KWARATA RETURN COMPLETE

KWARATA RETURN COMPLETE

[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ BRILLIANT WRITERS ASSO ????
-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-

      *KWARATA RETURN...*
 _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

Rubutawa…
JAMILA MUSA…

  *SAI NA AURI D ' K*

???? —— 1

 Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai.... Dakel aka fiddoshi daga wurin , dan bashi da hankali akan ɓarar da kuɗi. Idan zai kwana a haka baya gajiya kuma ba zai daina ba , zaiyi ta zubawa ne baya gajiyawa , haka kuma idan zai bayar yake kyauta maisa ɗimuwa.


 Wace ce ita...............???


 Wata irin dariya yakeyi bayan an fito dashi yana tsaye gaban Momy data bishi da kallon takaici , hahahaha yaci gaba da dariya yana kallonta , nima binshi nayi da kallo ina murmushi saboda ba ƙaramin kyau yakeyi ba idan yana dariya....

  Momy tace idan ka gama haukar ka ɗauki matarka ku tafi gida , daina dariyar yayi tare da taɓe fuska , a yatsine yace ai ba tare nazo da ita ba. Murmushi mai cin rai nayi , ba tare dana sake kallon inda yake ba. Kafin inyi magana akaja Momy wai anayin faɗa , binta Rabiya tayi da sauri ni kuma na kalli Dikko ƙasa da sama a yatsine nima nace , tir tittir nabi tsoho ya ɓatamin wanka , nine tsohon ? Ya tambayeni yana nuna kanshi.

  Yadda ya ɓata ranshi yasa nayi shiru ina kallon ƙasa , jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai sannan yace Allah ya maida mu gida lafiya , banyi magana ba kuma banyi gigin sake ɗagowa na kalleshi ba , nine dai tsoho ko ? Ya sake tambayata da yanayin ranshi ya mishi babu daɗi , hmmm tsoho , ƙara jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai , mtswww , ya wuce daga wurin yana magana ƙasa².

  Da sauri na ɗago ina kallonshi dan harya tafi ya sake dawowa , nine dai tsoho ko ? Dan ina tausayinki kenan yasa kika raina ni ? Har nine zaki kalli tsabar idona kicemin tsoho tsabar kin ɗaukeni sallau , duk shekarar nan ni banma samu wanda ya ɗaukeni sakarai ba kamar ki , ajiye kai yayi da ɓacin rai , zaki ci gidanku Allah ya maida mu gidan lafiya zaki faɗamin nine tsohon idan na riƙeki , yana faɗin haka ya wuce , a firgice na juya bayana da sauri , Rabiya ce ta dafoni ta baya , nayi tunanin shine ya sake² dawowa.

 Ana fita da Dikko itama ta sulale ta fice daga cikin holl in da farin cikinta , ta wani ɓace abunta ba tare da anga fitarta ba , jikin motar ta , ta tsaya ta saka hijabi da niƙaf , bayan ta gama ta wani shige tayi layar ɓata abunta , wannan shine ɗabi'arta , hijabi da niƙaf , bata rabuwa dashi ita musulma , idan kuma zata tafi bariki bata fita da motarta dan gyaran tako.....

  Wai ke me zakiyi mata ne kike neman ta ? Barni na ganta sai in ɗauki mataki a gabanku , tou wai yaushe suka saba haka har ya saki jiki yana mata ɓarin kuɗi a gaban bainan nasi....? Waye ma zai iya sani ? Tsoki ƙawarta tayi cewa wai kema Jiddah bazaki bar wannan banzan Dikkon ba ? Sai kace Dikkon diamond ? Murmushi Jiddah tayi tare da kallon Mardiyya cewa faɗa mata waye Yaya D ' K.

Cike da tsantsar soyayyar Dikko Mardiyya ta fara rattafo mata , hmmm ai ya wuce duk inda hankali baya tunani , saima kin ganshi , gashi mai kyau , ɗan gayun bala’e uwa uba ga kuɗi ga mulki , idan yana magana sai ya baki sha’awa , gashi sakatacce wani irin kallo yakeyi mai burgewa , Dikko matashi ne mai wayewar kai , buɗewar ido da gogewar rayuwa amma bashi da mutunci ko kaɗan , damen ɗan iska ne , kuma shiɗin ƙyalƙyal na lariya ne , tantirin kwallon ɗan iska ne yanzu mutum anjima bai sanki ba , yana da baƙon hali , haƙurin zama dashi sai ɗiyar ɗan caca , dan itama “yar tasha ce. Kinsan auren tasha baya ƙarewa saida aci uban juna yanzu , anjima kuma a zama masoya , duk da biyu Mardiyya tayi wannan maganar , sanin manufarta na faɗar haka sai ita da kanta.

  Ƙawar Jiddah tace tou ni me yasa baku kirani na ganshi ba lokacin daya shigo ? Murmushi Jiddah ta sakeyi tare da cewa har hanzu baki makara ba , Mardiyya bata hotonshi ta gani , a duniyance Mardiyya tace waye yaba Mardiyya hatimin nasara ita ba jikar matsafi ba , ai hoton Dikko sai wurin matarshi , gaba ɗaya suka ɗingumo suka yo wurina !

 Sultana Momy tace muje in ajiyeki gida , tou na faɗa tare da kallon agogon wayata 11:22am gaba nayi ba tare dana sake magana ba , ta baya Jiddah ta riƙomin riga , da sauri na juyo dukana dan ganin waye ya rainamin wayau haka ? Cikina ta kalla sannan kuma ta kalleni amma yanayin fuskarta ya nuna taji babu daɗi , amma dake "yar duniya ce , saita wayance da murmushi cewa ina ta magana shiru nace ai nasan bakiji ba , banyi mata magana ba na tsareta da ido , dafe kafaɗa ta tayi kamar ƙawarta tana cewa Aunty Rabiya ai muma a gidan Yayan zamu kwana.

 Rabiya bata kalleta ba tace ai kina da numbershi ki kirashi ki faɗa mishi , ai basai na kirashi ba kuje gidan muma muna zuwa bayanku , Rabiya bata sake magana ba ta wuce , sauke hannun Jiddah nayi daga jikina nima na wuce muka tafi , har muka zo gida Rabiya batayi magana ba nima banyi ba , a waje ta ajiyeni ta wuce. Ni bansan abinda ya haɗasu ita da ɗan uwanta ba , ni na shiga da kaina ciki raina a jagule , a get na biyu na haɗu da Ashiru , yana gani na ya tsaya yana cewa ranki ya daɗe mai gida yace naje na taho dake , ko inda yake ban kalla ba kuma banyi masa magana ba na wuce , shi kuma ɗayan marar kunyar a get na ukku na haɗu dashi shima fita zaiyi , wato bai gaji da iskancin ba zai sake komawa , kenan dawowa yayi gida ya sake sabon wanka , yanzu garin nashi ya waye , ko wane bawan Allah idan dare yayi yana gidanshi yana bacci , koba a gida ba duk inda kake idan dare yayi zaka samu natsuwa , idan bakayi bacci ba , tou kana kusa da ubangiji kana bauta masa a dai² irin wannan lokacin , amma banda Dikko daya maida dare lokacin huɗɗoɗinshi.

 Shima magana yayi min wai daga ina nake ? Kuji fa ? Wai ma daga ina nake ? Kamar ma baisan ina ya baroni ba , shima ko inda yake ban kalla ba na wuce , An mata bakyaji ina miki magana ne ? Ban dawo ba kuma ban tsaya ba na wuce , da ribos ya biyoni saida yazo inda nake yace ke Yarinya bakiji ina magana ne ? Canja hanya nayi naci gaba da tafiya , An mata dake nake fa ? Ganin Sultana tabi hanyar da zata shigar da ita ciki batayi mishi magana ba , yasa yayi parking ya fice da sauri yabi bayanta.

 A palo na zauna ina cire takalmi na , idona cike da hawaye , ai dama Inna ta faɗamin Dikko ƙyalƙyal na lariya ne , bana iyawa da duniyancin shi , tace Dikko ba mijin aure bane ba , amma na kafe kai nace ni ina sansa a haka , yau naga kaɗan daga iskancin shi. Goge hawayen da suka gangaromin a fuska nayi tare dayin shashshekar kuka , shine saida aka tara taron dubu da dubu ya fito yana ma wata liƙi dan ya nuna ma duniya ni ban kai mace ba , ni ban kai sahun irin matan da yake aura ba , ya nuna ma duniya ni ba'a bakin komai nake ba a wurinshi , Momy tace masa ya taho dani gida yace shi bashi ne yazo dani ba , ashe kuma gidan zai taho dan ya sake nunamin ban kai macen dashi zai saka a gaban mota ba ko wayewa yasa ya taho ya baroni , hakan bai mishi ba zai tura Ashiru ya ɗaukoni dan ita budurwar tashi taga shi bashi ne ya taho dani ba , ta gani saida shi ya koma gida sannan ya turo driver ya ɗaukoni , dole Ashiru ya ɗaukoni mana tunda dare yayi yanzu ne yasan amfani na , maganar Inna ta sake duwomin da tace , haka zaiyi ta ɗura miki ciki kina haifar mishi "ya "ya nan ne kaɗai matsayinki.

  Da sallama ya shigo palon , takalmana na ɗauka nayi gaba , ban ansa sallamar ba haka kuma ban kalleshi ba , An mata baki lafiya ne ? Yayi maganar yana biyo bayana , ban mishi magana ba har ɗakina , ina shiga na fara tattara kayana , miye haka kikeyi ne ? Haba An mata wai duk miye na fushi ? Kiyi haƙuri akan abinda ya faru dan Allah , goge hawaye na sakeyi naci gaba da tattara komai nawa , kusa dani ya matso yace An mata Dikko zaki ma yaji ? Haba jarumar mata ban sanki da irin wannan halin ba , kiyi haƙuri ya ƙarasa maganar yana riƙeni jikinshi , kalleni , saida na sake goge hawaye na kalli Dikko , nine ? Yayi maganar kamar zaiyi kuka , banyi magana ba ina kallonshi shima ni yake kallo , a kasalance yace kinyi haƙuri ko ? Ya ƙarasa maganar yana warware fuskarshi da yanayin burgewa , har yayi surutunshi ya gama bance masa kaci kanka ba , saida ya gama rattofo yaudararrin kalamanshi yai tafiyarshi ya barni.

 Tun daga ranar Dikko ya sake ɗaukewa , ma'ana ban sake ganinshi ba , nima ban sake komawa gidansu ba , Jiddah kuma a ranar waje ya ganta masu gadi sun hanata shiga , saida yayi mata rashin mutunci mara ɗaura zani ya ƙara da cewa dama yana cike da ita akan abinda tayi ma Papi , akwai lokacin daya iba mata zai sameta har gaban uwarta anan zai nuna mata tsabar rashin mutuncin shi , duk su basu san halinshi ba labarin iskancin shi sukeji. Tou zaizo har Kadunar , shiru yayi yana kallon wayarshi , bayan wani lokaci yaci gaba da cewa tou a ranar zataji shi yadda yake , kuma idan take sake shiga sabgar iyalinshi kota kuskura ya sake ganinta a goruba koba gidanshi tazo ba , ya jinjina kanshi tare da cin taya ya barɓaɗeta da ƙura , ta gane abinda yake nufi , kawai zaibi ta kanta ne kamar yadda yaci ƙasa ya wuce abunshi....

 Ko a makaranta , haka nake kasancewa suku². Banayin wata walwalla , ina ɗauke da damuwar da tafi ƙarfin shekaru na , cikin kwanakin da basu wuce biyu zuwa ukku ba nayi duhu na rame , kuma ba rashin ci ba nasha , babu abinda na nema na rasa , ina tunanin Dikko ne kawai dakemin wahalar gani , dan yanzu ankai gafen dako text na tura mishi baida lokacin bani ansa , idan na dameshi sai yacemin wai bansan yadda abubuwa suka sha mishi kai ba , saiya rufeni da faɗa ta waya , idan kuma nace na taga barinshi Inna bama zata anshe ni ba , haka nan kawai na fashe da kuka a class , kuma gaba ɗaya ajin yayi shiru saboda malamin dake ciki , duk wanda ke cikin kilas in maza da mata kowa ya juyo yana kallona , miƙewa nayi na fara tafiya ina ƙara yawan kuka na , har nayi nisa. Na dawo na ɗauki sch bg ina da makullin mota naci gaba da kuka ina fita daga cikin ajin ko malamin baimin magana ba.

 Daga makaranta kai tsaye gida na nufa har naje kuka nakeyi , dakel nayi parking na fita ko gabana bana gani na shiga ciki , a palo na sameshi zaune , hankalinshi kwance yana cin abinci baida wata damuwa , kenan idan ina makaranta yake dawowa gidan yayi duk abinda zaiyi ya tafi kafin in dawo tunda yasan lokacin dawowana , sannu da zuwa ya faɗa tare da bina da kallo , cike da ɓacin rai na nufi kicin na ɗauko wuƙa ina cewa saina kashe ka , da sauri ya tashi yana innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , An mata kinyi hauka ne ? Yake tambayata yana nuna saman ƙoƙon kanshi , ey hauka nakeyi , na faɗa ina matsawa kusa dashi , da sauri ya koma can saman inda ake jingina na kujera idan an zauna ya zauna ƙafafuwanshi a saman wurin zaman , yace waye yace miki ana wasa da wuƙa ? Ba wasa nake ba kashe ka zanyi kowa ya huta na gaji da baƙin halinka ko kuma ka sakeni in kama gabana , ta baya ya sauka yana dariya. Lallai An mata amma ban taɓa sanin mahaukaciya bace ke sai yau. Ai dole zakacemin mahaukaciya tunda ka samu mai hankali , riƙe wuƙar nayi dai² yadda zatamin sauƙi wurin burma mishi nace ka sakeni kafin in tuno maka asiri , dafa kujera yayi yana kallona ,

Zagayawa nayi inda yake har yanzu ban daina kuka ba , dariya yakeyi sosai , cikin dariya yake cewa ni idan wasa kikeyi nawa na gaske ne , ina nan yadda kika sanni ban canja ba. Dan kinga kwana biyu na ƙyaleki kike duk iskancin da kikaga dama , cike da tsantsar ɓacin rai yazo kusa dani yace cakamin wuƙar , cikin hayaniya yace caka׳ , shiru nayi nasa wuƙar ta kalli ƙasa , ƙaryar rashin kunya dakin sake nunamin ita dasai na burma miki ita kin mutu kuma na kashe banza , bari jin Mama tace ke taurin kai gareki , ke kuma kina iƙirari idan kika sa kanki abu babu wanda ya isa yasa ki bari ni nafiki taurin kai da rashin kunya , zanje in zauna ko motsi mai ƙarfi kika sakemin sai kinga yadda zanyi dake , yayi maganar yana komawa inda yake yaci gaba da cin abincinshi.

Kuma koba yau ba saina kashe ka , ke idan wasa kike ni zan kasheki da gaske ne , a tsorace na wuce ban sake magana ba , shi kuma yace zoki ki zauna muyi magana , ƙara fashewa nayi da kuka nace bazan zo ban , ki daina ganin ina lallashin ki , duk ranar da kika cika ni idan kika bari na riƙeki jikinki zai baki labari yayi maganar yana nunamin belt in dake ɗaure ƙugunshi , a wurin da nake wucewa na yadar da wuƙar na wuce ciki ina gunguni , kuma saina ɗauki number duk wata mace a wayarshi , anan zan gano wace ce zai aura saina cicci ubanta…..

