idan zasuci banzar samari. Tsoki Yazeed yayi cikin gunguni yace ummm , Ya Yazeed ya naji sai wani riƙe fili kakeyi ko baccin rana kakeyi ne ? Ummm ya faɗa da yanayin rashin san yayi wayar , kuɗi fa sunzo ta faɗa cikin farin ciki da zaƙuwa , yaji daɗi sosai amma bai nuna ba , yace wasu kuɗi kuma ? Yayi maganar yana ɗan sakin muryarshi kaɗan. Cikin warwarewar lissafi tace Yaya D' K ya turomin da 10miliyan na biko , da sauri Yazeed ya miƙe tsaye yace kina ina ne yanzu ? Ina inda ka sameni jiya , yanzu D ' K yana sanki kenan ko ? Ummm itama ta bashi amsa cikin yanayin jin daɗi da kuma kunya haka kaɗan , ba damuwa gani nan zuwa muyi magana , sai......ka.....zo muah. Ta bashi kiss tare da tsinke kiran.

 Yazeed yace wawiya wane ɗan tashar bokan ne yace miki D ' K yana bikonki ne ? Halan yayi haka ne dan ya ruftaki , tunani yayi sosai bayan wani lokaci yace kai ai ba haka yake fitar da zakka ba , jakunnan banzaye kuso Yazeed ko ba kuɗi yarinya ta hau network mai service , ai dake da Sharifa da ma duk wata ƙazarma mace na rantse da girman Allah baku gabanshi , da dai yana ɗan biya allon mata { danbe } da sai ince zai wanke ku ne yayi gaba abunshi. Bara dai in tafi da wuri kafin wani malamin tsubbun ya rigani ƙwacesu.

 Da wata irin rashin lafiya mijin Halima ya tashi yau , ko idonshi baya iya ɗagawa , yayi amai tun cikin dare baisan iyaka ba , yayi na safe yayi na rana har a marecen nan sai yunƙuri yakeyi , waƙƙƙ , yaci uwashi yaci ubanshi har yai laushi. Duk ƙawayen matarshi zagaye dashi sai jera mishi sannu sukeyi kamar sakin kurwar mayu. Halimatu kuma na gefe tana ta duba sabbin kayan matar da ƙawarta ta aiko mata dasu tana karantawa da kuma irin matsayinsu da wutar da suke bayarwa idan an shiga tsakiyar filin wasan danbe. Saidai ayi murmushi idan aka karanto "yan bala'e , ita a gefe ƙawaye a gaban gado.....

 Da gudu na fito daga toilet jin wayata na ƙara , nayi tunanin kila ma ko Mai gilashi ce ? Dikko na gani tsaye gaban wayar zai ya ɗauka , aikinshi kenan idan yana nan aka kirani , An mata waye ya kiraki ? An mata me akace ? Kawo in gani ? Shi gani yakeyi ta waya ake zuge mishi ni. Da Allah nace ka daina taɓamin waya , kai ake nema ko ni ne wai eye ? Haƙuri ya bani tare da miƙomin yana cewa na ɗauka fa Mama ce ta kira. Idan Innar ce kai take kira ne ? Nifa gaskiya bana san abinda kakemin ko kai zuwa nakeyi ina tsareka idan kanayin cht da karuwowinka ne ? Sa ido kamar maƙocin mai kura. Ansar wayar nayi daga hannunshi , baƙuwar number ne kuma kiran ma ya tsinke. Kayan dana cire na ɗauka na wuce ɗakina ba tare dana gama wankan ba , ina zuwa na rufe ƙofa na zubar da kayan ƙasa na wuce toilet.

 Gefen gado Dikko ya zauna cikin ɓacin rai.... Yana ƙoƙarin riƙe ɓacin rai amma An mata bata gani dai ko ? Tou wallahi idan dai ta kuskura ya riƙeta na lahira sai yafita jin daɗin , wai karuwowinshi ? Jinjina kai yayi cikin tsananin ɓacin rai a hankali ya furta saina kashe ki.... Ya faɗa yana riƙe wuyanshi... Rufe idanuwanshi yayi yana hasko lokacin data fito da gudu daga toilet , banda ma hauka da yarinta ji yadda ta wani fito da gudu ? Da taje ta faɗi ta kashe mishi babynshi , taci albarkacin ko ma waye kwance a cikin cikinta , amma akwai ranar ƙin dillanci , wato ranar da wandon mai gari ya ɓace.......

  Tunda na shiga wanka kiran yake ta sake shigowa har na gama wanka ba'a daina kira ba , ni nayi tunanin Mai gilashi ce dan haka na ɗauka , suna na *SHARIFA...* , wai Allahna na rantse da girman Allah na kaɗu gabana ya yanke ya faɗi kawai dai naji tsoro , dakel nace to ya akayi ne ? Kiranki nayi in faɗa miki nice wacce Dikko yake so. Kuma ni kaɗai yake ma soyayyar da bata da farko ballantana ƙarshe , ya gina min soyayya mai girma tsakanin saman sararin filin zuciyarshi zuwa tawa. Ni kuma na gina mishi tawa soyayyar bulo da bulo tsauni da tsauni tafiya da tafiya kalma da kalma tsakanin dare da rana na gina a cikin zuciyarshi..... Nice yake ma soyayyar da bayayi miki irinta , iska ce ni idan na kaɗo saina ɓaro da "ya "yan kanya daga jikin uwarsu iska ta tana ƙarfi. Ki tsaya ki gani haka zan kakkaɓeki tsaf inyi waje dake.......

Murmushi nayi mai sauti tare da cewa aikin banza an tura agwagwa ruwa. Duk lokacin da kikabi kika gina ko ya gina wannan ba matsala ta bace ba. Nidai abinda na sani na kuma fahimta ke daƙiƙiya Dikko ya ɗaukeki , idan kuma kina ganin shi zai aureki tou ƙarya yayi miki dan har yanzu zuciyata ta ƙaryata aurenshi. Bata faɗamin ƙarya akanshi wallahi duk abinda ta faɗamin ko ta ansa akan shi tou wallahi zai faru , liƙi a idon bainan nasi bashine yake tabbatar da soyayyarki a zuciyarshi ba , idan ke iska ce to Dikko guguwa ne. Gittawarshi tashin hankali ne domin idan ya taho kowa saiya gudu ya ɓoye saboda girman hatsarinshi , sahun keke ne shi mai gasawa mata azaba a tafin hannu , naji ke iskace. Kanyar kaɗai kike iya ɓarowa banda ɗan kuka , zubdo ɗan kuka saida babban makami badai iska ba ko jifar ƙananun yara , Dikko kuwa iccen kuka ce shi koda karfinka saida rabonka ko ka jira bushewarshi , to shi ɗanye ne yini ɗaya zur kana jefa amma baya faɗowa sai kayi jan ido , idan kuma kika ce ki hau tou lallai sai kin sauko gurguwa. Icce kuka hawanshi sai an shirya , idan ba'asha dare ba asha rana. Dan haka ni soyayyar da yake miki bai shafeni ba , nawa na tabbatar tunda ya kawoni gidanshi ya adanani a matsayin matarshi , ku ya ɗauka mahaukata abon firarshi idan ya fita , jakuna banza da baya zuwa firar zance wurinku a gidan iyayenku saidai ku baro gidajen iyayenku ku biyoshi , ni ban ɗaukeki a bakin komai ba. Saboda duk abinda zaki faɗa masa ko ya faɗa miki a kaina ya fara faɗa , kuma daga gareni ni kalamanshi kaf suka ƙare banza sharar bisa titi mai kauyawan kalamai Dikko baya auren karuwa....... 