 Satina ɗaya rabona da zuwa makaranta , kuma Nabeela da kanta ta tabbatar min cewa Yaya zaiyi aure , zai auri ɗiyar ƙanwar Dady da suke Baba ɗaya , { idan baku manta ba shi Dady a ɗakinsu shi ɗaya ya rage , "yan uwanshi kaf sun rasu sakamakon gobara data cinyesu , su kuma sauran matan bayan an basu kuɗi ko wace ta kama gabanta ita da "ya "yanta , dalilin auren ne yasa yake aikin gidanshi na G R A , kuma itace yarinyar da yayi ma liƙi , Dady ne yakejin farin ciki Dikko zai auri ɗiyar "yar uwarshi kuma shine yayi mishi tayin auren dan ƙara ƙarfafa zumincinsu a matsayin shi na babba , wanda shima Dadyn Mamar yarinyar ce ta nuna masa alfanun hakan , tunda tayi tayin Dady ya karɓa dan cika farin cikin mahaifinsu da yace yasan ko baya raye Umar zai zama jigo ga "yan uwanshi , wanda shima Dadyn yake fatan Dikko a zama bango ga "yan uwanshi mata idan baya nan , shi yasa ya miƙe tsaye saida ya tabbatar Dikko ya daskaru hankalinshi ya kwanta tare da binshi da addu'a , Momy ce bata san auren dan ta raina ahalin Dady yadda mai tunani baya zato , wannan dalilin ne yasa duk suke fushi da Dikko , da Momy ta fara wani tirje² Dady yace ta bari kar rabo ya kashe ta , ai itama an auri nata "yan uwan amma ba'a dace ba , dan haka a bari a taga gaba ko a dace dan auren zuminci abu ne mai kyau , wannan kenan. }

 A makaranta kuwa an kira Dikko cewa na daina zuwa makaranta , su kuma ƙawayena har gida suka zo , suka tambayeni abinda yasa nayi kuka a waccan rana , da abinda yasa na daina zuwa makaranta , na faɗa musu mijina ne zaiyi aure , kuma auren ma na zuminci dan dai kawai su haɗemin kai da "yar uwarshi ni a juyamin baya , na kuma basu labarin liƙin da yayi mata , wanda ni bansan dalilin da yasa yayi shi ba , juyamin baya da rashin san kasancewa dani a inuwa ɗaya , rashin dawowa gida da wuri sai nayi bacci , fita tun safe kafin in tashi , da dai wasu halayya dani bansan yana dasu ba sai yanzu da zai ƙara aure , shine Farisa tacemin ai mazan yanzu idan ana raga musu iskanci suke na wuce shari'a , kar in wani damu kuma na daina ajiye damuwa idan ba haka ba hawan jini zai kamani na mutu a banza in bar yarana , shi kuma zaiyi jimamin rashina na kwana 3 daga nan yayi aurenshi ya buɗe sabuwar rayuwa ya manta da labarina , "ya "yana kuma ayi ta gana musu azaba , su tashi babu wani galihu ko "yanci kamar almajirai , itace ta bani shawara ƙauracewa ɗakin miji , daina bashi abinci , rashin kunya kuma saina cire shakkun Dikko dan matsoraci baya zama gwani ko waye , ta ƙara da cewa na fita sabgar kaf ahalin miji dan dasu ake haɗa duk munafurcin , wannan duk ɗabi'ar mahaifiyarta ne , idan suka samu matsala da Dadynsu bata zuwa ɗakinshi kuma batayin yaji saida tanayin gayu mai ɗaga hankalin namiji , tace idan anyi yaji babu ta inda za'aga miji bare a samu damar gasa masa aya a hannu , a gida za'ayi duk masifar ayi a gama , tou kundai ji matan aure , shine fa tun daga wannan rana na birkice na zama fitsararriya , abun bai tsaya a iya Dikko ba ya shafi kowa da kowa.

 Wani irin gigitaccen mari na yankawa Papi tare da ce masa dan ubanka waye yace ka zubarmin lemu a kafet......? Tashi Papi yayi ya tafi wurin Dikko.......! Da fatan mai karatu ya gane...........???

 Ci gaba nayi da cewa ni banajin tsoron wani zare²n idon banzar mutum , idan taƙamar mutum yace zai dakeni saina bari ya kwanta bacci in mishi wanka da ruwan zafi ko in dafa mai in toye mishi fuska , ko inda nake Dikko bai kalla ba yaci gaba da rirriga Papi da yaƙi ya daina kuka , ni har an nunamin iya zare ido ? Ko rashin kunyar kafi ni iyawa ne ? Nima nan na iya ai shiru² ba tsoro bane ba , kace tuf ka gani , saboda nasan nayi masa nisa , dan tunda na mari Papi na koma matakal bene na zauna daga wurin nake yanko magana , { idan kun tuna benen g r a ya sauke lokacin dana faɗo , na goruba kuma na hau nace zan faɗo ? Yace shine zai jefani na faɗa na mutu , wanda bayan na gudu da yake bani labari yace shi ya ɗaure kanshi da wayar wuta ya faɗo daga sama , wanda ya tafi doguwar jinya.... } fita yayi yaje ya bada Papi ya dawo , har lokacin ban daina zage² ba , shine yajani yakaini ɗakinshi ya rufe bakin rashin kunya.

An mata wai meke damunki ne ? Gaba ɗaya kin zama mahaukaciya , cike da ɓacin rai nace kaine mahaukaci........ , duk girman kwanakin da kake saukewa ai ba'a kaina kakeyi ba , wannan matsalarki ce , tunani da neman mafita ya rage naki ƙaramar yarinya......! Riƙe yatsana yayi a bakinshi....... ` saida ya gama duk abinda zaiyi ya shirya ya fice abunshi.....

Wasu irin zafafan mata ne zagaye dashi ,,,,,,,,,,,,, duk girman daren nan batajin shi bata kuma ganin shi.````, tsaye take a jikin madubi , fitowarta daga wanka kenan , da wayarta ta saita kanta bayan ta danna video , cire towel in dake jikinta tayi taci gaba da ɗaukar kanta tana iskanci .......... Madaidaicin gida ne a cikin anguwar kwaɗo duk yara²n mata ne suke ta gulmar mazajensu , wayarta ta kanga a jikin ƙugunta tayi wasa da jigidar dake ɗaure a ƙugunta , Jiddah bata da burin daya wuce Yazeed yayi auren kishin wuta da ita , *KWARATA RETURN...* fatan mai karatu ya fahimta ko....?

 Ƙwas׳ ƙarar takalmin ta kakeji a saman tayils , duk lokacin data motsa dan takawa sai jigidar dake ɗaure jikin ƙugunta ta wani ce cas׳ , idan tayi girgiza kuma sai ta wani ce kacau׳ , gyara zaman ɗaurin kallabinta tayi tana ci gaba da tafiya , harta bayyana a cikin palon , sai yanzu ta samu damar fesa turare bayan ta tsaya a gaban wani mutum wanda shekarunshi zasu kai kimanin 50 , Alaji barka da safiya , ta faɗa a shagwaɓe tana kwarkwasa , ɗagowa yayi da niyar ansa gaisuwar , ita kuma ta ɓalle botiran gabar rigarta dake sanye a jikinta , after dress ce a jikinta. Tana buɗewa ƙanan kayan data saka daga ciki suka samu damar bayyana , a aljihun wando ta tura kwalbar turaren data gama shafawa dakel tare da gyara kitson atach ta watsoshi ta gaba da bayanta , miƙa tayi sosai tana cewa yi haƙuri Alaji na rashin fitowa ta da wuri take maganar tana wani mimmiƙewa kamar macijiyar data samu wurin sanyi a lokacin zafi , cikin ɓacin rai mutumin yace ke me yasa baki da ɗa'a ne ? Kuma ni bake nake nema ba mijinki nake kira , 

 Cire after dress in tayi ta wurgar a ƙasa ta ƙara matsawa sosai kusa da Alhaji tana cewa taya zanyi ɗa'a , mai siyar da kayan ƙara kuzarin maza me ya haɗata da ɗa'a tarbiyya ko kunya ? Kaje anguwarmu kayi binciken Sa'adatu mai gilashi kaji me zasu ce maka ? A wannan duniyar idan akwai wani sirri daya kamata al'umma ta sani akan mu'amalar aure tou bai wuce na mata da miji ba , dalili kuwa shine sirrin da ba'a koyar dashi a makarantu ko a gidaje , shi kaɗai ne sirrin da sai wani da wani ke saninsa , to amma kasancewar hanyoyin isar da saƙon sun yawaita nake ganin ta wannan hanyar ya kamata kasan wani daga cikin irin nawa sirrin , matar malam bahaushe ce kan gaba wajen shiga matsalolin aure , kamar yanda zakaji matan na faɗa babu soyayya tsakanina da mijina , shi yasa nake fuskantar matsaloli a gidan aure na , ni gaba ɗaya wannan matsalar duk na tattarata na jibgata akan mata , ɗan yatsina fuska tayi tare da ci gaba da cewa nima dai hakan take daga gareni tunda banyi auren soyayya ba , tsoki tayi sannan taci gaba da cewa , kawai ƙusani akayi wanda ni ba haka naso ba , wannan auren baya hanani neman mazan waje kamar dai yadda nake nemanka. Ci gaban da aka samu na sanin sirrin rayuwar da nayi maka magana shine , hanyar kula da mazaje ta yawaita , wayewar kai da buɗewar ido , zamani ya kawosu sun kuma yawaita ta haryar gidajen karuwa da kuma ganin wannan sirrin ta kafofin yaɗa labarai a nahiyar yana giza gizo a maimakon da can zamanin iyaye da kakanni da wannan sirrin yake ɓoye , an samu ci gaba sosai wanda har takai yanzu idan za'ayi ma yarinya aure basai an faɗa mata cewa idan mijinki yazo yaja zariyar wando karki gudu , ko kuma idan yayi haka , ta zage zif in wandonta , cikin yanayin jin kunya Alhaji ya kauda kanshi gefe guda , wata "yar munafikar dariya tayi tare dayin wasa da yatsun hannunta taci gaba da cewa , suma ƙawaye dake zuwa gidajen ƙawayensu idan sunyi aure danjin labarin sirrin auratayyar yadda yake sun daina zuwa saboda zamani ya kawo manashi sauƙaƙe , ni da kuma kai kowa yasan abinda yake faruwa tsakanin namiji da mace idan suka keɓance , amma ci gaban zamani yasa yanzu su kansu iyaye sun daina wannan huɗubar wa "ya "yansu saida kaji ana cewa yi nayi bari na bari , me zakiyin me kuma zaki barin ne......?

  Murmushi Alhaji yayi tare da kallon Sa'adatu , ɗan girgiza ƙirjinta tayi cewa tou ya kaga nan , da kuma nan tayi maganar tana nuna gabanta da kuma bayanta , bayan ta tabbatar ya kalla ta fara bada step tana tafiya cikin salon mai ɗaukar hankali , saida ta ɗanyi tafiya kaɗan ta juyo tare da ɗan zira yatsunta a aljihun wandonta , gaɓar hannunta riƙe da ƙugunta taci gaba da karkaɗo ƙugunta tana tahowa wa da girgiza , girjinta yaci gaba motsawa , dariya tayi a dai² lokacin data dawo gaban Alhaji ta riƙo kanshi ta ɗora fuskarshi a saman ƙirjinta cewa ya kagani ne ? Shiru Alhaji yayi , ita kuma tace karka damu ina da sirri , sakin kanshi tayi tare da ɗaukar rigarta bayan ta ajiye mishi number wayarta a rubuce jikin takarda tace idan kana da buƙata ka kirani , tana faɗin haka ta rataya rigarta a ƙafaɗar ta fice ba tare data maida rigar ba....... Kamar wani gelele haka yabi bayan Sa'adatu da kallo. ????????

Cikakken sunan nata shine Sa'adatu Ibrahim , iyayenta talakawa ne na bada misali , babu arabi ba boko haka ta taso a sake kamar ɓatattar dabba , bata nan bata can , bata da aiki sai tallace² , cikin tasha kasuwa da sauran madakatar "yan iska , idan kuma dare yayi sai a kasa mata tallar kayan mata take bin gidajen karuwai , a gidan karuwai ta fara sha'awar shiga sabgar karuwanci dan tana ganin yadda karuwai keyin sabgoginsu , da kuma yadda suke wasa magungunanta da faɗar irin matsayinsu da aikinsu idan sunyi amfani dasu , ita abinda yafi bata mamaki shine , yadda karuwa ke cika ƙatuwar roba irin ta wankan jego da ruwa , mintuna kaɗan namiji yana jiga ɗaki zai fito ya bada maƙudan kuɗaɗe , idan namiji ya fita sai ita karuwar ta shiga cikin robar ta wanke ƙasanta da wannan ruwan , ashe lemun tsami ne ake matsawa a ciki shine ke hana namiji daɗewa idan ya kwanta da mace , yana zuwa akan mace batsal² zai sauka ba tare da ya biya buƙatarshi ba yadda yaso ,

 A gidan karuwai ta fara laɓe jikin window idan mace da namiji sun keɓe , nan ta fara sanin muhinmancin kanta da kuma taƙama da ƙatuwar ƙaddarar da gareta , jin manyan maganganun da suka girmi tunaninta yasa itama ta farajin shauƙin buƙatuwa da abun , wannan dalili yasa ta fara kokowa da maza a tasha , da namiji yayi mata abu saita kamashi da kokowa , shine ta samu wani damen ɗan iska ya fara ɗora mata hannu akan alƙalaminshi , daga nan abun ya zame mata abun tunani da san ganin alƙalamin rubutun maza yadda yake a bayyane , tun daga wannan ranar taci gaba da binshi da kokowa , shi kuma duk lokacin data kamashi saiya ɗora mata hannunta , a hankali ta fara warwarewa ta kwace gaba ɗaya , ta daina bari saiya taɓa mata , daya zo sai kawai ta cafko wurin , shi kuma idan ta taɓo sai yake ƙara gudun numfashin alƙalamin , a hankali dai ya samu ya maida ita "yar hannu ,

 Itama lokaci guda ta faso ta zama riƙaƙƙar "yar iska , tafi ƙarfin iyaye ta daina ɗaukar talla , kafin wani lokaci ta zama Sa'adatu mai gilashi , bayan wani lokaci kuma ta koma mai gilashi kawai , ganin tana ta ansar wuta a harkar bariki yasa iyayenta suka kwantar da ita da aure , tsaye take har yanzu , tunda akayi aurenta taga ita bata dace da zaman BQ ba , Alhajin ne ya kamata ya aureta ko kuma kawai taci gaba da saƙashi a ɗaki tana ci mishi uwa a gado , tunda tazo gidan ta fuskanci yadda Alhaji ke zama da iyalinshi shi yasa take ta mishi tayin kanta , amma ya cika kafiya har yanzu bai amshi tayi ba , ita kuma ta duƙufa akan saita farautoshi ya zama nata ita ɗaya , ta bashi yaƙi ansa , shine wata rana taje ta bashi number wayarta , yadda ya fara kiranta har aka ƙulle duk zamuji....

 Riƙe take , ta wanku iya wankuwa , tana sanye cikin wasu irin sheɗanun kaya masu nuna shatin bireziya da fant , a haka ta tunkari Dikko tana tafiya irin ta riƙaƙƙin "yan bariki , ƙafa ɗaya ake fara shigar da ita ta gaba sai wata ta biyo bayan waccan ta fita , ba bazar² ake tafiyar ba a nutse akeyin tafiyar kuma takon bada tazara ake miƙashi ba , sai tafiyar taɗan riƙayi kamar mutum yana harɗewa kai baƙon abun sai kaga kamar mutum zai faɗi , ba kuma kamar yayi tuntuɓe ba , sudai "yan duniyar sune suka san dalilin yasa sukeyin irin tafiyar a gaban maza , ita kuma tafiyar idan anyita zata ba jiki damar motsawa , kafin ta ida isowa ya gama kalleta tsaf daga ciki , tunda munafikin gilashi ne motarshi , wato na ciki ke ganin na waje , shi kuma na wajen baya iya ganin ka dan duhun gilashin motar , ɗan taɓe baki yayi tare da ɗage girarenshi ya gyara gemunshi sannan ya saka cingom a bakinshi. Saida tazo jikin motar ta kama da niyar buɗewa taji ta a rufe ,

 Ɗan fara kwanƙwasawa tayi , bata san ya ganta ba kuma yaga zuwanta iskanci ne kawai yasa ya basar da ita saiya gama kallonta zai fito , idan ya fito kenan bazai kalleta ba bare ta gane tayi ko batayi ba , har ta gaji da tsayuwa taɗan fara canja wuri Dikko bai fito ba kuma bai buɗe ba haka kuma bai daina kallonta ba , Sultana ya kawo ya jera kusa da Yusra , girgiza kanshi yayi tare da cewa kai An mata fa ƙarshe ce , murmushi yayi tare da kallon hotonta a waya yace rashin kunya kenan , Dikko ׳ suna na kenan a bakinki ƙaramar yarinya , dariya yayi tare da ƙara zuƙo hoton yace wai nine zaki dafa mai ki ƙonamin fuska ke mahaukaciya , in Allah ya yadda saina samu lokaci na zaneki An mata dan naga iskancin naki kullum gaba yakeyi , ya ƙarasa maganar yana sumbatar hoton yace ina sanki ƙawar faɗa ta. Ƙara kallo Yusra yayi sannan ya sake kallon hoton Sultana , yace An mata babu inda Allah ya rage ki amma da wannan yajuju wa majujun aka tsere miki , me na rage miki ne ? Fita goma idan zanyi saina shigo miki da duk abinda nasan zaki ƙara sama dashi a zuciyata so goma , ragamata gaba ɗaya na miƙa miki amma kin kasa riƙewa , babu abinda kika aje sai rawar kai kafiya da rashin kunya nan kaɗai kikafi auki.

 Mafiya yawan maza da irin wancan ƙarshen duniya mata ke fizgar imaninsu su cusasu harkar bariki ko basu shirya shiga ba, wasu kuma mazajen laifinsu ne , misali , banbancin matar aure da karuwa , rashin adalci da wasu mazajen sukeyi shine , su kansu kaɗai suka sani kuma rayuwarsu kawai suke ginawa ta hanyar ba kansu cima mai gina jiki da kuma sutura mai martabasu , ka auri matarka ka kawota gida ka jibge , sabulun wanka da turare man wanke baki da kuɗin kitso da ƙunshi ka gagara tsare mata su , amma kai duk sabon yadi ko shadda takalmi da agogo sabuwar fitowa ko wata hula ka siya kai kanka kawai matarka kuma ko oho , kamar Babansu Sultana kenan , ka gagara ciyar da iyalinka da abinci mai kyau ka haɗata da ƙanzo ko garin kwaki , kwaɗon tuwo taliya da manja , kai ko kullum kana can biye da santa lungu da saƙo kana gano sabbin gidajen dahuwar abinci da aka buɗe , kabar matarka da koko kai kuma kaje ka raya kanka da lafiyayen shayi da biredi saboda rashin adalci , abin nufi anan shine ita matar aure ga Allah ta dogara gareka ta dogara , kaine duniyarta kuma kaine take jira ka bata komai na rayuwa , tou bakayi mata ba kuma baka bata ba , ba tada wata wadata ga kuma rashin kwanciyar hankali lokaci guda saita buge gaba ɗaya ta tashi aiki , ga masifar ka na yawan buƙatuwarta gareka , bata da wani ishashen ƙoshi bare ta samu ƙarfi da kuzarin anshe jarabarka kafin a ankara mace ta tashi aiki.

  Shikenan kai kuma ka gama da ita , baka da aiki sai zaginta idan ka zauna majalisa , matarka ƙazamiya ce , bata kitso ba wanka ba ƙunshi gaba ɗaya ta tsofe , tare mukayi aure da wane ko wane ya rigani aure amma har yanzun matarshi kamar yanzu ya aurota , bata tsufa kullum "yar yarinya take komawa kaza׳ bayan kaine mugun , kuma kaine ka tsofar da ita , ka kuma ƙazantar da ita ta hanyar rashin bata duk irin kular daya kamata , shi kuma wanen da kake magana yana kula da matar tashi , yana tsaye akanta wurin ganin ya ciyar da ita ta yadda ya kamata , duk sabuwar atamfar data fito ko wani less janbaki sabon yayi saiya siyo ya kawoma matarshi , sai kuma akaci sa'a mai gayun ce da ansar wanka ba dole zata zama yarinyar ba ? 

Ana haka sai kaga wata "yar budurwar tana wucewa da ƙyallinta , iyayenta suna tsaye kanta suna ta siyen fauda jagira da sutura basa gajiyawa , data wuce ku majalisa saita bar muku ƙamshinta , daga nan sai kace saika aurota , kaje kayita ɓarin kuɗi ka samota dakel itama ka kawota gidanka , kamar ta farkon itama haka zata bige saboda rashin kula kafin ka ankara ka tara mata kuma duk ka kasa riƙesu , babu sauran wurin dan haka saika fara harin na waje. Tunda su sun iya shafa fouda,

Bayan duk “yan shafe²n da sukeyi da ƙwalisar suna ɗaukar ido duk a aljihunanku suke tatsar kuɗaɗen , baka raya gida ba amma ka raya waje , baka siyawa matanka kayan shafa da sutura ba ka siyawa matan bariki wanda bakai kaɗai ne kake morarta ba , wasu kuma matan laifin nasu ne , a siyo a kawo musu amma basa dai gyarawar , matsalolin dai daban² ne , wasu rashin kula da mazajen nasu ta hanyar gagara fita haƙƙinsu da kuma rashin iya kula dasu a makwancin , ɓangaren sabta rashin iya kalami mai laushi da kuma rashin girmama miji kesa suna fita daga zukatan mazajensu , mtswww nima dai gani nan…. Fita dai haƙƙin iyali kawai shine mafita.

 Ɗaure fuska yayi ya fito da fuskar rashin mutunci , baima Yusura magana ba ya wuce tabi bayanshi tana mishi sannu da zuwa , bai tsaya ba bai kuma ansa ba itama bata daina binshi ba , motarta ta koma ta ɗauko wayarta da wata "yar ƙaramar food flarks wai tayo mishi danbun nama....

  Da Abbakar suka gaisa shima ba magana sukayi ba hannu sukayi kawai ya wuce , Abbakar shima bayanshi yabi kamar dai yadda Yusra kebin bayan shi , haka yaita gaisawa da mutane sune rufa mishi baya , duk taron mazan nan Yusra ce kaɗai mace da shiga irinta kafirawan da basa zuwa coci , har wurin da Dikko yake zama , daga nan yace kowa yaje kenan zai gana da Yusra , bayan sun fita ne ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa ya gda ? Lafiya qalau ranka ya daɗe ta faɗa tana miƙa mishi kular data zubo mishi danbun , ansa yayi a mutunce tare da kallonta kamar na minti ɗaya , sauke kanta tayi ƙasa tanajin kunyarshi , ɗan tauna cingom yayi sannan yace zauna yayi maganar yana harɗe ƙafa ɗaya saman ɗaya.

 Bata zauna saman kujera ba ta zauna ƙasa dan bashi girma , ta fahimci shi mutum ne mai san a girmamashi , su masu kuɗi duk ƙanƙantarsu suna so a basu girma na musamman saboda kuɗi , kuɗin ne kesa musu girman kai , izzar kuɗi kesa suke ganinsu su wasu manyan shegu ne na daban , tou bare Dikko daya raina mutane , gashi da rainin hankali dan idan ya raina maka ƙura babu daɗi , bare su dama Mom insu bata nuna musu sanin darajar mutane ba wanda yin haka ba kyau ba , kawai dai iskanci da rashin kunya a cikin jininsu take.

 Buɗe kular yayi tare da cewa ya akayi ne ? Ya maida ya rufe , ba komai ranka ya daɗe kawai dai naji anyi maganar dambun nama ne shekaran jiya da kuna fira sai nace bara inzo maka dashi , ba tare daya sake kallonta ba yace da kyau , bayan wani lokaci yaci gaba da cewa zaki iya tafiya , ba haka taso ba , dole ta tashi ganin shima ya miƙe ya fice , kallon kular tayi sannan tabi bayanshi da kallo tuni ya fice , a waje ta sameshi yana magana da mutane , saida safe tayi musu ta wuce , su Abbakar suka cinye dambun nama , shi kuma mota ya koma yana tunanin girman rashin kunya da raini irin wanda Sultana tayi mishi har 12 tayi , lokacin nayi ya buɗe wayarshi ya fara ansa kira daga mutane daban² , waya biyu kawai ya ansa duk da tarin yawan kiraye²n dake shigowa ya leƙa yanar gizo , a whatsapp saƙo biyu kawai yayi reply , ɗaya na ɗiyar ƙanwar Dady , data turo mishi fatan alkairi da addu'ar samu nasara a rayuwarshi , ya tura mata ngode. Saina wani abokinshi daya ya samu ƙaruwa , yace Allah ya raya , saƙon Yusra kuwa kasa kalla yayi , yana ƙorarin gogewa text in Sultana ya shigo a ɗayar wayarshi.

  Dubawa yayi , bayan ya gama karantawa ya kirata , An mata ki kiyayi ɓacin raina tara ki nakeyi karki bari in riƙeki , magana tayi cikin kuka , yanzu me zan miki ne ? Magana ta sakeyi , to wai me zan miki a gidan ne ? Bayan tayi magana , yace da Allah bazan dawo ba , wallahi bazan zo ba karki ɗaukeni ƙaramin yaro mana , ba yanzu kika gama zagina ba ? Ey bazan dawon ba sai 3 na dare , yana faɗin haka ya ajiye waya.

Yauma bai dawo gida ba sai 3 na dare , kuma idona biyu , inajin lokacin daya shigo ya kwantar da Papi ya kashe fitila ya fita , yana fita na kunna hasken , saida na tabbatar ya isa ya shiga wanka na nufi ɗakinshi , wayarshi na ɗauka nabi jerin kira babu kiran mace ko ɗaya kuma shima bai kira ba , danshi dama ba ma'aboci waya bane ba , inbox na koma ban samu ba dan haka na tafi whatsapp na fara dubawa , har cht in da bai buɗe ba saida na buɗe , 

Wayata na ciro daga jikina na fara ibar numbobi , bayan na gama naci gaba bin cht ina dubawa , wata irin zufa ta ketomin ganin hoton mace tsirara aihuwar uwarta a wayar Dikko , kyarma jikina ya fara , da sauri na fara ƙoƙarin turawa a wayata , jikina yana kyarma , bansan lokacin daya fito ba kuma har yanzu jikina bai daina kyarma ba , saida na gama na ajiye wayar , zan fita na ganshi jikin ƙofa tsaye ya rumgume hannayeshi yana kallona.

 Baimin magana ba ya taro hannunshi in bashi wayata , ba gardama na miƙa mishi , goge videon yayi ya maidomin wayar tare da bani hanya ya nunamin da hannunshi in fice , ƙin fita nayi ina kallonshi , ya akayi ne ? Ya tambaye ni , cikin kuka nace kadai ji kunya , da yanayin ko a jikinshi yace you sai me ? Ni banji kunya ba kece dai kikaji kunya da kika kasa ɗaukemin idona akan su , yayi maganar yana nunani da ɗan yatsa , to kinga ke kin ɓoye naki , ga na wata nan a wayata , kyauta ta bani ko sisi ban biya ba duk saboda inyi farin ciki , kuma banyi "yar murya ba cewa a taimaka min na gani , bina takeyi na taimaketa na bata abinda ke nake haɗaki da Allah in baki bakya so , to ita ni take haɗawa da Allah in bata ya ƙarasa maganar yana riƙe ƙugunshi yana ci gaba da cewa shin na bata ne ko kuwa kina so ? Tirrrr na faɗa tare da fashewa da kuka , hanya ya sake bani a karo na biyu yana nunamin da hannunshi cewa ai baki fara kuka ba sai amarya tazo tunda ke daƙiƙiya ce , zoki fitar min daga ɗaki.

 Fita nayi ban mishi magana ba na nufi ɗakina ina kuka , ɗan gajeren tsoki yayi bayan fitar Sultana sannan yace kyaji dashi , kashe haske yayi yai kwanciyarshi , tunda ya kwanta zuciyarshi ke cewa ya kira Sultana kartaje taita kuka , gyara kwanciyarshi yayi a bayyane yace da Allah ƙyaleta tunda bata da wayau.


 Bayan sati 2.

  Har yanzu banje makaranta ba , Dikko yayi faɗa harya gaji ya ƙyaleni , dan yanzu ko zai kasheni bana magana , bana tura mishi saƙo , idan dai yacemin inyi mishi kaza , zanje inyi ne , amma bana masa magana kuma bana masa dariya , idan ina palo ya shigo kawai zan tashi ne , ko ina naje idan ya biyoni zan bar mishi wurin idan yayi magana ba amsa saidai in aikata kawai a aikace. Na zamar mishi kurma a magana.

 Ita kuma Inna naje wurinta kuma na faɗa mata Dikko zai ƙara aure , tace ni na jiyo kuma damuwar nice wannan bai shafeta ba , a ranar gidan na yini dani da Papi sai 9:37pm na koma gida , yace ina wuta ya sakani ina naje nayi wannan zaman ? Yafa gaji da iskanci na in ajiye mishi ɗanshi in koma daga inda na fito , keda ke gidanki idan kinji shi tou naji abinda yace , cike da masifa yazo gabana ya ɗallarmin bakina da yatsunshi , da sauri na zabura tare da rufe idona saboda azabar ɗallin da naji a bakina, bakyaji ina miki magana ne ? Ban kalleshi ba kuma banyi magana ba , shigowar Papi ɗakin ne yasashi fita yana magana ƙasa² wai zai dawo dana rainashi yanamin magana nake mishi shiru.

Har safe bai dawo ɗakina ba , ni kuma yau na shirya dan zuwa makaranta........

JAMILA MUSA…
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ BRILLIANT WRITERS ASSO ????
-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-

      *KWARATA RETURN...*
 _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

Rubutawa…
JAMILA MUSA…

  *SAI NA AURI D ' K*

ASMA’U ZAYYAN {{ Asmeenat Xeyyan }}

???? —— 2

  Palon ƙasa cike yake da duk wani ma'aikaci dake gidan mace ko namiji gaba ɗayansu hallare suke zaune a ƙasa amma shi mai gidan baya wurin. Duk yadda akayi zaibar ƙasar ne , duk lokacin da akayi irin wannan zaman zaiyi tafiya ne , idan zaije Abuja ko ina ne ba'a haɗuwa sai zai tafi yabar nigeria. Ina ganin haka banma yadda na sauko ba na nufi ɗakinshi.

Da sallama na shiga ya amsa yana gyara ma Papi riga , kusa dashi naje na tsaya ba tare da na sake magana ba , shima baimin magana ba yaci gaba da abinda yakeyi , bayan ya gama yace ma Papi yaje ya jirashi wurin Ashiru yana zuwa , saida ya taɓoni yana murmushi yace kayyalni nayi cau….? Murmushi nayi nima tare da cewa kayi kyau , na ƙarasa maganar ina kallon Dikko dake ta wani haɗe rai , Papi yana fita na ƙara matsawa kusa dashi nace ina kuma zakaje ne ? Rai a riƙe kuma bai kalleni ba yace inda kika aikeni…..

 A ɗan tsorace na taɓashi da hannuna na dama ina kallon fuskarshi , da yanayin tsoro nace yanzu kuma meya faru kake fushi ? Ba komai ya faɗa a taƙaice yana matsawa daga kusa dani , ƙara matsawa nayi inda ya matsa jikin madubi yana tattara wasu takaddu , baimin magana ba saida ya ajiye makullin ɗaki a gabana , girgiza kai nayi alamar a , a , to minene ? Cikin rawar murya nace zanji babu daɗi ne idan ka tafi , da gaske ? Ey , kin tabbata ? Na tabbatar da haka , ai bazan daɗe ba ya ƙarasa maganar yana ɗaukar takkadun ya matsa gaban gado ya ajiye sannan ya nufi wurin weldrop , ƙara binshi nayi na fara kuka , har yanzu yaƙi ya kalleni , amma a tausashe yace kinsan ni bana san wannan kuka²n ko ? Yayi maganar yana miƙomin hannunshi. Riƙe hannun nashi nayi shi kuma ya riƙe tare da shigar dani jikinshi. A kasalance yace yi shiru An matana.