  Zagina tayi sosai tare da cemin *SAI NA AURI D ' K* nace ƙarya takeyi , ta sake maimaitawa , nima na maimaita ƙarya takeyi Dikko ba ƙaddarar mallakin ballagazun mata bane ba , haka mukai ta caccakar juna kowa yana yanka kalamai masu ciwo tare da yima abokin faɗar tashi gori , ita ta gaji da kanta ta kashe wayar ta bayan ta tabbatarmin da sai na fita a gidan Dikko. Tsoki nayi bayan ta kashe nace shirmen banza shirmen wofi.

  Haka yaita garari tsakanin Qerau da duk inda yasan akwai wata madakata ta "yan iska har dare amma baiga Hafsa ba kuma babu Amisty , Qerau ya koma ya kafe motarshi ya fito ya daki gaban motarshi ya halbi tayar da ƙafarshi yace wallahi idan Amisty da Hafsa basu fito ba saiya cinna wuta ga duk wani gida dake cikin Qerau kuma haka duk wata karuwa daga yau kasuwarta ta mutu dan duk wata karuwa dake anguwar nan sai ta koma gidan ubanta , "yan iska kowa tabar jaharta da iyayenta sunzo sun zamar musu annoba a cikin garin Katsina. "Yan iska zuwen banza da wofi , tou yanzu zanyi waya a kawo min tankar man fetur duk saina babba gidajen dake cikin anguwar nan , haka yaita ɓuɓɓurma zagi kamar sabon hauka lokacin da sarara.

 Babu wanda yayi ma Dady magana. Haka ya kashe santa yaci gaba da ƙaryar rashin kunya iskanci kuma sanka² , karuwan dake zaune a ƙofar gida saman dakali suna lido ko kallo bai ishesu ba , ganin zasu ɗaukeshi mahaukaci da hankalinshi yasa ya samu wani yaro yace yaje maza bakin titi ya kira mishi duk wani ɗan bunburutu kuma su taho da jarkar fetiri. Yaro ya ƙwalƙwala da gudu ya tafi dan tattaro duk wani mai siyar da fetir. Wata tsohuwar karuwa ce da ta gaji da karuwanci har ta gagara tuba ga Allah ta tsufa iya tsufa , breziya ne a jikinta sai zani ɗaurin ƙugu da kallabinta tayi mishi ɗauri irin na tsofaffin "yan iska , kai da ka kalleta kasan ba Allah a lamarinta domin har yanzu duniyar gaba suka bata ba baya ba , tsaye take a ƙofar gidan Amisty fitowarta kenan daga cikin gida tana shan sigari , riƙe tabar tayi da bakinta ta dafa hannayenta a ƙofar. Saida ta gama kalle waje tass sannan ta fito da rangwaɗa....

  Wuri ta samu ta zauna ƙafa ɗaya saman ɗaya tana ci gaba da kora hayaƙi tana wani hankaɗe kai sama cikin iskanci da sanin hannunta wurin kwarema iya jan sigari. Kallonta Dady yayi yace ke tsuhuwar karuwa ko kinga Hafsatu ne ? Banza tayi dashi taci gaba da jan hayaƙi tana aikashi sama , wurinsu ya matsa yana cewa zaku fiddosu ko saina tona muku asiri ne ? Sai yanzu tsohuwar tayi magana cewa , karuwan yanzu kamar man kitse ne a saman wuta , yayin da suka ga hasken rana sai su gudu su koma ciki gudun karsu narke , zamaninmu mu kuma , ta nuna kanta tana tafiya da maganar ta cewa mu wutar muke nema ido rufe amma da ta hangomu sai ta suƙe kafin mu iso , ni da lokacin da nake Adda ta ce da saina rabaka gida biyu bayan na ɗaukeka na saka cikin ɗakina shegen nan dasai nayi maka fyaɗe , karuwan yanzu matsorata ne. Su ke gudun mazan ba mazan ke gudunsu ba , zamani na ni kuma da nayi iskanci maza idan suka ganni ɓoyewa sukeyi saboda wutace ta doso wuri , kallon taron yara²n karuwan dake zaune tayi tare da cewa mataye....... Gareku tayi maganar tana nuna Dady. Sannan ta haɗe kai dasu tayi musu ƙus² a dai² lokacin da yaron ya dawo da "yan bunburutu layi ɗaya kowa ɗauke jarkar fetir.....

  Gaba ɗaya karuwan suka haɗa baki cewa. Dan Allah Dady kayi haƙuri , ????????idan ka ƙone mana gida ina zamu zauna ? Wannan gidan da kake gani ba namu bane ba , amma tunda munga da gaske kakeyi bara mu faɗa maka gaskiya , har yanzu tare suke magana kuma a tare kowa ta nuna da ɗan yatsanta manuni suna cewa ai Hafsa da Amisty suna hango motarka suka shige can gidan suka ɓoye suka nuna gidan da Dikko ke kiwon dawakan shi , tare sukeyin magana babu wanda yake wuce wani kamar suna biya karatu , amma kayi haƙuri karka ƙona gidan idan ka ƙonashi wannan gidan za'a siyar a biya masu gidan can kuɗin fenti da abinda ya ƙone , idan kuma aka siyar kaga shikenan kasuwarmu zata mutu kamar yadda kace kayi haƙuri don Allah , suka ƙarasa maganar suna haɗa hannayensu wuri ɗaya na neman gafara.....