 Cikin kuka nace to me yasa zaka tafi ne ? Yi haƙuri ai zan dawo in Allah ya yadda , kwantar da kaina nayi saman ƙirjinshi naci gaba da kuka , bai sake magana ba kuma bai ɗagani daga jikinshi ba , yadai cire hannunshi daga kaina ne tun lokacin daya shigo dani jikinshi. Kenan bai rumgumeta ba , saidai a ranshi yaji babu daɗi tanayin kuka , a zahirance kuwa ya nuna ko oho da yanayin ma idan tai mishi ɗanyen kai zai zaneta ba abinda ya dameshi , Allah ya sani yana san An mata kuma yana tausayinta amma ta rainashi iya raini dan ko gaban waye idan ta tashi mishi rashin kunya sai taje inda take so hankalinta zai kwanta , kuma ita rayuwa ba'ayinta haka wannan dalilin yasa shi yaja mata layi ya kuma tsare gida yanzu yasan tsoronshi ya fara hawa zuciyarta. Gashi yanzun ma taji tsoronshi shi yasa ta firgita dashi take mishi magana a tsorace , naso na tambayeshi abinda yasa zaiyi tafi bai faɗamin ba , kuma ince mishi kenan da banga ma'aikata a palo ba saidai inji labari baya nan , tou ya wani haɗe rai cikin rashin mutunci , sauka nayi daga jikinshi bayan nasha kukana harna gode Allah duk na ɓata mishi rigar jikinshi da hawaye , ina sauka ya cire kayan ya canja wasu.

  Bayan ya gama ya ɗauki abinda zai ɗauka da wayoyinshi danshi bayayin tafiya da kayan sakawa shi kaɗai ɗinshi yake tafiya saidai ɗan abinda ba'a rasa ba , da ya tashi fita yayi bankwana dani kamar yadda ya saba , ya sumbaceni tare da shafa gefen fuskanta , ya riƙe haɓata yana ɗagota dan mu kalli juna , na kalli cikin idonshi yayi murmushi mai tattare da tsantsar so sannan ya ƙara shafa fuskata ya kama kumatuna da yatsu biyu kamar anayi ma yaro wasa yanamin wani irin kallo , ajiyar zuciya nayi tare da sauke idona wani wuri daban na daina kallonshi , wasa yayi da tafin hannunshi a gefen fuskata { kumatuna }sannan ya fita daga ɗakin ba tare da yayi magana ba. Yana fita na fashe da wani irin kuka mai kama zuciya , yana jin kukan Sultana har a ranshi amma ya daskare yai tafiyarshi.......

 Wani irin ihu nayi tare da buga wayata da bango ta watse lokacin da naga kuɗi sun shigo a cikin asusun bankina , kuɗin banza kuɗin wofi ko an faɗa mishi kuɗi nake so ne wai....? Nayi kuka׳ , bana san Dikko yanamin nisa nafi so ya zauna gida muyi ta faɗa.... Duk taron mutanen dake palo suka ɗinguma dan rakiya bayan Dikko ya bulalesu da manyan kuɗi , su Ashiru kaf dasu aka tafi hada Papi.

  Sai azahar nabar ɗakin Dikko bayan nayi sallah kuma banje makarantar ba , a ɗakina na haɗa wayata data fashe na kira Mai gilashi , babu wani ɓayata lokaci ta ɗauka , bayan gaisuwa nace ko kirana bakya iyayi kinga kwana biyu bana zuwa makaranta , ai kyace ita wannan lafiya....? Daga haka nayi shiru danjin amsar da zata bani , wata irin dariya nayi sosai dan wata irin ƙatotuwar batsa data sako , jin ina dariya yasa tace bana san iskanci fa sai anjima , ah jira Mai gilashi zaki zo gidana ? Keni fa na faɗa miki bana iya zuwa gidanki , babu munafurci tsakanin ni da kuma ke , D ' K ka haɗa hanya dashi ya maka rashin mutunci ina kuma kazo gidanshi....? Gaskiya ni bana iya zuwa gidan D ' K , baya nan fa , kizo dan Allah , kashe waya Mai gilashi tayi tare da ƙurawa wuri ɗaya ido.....

   A bayyane tace gidan D ' K , hmmm....

 Kyakkyawan murmushi ta hasko yayin da aka gurfanar da ita a gabanshi , da wannan kallon rainin wayan nashi da yake ma mutane ya kalli Mai gilashi , cike da duniyanci ya ke wani murza bakinshi yana cin cingom cikin salonshi mai ɗaukar hankali , kuma shi bawai dan ya burge wani ko wata ba yakeyi , a , a ra'ayinshi ne yake ci , sai yakeyin abun cikin yanayi mai motsa ma mata hankali , dan ita mace abu ƙalilan yake ɗaukar mata hankali tare da tayar mata dashi , yana da kyakkyawan baki ne , ga gemun daya ajiye kamu ɗaya. Kuma gemun yayi matuƙar martaba mishi kyakkyawar fuskarshi gashin gemun ɗan gazar² kuma gazar ɗin mai ladabi da sheƙi dan ko bai gyarashi ba baya wani duƙunƙune wa ɗin nan yayi kalar ƙazanta ko rashi kyau. Yana da kyakkyawan gashin gemu mai burgewa , sai kuma kyau ya haɗu da gyara , kuma shi gemun nan fa ba dan wata ya ajiye ba. Shima kwalliya yayi ma matarshi An mata dan ya riƙa burgeta tunda yaga gemun yana burgeta dan tana yawanyin wasa dashi idan suna tare. Shi yasa yabar mata dan tayi farin ciki. Ita kuma taunar cingom inshi baiwai taunar hauka yake mishi ba , baya buɗe bakin motsawa yakeyi cikin natsuwa sai salon ya bada wani irin sirrintaccen sirri mai ɗaukar hankalin mace da sa mace taji ya burgeta kuma ta kasa daina kallonshi , kawai dai zataji sha'awar yadda yakeyi , cikin sakata irin tasu ta rigimamin yara yace kece kike san gani na ido² ko ? Ya ƙarasa maganar yana murmushin mugunta , yadda yayi maganar ne yasa ya bata sha'awa dan haka itama mai gilashi tayi murmushi tare da sauke kanta ƙasa tayi shiru.

Murmushi Dikko ya sakeyi a karo na biyu ya ɗauka robar ruwan dake gefenshi yasha , turo leɓonshi na ƙasa yayi kaɗan tare da riƙe shi da leɓonshi na sama yana mata wani irin ƙazantacen kallo , saida taji cikinta ya juya lokaci guda jikinta ya nuna taji tsoro. Ɗan karkace kanshi yayi shima kaɗan da alamar kowa ya fita , da sauri ta fara juye² tabi mutane da kallo har suka gama fita , ya akayi ne...? Ya tambayi Mai gilashi , cikin rawar murya tace yi haƙuri ranka ya daɗe , a , a , kuka ta farayi tana ci gaba da cewa kayi haƙuri dan girman Allah , gyara zamanshi yayi cike da mugunta yana cewa har kin gama gani na ne ? Ya ƙarasa maganar yana mata kallon ɗage , shiru tayi shi kuma yace tou kin fasa ɗaukar hoton dani ne...? Tuba nake ranka ya daɗe , zo nan ? Yayi maganar yana nunawa da hannunshi ta matso gabanshi , matsawa Sa'adatu tayi tana ci gaba da kuka , tashshi { yaji } ya ɗauko cikin wata "yar ƙaramar roba ya watsa mata a ido.... 

 A firgice Mai gilashi ta goge zubar data tsatstsafo mata a fuska ta goge idonta dake ɗigar da zufar hawayen azaba dan tuno azabar da Dikko ya gana mata kamar yanzu ne yake zuba mata yajin , wanda ba kowa ne yaja mata ba sai Sharifa , kuma itace wacce Dikko yayi ma liƙi , kuma Sharifa karuwa ce ta gaban mota amma musulmin karuwanci takeyi , murmushi ɓacin rai Mai gilashi tayi tare da ɗaukar wayarta ta fara kiran Sultana....

Ina kallon kiranta yana shigowa yana fita nima nayi fushi. Murmushi Mai gilashi tayi tare da turama Sultana text , Allah ya huci zuciyarki uwar gidan D ‘ K kuma Amarya , daga kanki idan dai kuɗin da D ‘ K zai biya da sunan sadaki ne dan ya auri wata mace , tou ina miki albishir daya ƙare. Kina ciki muna waje , a gida kika san Dikko a waje mune zamu baki labarin ko waye D ‘ K , kizo makaranta idan Allah ya kaimu gobe akwai labari.

 Maƙiyi zai iya mutuwa amma har abadan duniya gaba baza'a daina ba , kamar yadda na faɗa muku karuwanci shine abinda mai gilashi ta zaɓa , to shine cinikinta kuma karuwanci shine sana'arta , Sharifa ƙawar mai gilashi ce ta hannun dama kuma ƙawancen an haɗashi a bariki ne. Sharifa tana alfahari da Dikko da kuma gwamna , ko taɓota mutum yayi sai ta fara burga a waya Yaya D ' K kaza² alhalin kuma ko number wayar Dikko bata dashi a wancan lokacin. Gwamna Yayan Mom inta ne , munyi waya da Yaya D ' K yana saudiyya ko yanzu yabar Madina ya tafi Makka , yaje London ko yana America kullum shine ƙaryar Sharifa idan aka zauna a mutane. Kiran sunan Dikko da takeyi yasa ake santa dan su a ganinsu zata jasu suje wurin Dikko yayi danbe dasu ya basu manyan kuɗaɗe , dan da harkar mata Dikko ya nufa da tunin duniya ya lalace dan zina ƙarshen rashin kunya ce. Kuma ba ƙaramin ɓarar da mutunci daraja da kuma martaɓar ɗan adam take ba , sun ɗauka Dikkon ɗan tsakiyar fili ne ashe ɗan bayan fage ne basu sani ba , suna mishi kallo go ashe back ne basu sani ba , yadda suka fassarashi kuma suka kalleshi haka yake amma iskanci shi da duniyanci da duk wata tasharshi shidai An matarshi kawai yake mawa , kafin ita Sa'adatu tasan Dikko sunanshi ta faraji da rashin kunyarshi.

Sharifa tayi alƙawari wa su Sa'adatu idan Dikko ya dawo nigeria zasuje wurinshi , ita kuma Sharifa ganin Sa'adatu tana san ƙureta yasa ta fara neman faɗa da ita , amma Sa'adatu ta liƙe taƙi zuciya tana dai manne bayan kuma ita Sa'adatun tayi bincike ance mata Dikko yana nan baije ko ina ba , ana haka ne akayi rasuwa can ahalin Maman su Dady , ƙanwar Kakar Dikko ta wurin uwa data aifi Dady , dake ba'a abu dan Allah ƙwai da kwarkwata ƙannen Dady da "ya "yansu suka je ranar addu'ar 3 , anje kara wa Dady , shi kuma Dikko dama baya shiga hurumin kowa tunda ko family meeting da sukeyi shi baya zuwa ba abinda ya dameshi da sabgar kowa daga doki sai mota sai kuma bugun zuciyarshi An mata da tazo daga baya ta hana ma zuciyarshi hutawa da soyayyar ta , a wurin ta'aziyar ne Sharifa ta ratso dubun mutane ta isa wurin Dikko tace mishi dan Allah ya tsaya suyi solfie , idan sunce shi ɗan uwansu ne sai ace ƙarya sukeyi , yadda tayi sakin layin ne sai abun yasashi yayi murmushi Sharifa ta ɗauki solfie kenan yana cikin yanayin farin ciki , wannan hoto fa shine ta maƙale mishi take ta yaɗawa a kafafen sadarwa na yanar gizo. Face buk , Instagram , whatsapp d p inta shine kullum , wannan hoto shine status inta ba dare ba rana , da ƙawaye suka fara mata gori mai hoto ɗaya , sai ta shiga familynsu ta samo hotunan Dikko irin wanda "yan uwanshi ke sassakawa masu numbobinsu suke samu , nan fa tazo taci gaba da kafawa , kuma itace tasa Mom inta ta sama mata number Dikko a wurin Aunty Bilki abiyar zaman Momy kenan , Maman Sharifa kuwa ta faɗa ma Aunty Bilki tana san Sharifa ta auri Dikko bata ɓoye mata komai ba saboda su biyun nan aminan juna ne kuma aminci ake na ƙuryar ɗaki. Gashi kuma Momy bata shiri dasu saboda ta rainasu rainin har na wuce misali , dake taga kishiyarta zata shiga damuwa yasa ta miƙe itama sai anyi auren nan dan Momy ta ƙuntata tunda tasan bata sansu , tana so ayi auren kodan Momy ta gune , da kuma buƙatar ta na daban tunda ba Al ' Ameen , tana so Sharifa ta shigo. Ta nan ne ma kaɗai zata rufe littafin rayuwar Dikko , tayi waje da Momy ta fasa gidan dan Dikko shine ƙaryar Momy da ma duk wanda uwarshi bata gdan.

Itace ta miƙe da gaske tasa Dady yasa Dikko ya auri Sharifa dan tasan Dikko baya tsallake maganarshi , su kuma maza basa gane makircin mata da irin "yar nehun nan , sai akayi ma Dady nehu haɗe da bariki shi kuma ya fahimci hakan abune mai kyau da kuma ƙara martabar zumincin su , shine fa Dady ya tura Dikko yaje wasan ya kuma ƙara da cewa ya riƙa zuwa zance akan lokaci dan su samu fahimtar juna , banda fushi ɗaure fuska kar yayi duka ya zama mai haƙuri da sakin rai idan yaje , Momy kuwa tace masa bata so , amma sai yace ta kwantar da hankali shi bazai riƙa zuwa zance ba , tace ita ba ma zancen ba auren nan ne gaba ɗaya bata sanshi kuma baya yinshi , dan jakanci fa shine ita kuma Sharifar take zuwa wurin Dikko , ko zai kai ƙarfe nawa bai tafi gida ba zata zauna dashi tana mishi fira , da lafazin su dai irin na "yan bariki har akayi mata liƙi , wanda kuma duk karatun Aunty Bilki ne dan itama sai jawo Dikko jikinta take danma shi Allah yasa mishi wani irin hali haka na kamar dai yanajin tsoron mutune , kuma baida sakin jiki dasu , kana iya zama dashi yau kuyi fira yafa sanka amma idan ya ganka gobe ya nuna shi baima taɓa saninka ba kwata² a rayuwa , kai ta mishi bayanin ka yace shifa bai wani gane ka ba , kuma zaiyi wahala ka bashi abu yaci ko yasha ko kuma ya saki baki kamar sakarai yaita maka surutu ko yawan murmushi , wallahi Allah akan Sultana kawai Dikko ya faracin abunda ya fito daga hannun mace a waje kuma daga kanta ya daina , shi kanshi ya natsu yayi nazari tunda yake bai taɓa ganin macen data bashi wahala kamar An mata ba , kuma shima babu macen da tasha wahalarshi a duniya sai An mata , yana santa soyayyar da tunda yake bai taɓa ma kowa irinta ba sai ita , akan An mata ya fara mafarkin mace , kuma itace farkon macen daya bi ya wuce , itace mace ta farko data mareshi ta zageshi taja mishi gemu yayi murmushi bayan ta gama , itace macen data kashe mishi dokin daya fi ƙauna wanda har yanzu idan ya tunoshi sai yaji babu daɗi saboda san da yake ma dokin , itace macen data maida rungumarshi ba,a bakin komai ba , yana san Sultana fiye da yadda tunanin mai tunani baya iya hasasowa amma bata kunya ko kaɗan haka kuma ta rainashi sai babban iskancin data koya yanzu na raba shinfiɗa dashi , ya ƙyaleta ya kuma zuba mata ido bawai dan baya san su kasance taren ba a , a saboda cikin da take dashi ya ƙyaleta dan idan ya riƙeta da fushi tou fa lallai za'ayi ɓarna. Yana addu'a ta sauka lafiya zataci ƙaniyarta idan ya riƙeta a ɗaki.....