 Dady ganin sun tsorata shima ya haɗa kanshi da masu bunburutu yace tou kuyi da wasa ku yayyafa fetir ɗin nasan zasuyi musu waya su fito , masu fetir zasuyi magana Dady ya toshesu da kuɗi yana cewa idan dai dan wannan ga kuɗinku , su kuma suna so su faɗa mishi gidan Dikko ne ya duba yaga wace karuwa ta isa ta mallaki gida layi ɗaya tun daga farko da kuma ƙarshen santa , amma sai Dady yace ai bafa ashana za'a ƙyarta ba , ya ƙara musu kuɗi , aje ma Dady fetir sukayi ya ɗauka yaci gaba da watsi dashi yana cewa saina ƙone shi , su kuma karuwai sukaci gaba da cewa Dady dan Allah ka rufa mana asiri karka toya gidan nan. Idan ka ƙoneshi asirinmu zai tonu komai da muka mallaka zamu rasashi wurin gyaran gidan nan , Dady yace saina tona muku asiri , a tare sukaci gaba da cewa ka rufa mana asiri karka tona asirinmu , ci gaba yayi da mita yana saiya tona musu asiri , saida ya gama zazzaga fetir ya ɗauko layter ya kunna yana cewa zan cinna fa.... A dai² lokacin da Umar ya fito shi kuma warin fetir in ya fiddoshi , idanuwa ya zaro tare da cewa kai׳ kashe mu zakayi ne ?

Dariya Dady yayi tare da cewa halan ka tsora ko ? Umar yace ba dole inji tsoro ba zaka kashe mu ? Matsowa Dady yayi da wutar yana cewa to koma ka fiddomin Hafsa da Amisty ance sun sayar min da gidaje 3 da suke duk a cikin lay-out masu haya a gidan ne suka kirani akan ban musu adalci ba na siyar da gida babu notice , su fito su kaini wurin wanda suka siyi gidan ni a bani gidajena , kasan ko miliyoyi nawa na siya ? Tou kaf kuɗin gadon "yan ɗakinmu ne na lashe yayi maganar yana nuna lashewa da harshenshi. Murya ƙasa² tare da matsawa kusa da Umar yana cewa dukiya...... Akan kuɗi babu abinda bazanyi ba , da hannun haggunshi ya murza "yan yatsu biyu sukayi ƙara cewa koma ka fitomin dasu kafin in toye wannan gidan.....

 Karuwai kuma cewa sukeyi mun tuba Dady kayi haƙuri karka toye , shi kuma Umar cikin rashin fahimta yake kallon Dady , dariya Dady yayi tare da nuno bayanshi yana cewa ya kaji suna cewa....? In rufa musu asiri fa , saina toye , shin na toye ko kuwa ? Zaɓa mutuwa ko kuɗin gidajena ne ? Umar ya fara takawa baya Dady yana binshi yana cewa me kace ne ? Hannu Umar yakai da niyar ɗora hannunshi akan layter amma sai Dady ya fizge , wurin fizagewar ne ta faɗi wuta kuwa taci gaba da ci.... Karuwai sukace yawwa tou kane asirin ka zai tonu gidan Dikko ne....... Suna dariya , aimu babu wani da ya isa ya kashe mana kasuwar karuwanci ko ya tona mana asiri saidai mu , mu tona asirin mutum , ana baka haƙuri kana rashin kunya , kaga sai kaje ka saido sauran gidajenka kayi mishi gara da ramuwar dokunanshi , tsohuwar tace dokin da aka kawo shekaran jiya na miliyan talatin da biyar ne , shin ka ajeta....? Kwaiwayon maganar Dady sukaci gaba dayi , yayin da Umar yayi gaba yana akawo ɗauki Dady kuma ya fara kiran "yan kwana² asara goma da ashirin.....

  Amisty da Hafsa kwance a wata lafiyayyar hotel dake cikin garin Abuja , banƙararren rago ne aka gaso musu , sai kaji da aka kaso musu sunkai ashirin , manyan lemuna na kwali masu tsadar gaske da kwaleyen sigari an jera su da kwalaben giya , ɗakin cike yake da manyan karuwai da suka gode ma zamani da zuwan wannan rana , ita kuma Hafsa daga kwance ta kwance hannunta ta ƙara ƙwalƙwaleshi tasha kukanta sannan ta maidai abunta ta rufe..... Daga kwance Amisty ta fara gabatar da bayani kamar haka.......

Barkanmu da kasancewa a wannan lokaci manya karuwa maza da mata , na baya , gaba , haggu da dama duk muna muku barka da zuwa , {{ wato masu maɗigo da "yan luwaɗi sai kuma mazinata.... }} kamar dai yadda kuka sani muɗin masu sa'ar rayuwa ne kullum nasara muke samu babu faɗuwa , mune manyan jajirtaccin karuwai da muka kafa manya² tarihi a cikin jahar birnin garin Katsina , kuma mune zamani na farko da muka kawo wasan danbe a duniya , kullum nasara muke samu dan haka ya kamata a jinjina ma bariki don Allah , shewa sukayi gaba ɗaya tare da ɗaukar kwalaben giya kowa ya ɗaga.....

   Saida kowa yasha yayi gyatsa alamar ta sauka ciki Amisty taci gaba da cewa. Bariki tayimin komai , ta biyani kuma ta raineni fiye da yadda nayi tunanin samu daga gareta , bariki ta itace uwata kuma itace ubata a cikinta na rayu tun bansan wace ce ita ba. Mutane na cewa bariki bata da tabbas , tou ni kuma na ƙaryata masu wannan maganar , bariki kuwa itace mai tabbas ga amana haɗin kai da kuma ƙaunar juna , a taƙaice dai ni bariki tamin tabbas....

A gurguje dai muyi abinda ya taramu a wurin nan , manyan gidaje dake can cikin lay - out na Dadyn su Hafsa mun siyar dasu akan farashi mai tsoka saboda kunsan komai shi ke siyar da kanshi , dalilinmu na siyarwa kuwa sirri ne tsakanin rayuwarmu mu biyun duk dai bama ɓoye ma juna sirrin juna tare ake ci kuma idan an samu , ku nawa ne duk taron ku ? Irga kansu sukayi sannan aka faɗawa Amisty ko su nawa ne , Amisty tace mutum goma ? Tou za'a bawa kowannen ku a ciki zunzurutun kuɗi har naira miliyan ɗaya a cikin kuɗin. Jibi kuma dani da Hafsa zamu wuce india mu wanko zumibi mu dawo..... Idan kuma aka sake samun wata sa'ar sai a tura wasu a cikinku su tafi , tou ya kuka ga tsarin ne ? Kowa yace haka yayi Kaka......

  Shagali...... Suka faɗa gaba ɗaya , dan haka aka rufawa kwalaben giya da sigari , suma kaji da naman rago aka ciccinye aka kora da ruwan lemu , bayan sunci iya cinsu aka tattara sauran aka fitar.......

 Mutumin da Amisty ta kai Hafsa a matsayin malamin tsibbu shine ya kira Amisty akan shima ta fiddashi , cikin maye tace ai babu kasonka a cikin , haɗata ya farayi da girman Allah amma fur Amisty tace ai ko Hafsa bata kashi da gaurayen kuɗin nan , kuɗi duka suna wurinta sun kuma zama nata. Mallakinta bata rage musu ko sisi kuma da asuba zata fece abunta ta tafi can ƙasar waje ta buɗe sabuwar da'irarta , karuwan suma da tace za'a basu one² miliyan ƙarya takeyi , ai ita ba daƙiƙiya bace ba tasan hannunta , ta siya sabuwar mota ta miliyan 5 dan haka daga nan zata canja akalar tafiyarta zuwa Mambila , idan taje ta huta daga can zata wuce gaba abunta ta wani ɓace cikin duniya kamar yadda jirgi yake lumewa a cikin giza²i dake saman sararin samani , dariya tayi sosai cewa kusha zamanku a Katsina Amisty ta tafi yawon buɗe ido sai mun haɗu a lahira. Hahahahaha tayi dariye cike da iskanci kamar zatayi kuka , Allah sarki zanyi ƙewarku Katsinawa...... Dariya ta sakeyi bayan ta kashe wayar tace Amisty tayi gaba kuma babu dawowa........

  Wata irin ashar ya fesa bayan Amisty ta kashe wayarta. Cikin ɓacin rai ya sake daddana ashar kamar rainon mutane gafiya , yarinya idan kinsan wata baki san wata ba , shima dake kwallon gigiye ne wurin iskanci da taurin kai , cikin garin ya famtsama a daren saida ya gano har hotel in da Amisty take a Abuja , mutanensu na can Kaduna da kuma "yan iskan dake saƙe a sansanin yanki Abuja manyan "yan ta'adda ya buga ya rattaɓa musu komai ya kuma ƙara da cewa su hari Amisty. Su ƙwace kaf kuɗaɗen har motar karsu bar mata....... Shima yana zuwa Abuja a daren nan , suma bayan sun gama waya dashi suka sanar da mutanensu na Katsina suka kuma tura hotonshi da adireshin cewa su ɓarar dashi suna da kaso biyu a cikin kashi goma na kuɗin , shiri suka farayi ta yadda zasu riƙe Amisty da kuɗin cikin sauƙi......

 Kirari yake ta goga mata kamar tsohon maroƙin da yayi shekara baici ba , su Jiddah saidai a juyar da kai ayi dariya kan׳ dariya irinta jakkan mata , haka Yazeed yaita ɗorata tana hawa shi kuma ya rungume banzar yaita lalubarta. Daƙiƙiyar ta saki baki taci gaba da dariya kamar kwarto yaga wa²n zama. Haka yaita suɗeta yana bazo mata manyan kalaman batsa , a cikin motar dai ya labbaceta ya buga round ɗaya na danbe , yau yanajin shi wani babban shege ne yabi hanyar da D ' K ya taka ya wuce..... Bayan ya karance tayi mishi transfer na 5miliyan. Sannan tace a tsaida ranar aure tunda an samu kuɗi , kai tsaye yace sati mai zuwa.... Da farin ciki Jiddah ta fice Yazeed kuwa ya wuce wurin harkar danbenshi tunda ya samu kuɗi.

  A ɗakinta dake gidan Rabiya ta kwanta ruf da ciki a saman gado tana tunanin Dikko , jinjinoshi tayi sosai sannan ta jinjino haɗuwarta da Yazeed kai zanen ba ɗaya bane ba kuma karatun yasha ban². Dikko fa daban ne yayi zarra + zarra , gaskiya da gaskiya ce , jarumta ta zahiri duka da duka , salo bisa salo ƙwarewa da iya gugar zanar sanin abinda ake kira da danbe yana nan wurin Dikko , wannan shi ake kira jarumin namiji ba lusari ba , kana ta ina ne haka ? Me kakeyi yanzu ? Kana tunani na ? Koma dai miye ina nan dawowa gareka ka ƙara haƙuri ɗan uwana.

  Sun nemeta har sun kaji , bokansu ya bugi ƙasa ya zana , ya goge amma ya kasa ganin inda Mardiyya ta shige , haka nan Suwaiba ta haƙura ta dawo Katsina. Kuma bata wuce Daura ba tana nan ta saƙe a cikin Katsina !

  Bayan anyi nasarar kashe wutar dake ci a wajen gidan Umar ya riƙe Dady tare da cewa saiya kaishi wurin Mai gidansu. Haƙuri Dady ya bawa Umar cewa shi baisan haka abun yake ba , iyakar dai wutar waje , babu abinda taci sai fulawowin da sukasha fetir dan haka suka babbake bangon wurin yai duhu. Umar ganin tashin hankalin da Dady ya shiga bai faɗawa Dikko abinda ya faru ba , saidai zaiyi sabon zubi na filawowin da sukaci wuta , sai fenti da yace gaba ɗaya kaf gidan daga ciki har waje zaiyi fenti dan idan akayi a wajen gidan kaɗai Dikko zai gane , idan kuma ya gane zaiyi tambaya shi kuma zai faɗa masa kai tsaye baya munafirci , sai shi kuma a bashi na toshiyar baki.

 Wannan tsohuwar karuwa ba haka taso matsalar ta tsaya ba , taso a toye kaf gidan dan Dady yaci uwarshi wurin yaron nan , ita sau ɗaya ta taɓa ganin Dikko shima abinda yasa yadda taji Hafsa tana zuzutashi , ita tasharshi da aka bata labarin abinda yayi ma Sultana ya burgeta yadda taga Dikko tana so taga Sultana itama , to shine fa ta matse lamba taga ɗan iskan yaron nan , da taga hotonshi ta matsa sai ta ganshi da idonta , matashi ne kyakkyawan yaro amma kai da ka kalli Dikko kasan baida mutunci ko kaɗan ɗan iska ne bugu ɗaya , kuma wasu irin firgitaccin idanuwa gareshi tsaitsaye na rashin kunya , ita a yadda ta auna shekarunshi zasu fara daga 35 har zuwa 38 ita dai a yadda ta ajiyeshi fa , dan yana da suffa mai ɓoye shekaru yana da cikar zati da ƙwarjini saidai daga ganinshi kasan sangartacce ne , yana da tsayi dai² kyau , yana da murzajjen jiki na zubin jaruman maza ba ƙaton jiki ba dan baida ƙiba kuma ba siriri bane ba yana dai da jiki mai kyau sai hutu ya zauna. Gaskiya Dikko yayi mata kyau , kuma kyakkyawar fatarshi ta dace da gemun daya ajiye mata , zuwa ɗaya idan kayi mishi dogon kallo yana da ɗabi'un mutanen kirki amma gogaggen ɗan iska ne kuma bashi da kunya yadda ta fahimce shi , tou taso ace gidan ya ƙone taga yadda zaizo yayi ranfar da akace yanayi wallahi yau taso aci ƙaniyar Dady a murje bakin tambayar kuɗin gidaje har sai Kaka ta dawo suma ta basu kasafinsu.... Itama dai Dikko ya burgeta gaskiya addu'arta ɗaya Allah yasa da rabon Hafsa a cikinshi.