Sa'adatu kuwa wani abokin barikinta ne ya haɗata da Yazeed , Yazeed shine ya kaita wurin Dikko bayan ya biye allonta shima { danbe }, daya faɗa mata ranar da zusu wurin Dikko shine take faɗa zatayi hoto da Dikko idan suka haɗu. Kuma tayi mishi shirin hana bacci , yau duk wasu musu ƙaryar suna tare da Dikko suma zasu je wurinshi kuma zatayo hoto dashi , Sharifa ce ta bawa Dikko labarin zuwan Sa'adatu wai akwai wata karuwa tana faɗa a gari zata zo tayi mishi fyaɗe , abun ya bashi dariya amma baiyi ba a gaban Sharifa saida ta tafi , yaso yaba Sultana labari amma daya koma gidan tai² mishi ɗanyar ƙwalwa , shi yana so ko abu ya faru dashi , ko ya gani , ko yaji yana so ya riƙa faɗa mata suyi farin ciki tare amma ita kwalwarta tana kallon ƙasa , ita kuwa mai gilashi tayi alƙawarin miƙewa tsaye da ƙarfinta da barikinta da tasharta sai ta rama abinda Sharifa tayi mata dan raba tarayyarta da Dikko kamar yadda ita Sharifa ta zuge wani mai san ita Sa'adatu ya fasa aurenta tou itama ta lashi bala'en hana aurenta da Dikko ko da kuwa hakan zai zamar mata silar barinta duniya , wannan kenan.

 Kamar wasu mayu haka suke ta yayam² suna cin shawarmar da Yazeed yasa aka basu , Jiddah ma data zo yanzu an bata nata kasafin itama ɗayar mayyar ta lashe. Bayan ta gama ci ne tace ma Yazeed wurinshi tazo fa , babu wani damuwa yace ina saurarenki yayi maganar yana bata umarni da hannunshi tayi magana , kasan dai komai yana buƙatar sirri ba , cikin matan ne wata tayi katsalandi cewa ba buƙatar sirri a wurin nan malama faɗi abinda ya kawoki basai kun wani tashi ba , ke bake a maganar nan dan haka tsamewa mutane baki , Jiddah ta faɗa. Idan naƙi kuma ? Sai jikinki yayi tsami , umarni karuwar ta bayar cewa jikin Jiddah ya tsamama yanzun nan. Dakatar dasu Yazeed yayi ta hanyar miƙewa yacewa Jiddah suje , a motar Jiddah sukayi masauki dukansu.

  A hankali ya turo ƙofar ɗakin kamar ɓaron tsakar dare a barikin sojoji , ƙiyyyyy ƙofar tayi ƙarar buɗeta a yayin daya fara tura ƙofar dan shiga cikin ɗakin. A tunanin shi tayi bacci amma da mamakinshi sai ya ganta zaune gefen katifa tana ta shafa wayarta mai tambarin apple a bayanta. Cike da ladabi ya takure daga bayan ƙyaure ya durƙusa cikin biyayya sannan ya matsa gaba kaɗan ya ajiye mata ledar daya shigo da ita da kuɗi cewa ranki ya daɗe gashi. Hankalinta yana saman wayarta tace masa nawa ne ? Cikin rawar jiki yace dubu biyar ne... ! Bakaji me nace maka ba ? Kiyi haƙuri dan girman Allah wallahi har rance na nema a daren nan ban samu ba , shiru tayi ta manta ma da yana cikin ɗakin taci gaba da sabgar gabanta a waya......

   Yazeed barka da dare , barka dai matar mai gida , kanta taji yayi mata wani irin gingime cikin izza da nuna ita wata shegiya ce tace , am Ya Yazeed meya haɗaka da Ya D ' K , shiru yayi na wani lokaci sannan hawaye ya gangaro mishi daga idonshi yace , hmmm dare ake bi a samu suna , inko ba'sha dare ba asha rana , idan kikayi duba mutum biyun nan basa sabgoginsu da rana ko safiya , daren nan dai shine suke bi su nema kuma sun biɗa sun samu , kiyi tunani duk ɓarowa sai dare yayi yake fita dan haura katangu , masu nema wurin ubangiji idan dare yayi su lokacin garinsu ya waye , zasu kasance ne a saman abinda sallah suna Allah ka yafe mana ka bamu׳ , shin ko kinsan dalilin yasa D ' K yake huɗɗonshi cikin dare ne.....?

  Kai kunnamin hasken can kaji , jikinshi yana ƙyarma ya tashi duk ya haɗa uwar zufa kamar manomin da ruwan damina ya ɗauke a lokacin da gero ya fara bininiy , duhu yabi ya lalubo makunnin fitila dan tunin duniya ta ajiye wayarta haka ne yaba duhu damar gauraye kaf ilahirin girman ɗakin , a kiɗime ya kalli Sa'adatu bayan haske yazo , cike da tasha tasu irin ta "yan tasha ta buɗe jikinta gaba ɗaya , idonta na dama ta kashe mishi cikin salon jan hankali , ha... Ya sauke ajiyar zuciya. Wasu wurare ta nuna masa a jikinta tare da bashi damar zuwa kusa da ita , tafiya yayi kusa da ita ya durƙusa ƙasa ƙiƙi² ya hunce ita kuma ta bashi damar tattaɓa jikinta itama tana tayashi da shashshafa mishi wasu mahimman wurare a jikinshi dan tabbatar mishi da martar cewa shima namiji ne. Kaɗan ta ɗan lulashi saman network saida ya tafi ya kusa cinma nasara tace dubu biyar ya ƙare , dan haka ta saukeshi daga saman katifarta ta mayar da kayanta sai ya kawo cikon dubu biyar zai shiga gabatar da wasan danbe...... Wani irin gurnani yayi tare sake nufa inda Sa'adatu take yana wani irin huci kamar an jiƙa mahaukaci a lokacin sanyi , dakatar dashi tayi ta hanyar cewa idan ka haumin katifa saina yaga mutuncin ka , ni nafika ƙaryar rashin kunya iskanci tasha da kuma lalacewa , tattara gashin kanta tayi cewa bani kazar inci...... Ta ƙarasa maganar tana ɗaga mishi gira. Kamar wani gele haka ya miƙo mata , yagar kazar ta farayi saida ta cika bakinta da ita sannan tace tou yi sauri kaje ka samo cikon kuɗin ka kawo ni kuma na ɗoraka a saman lambar girma tayi maganar tana murmushi tare dakai hannunta ta nuna mishi tsakiyar filin wasan danbe...... Bashi da yadda zaiyi dole ya maida kayanshi ya fita daga ɗakin dan yasan tashar Ade mai gilashi ta girmin tunaninshi.

 Gyara zama Jiddah tayi ta kalli Yazeed sosai sannan ta tambayeshi kamar yadda ya tambayeta itama tace me kuwa yasa yake huɗɗonshi cikin dare....... ? Yazeed yace shine abinda nake so na sani tun farko kenan dan duk yadda akayi nasarar rayuwarshi a cikin dare take , kinga D ' K baya waya da rana saida daddare idan kika cire wasu ƙalilin mutane wanda su wayarsu ma daban ya fitar musu , uwa uba matarshi sai Ashiru danni tunda Ashiru ya wulaƙanta ni ya korani daga company ya kawo Abbakar bana samun layin da nake kiranshi dashi da rana ko safe duk dai lokacin dana so nayi magana dashi. Jiddah tace nima yanzu ko na kira saima acemin number ma babu ita a duniya saida na sameshi a layin da kowa yake samunshi , idan kuma na saka number a wani waya shima dai baya tafiya wai meya ɗauki mutane ne.... ? Jiddah tace koma meya ɗaukemu zamuji mu kuma gani idan na koma gidanshi.

  Wani irin kallon raini Yazeed yayi mata mai nuni da tama samu warwarewar tunani , ita kuma tana ci gaba da cewa manta da wannan damuwar kaji abinda ya kawoni wurinka , inajin ki ya faɗa bai sake kallonta ba , hoton Sharifa ta nuna mishi tana ce masa kasanta ne ? Kallon hoton yayi sosai sannan ya miƙawa Jiddah yace ya akayi ne ? Yaya D ' K yayi mata liƙi kuma aurenta zaiyi , kai tsaye Yazeed yace wallahi D ' K bazai aureta ba , ke kina wasa da Dikko ko ? Tou D ' K mashaune shi ɓadda musulmi , shi kanshi tsoron kanshi yakeyi kuma bai yadda da kanshi ba , ita wannan yarinya da kike magana yanzu haka tana wurinshi Abuja taje mishi rakiya zaiyi tafiya. Jiddah tace zai aureta , Yazeed yace bazai aureta ba , haka sukayi ta maimaitawa kusan sau goma , shi Yazeed yace Dikko bazai auri Sharifa ba , Jiddah tace zai aureta , daga ƙarshe dai suka rabu a haka kowa yana cewa zaka gani , shima yace mata zaki gani.....

  A wahalce ta ajiye kwalbar cikin maye tace wallahi saina auri D ' K , wata irin dariya Amisty tayi tare da cewa Dikkon ne zai auri "yar shaye² ? Cikin maye tayi magana cewa tsaya kisha kallo...... Dariya Amisty ta sakeyi tare da cewa me kuwa zan kalla saidai inga yadda zakici ubaki , murya a lalace da maye Hafsa ta nuna Amisty da ɗan yatsa tana rufe ido da yanayin buguwa murmushi ɗauke a fuskarta tace kema kina layin "yan hassada ko......? Tayi dariya. Tou dama malam ya faɗamin "yan hassada zasu fito ɗaya bayan ɗaya ngode ma Malam daya nunamin ke Kaka , ashe haka kike hassadata ban sani ba ? Gaki nan Malam ya zaƙulomin , buɗe tafin hannunta tayi tare da nuna ma Amisty tace me kika gani ne ? Wata irin ƙatuwar ƙuna ce a tafin hannunta , bayan ta tabbatar Amisty ta kalla ta naɗe hannun da tsumma kamar yadda yake farko cewa malam yace wannan ƙunar sai a gidan D ' K zai warke , ta ƙarasa maganar tana dariya irin ta mashaya......

  Da massara ya isa Abuja shi yasa tunda ya shiga ciki bai fito ba yana kwance a gado jikinshi har ƙyarma yakeyi , saida yayi sallah isha'e yasha magani ya koma bargo. Ba tare daya juya bayanshi ba yace Papi tashi ka kawomin wayata ana kirana , sauka yayi ya ɗauko wayar ya kawo mishi , samin a kunne na yayi maganar yana kallon Papi , yadda yaga anayi idan za'a ɗauki wayar yayi tare da ɗorawa a saman kunnen Dikko shi kuma ya fara magana , bayan gaisuwa yace wallahi banajin daɗi ne Momy , magana tayi sannan yace a , a , shiru ya sakeyi bayan wani lokaci yace gaskiya ban sani ba. Ey Papi Momy zatayi magana dakai , cire wayar yayi daga wurin Dikko ya kara a kunenshi yana magana da tsantsamar muryarshi , kusa da Dikko ya ajiye wayar bayan ya gama ya koma ya kwanta gabanshi , yana mishi sannu , cikin yanayin damuwa yace Papi kaga Momy bata kirani ba ko ? Ta kiyaka Yaya , a , a Momyn goruba , ɗaukar wayar yayi yana cewa bari a kirawota Yaya , 

Tsareshi da ido Dikko yayi , saida ya yagaji da shirmenshi ya ajiye wayar ya fara bacci tunda bai iya kira ba , saida ya tabbatar Papi yayi bacci yayi mishi addu’a tare da gyara mishi kwanciyarshi shi kuma ya fara kiran Sultana , amma tsabar iskanci taƙi ta ɗauki wayar , ya kira harya gaji ya haƙura wanda bai ɗauki waya ba taya zaiyi lokacin duba wani saƙon banza can….

 Tunani daban² a ranshi na sabon iskancin da An mata ta koyo , amma yayi alƙawari bazai sake kiranta ba taje can ta ƙari rashin wayanta. Yau sai 12:23am ya cire wayarshi daga jirgi , yana buɗewa kiran Yusra yana shigowa da bazai ɗauka ba amma sai yaji tausayinta har wane tsawon lokaci ta ɗauka tana ta kiranshi sai yanzu ta samu kuma bata gaji ta daina kiranshi ba haka batayi bacci ba. Yasan dan dai kawai tayi mishi sannu da hanya ne wacce ma baa matarshi ba ta damu dashi da san sanin halin da yake ciki , shidai bai faɗa mata ba amma yasan kila taje g r a ance mata yayi tafiya ne , ɗauka yayi tare da kara wayar a kunnenshi yayi sallama.

Ajiyar zuciya Yusra ta sauke cikin kissa sannan ta amsa sallammar da mairainiyar murya , ya gda ? Ya tambayeta , bata ansashi ba taci gaba da watso kalamai na matan waje cikin rashin kunya tana kambamashi da zugashi tare da turashi wata madakatar da bai isa zuwa ba , murmushi yayi kaɗan kuma mara sauti ya kalli Papi dake bacci ya riƙe mishi wuya da hannu ɗaya , shiru yayi yaƙi magana ita kuma taci gaba tunda ai tasan yana jinta , duk kiran dake shigowa bai ɗauka ba kuma bai tsinke kiran Yusra ba haka kuma baiyi magana ba yana dai kallon Papi , itace ta gaji ta sauka a layi.

 Kiran Hafsa shima ya ansa saidai ita bata doguwar tafiya dan bata da irin kalaman da yake so , duk da yanajin haushin Jiddah yana ɗaukar kiranta , itama Mardiyya tayi nata kuma duk sun hura mishi kanshi yanajin yakai wani baban shege , Sharifa kuwa ai suna tare amma ba'a ɗaki ɗaya ba. Yau ko namiji ɗaya baiyi magana dashi a waya ba saidai a cht , tunda ya buɗa wani saƙo ya haɗe leɓunanshi tare da riƙe na ƙasan ta ciki da haƙori ya kura ma hoton wata kyakkyawar yarinya ido , ɗayar wayarshi ya ɗauka ya kawo hoton Sultana a bayyane yace akwai tazara har yanzu..... Ajiye waccan wayar yayi yaci gaba da kallon hotunan Sultana yana murmushi wani kuma yayi dariya yace An mata rigima Allah ya saukeki lafiya jarumata.......

A dajin data gama tsibbunta a wurin ta kira Dikko tayi magana dashi kamar yadda mushiriki ya faɗa cewa idan ta gama ta kirashi kuma zai ɗauka idan harya ɗauka a lokacin ruwa da iska baya hana Dikko ya aureta sai sunyi aure ,

  Ɗan madaidaicin gidane a nan cikin anguwar kwaɗo duk yara²n mata ne suka taru suna ta gulmar mazajensu.......... Har 12:39am gidan cike yake wai ana fira , wasu mazajen su matafiya ne basa nan , wasu kuma suna da abokan zama mazansu suna gidan abokiyar zamansu , ita kuma mamallakiyar gidan mijinta yana can majalisa.

 Jakar mace da ita , duk sauran mata sun gyaro gidansu sun gogo ɗakunansu sun saka turaren wuta sunsha wankansu sun taho gidan ballagazar mace fira , ita kuma daƙiƙiyar ta kora mijinta waje ƙawaye sunfi miji dai. Bursunai² da ita sai wari takeyi ba wanka bare wanke ido , wacce batayi haka ba wace fikra gareta na sanin rayuwar duniya....? Tou hausawa dai sunce wanda maciji ya sara idan yaga igiya guduwa yakeyi , masu iya magana kuwa cewa sukayi wanda aka mara yayi hankali yafi wanda aka haifa dashi. Ɗaki daya ne tsal a gidan , nan kicin yake bedroom da toilet , palon nan da kujerunta sunyi daƙa² kalar tashin zuciya , kwanukan da sukaci abinci da wanda aka zuzzubar duk ba'a ɗauke ba , tunda sun ɓata palon kuma wai sai suka koma ƙuryar ɗaki ana fira ,

1 saura mijinta ya shigo gida , a palo ya ajiye ledar biredi daya shigo da ita da ɗan naman daya riƙo musu ya fara tattara kwanukan dake palon , jin buruntu a palo yasa ita mai gidan tace Hadiza leƙa kiga waye , ita Hadiza data tashi fita sai ta cire hijabi ta gyara ɗaurin kallabi tayi palo.....