  Misalin ƙarfe 11 da wasu "yan mintuna na dare na ɗaure Dikko dake kwance yana bacci saman gado da igiya. Buɗe idonshi yayi ya kalleni cikin ɓacin rai , cike da rashin kunya na murguɗa baki tare da zazzaro ido nace yau na ɗaure ƙafar yawo wallahi , sai naga ta inda zaka bi ka fita , da chat in dare da fita yau gaba ɗaya An mata ta hana nayi maganar ina watsa hannunawa alamar babu , fiffizgewa ya farayi yana cewa idan na kwance sai na zaneki An mata , zama nayi gefen gado tare da faɗa cikin rainin wayau cewa ai bama zaka iya kwuncewa ba , taimako ɗaya zanyi maka. Bara in kunna maka kwallo ka kalla , nayi maganar ina ɗauka rimot kusa dashi na kunna tv. Tsoki yayi a gajiye ya koma ya kwantar da kanshi yana bina da kallon takaici....

  Ka daina kallona ka kalli talabijin na nuna mishi tv , ajiyar zuciya ya sauke tare rufe idanuwanshi. Tashi nayi daga inda nake zaune na koma cikin kujera na zauna inacin gurguruna { pop corn } ina cin abuna ina kallon kwallo , buɗe idonshi yayi ya kalli Sultana sannan yace An mata kizo ki kunce ni kafin raina ya ɓaci , naji shi sarai amma sai na ƙure volume ina cewa ka rufe min baki bana san surutu ina kallon kwallo ka kalla nace , nayi maganar ina watsa gurguru baki. Ke......... Zoki kunce ni nace , cikin faɗa nace anƙi a kuncen kan kuma ka rufemin baki bana san surutu idan ina kallon nace maka , An mata......... Ban barshi yayi magana ba na zaro ido tare da haɗa masa da shittttt ???? nayi masa ina ɗora ɗan yatsa na a saman baki.

 Kallona ya ƙarayi. Bayan wani lokaci yayi ɗan taƙaitaccen murmushi kaɗan ya kauda idonshi gefe yana nazari..........








   *JAMILA MUSA...*

[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ BRILLIANT WRITERS ASSO ????
-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-

           *KWARATA RETURN...*
  _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

Rubutawa…
JAMILA MUSA…

   *SAI NA AURI D ' K*

???? —— 7

    Ƙasa² nake magana ina cin gurguru cewa. Ƙaryar rashin kunya. Ai sai an bar zomo yake zama guza. Kowa ai ɗan iskan kanshi ne , ni har an nunamin hanyar hukunci , a dai² lokacin daya sake kalloni da dogon kallo , murmushi nayi kaɗan tare da ibar gurgurun kamar zan bashi bayan kuma muna da tazara. Ya² ne ? Zakaci ? Na faɗa ina murmushin nasara. Girgizamin kai yayi alamar a , a , ya bani amsa. Ban sake magana ba na ci a bakina ina cewa saina..... Na nuna da hannun hagguta yankawa alamar zan yanka mishi wuya kenan. Idan bai daina kallona ba kalli can nace ma na ƙara nuna mishi tv...

 Gyara bakinshi yayi ya kalli talabijin. Ni kuma naci gaba da cewa wato da ka kwanta kayi bacci , misalin 12 saura ka tashi. Daga saman gado zaka wuce bayi ka watsa ruwa , zaka fito ɗaure da rigar wanka. Kana fitowa sai ka tsaya jikin madubi , zaka goge jiki da towel , da hannuwa na na nuna yadda ake shafa mai ina shafawa a fuskata , daga fuska naci gaba da nuna duk inda ake shafa mai a jiki. Bayan ka gama saika fara goge fuska , ummm na nuna yadda yake sharce gemu da kuma yadda yake shafa turare dariya nayi sosai tare da komawa da baya na kwanta cikin kujera , bayan ka saka kaya sai ka wani fece abunka. Cikin dariya naci gaba da cewa tou yau Jarumarka ta ɗaure kafafuwan yawo , no cin cingom & no cht na nuna yadda yake riƙe waya da wayata , da hannun dama na sake nuna babu. Ina cewa kaji....??? Na riƙe kunne na dan ya tabbatar min yaji.

 Baiyi magana ba kuma bai kalleni ba yaci gaba da kallon tv kamar yadda na sashi. Banda tuƙuƙi babu abinda zuciyarshi ke mishi , yana ta ƙoƙarin riƙewa da kuma dannewa ya gagara , cikin wata irin murya yace ke kunceni nace miki. Ya faɗa yana rufe idanuwanshi. Da hannu na nuna karka dameni da baki kuma nace ka fita idona in ba haka ba mizanete kana daga kwancen nan. Kai............. Nine zaki dakar ? Tou saina kunce kuma saina kashe ki , da sauri na tashi ganin yana fiffizgewa da ƙarfi , saina kashe ki........ Da gudu na fita a bakin ƙofar fita daga ɗakinshi na zame , shi kuma ihunshi ya ƙara yawa , ninen ma zaki daka ? Yau idan basai na ma kasheki ba tabbas saina kashe kaina...... Da sauri na tashi nayi ɗakina ina kuka ashe har yanzu Dikko bai warke ba. Rufe ƙofa nayi har nayi fitsari saboda tsoro. Har yanzu ina jiyo ihunshi yana faɗin saina kashe ki...........² ƙyarma jikina ya farayi kodai in fita in gudu ? Nine zaki daka ma.......... ? To zo ki dakenin , kai.............. Saina kashe ki............. Kowa da kowa ma saina kashe shi....... Ah² ba lafiya ? Na faɗa ina ƙara fashewa da kuka. Babu wani ruwana da ciki har babyn shima sai na kashe shi................. Kai......... Wai nine ma mace zata zane , a sauƙaƙar murya yace aiko dana zama lusarin namiji. Daga haka ya ɗauke. Tunda ai kunga yana kwance ne , dan dama idan ciwon ya taso mishi kwantar dashi ƙasa akeyi , idan dai aka kaishi ƙasa anci galabarshi. Sai a bashi magani dan idan ya tashi dawowa ya dawo da tunani.

 A firgice na juya inda na yada wayata tana ƙara , ummm na faɗa tare da goge zufar dake bin fuskata. Rairafawa nayi inda take na ɗauka , Ashiru ne yake kirani , ɗauka nayi cikin kuka nace Dikko ne baida lafiya , ke kina ina ne ? Na kulle a ɗakina. Waye ya ɗaureshi ne ? Cikin kuka nace ai kaine ka siyo igiyar , Ashiru yace ba wanda ya siyo igiyar ba wanda ya ɗaure shi nake magana , nice na ɗaureshi , meya haɗaku ? Shiru nayi banda abin cewa , Ashiru yace kizo ɗakinshi. Cikin kuka nace ni gaskiya bazan zo ba , ranki ya daɗe kizo mu duk muna ɗakin , tou na faɗa tare da ajiye waya. Toilet na shiga na wanke jikina sannan na fito na gyara inda na ɓata da fitsari , kaya na canza bayan na gama na kira Ashiru yana nan ? Ya tabbatar min suna nan , hijabina na saka na buɗe ɗaki na nufi ɗakin Dikko.

  Gaba ɗaya su Ashiru suna wurin , Dikko yana kwance a ƙasa ya dafe kanshi da hannun damarshi cikin yanayin jigata , ya fiffizge igiyar , wurin saukowa daga saman gadon ƙafarshi ta riƙe shi yasa ya faɗi kenan ? Kallona Ashiru yayi cikin ɓacin rai yace amma me kika faɗamin maganar siyo miki igiya ? Shiru nayi ina ta karkasa ido kamar an kama ɓarawon "ya "ya ina kallon Dikko sai kuma in kalli Ashiru. Gaskiya baki kyautawa abinda kikeyi. Mai gida dai kike ma haka ? Ya faɗa yana jinjina kanshi , kausasa murya yayi da fushin zuciya yace tabbas ke yarinya ce. Amma komin yarintarki ya kamata ki riƙayin abu da lissafi , tunani da kuma hasko abinda kaje ya dawo. Wannan ɗin dai da kika raina shine bangon rayuwarki idan har kika ɓata mishi ko wulaƙantashi kanki , idan kuma ya mutu tabbas ke zaki shiga3nki. Shawara da neman mafita ya rage naki. Ya ƙarasa maganar yana gyara mishi kwanciyarshi.

Durƙusawa yayi gaban Dikko yana kuka kamar ranshi zai fita , bayan wani lokaci yayi magana cikin hayaniya cewa ke bake kaɗai ba. Bango ne kuma jegone ga duk wani da kika ganshi yana tsaye a wurin nan yayi maganar yana nunasu hada kanshi , ƙasa² yayi da murya cewa duk yawancinmu nan da kika ganmu kusan mu goma sha wani abu rabin mu duk mu marayu ne , rabi daga cikinmu duk basu da uwa uba ko ahali , haka akaje aka kwaso mu aka kawo mu domin kula dashi , an ɗaukomu ne kamar karnukan shi muyi haushi yayin da wani yake tunkaroshi , babu wanda yasan darajarmu ko tausayin mu rayuwar da zamu shiga. Mu rayu ko mu mutu ba damuwar su bane ba shiɗin dai ake so mu ba rayuwarshi kariya , muyi haushi wan² yayin da wani yake zuwa dan taɓashi , mu kula dashi bayan ƙarshen wata biyu abamu naira dubu hamsin.

  Cikin ɗaga murya yace amma shi bai mai damu karnuka ba........... Shine ya jawo mu jikinshi ya ɗauke mu kamar "yan uwanshi , ya soke wata banzar dubu hamsin da Mai gidansu yake bamu {{ wato Dady }} bayan ya nuna mana kowa yaje yayi rayuwarshi , haka mukai ta kuka ya rufa mana asiri ya barmu mu zauna dashi koda an daina biyanmu albashin zamu zauna dashi saboda dubu hamsin ɗin dashi bai ɗauketa kuɗi ba , ganin yadda muka shiga tashin hankali yasa shi da kanshi yace zai riƙa biyanmu , shin kinsan farashin da yake biyan ko wane ɗaya a cikinmu ? Me mukeyi masa ne ? Bamayi masa wanka bama dafa mishi abinci bama masa wanki bama shara komai bamuyi mishi , zaiyi fita goma bai fita damu ba. Muci musha kowa dake wurin nan mazaunin shi yana a cikin gidan da yake rayuwa. Duk inda yake muna da gidanmu muma a can ƙarshen gida , palo bedroom toilet yadda yake da A C a ɗakinshi muma namu dashi. Yaga munyi kuka shi yasa yake san ya rayu damu domin muma muyi farin ciki kamar shi. Masu kuɗi nawa sukeyin haka ? Wanda sun ɗauki duk wani ɗan aikinsu kamar wani jakinsu. Shi yasa suka kira talaka da suna bawa.......... Cikin kuka yace wai talaka shine bawa , wai bawa ? Kuma alere dangin jaki wai ya mutu gobe a sake sabo. Tou shi bai banbanta ba saboda soyayya , abincin da mukeci shi kanshi abun duba ne , idan ciwo ya kama ɗayanmu shine magani kuma ba'a cikin wanda zai bamu ba , albashin kowa a cikinmu da yake biyanmu idan kikaji sai kanki ya kwance , kafin albashi kuma ya bamu׳ , ya ƙara mana² , kullum cikin bamu yake , da marainiyar murya yace wai dandai muyi farin ciki , shi bai ɗauki duniyar a bakin komai ba dan ba itace gabanshi ba , tsaye yake ba dare ba rana , ya hana idonshi bacci zuciyarshi da kwalwarshi sunƙi samun natsuwa , bawai dan ya rasa yake nema ba. Ba kuma dan zai rasa yake tarawa ba , akwai su... Kullum zuwa suke da yawa..... An tarasu tun ba'asan amfanin kuɗi ba , tashi yayi ya ganshi cikin arziƙi tunda ya buɗe idonshi duniya kuɗi ya fara gani ba labarinsu yaji ba. Tunda Mai gidanmu ya girma suma kuɗin san ganinshi sukeyi , da kansu suke zuwa domin suma kansu sun san shine zai yaɗasu domin suje inda ba'a da labarinsu. Yana nema ne domin al 'umma kuma nemanshi yanayin shi ne domin ya gina rayuwar duk wanda yake da rabo a ciki. Akan Mai gida gaba ɗayanmu zamu iya sadaukar da rayuwarmu dan nema masa farin ciki. Ya ƙarasa maganar yana dukan ƙirjinshi bisa gaskiyar shi. Mu bazamu yadda ba , haka kuma bazamu lamunta ba , idan ke baki san darajarshi ba mu mun sani , idan bashi da amfani a wurinki mu yana dashi a wurinmu , idan kin gaji mu bamu gaji ba. Ya ƙarasa maganar suna maida Dikko saman gado. Duk ma wani mai cewa Mai gidanmu bashida mutunci ko ɗan duniya ne ko ya raina mutane koma dai miye mu yana da kyakkyawan hali a wurinmu. Mune muka sanshi muka zauna dashi muka kuma san ɗabi'unshi dan haka mune zamu faɗi ko waye shi...... Yayi maganar yana kaima bango naushi da hannunshi. {{ yadda yayi maganar hasashe na ya bani da Inna yake... }}

       Duƙawa yayi tare da dafa gefen allon gaban Dikko yana ci gaba da cewa. Me kike so ? Idan soyayyar ce an baki , kuɗi ne damuwarki ? Suma an baki. Sultana me kike nema ne wai .....? Ko har yanzu kuɗirin fansa bai goge ba ? Rungume Dikko yayi ya ƙara yawan kukanshi yana cewa bawan Allah da wannan dalilin ya ƙwammaci ƙare rayuwarshi ba aure. Yana sanki amma yarinta da rashin tunani ya hana ki fahimta. Iya ruwa iya fidda kai......... Ko wae'...iya allonshi ya wanke. Gaki ga Mai gida tunani da samun mafita yana wurinki , dabara da sanin sirrin rami ya rage ga mai shiga rijiya. Daga haka bai sake magana ba ya riƙe hannun Dikko cikin soyayya yana mishi kallo mai nuni da tausayi , janshi aka suka bar ɗakin Ashiru yana ci gaba da kuka.