  A palo , da sauri ta isa wurin mijin Halimatu tana riƙe tsintsiyar dake hannunshi cike da makirci irin namu na mata tace haba "yar laɓai ai wannan aikin ba naka bane ba , a gafarcemu tayi maganar tana murmushi mai tattare da ɗaukar hankali , shima riƙe tsintsinyar yayi yana cewa ta bari kawai zai share ya faɗa yana murmushi , suma na bedroom sunaji amma Halima bata fito ba sai kuma Zainab ta fito aka baro Fadila da Halimatu matar gidan kenan a bedroom. Ita kuma Hadiza tana riƙe da tsintsiyar suna jayayya da mijin Halimatu akan bazai saki ba zai share...

Itama Zainab tana isowa ta riƙe tsintsiya haba ranka ya daɗe ina za'ayi wannan abun kunya ka rufa mana asiri mu share , daga cikin bedroom kuma Halimatu tayi dariya tana cema Fadila ai dake bashi da matsala shine zai share bazai basu ba , a palo kuma Hadiza sai cewa takeyi ya bada tsintsiya , ganin dai sun dameshi yasa ya haƙura ya bata tsintsiyar kuma idan sun gama shine ai rakasu gida ,.......

  Idan namiji bashi da matsala kece kike koya mishi ya zama mai matsala , idan namiji bai iya yawon majalisa ba kece kike koya mishi , Halimatu da mijinta auren soyayya sukayi , mijinta bashi da kuɗi amma yana da rufin asiri kasancewarshi ƙaramin ma'aikacin gwamnati , sauran matan nan dana lissafo su 3 , ɗayan su huɗu ne a wurin mijinta , bata yini gidanta kuma batacin abincin gidanta kuɗin cefanenta da komai nata take aikashi wa iyayenta tunda ta samu na mijin ballagar mace iyayenta suna buƙata tunda ta wadata saita wadatasu da kasonta na gidan miji. Kullum da ita ake majalisa amma idan mijinta yazo gidanta zata zauna ta kula dashi ta bashi duk irin kulawar da yake buƙata asha soyayya sai ya tafi taci gaba da zuwa kuma shi baisan tana wannan iskancin rashin zama gida ba.

 Ita kuma ɗaya mijinta driver ne , idan ya tafi sai yayi wata biyu bashi nan , itama a gidan jakar mace take ci tana sha tayi wanka da wanki itama kuɗin da mijinta yake bata idan zai tafi sai ta shiga adashe tunda an samu na mijin daƙiƙiyar mace , ɗayar kuma mijinta gadi yakeyi a asibiti shi dama baya bayar da wani kuɗi saida idan an samu albashi ya ɗan sissiyo abinda ya sawwaƙa daga ita har mijinta a gidan mijin wawiyar mace suke ci suke sha , itace Hadiza , Halimatu kuwa matar gida ba , mijinta yana aiki a C B N ubangidanshi ya cusashi da satifiket ƙaramin ma'aikaci ne amma dogon buri yasashi yakeyin digiri karatun asabar da lahadi , { part - time } ya kusa gamawa ubangidan nashi yake san ganin ya tashi daga ƙaramin ma'aikaci ya zama babba.

Sai 4 saura na sauka a abin sallah , kuma sai a lokacin naje inda wayata take , bayan na ɗauketa ne naga miss calls inshi 7 , data na buɗe nasan yana online , baya online ya daɗe ma da sauka amma ya turo min hotonshi shida Papi suna kwance a saman gado , wai suna gaisheni kuma in sa Allah a raina in daina fushi. Su basuda zuciya kamar yadda nake mishi gori suna gaisheni. Murmushi nayi tare dabin hoton da kallon , ko ina zaije da Papi ? Oho……! Bakuyi kyau ba shine abinda na tura mishi nima na sauka.

 Yau na samu damar zuwa makaranta , kuma Mai gilashi ta bani labarin Sharifa ta tsoratani sosai akanta ta firgitani , na gigice na tsorata , ta ƙara da cewa idan ina maido hankalina jikina tou in tashi daga wannan asararren baccin da nakeyi , ta nunamin hotunan Sharifa ita da Dikko wanda koni da nake aurenshi ban taɓayin irinsu ba , bawai riƙeta yakeyi ba ko taɓata ba dan shi baya da ɗabi'ar taɓe²n mata kawai dai anyi hotunan cikin takon so. Hotunanshi shida Yusra , abindai yamin babu daɗi , raina ya ɓaci matuƙa , amma dake ina da ɗanyen kai kamar yadda Dikko yace sai nayi ma abun bahaguwar fahimta akan yadda ita Sa'adatu ta fahimtar dani , maimakon nabi abun a sannu naji yadda sirrin abun yake saina fara kiran wayar Dikko , wayar a kashe take ma wacce baya rufemana ita kwata² duk lokacin da mune muka kirashi zamuji shi.... Haka na haukace cikin aji naci gaba da turawa Dikko saƙon zagi na kirashi da mayaudari munafuki ɗan iska , Farisa taci gaba da zugani ina ta ɓarke²n zagi kamar mahaukaciya tana cewa ai wannan ma nuna miki yakeyi tsaron gida ya barki , ya barki gadi matar tana waje ya tafi da ita ke kuma an barki tsaron gida , haka taita tunomin lokacin da yayi mata liƙi na ida ƙwacewa gaba ɗaya na warware kamar falfela , duk yadda Sa'adatu taso ta fahimtar dani naƙi saurarenta saida na gaji dan kaina na tsaya , bayan wani lokaci kuma na tura masa cewa tunda dai kai ka lalace ka zama karuwa saina fitar da cikin nan. Duk haka bai isa ba na farakiran wayar Ashiru , shima nashi a kashe yake , shima na tura mishi saƙo cewa Allah ya isa tsakanina dakai har kaga ana cin amana bazaka faɗamin ba , munafukai "yan partyn amarya.....

 Umar na kira shima na zage tatas kuma nace masa munafuki da kilbibin faɗi ba'a tambayeka bane ka iya faɗa , dake shi Dikkon tsoronshi kakeji shine baka faɗamin ba yana tare da "yan mata , shima dai na tata mishi ɗan ƙaramin haukata na kashe waya. Wannan duk ya zama zargi da wani tunani daban irin namu na mata , duk lokacin da akace miki mijinki yana can yana kaza ko yayi kaza ko kaza yake aikatawa karki kuskura ki yanke hukunci akan abinda baki da tabbaci akanshi , zargi baida kyau haka kuma yanke hukunci cikin fushi yake haifar da ɗa mara ido , domin ita zuciya kamar iska haka take halbawa hawa take da sauka , ƙoƙari ake ana danneta ba'a biye mata haka kuma ba'a bata abinda take so domin za'ayi nadama da dana sani idan ta kwanta.....

 Har aka tashi makaranta ban sake magana ba , haka na koma gida jikina suku² duk abin duniya ya dameni na rasa ina zansa raina , sai yanzu na fara tunanin hukuncin da zai biyo , dariyar shi na tuno da yake cemin ki daina ganin kwana biyu na zuba miki ido ina nan yadda kika sanni ban canja ba halina yana nan yadda kika sanshi. Me zai faru idan Dikko yaga texses in nan ? Me zaice ? Ya zaiyi ? Ni kuma ya zaimin ? Me zai faru.............??? Zuciyata tace duk abinda ya faru sai me ? 

Jikin madubi na matsa na kalli kyakkyar fuskata da idanuwa na masu burgewa zararan giraren idona da suka ƙara fitomin da kyan idanuwa na , girata yadda tayi wata kyakkyawar ziririyar saƙa su biyun suka haɗe suka ɗanyo ƙasa , dogon hancina na kalla da kyakkyawan bakina , murmushi nayi tare da maida idona saman goshina. Lallausan gashi ya kwanta luf abun gwanin burgewa , ida cire kallabin kaina nayi nabi gashin kaina mai cikar kyau da ɗaukar ido irin na cikakkin fulanin asali da kallo , dirina na kalla ga haskakakkar fatata komai yaji ga hutu ya tabbata a gareni , zuciya tace kallarki Sultana ɗanyar yarinya dake kin cika ta ko ina komai ya zauna kalar burgewa , shekarunki ma yanzu suke tafiya dan zuwa 20 , me zakiyi da Dikko wanda yaƙi yadda ma ya faɗa miki shekarunshi saboda yawansu , gashi nan ma harya fara squeezing , Allah ma yasa yayi fushin kiga yadda zakici wuta a garin nan , ga kuɗinki a account ga mota ga tsadaddun suruta masu yawan gaske. Sarka "yan kunne zobe ɗan hannu duk na zinari kala² , idan kika fita zaki ci gaba An mata da hannuna na nuna da bakina yadda jirgi ke tashi sama , dariya nayi tare dayin rawa a jikin madubi dan mafitar dana samu , kai zanci uwar² uwayen masu wuta , ashe ma hauka yasa nayi aure a Katsina ? Ai ban taɓa lura da haka naɗu ba sai yau , ana ta faɗamin ban ɗauki abin serious sai yanzu na ƙarasa ina wasa da kyawawan idanuwana.........

  Rawa naci gaba dayi ashe dai na haɗu da yawa shi yasa shima kanshi Dikkon yake cemin An mata , gani da tsawo dai² kuma ni ba ƙatuwa ba. Kai gaskiya inada siga da kuma launin burgewa gani kuma yarinya , Sultana yanzu lokacinki ya fara........

JAMILA MUSA…
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ BRILLIANT WRITERS ASSO ????
-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-

      *KWARATA RETURN...*
 _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

Rubutawa…
JAMILA MUSA…

  *SAI NA AURI D ' K*

Naki ne “yar uwata ????????
ASMA’U ZAYYANA
{{ Asmeenat Xeyyan }} alfaharina bugun zuciyar JAMILA MUSA…

???? —— 3

 Bani kaɗai ba , mafiya yawan mata haka muke. Duk lokacin da muka shiga cikin wata ni'ima ta daban sai kanmu ya fara rawa mu riƙa yin wani hange na daban , wasu matan basa fara gilu² da kansu sai sun ƙoshi nan zasu ɓalle ƙofar iskanci da rashin kunya. Kamar dai ni yadda na kasance. Gani na tsaya a jikin madubi ina ta kallon kaina yayin da wani sashe na zuciyata ke nunamin in kalli kyauna ! Ashe haka na haɗu ? Haka nake kyakkyawa ? Aiko yadda nake mai kyan nan baima kamata ace ni ina aure a katsina ba , kamata yayi ace ina irin su Abujar nan idan ba Abuja ba ina can wasu ƙasashen duniya mijina ya ɗaukeni yabar nigeria dani , abun ba haka yake ba kuma ba'a kyau take ba. Jin daɗi da arziƙi duk kyanki da iya haɗuwarki sai Allah yaso zakiji. Ba'a kyau , asali ko nagarta yake ba. Arziƙi da hutuwa baiwa ce daga Allah idan yaso sai ya baka ya kuma sa kaji , ni'imar aure daban ce. Allah ya darata ta haka kuma ya martaba ma'aurata. Idan kina ƙarƙashin inuwar aure kinfi ƙima daraja da kuma martaba duk kuwa irin talaucin da mijinki yake fama dashi , kiyi haƙuri kiyi zamanki a gidan aurenki arziƙi na Allahna , kuma wannan ɗin dai shine hatimin tsirarki. Yayin da kika kalli kanki a madubi kika ga ke kin kai ƙarshe wurin haɗuwa ko kyau tou albarkacin martabar aure kika ci , daga zaran inda kikayi yarinta irin tawa kika zuge auren nan kin tashi aiki.

 Saboda kiyi duba da wani abu. Gidanku da gidan miji akwai ƙaton banbance² , karki kalli gidanku ana kashe kaji goma duk rana , ana yanka rago duk sati , kina da ɗakin sama ƙaton gado da a c ba'a ɗauke wuta ga wata ɓarkekiyar talabijin ta cinye rabin bango. Kuna cin shagali shayi da biredi duk safiya a haɗa da wani lafiyayen kayan cikin rago , dankali doya kwai da rana a samu wani lafiyayen abinci aci ku kulle na dare da wasu kayan marmari , idan zaki fita a baki driver ko ke ki tuƙa kanki , idan buƙatar shiga bayan gida yazo zaki sauko ne kawai daga saman gado ki shiga toilet hmmmm. Gidan miji kuma koko , tou wallahi wannan kokon ya fiye miki mutunci da kuma kwanciyar hankali , idan kuma kina ganin kin haɗu bara ki kashe auren kiyi gaba , tou budurwar bana tafi ta bara , duk haɗuwarki duk nasabarki duk mutunci duk yadda kike jin kina da nagarta siga ko kyau duk haɗuwarki duk kuɗin gidanku duk iyakar gogewarki da haɗuwarki idan wasu matan na wure tou wallahi ke mayino ce , da kika kalli madubi kika ganki ke kyakkyawa ce ko kin haɗu tou darajar aure ne yasa kika zama haɗaɗɗar idan har tsautsayi ya kaiki kika cire auren nan kina tunanin zaki auri sarki tou fa lallai ko dogari ba naki bane ba danma karki ji ƙamshin masarauta. Ku kiyayi rashin kunya wa mazajenku , kar kuyi irin nawa kuga zagin miji ko rashin kunya ƙauracewa shinfiɗarshi ko rashin mishi sannu da zuwa hanashi abinci da rashin yi mishi magana shine mafita , a , a , wannan babban zunibi ne ga kuma ke mai aikatawa kina kashe kanki ne , kuma kina rage ma kanki mutunci , duk duniya babu abinda yafi mutunci haƙuri da kuma biyayya , zaman lafiya yafi komai karki kuskura ki zama mai tashin fitina a gidan aurenki , ki zaɓi zaman lafiya yafi komai ki kuma kiyayi kanki da haƙƙi....... Karki ce irin halina ya burgeki uhum a , a kar kiyi....

 Har dare haka na samu aiki jikin madubi. Saidai inyi sallah in dawo inci gaba da kallon kaina , saida aka kira isha'e nabar jikin madubi naje nayi wanka tare da ɗauro alwallah dan gabatar da sallah , ina gama sallah na fito dancin abinci. Zama na kenan ban fara cin abincin ba akace min wai Umar yana jirana a palon ƙasa ,

 Cewa nayi aje ace masa banda lokacinshi , tunda dai na gano makircinshi nasan yadda zan zauna dashi. Ai ni lokacin nida Dikko zai aureni shine yaje ya faɗawa Jiddah , amma ni za'amin bazai faɗa ba , shima Dikkon zai dawo ya sameni sai ya sakeni tunda ba tare aka haifeni dashi ba....

 Momy kuwa idan hankalinta yayi dubu ya tashi ɗaya bayan ɗaya , Aunty Bilki baƙar muguwar munafuka ne ta bugawa a jikin mujalla , Umar yazo ya faɗawa Momy Mai gida fa yayi tafiya da Sharifa , wai duk girman Dikko ita Momy bata daina fargaba akanshi ba , ga kuma Papi data matsa mishi tace dole sai yaje dashi tunda hada su Ashiru zai tafi. Saida aka kai ruwa rana ya yadda yayi tafiya da Papi.