  Kamar wata jaka haka nabi bayansu da kallo har suka gama fita daga cikin ɗakin. Goge hawayen daya taru a fuskata nayi. Na maida kallona inda Dikko yake kwance yana bacci. Tou ya haka ? Meya faru Dikko ya sake warwarewa ? Ko wayau yayi min daya bani labari cewa ya warke ? Ko yayi tunanin ni bazan iya ci gaba da zama dashi ba idan bai warke ba ? Labarin daya bani G R A a ɗakinshi ya tunomin da yacemin.....

 _Naso naga Al ' Ameen dan naso zanyi magana dashi amma hakan bai yuwu ba. Shi Mustaphan yayi ma Ashiru jagoranci zuwa inda suka binne tsafe²nsu , komai Ashiru yayi saida suka gama komai lunfashi na ya dawo , tunda nake ban taɓajin irin wannan tashin hankali ba wai an shanyemin numfashi kiji wani masifa ? Hmmm Yazeed kuwa Ashiru yaci ubanshi kuma shine ya maido Abbakar company duk bansan anyi ba._

   Dogon nazari nayi , na hasko duk maganganunshi na baya. Tabbas a maganar Dikko akwai lauje cikin naɗi. Wato ni zaima ƙarya ? Dani da ku masu karatu idan baku manta ba , ni yacemin wai yaje yayi jinya har na tsawon shekarun da nayi ina zaune a gidan Inna , ku kuma tuno. Tou ya akayi ya saki Jiddah bayan shi baisan inda kanshi yake ba tun daga ranar da ni nabar gidanshi naje gidan Inna ? Ya akayi takebinshi har Abuja ? Me yasa yayi min ƙarya cewa dawowarshi kenan yazo ya tafi dani a ranar daya aiko Abbakar ya kawomin waya ? Bayan tafiyar Abbakar kuma Ummar yazo da Umar ya tafi kuma shi Dikkon yazo da kanshi ! To me gaskiya ? Ni miye matsayi na a wurin shi ? Meya ɗaukeni ne ? Me yake nufi dani ? Tabbas duk yadda akayi maganar Inna itace gaskiya Dikko baya so na......... Mai gemun yaudara na faɗa cikin hayaniya ina cewa yau saina bar maka gidanka kaje ka samu daƙiƙiyar da zata zauna dakai , ka raina mutane ni nafi ƙarfin kai ka rainani...... Wai ni zaka faɗawa ka ɗaure kanka da wayar wuta ni zaka ba labarin "yan sfires {{ Express }}....? Fuuuu na fice daga ɗakin na koma ɗakina. Wayata kawai na ɗauka da makullin mota na fice.....

   Da gudu na fito waje ina kuka har wurin mota ta , ina shiga mota Ashiru ya iso wurin yace ina zakije ne ? Cikin ɓacin rai na nunashi da makulli cewa zanje gidan Babana. Ai kasan nima Babana da Mamana suka haifeni ko ? Yadda iyayen Dikko sukeji dashi kuma suke ƙaunarshi nima Babana haka yake so na , yadda yakeji shima ɗa ne a gidansu nima ɗiyace na nuna kaina , yadda aka haifeshi nima haifata akayi ba ta sama na faɗo ba , har yanzu hannu na yana kan ƙirjina ina nuna kaina. Goge hawaye nayi da hannun haggu na ina ci gaba da cewa duka׳ kullum Dikko saiya dakeni doke²n shine soyayyar da kake iƙirarin yana nunamin wacce har kake min gori akan ta ? An baki soyayya da kuɗi. Cikin marainiyar murya nace shin baka tambayeni me nake nema ba ? Saki nake buƙata daga wurin Mai gidanku. Bana san ɗaya ko biyu a rubutoshi duka a aiko dashi a gidanmu na ƙarasa maganar ina karta makullin motar a jikin sitiyari , zana makullin nayi a goshina ina ci gaba da cewa Sultana bata ɗaukar fansa kuma ba ƙudirin wata fansa zamana da Dikko , kafin insan Dikko inayin rayuwa dan mun rabu yanzu kuma bazai sa in mutu ba , nayi maganar nima ina dukan sitiyari cikin ɓacin rai. Nuna Ashiru nayi da makulli sannan na cije leɓina na ƙasa na tashi mota ina kallonshi..... Riƙe murfin motar yayi yana cewa idan dai kinga kin fita a gidan nan sai idan bana numfashi.....

 Ko kayi rayuwa ko ka mutu bai shafeni ba , nasan dai ni na gama magana kuma tunda na yanke hunkunci magana ya ƙare. Ba tare daya kalleni ba yace can baya na taɓa faɗa miki kiyi haƙuri idan baki manta ba , yauma shine nake daɗa baki Hajiya , bayanshi banda abinda zan iya baki a duniyar nan , tunda kike a duniya kin taɓajin wanda yace rashin haƙuri ya sa yacimma nasara ne ? Saidai kiji ance haƙurinta yasa ta cimma nasara , ba wanda zaiyi haƙuri yaji nadamar yinshi saidai nadama takan zo yayin daka gagara haƙuri. 