Dikko kuma koda yaga saƙonni Sultana baima da lokacinta bare kuma yasa ran zaiyi tunanin bata amsa , mafiya yawan mata suna da cusashshiyar ƙwalwa , ƙalilin ɗinsu ne zasuji zancen ƙarin aure suyi abu na hankali da tunani , ita An mata bai ɗauketa mai hankali ba. Amma insha Allah idan yaga wanda zai auri mai ƙaramar shekaru irin An mata saiya bashi shawara kar ya aura yaje ya auri macen da tasan abinda takeyi , shidai yau gashi har An mata tace mishi karuwa wai shi.... Shine karuwa kamar An mata ta zauna ta rubuto mishi zagi na rashin mutunci , haka Jiddah itama tayi lokacin da zai auri An mata tayita hauka tana zaginshi. Jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai yace aure ba fashi sai nayi idan kin gune ki gyara hali. Kallon Papi yayi dake kwance jikinshi yana bacci duk ya rirriƙeshi saboda gajiya , a bayyane yace idan An mata batayi hankali yanzu ba yaushe zatayi hankali ? Shi kuma yana ganinshi babba duk ya wuce irin wa'anan shirmen , da kuma anyi rashin sa'a suna wuri ɗaya tayi wannan maganganun zai ɗauki zafi shima ya yaɓa mata magana mai zafi ita kuma ta kasa riƙewa ta tattaro nata ɓacin ran da yarinta ta kwaɓa mishi rashin wayau.

 Daga nan sai duka , ita kuma a kunne take sai fuuu ta tafi gida tayi yaji. Yadda Mamarta bata sanshi bata ko ƙaunar ganinshi itama sai ta tafasashe ta fara turo doguwar wasiƙa a saki "yarta , ƙalilin matsala ta fito amma ƙaliliyar magana bata iya kashe wutar dake ƙoƙarin ruruwa. Yana ta ƙoƙari wurin ganin ya farka da ita daga baccin rashin wayan data tafi amma baida lokaci kuma shi a ganinshi abinda yasa An mata ta rainashi girmanshi tun farko daya buɗe a gabanta. Yana gani shekarunshi yakai na ita ta girmamashi tasan matsayinshi da ƙimarshi ta kuma riƙa kiyaye wasu kalaman akanshi bata gani kuma bata dainawa. 

Shidai da shine mace mijinshi ya tashi ƙara aure ba zagin mijin zaiyi ba , zagin miji , rashin kunya , ƙauracewa shinfiɗarshi da zance yaji ko tambayar sakin aure bashi ne mafita ba. Haka kuma bazai daina dafawa miji abinci ba , sannu da zuwa da Allah ya kiyaye hanya duk sai yayi , da farko dai abinda zaiyi shine , zai duba wace ce mijin nashi zai aura , shi kuma ɗin waye shi , ita wacce za’a auron ya take ? Shima ɗin ya yake ne ? Me yafi ta me tafishi ? Me gareta wanda shi bai kai ba ? Duk namijin da zai ƙara aure dole yana da wani dalili nashi na daban tunda kowa da ra’ayinshi kuma ba a bayyane yake ba a ɓoye yake. Gyara dai kawai shi yafi a gareki , bawai sai auren yazo ba kullum ki kasance a gyara da kiyayewa tsafta biyayya iya lafazi da girmama shi. Kuma duk hakan bazai hanashi ƙara auren ba idan Allah ya rubuto da wani rabon. Kije kiyi duk abinda kikaji kina iyawa danni banda lokacin da zan zauna na koyar dake zaman takewar rayuwa na yau da kullum ƙaramar yarinya dake.

Duk kyan mace idan ba gyara zero. Duk nagartarki da sigarki idan babu biyayyar aure zero. Duk kuɗin gidanku idan kinajin ke wata shegiya ce idan baki bi mijinki kuka zauna lafiya ba baki haɗu ba. Duk kuma yadda namiji yake sanki a zuciyarshi rashin kunya da rashin mutuntashi ke ƙaton zero ce mai ido da kunnuwa a wurinshi dan rashin biyayya wa namiji ba ƙarami rage miki martaba yake ba. Amma duk rashin kyanki idan dai kina da ɗa'a da biyayya haƙuri tsafta iya girki kauda kai akan duk girman abu bawai dan ba'a ɓata miki ba , a , a haƙuri dai kikayi kika bashi baya tou kinyi a haka idan kika haɗa da iya gyara tsakiyar filin wasa. Misali duk kyau ko haɗuwar abinci. Yaji manya tsokokin nama yasha mai idan dai babu kayan masarufi da aka sarrafashi dasu duk wannan manya namomin idan kaci sai ka tofar saboda ba'a ƙawatashi da abinda zaisa ya ciwu ba , wasu zasu nemi magi yaji da ɗan gishiri su gyarashi dan su samu damar ci a sauƙaƙe amma bazaiyi daɗi ba a hakan ma tunda ba'a dafo dasu a tare ba , ɗan ɗanon dai zai bada wani iri daban kawai dai babu daɗi , tou haka kyakkyawar mace take idan babu abinda na lissafa a sama ko an zauna da ita sai an tofar. Ku gyara domin zamani ya canja akala fa......

 Daga Abuja Sharifa tayi sallama da Dikko ta juyo bayan ya ajiye mata manyan kuɗi a account ya kuma bata wasu a zahirance , danshi mutum ne mai bala'en san yaga kana girmamashi ka kuma yi mishi ladabi. Haka kuma Dikko yake san godiya idan yayi maka abu kuma wannan halin shine tuni yake ƙoƙarin ganin ya koyawa Sultana , tunda ko dukanta yayi zaice ta gode masa.

 Tunda Sharifa ta dawo katsina taci gaba da halba hotunan da ta ɗauko ita da Dikko , da yake ta iya kwanciyar aska har Papi ta jawoshi jikinta yana kwakwarta. Dan da zata tafi shine Papi yaita kuka yana cewa Yaya mu tafi da ita , shine abun ya bawa Dikko mamaki tunda Papi yake bai taɓa kuka idan An mata bata nan ba , ko idan zata fita. Sai yaga zama ɗaya duk rashin yadda na Papi yana kuka dan Sharifa zata tafi. Wannan abu ya ɗaga hankalin Dikko anya An mata tasan abinda take ....?Tsakaninta da Papi duka ne idan kuma yayi mata magana sai tace ai shima haka yake dukanta kamar wata jaka saboda haka wurin ɗanshi zata rama duk dukan da yasan yayi mata a duniya.

Mai gilashi kuwa tana ganin status in Sharifa kuma tabi duk ta yaɗa a kafafen sada zumunta na nahiyar yanar gizo. Hankinta fa ya tashi , kuma tayi alƙawari da rayuwarta ko zata mutu yadda Sharifa ta lalata mata aurenta wallahi babu gudu ba ja da baya itama sai ta lalata nata da Dikko. Addu'arta ɗaya shine Sultana ta bata haɗin kai a dai² lokacin da Sultana ta ɗauki waya. Mai gilashi barka da dare. Yawwa matar D ' K ya gda ? Lafiya qalau ya Papi ? Wallahi baya nan yayi tafiya da Babanshi. Zuwa ina haka ? Kinga ni wallahi bansan ina suka tafi ba , kai ƙawata ƙaddarorinki har biyu basa nan kuma baki san ina ne suka je ba ? Ey bai faɗamin ba nima ban damu da sanin can inda zaije ba , kai Sultana ? Tou me yasa haka ? Ke kindai san halina sabgar gabata ma ta isheni...... Lallai sai wata "yar iskar banza da bata aurar miki miji ba tasan ina zaije. Gaskiya ke Sultana jakace , nice jaka Mai gilashi ? Cikin kwantar da murya Mai gilashi ta fashe da kuka tace Sultana kiyi haƙuri idan ranki ya ɓaci matsala ce na hango miki ina ta ƙoƙarin gyara miki amma kin gagara fahimta ta , wata maƙiyata mijinki zai aura , idan har kika kuskura ya aureta wallahi׳ ƙaryarki ta ƙare........!!! Tana faɗin haka ta tsinke wayarta.

Mai gislashi na fita a wayar Sultana kiran Momy yana shigowa , irin zagin da take ma "ya "yanta irinshi tayi min , kuma tayi min rantsuwa da Allah idan har ban raba Dikko da Sharifa ba idan tazo gidan abin bazai min kyau ba , kuji wani irin ɗanyen hukunci. Momy wace Sharifa ce ? Kamar dai yadda Nabeela ta faɗamin haka Momy itama taimin bayani. Sannan ita ma ta kulle da cewa , idan har kika kuskura Dikko ya auro Sharifa wallahi׳ kashinki ya bushe , Dikko tsabar tantirin kwallon ɗan iska ne shi. Duk yadda baki zato ko tunani ya wuce. Idan kika bari ta shigo tou tabbas kece a waje.......... Tana faɗin haka ta kashe wayarta. Abin duba anan shine , da Dikko manemin mata ne idan har Sharifa ta dafeshi sai ta Allah saboda sabon halin da nazo mishi dashi , kunga dai nice da kaina na ƙirƙiri matsala a gidana saboda ɗaukar shawara marar makama , idan kuma an samu namiji mai surutu daya je wurin mace zai kwace ɗimi kamar ya lashi wuta matarshi kaza². Tou macen bariki bata bashi haƙuri saidai tace rabu da banza taje can ta ƙunshe har yayi wari , duk lokacin da kaji kana buƙata kazo in baka. Kinga daga nan kin zama ruwan kwance , haka take faruwa ne yanzu. Kina zaune da mijinki lami lafiya hankalinku kwance baki nemi komai a wurinshi kin rasa ba , haka kawai sai kiga ya tsiro miki da wasu sabbin ɗabi'u yana cin ubanki babu gyara babu dalili. Duk yabi ya ƙuntata miki ki rasa abinda kikayi mishi ya fito da wasu manyan miyagun halaye wanda kuma ke ada sam baki sanshi dasu ba , hmmm bance mijinki ba kila ya samu wata mace can ta riƙe mishi wuya an barki da ciwon damuwa. Haka suke matan bariki su ba aure suke ba mazajen wawayen mata suke mayar wa jarinsu , sune zasuyi ta karta suna ƙwalƙwale musu aljihu. Su riƙesu da bariki suyi ta gabatar da wasan danbe kina gida kwance kamar asara kinci kinsha sai neman fitina da hana ma miji zaman lafiya , ɗari biyar tayi miki wahalar gani dubu ɗarin shi tana wurin mata. Wanda kuma ya faɗa miki gaskiya ya zama abokin gabarki rai ba haƙuri sai a tattara kaya ayi gaba.... Kudaiyi nazari sai ku gano inda damuwar take mune ko su ?...... 

Bayan Momy ta kashe waya taci gaba da faɗa , waime ma Sharifa take dashi baƙar banza , me Dikko ya gani a jikinta ? Ga matarshi kamar balarabiya ta fara haifo mishi kyakkyawan ɗa dan Papi yana da kyau sosai masha Allah , ita ko Momy tana ma mamakin yadda Dikko lokaci guda ya zama mara kunya , saboda a da ta mishi maganar Sharifa da farko kenan dai yace mata ta kwantar da hankali komai zaizo a sauƙaƙe , jiya kuma da zaiyi tafiya tai mishi maganar Sharifa ce mata yayi ci gaba ake san samu. Dogon nazari Momy tayi tou wane ci gaba zai sama wanda matarshi bata bashi ba ?Tayi maganar a bayyane tare da rufe idanuwanta tana wasa da wayarta a saman goshi.

 Babban gidan daya sha ado da ciyayi , sai mamallakin gidan ya fara samun matsala. Misali , tsakar dare sai yaji ana dukanshi sai ya tashi dan ganin mai dukan nashi , amma saiya duba ya duba baiga kowa ba. Ya sake komawa ya kwanta a tsorace ya kasa bacci sai yaji haniniyar doki da ƙarar takonshi yana tun karo shi. A firgice sai ka tashi , kana tashi saika sake ganin ba kowa. Amma sai aka gaggaɓe maka da dariya , me zaka fahimta ? Da farko dai idan zamanka ne na farko a gidan zakace iska ne , idan kuma ka daɗe a gidan baka taɓa jin irin haka ba zakace jifa ce { asiri } daga nan sai ka samu ayi maka addu'a dan kawar da wannan matsalar. Amma sai abun yaci gaba maimakon a samu sauƙi sai damuwar taci uwar ta farko , bayan wani lokaci sai kaji ana cewa idan baka tashi ba a gidan nan zamu kashe ka , ko zamu nakasa ka , sai kaƙiji baka tashi ba. Bayan wani lokaci sai a nakasa maka ɗa ɗaya ko kai. daga haka kai mai gidan zaka fara nazarin canja muhalli ƙarshe kana iya samun ƙaramin gida wanda baikai ƙwatar wanda kake ciki ba. Ba shakka ci gaban da Dikko yake nema matsalar tana nan ta tare a wurin Sultana. Wata zuciyar tace a , a matsalar tana wurin Dikko , wani sashe na zuciyarta kuma yace wallahi Sultana ce mai matsalar amma abinda za'ayi ki fara zama da ita ki gano ina damuwar take , idan ta gyara zakiji zance aure ya mutu , idan kuma Dikko yayi aure tabbas matsalar tana nan wurinshi......

Duk da bazai yuwu mace ta hana mijinta aure ba idan Allah ya rubutu hakan. Wayonki ko dabararki hikima da iya tattalin miji duk kissarki duk kwarkwasarki duk feleƙenki da iya duniyancinki idan Allah ya rubutu da rabon wata a cikinshi sai tazo , idan kuma kika taso da hauka sai ajalin rabo yazo yayi gaba dake. Ita bawai ta hana Dikko yayi aure bane ba a , a iskancin ita Sharifa ya girmi tunanin duk inda mai tunani baya tunani , musulmin karuwanci takeyi gata da kisan mummuƙe kuma haka ta kware wurin iya kwanciyar kwantar ɓauna. Ba Sultana ba har ita idan har Dikko yayi gigin aurar Sharifa tou fa lallai itama kanta Dikko ba nata bane ba.

 Wata irin dariya suka gaggaɓe da ita gaba ɗaya duk karuwar dake wurin , ƙarar kiɗa ta karaɗe kaf ilahirin girman gidan karuwan dake can wurin Sitirolin , sanye ta shigo cikin wata irin zureriyar hijabi tasha niƙaf da safa , tana shigowo aka canja sabuwar waƙa ta matan bariki , da rawa Sharifa ta shiga tana shiga tsakiyar wurin da ake gabatar da shagalin ta cire hijabinta daga ita sai fant da bra , *KWARATA* n ta kuwa sukace gasu nan , a tsakiyar fili suka fara ɓarin kuɗi....

 Mai gilashi kuwa tana gama waya da Sultana ta fara kiran wani kwartonta , babu wani daɗewa da ɓata lokaci ya ɗauka , ba ko gaisuwa tace kana ta ina ne haka ? Ina gidan "yanci ya faɗa a taƙaice , na wace anguwa ? Ya faɗa mata ko wane yake , kaga Sharifa ne ? Bana tare da ita tana can babban gida. Lafiya ne dai a wurin ? Ey tanayin shagali ne , wanda zata aura yaje egypt daga can zai wuce yayi umara yana dawowa za'ayi musu baiko.... Waye zata aura ne ? D ' K mana. Shima ya zama ɗan hannu kenan ? A , a , to me yasa zai aureta ? Nima dai ban sani ba , shiru Mai gilashi tayi tana nazari bayan wani lokaci tace sai anjima ta kashe wayarta....

 Bayan sati 3...

Haka dai rayuwar take ta doka ƙaraurawa tsakanin rayuwarmu gaba ɗayanmu. Kwaɗo , ni su Amisty , Mai gilashi , Sharifa , mardiyya , Yusra Yazeed Jiddah Aunty Suwaiba Momy Aunty Bilki & Dikko…..

Har yanzu Dikko bai nemeni ba nima na manta dashi , ina nan ina fama da girman kai , kuma kullum saina ganshi online. Bayamin magana nima bana mishi , dani dashi kowa yana huɗɗar gabanshi kawai , ko hotunan daya turomin nace masa basuyi kyau ba. Daya gani bai bani amsa ba , 

Dikko kuma bawai yayi fushi bane ba , a , a ya dai zubawa Sultana ido yaga iya gudun ruwanta da hankalinta. Shin zata nemeshi ko kuwa ? Shima kullum yana ganinta online , idan ya ganta saidai yayi murmushi yace An mata kina ɗauwaniyar da yarinta , wai ni ? Nine kike ma haka ko ? Hmmm ai ya miki kyau....