Ban faɗa miki maganganun nan ba dan kiyi zuciya ba , raina ne yaimin babu daɗi. Baki gaji fushi da gudu daga gidan aure ba dan wani ƙalilin abu. Tarbiyya kika gada , Babanki idan yana nan bazai so yaga kinyi yaji ko kina cewa a sakeki ko faɗa da miji. Kuma da yana raye ko kin tafi zai dawo dake bayan yayi miki faɗa da ƙara nuna miki matsayi da kuma martabar miji , dika² ma miye abun fushi ? Ya tambayeni yana murmushin ƙarfin hali , yaci gaba da cewa ai anyi wanda yafi wannan kuma anyi haƙuri sai ɗan wannan Hajiya…..? Wanda bai dakeki ba bai zageki ba ? Ki ƙara haƙuri tunda an hau tudu ai gangarewar baya wahala , kalli ya nunomin hoton Papi a wayarshi , ji yanayin farin ciki kin ajiye ɗan digu²n Papi ina zakije ki barshi ne ? So kike yayi kukan rashin uwa bayan kina raye ? Rayuwar aure da kika ganta gaba ɗayanta haƙuri ne a cikinta , idan akayi haƙuri sai a samu mafita , kiyi haƙuri sai Allah ya baki ladar haƙurin , kibi mijin ki zauna lafiya kiyi masa biyayya saiki samu albarkar rayuwa. Ki nemi gafararsa sai ubangiji ya gafarta miki , fito ki koma dan Allah ki kwantar da hankalin mijinki kema sai naki hankalin ya kwanta. Ya ƙarasa maganar da yanayin tausayi….. Yana ci gaba da cewa ba’asan maci tuwo ba sai miya ya ƙare , masha ruwa magirbi karki biye fushin zuciya kiyi abinda zai jawo miki damuwa. Da yaji da tambayar sakin aure sai “yan gidan da basu da tarbiya , ke ko kina da tarbiya da ɗa’a kiyi haƙuri ki koma idan har kika tafi zaki naƙasa matsayinki da kuma mutuncinki. Kiba Mai gida haƙuri zai haƙura kuma bazaiyi fushi ba danshi mutum ne mai mantawa da damuwa , a inda akayi mishi yayi faɗa ya gama da wurin. Yana da zuciya amma yana da ba abun duniya baya….. Fita ki nuna masa ke ɗin “yar Babanki ce….. Ki basa haƙuri domin ya ƙara tabbatarwa keɗin mai tarbiyace , ki nemi gafararshi sai yayi alfahari da iyayenki domin sune suka koya miki tarbiyar bawa miji haƙuri.

  Ko ba komai naji daɗi daya kira iyayena da masu tarbiya duk dai nasan za'ace niɗin eyar ɗan caca ne , ci gaba yayi da magiya yana bani haƙuri , kashe motar nayi tare da zare makullin na wuce banyi magana ba , ɗakina na koma na zauna gefen gado. Yayin da wani sashe na zuciyata yake cemin inyi haƙuri kamar yadda Ashiru yace , kuma in bawa Dikko haƙuri , ba ruwana da wani ciwonshi idan yayi aljannunshi idan ya gaji zai sauka , ya warke ko bai warke ba , ba damuwarki bane ba Sultana , abinda ya hanashi zuwa ya dawo dake tuni shima bai dameki ba , lokacin da ya saki Jiddah da binshi da takeyi dashi da ita da kowa ma can su ta matsemawa , kiyi tunani ki rufawa kanki asiri ki dawo daga rakiyar shaiɗan tun kafin duniya tai gwanjonki.

 Tunda ta gama waya da Sultana take ta ɓaɓɓarka zagi , wayar Mai gilashi ta kira amma kafirawan company suka ce mata a kashe yake. Dan haka ta bugi mota tayi gidanta , ba yabo ba fallasa Mai gilashi ta tarbi Sharifa kuma bata , bata izinin shiga ɗaki ba. Haka kuma babu maraba bare kuma sannu da zuwa. Da yanayin tsinkuwa Sharifa tace Mai gilas an fa samu matsala , dakel ta kalli Sharifa tare da tambayarta meke faruwa ne ? Mu shiga daga ciki cewar ita Sharifa , Mai gilashi tace ba buƙatar sirri a ƙuryar ɗaki , magana dake a fili da ɓoye duk iri ɗaya ne. Da mutum yayi maganar sirri dake gara yaje B B C ya faɗa kila idan anci sa'a a ranar wani bai kamo tashar ba. Faɗi abinda ke tafe dake ko na iya baki shawara. Mai gilashi ni a gwadamin iskanci ne ? A , a , waye ya isa ya nunawa na rigingine hasken farin wata ? Cewar Mai gilashi.  Sharifa tace to ni matar D ' K ta zaga , ta faɗamin magana , tayimin gori ta wulaƙantani ta muzantani ta tozartani sannan kuma ta tonamin asiri.......

  Cikin ko in kula tace duk me yayi zafi haka ne ? Zama kusa da ita Sharifa tayi cewa kwana biyu kenan bama waya bama cht kuma bana ganinshi , Mai gilashi tace kila a tunaninta yana wurinki ne ko ? Cikin rashin fahimta Sharifa tace kamar ya ? Riƙe bakinta tayi da sauri tare da cewa rufama kanki asiri kar aji mutuwar sarki bakinki Ade.... Inji Mai gilas.

 Sharifa tace kamar ya haka kuma ? Me zaki ɓoyemin ne bayan kinsan duk karatun iri ɗaya. Mai gilashi tace aini kin daina shawara dani faɗin gaskiya kuma zamanin nan yayi wuya , ina iya faɗa miki kije kiyi ta tallar terere dani , dan girman Allah Mai gilas faɗamin , Mai gilas tace gaskiya Sharifa ni inajin tsoro , dafa Mai gilashi Sharifa tayi tare da cewa idan dai baki faɗamin ba duk yadda tarenmu take tou lallai ƙullu yaci amanar koko , ɗan motsa kanta tayi alamar ta sanar da ita tare da cewa na baki dama kuma nayi miki alƙwari babu wanda zaiji ba wanda zai san anyi.

Mai gilashi tace:• shin bana faɗa miki kina da kishiyoyi ba ? Wanda suke ta harar Dikko a waje ba ? Sharifa tace kin faɗa , shin tunda kike ke Dikko ya taɓa² koda hannunki ne ? Ai bama ya kallo na , tou lallai cikin hijabi kike je mishi zance , Sharifa tace ey wallahi , kina zama kusa dashi ko a , a ? Shiru Sharifa tayi , Mai gilashi tace tou lallai nesa kukeyi da juna ta faɗa tana dariya tare da nuna Sharifa da ɗan yatsa , kallonta Sharifa tayi cewa ai babu ma ta yadda za’ayi ni na zauna kusa dashi , Mai gilashi tace da irin wannan baƙauyar soyayyar zaku cinma nasara har a kai ga matakin aure ? Miƙewa Mai gilashi tayi ta kalli Sharifa sosai sannan tace duk dabbar da tayi kuka tana da dalilin da yasa ta koka , yayin da wasu kan koka lokacin da suke buƙatar abinci , wasu kuma sukanyi kuka yayin da suka ƙoshi ne , kare yakanyi haushi yayin da rigimarshi ta motsa , duk wanda kika gani kwance kila yana rashin lafiya ne ko kuma yana da ƙatotuwar damuwa , haka take ga duk namiji daya tirki ƙarin aure…..

Previous page 1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Back to top button