Kullum sai Momy ta kirani tace nayi waya da Dikko ? Sai ince mata nayi. Shine ya faɗa mata bana kiranshi koma dai miye nikam ban sani ba. Nabeela ma ta kirani tace matar Yaya kinyi waya dasu Papi ? Itama nace mata nayi Rabiya ma haka......

 Gaba ɗayanmu zaune muke a palo. Duk mu 6 ɗin babu wanda yake magana , palon yayi shiru irin yadda yara kecewa mutuwa ta ratsa da ba'ayi shiru ba data ɗauka. Mai gilashi kuwa ta tsareni da kallon takaici nima na ƙura mata ido naƙi na daina kallonta. Kowa yana kallon kowa bayan ta faɗamin cewa ta gaji da rashin zuwata makaranta kullum² da banayi kuma bana ɗaukar wayarta sai naga dama to tashawo ta dubu tazo. Murmushin takaici tayi tare da kauda kanta gefe tana girgiza kanta cikin yanayin damuwa........

 Gabatar min da ƙawayenta tayi. Hadiza Fadeela Halimatu Zainab sai ita duk dani mun zama shidda kenan. Ƙawayena ne su dukansu kuma duk matan aurene. Wacce ta kira da Hadiza ta nunamin tana ci gaba da cewa kinga wannan ƙawata ce sosai Hadiza kenan , amma mu a cikin ƙawayenmu muna kiranta da ashana. Kallonta nayi sosai bayan wani lokaci nace ƙona gidan kowa na faɗa ina jinjina kaina. 

Ita kuma mai gilashi taci gaba da cewa , su duk maƙota ne kansu a haɗe yake kowa bata ɓoye sirrin kowa. Nuna su tayi duka , tana nunasu tana tafiya da maganarta cewa kuma mu dukanmu a gidan wannan muke zaman majalisa ta nuna wacce ta nunamin a matsayin Halimatu. Idan kin yadda zaki shiga cikinmu kema kije majalisa ko azo gidanki ayi. Inji Hadiza kenan ta anshi maganar daga hannun Mai gilashi. Nace a , a , me yasa ne ? Saboda nan ɗin ba gidana bane ba. Tace ya raina ki kenan shi yasa kika ce haka ? Ummm gaskiya kam ko bai rainani ba ni har yanzu banfi ƙarfinshi ba saidai , zan bar gidanshi na faɗi barin gidan a zuciyata. Ita kuma Halimatu tace nikam nafi ƙarfin nawa domin ina amfani da kayan mata masu kyau shine yake bina bani nake binshi ba dan yana tsoron yayi min laifi dare yayi in juya mishi baya....

Wata irin haramtacciyar batsa Mai gilashi ta liliyo ta watso , gaba ɗayanmu dariya mukayi na tsere Mai gilashi da ido danni dai Allah ya sani ɗan tasha yana burgeni sosai. Har kowa ya gama dariya ni ban daina ba , wayata na ɗauka na rubuta batsar ina dariya. Ban gama dariya ba ta fara bada labari dan kawar da zance ni na shiga madakatarsu ita tafi so tayi zama daga ita sai Sultana dan ganin Dikko bai auri Sharifa ba...

 Ita kuma idan ta faɗi zancen iskanci bata dariya sai ta ɗaure fuska taci gaba da bada wani labarin , kai da ake bawa labarin kaine abun zai daɗe yana zungurar zuciyarka kana dariya. Kuma ita bata munafurci akan iskancin da takeyi duk namijin data nema sai ta faɗa. Ci gaba tayi da cewa , wata rana naje asibiti banda lafiya dani da Hadiza mukaje , ta nunata , murmushi Hadizar tayi tana kallon Mai gilashi. Ita kuma bata kalli Hadiza ba taci gaba da cewa , ciwo ya isheni kamar zan mutu , sannan ban daɗe da aure ba. Kuma ban fara tararayya da Alhajin da muke gidanshi ba. Nadai ɗana masa tarko yana ta wani zuƙewa , ni kuma jin labarin zamu zauna a BQ in gidan wani attajiri yasa nasha uban gyara , ashe abun ba sauƙi ne dashi ba , wasu mazan tayi ɗaya kake musu su amsa wasu kuma sai ankai ruwa rana sai ka nuno musu maitarka fili , jin zanzo zama a BQ n gidan kuɗi yasa na ɗirki kayan mata kamar ba gobe. Mara ciwo ciki ciwo kamar zan mutu , shi kuma ango ya saki baki yana jiran a kawomishi Sa'aden banza yashani basilla. Auren da akayi da ganganɗe² sai kawai inzo in zauna ya sussukeni kamar ƙasar kasuwa yaita bi yana wuce babu wani gata. To banzo gidan ba saida naje aka sakamin allurar tazarar iyali na shekara biyar implant , abinda yasa nayi har na shekaru biyar shine.

Na farko dai zan fita daga gidan wanda nake aure a yanzu zanje in samu matashi mai ƙarfi da wadatacciyar lafiyar gabatar min da wasan danbe ko ba abinci dan ina tara manyan kuɗi a asusun banki na , saboda idan nayi sabon aure ba maganar zina zan tuba ga Allah ne na nemi lahirar da gaske tunda dai mun samu mun ajiye tarihi a katsinar.... Duk gidan karuwan dake garin nan idan kikaje hotuna ne na farko a jikin album insu saboda nice karuwar data fara lalata namijin da bai taɓa karuwanci ba. Nice karuwar dana fara karuwanci da "yan samarin yara wanda suke makarantar gaba da primary , wato secondery sch. Makarantar masu kuɗi nake bi ina zaliƙo "ya "yan wanda Babansu yafi kuɗi , nice nake ɓatasu in kuma sa suyomin satar kuɗi a gidajen iyayensu su kawomin ni kuma na ɗorasu a network sune sukaji yadda abun yake sai suke farautomin abokansu ina basu suna bani kuɗi. Tarihi ya nuna ni nice karuwar danayi iskanci da wani tsohon malami wanda yake wa'anzatarwa da tunatar da karuwai muji tsoron Allah mu daina zina , to nice naje na rufe bakin wa'azi dan shima malam ya zama kwarto , nice karuwa ta farko da tayi ma namiji fyaɗe kuma Baban ƙawata ne har a cikin ƙuryar ɗakinshi kuma a cikin gidanshi.

Nice karuwar dai da karuwancin yasa na fita ƙasashen ƙetare , { wai kunsan ina take nufi ? Wasu states in fa take magana } na kafa manyan tarihi sosai nice karuwar da ƙasa ya kamata tayi alfahari dani amma har yanzu gwamnati bata nemeni ba duk yadda na jajirce wurin yima jahata hidima. Na bautata ma jahar katsina sosai wurin ganin na ciwo mata babbar lamba a cikin sahun manya karuwai duk a cikin shekaru 2 nayi wannan ɓarnar ina da shekaru 28 a duniya. Amma har yanzu ba'a haskoni a cikin talabijin ba , saidai dana kamo tasha dan ganin ko za'a hasko ni sai inga ana cewa wannan ce taje gasar karatu a wata ƙasa , sune sukaje fareti gaban gwamna , manyan "yan kwallo sune suka ceci wane daga kaza , an kamo manyan ɓarayin da sukayi sata a wuri kaza suka samu damar nasarar guduwa tou an kamosu , ko sune sukaje wurin musabaƙa , ɗan sanda kaza ya kamo "yan ƙwaya da dai² sauransu wannan itace ta zama kaza² amma an kifewa karuwai ciki duk babu su a cikin tv. Haba ai nayi ƙoƙari sosai shi yasa ko kinje gidan karuwan dake garin nan sai an baki hotuna na kin gani tare da bada ɗan taƙaitaccen tarihin rayuwata cewa kiyi koyi dani. Tarihi kuma dai har yanzu ya sake nunawa nice karuwa ta farko da nayi aure na koma makarantar boko. Kuma nice karuwan dana faɗi bayan na haɗu da abin harin nawa { haɗuwarta da Dikko kenan } , zan tuba amma sai nan bayan shekaru biyar. Idan kika mutu kafin lokacin fa ? Na tambayeta , kallabin kanta ta cire tana duƙomin da kanta daya yasha kitso da ƙarin gashin doki , furfura nawa kika gani a kaina ne ? Ba ko ɗaya na bata amsa , rufe kan tayi tana cewa sam mutuwa bama zata fara zuwa wurina ba a yanzu. Ke kina da matsala ana maganar arziƙi kizo ma mutane da wata maganar da bata dace ba. Ta ƙarasa maganar tana tsoki tare da gyara zaman gilashin dake manne a saman fuskarta cewa tunda ma kika kira mutuwa na fasa baki labarin. A haka dai ta tsaya bataci gaba ba ta tattara zugar ƙawayenta suka tafi tana cemin inyi ƙoƙari inzo makaranta...

  Duk mutanen dake cikin gidan sun kasa bacci a daren nan saboda wani irin kuka da Hafsa takeyi mai tada hankali. Sai burgima takeyi tana riƙe hannunta dake zubar da wani irin ruwa marasa kyan gani , da anzo warware hannun sai tace karku buɗemin hannu ku tafi ku barni , fita kowa yayi daga ɗakin aka barta ita da Amisty , tagumi Amisty tayi tana tunanin yadda sukayi da malamin. Tayi masa bayani kaf akan labarin rayuwar Hafsa da kuma yadda take san Dikko kamar ta kashe kanta , tace zata rako Hafsa idan tazo karya nuna yasanta suna zuwa yaja zare ya karanto mata komai kuma yace zai iya aikin yasa kuɗi masu yawa , ita zata ma Hafsa wayau ta saido gidajen Dady a kawo kuɗin sai ita da Malam su raba kuɗin , ya yadda ? Yace ya yadda da hakan.....

Cike da yaudara Amisty ta fashe da kuka ta rumgume Hafsa sukaci gaba da kuka tare , saida suka sha kuka har suka gode Allah sannan Amisty tayi ma Hafsa labarin ta gano inda malamin Sultana yake ta kuma ƙara da cewa shine yayi ma Sultana aiki ta auri Dikko dan haka zasuje wurinshi idan Allah ya kaimu , Hafsa taji daɗi kuma tayi na'am da haka ta ƙara riƙe Amisty sosai a jikinta tana godiya.

  Ya Yazeed idan baraka damu ba ina so muyi auren sati ɗaya , sarai fa ya gane amma sai yace ya auren sati ɗaya yake ne ? Zaka aureni ne bayan sati ɗaya saika sakeni ina so zan koma ɗakina ne , kallon rainin wayau Yazeed yayi mata cewa gaskiya banayi , dan Allah Ya Yazeed , cike da duniyanci yace tou faɗi farashi ɗaya mai tsoka naji , wane irin farashi ne ? Jiddah ta tambaya , Yazeed yace kije ki fara tambayo yadda abun yake , yana faɗin haka ya wuce wurin motarshi ya shige yaja ya kama gabanshi cikin farin ciki. A ranshi kuma yanajin yakai wani babban ƙwaro shi zai auri matar da D ' K ya saki , farashin da yake magana kuma shine ita Jiddah nawa zata biya shi ya aureta , idan kuma ya aureta zataci ubanta sauran ƙudirin nashi kuma shine da zuciyarshi yabar ma ranshi......  *JAMILA MUSA...*

[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ BRILLIANT WRITERS ASSO ????
-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-

      *KWARATA RETURN...*
 _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

Rubutawa…
JAMILA MUSA…

  *SAI NA AURI D ' K*

???? —— 4

 Saida Yazeed ya ɓace ɓat Jiddah ta kalli agogo. 10:29pm , tou ? Wannan wane irin farashi ne haka ? Kuma farashin wai mai tsoka....! Haka kidahumar ta gaji da tunani amma tsabar doɗewar basira ta gagara gane irin farashin da Yazeed yake nufi. Haka ta haƙura itama ta koma motar ta taja ta nufi gidansu Dikko da ɓacewar tunani...

 Zaune suke a gaban bokan Al ' Ameen. Saida bokan yasha kuka sosai dan rashin Al ' Ameen a cikin wannan duniya. Yana faɗin Allah ne kaɗai yasan tsakaninshi da Al ' Ameen da irin girman amanar dake tsakaninsu , bayan yayi shiru ne ya warware wani bakin ƙyalle yayi tsafe²nshi ya wurgashi sama , cikin ƙanƙanin lokaci ya dawo ƙasa fari fat dashi. Ɗauka yayi ya miƙawa Mardiya yace taje ta cire kayanta ayi mata wankan gawa , idan ta gama ta fito ga mankara can ya nuna mata yana ci gaba da cewa a cikinta zaki shiga a sallaceki bayan an gama za'a kaiki maƙabarta ki kwana. Zaki dawo nan wurina alfijir yana ketowa , idan kika yi wannan idan har Dikko bai aureki ba , ni ba ɗan sunna bane ba....

  A gigice Mardiyya ta kalli Aunty Suwaiba cikin kuka tace tsoro nakeji Aunty , Aunty Suwaiba tace duka² miye wani abun tsoro a wurin ? Da Allah malama tashi , Mardiyya tace ita dai tsoro takeji , boka yace ai magana ya ƙare wannan shine abinda rauhanai suka aiko dashi , ko taje gida ta kwanta zata tashi ta ganta a maƙabarta ne. Kuma wallahi iskokai zasu shanye mata jini ta mutu , wankan da sallah shine zaisa basa iya mata komai , shawara ya rage nata. Ihu Mardiyya tai tayi , ta bani ta lalace , amma Aunty Suwaiba ta riƙa ƙarfafa mata guiwarta dan na yau kaɗai ? Tou meye a ciki ? Taje tayi kawai.

 Aunty Suwaiba itace ta raka Mardiyya inda boka ya nuna musu wurin wankan gawa , gurguwar banza itace ta zauna kamar gunkin baƙin kafurawa , Mardiyya ta kwanta irin yadda matacci sukeyi akayi mata wanka , bayan an gama aka saka likafani , sallah a makara tafiya zuwa kaita maƙabarta....

 Tunda Mai gilashi tabar gidan Sultana bata koma gidanta ba har 11 ta dare tana ta yawo a gari tana neman Sharifa amma bata ganta ba. Ganin bata samu ganinta ba yasa ta tafi anguwarsu , tayi bincikenta kamar haka.... Sharifa tana bin malamai ne ? A , a , amma mahaifiyarta muguwar mai neman asiri ce kamar rainon maguzawa. Ƙarfe nawa take komawa gida ? Aka faɗa mata , Dikko yana zuwa gidansu ? Baya zuwa ! Ya yanayin ibadarta ? Bata damu da sallah ba gaskiya danko azumin ramadan batayi , idan an mata magana sai tace tana ulcer , mutanen da mahaifiyar Sharifa ke mu'amula dasu a cikin anguwa ta nema tayi musu wasu "yan tambayoyi , tana gamawa ta wuce babban gida , a wurin ne takejin wai ta tafi kano wurin taro Dikko.

 Idan hankalin Mai gilashi yayi dubu ya tashi ɗaya bayan ɗaya. Kiran wayar Sultana ta farayi amma ba'a ɗauka , ta kira so adadin da ita bata iya ganewa amma sam Sultana bataji ba dan wayar baya tare da ita. Kai tsaye gidan Sultana ta dawo , amma fur aka hanata shiga , number Sultana ta nuna da duk wani abu da zaisa a yadda tasanta , amma aka hanata shiga idan dai Sultana ta ɗauka waya zata sanar dasu ne su kuma sai su yadda taje , tou bata ɗauka ba. Har 11:38am Mai gilashi bata tafi ba , Sultana bata ɗauka waya ba kuma bata kira ba haka basu barta ta shiga ba. 11:40am ta daki get in gidan cikin tsananin ɓacin rai da takaici tabar ƙofar gidan....

 Saida tayi tazara mai nisa ta fara kiran wayar Sharifa , ita kuma saida ta mula tasha iska ta ɗauka cikin yauƙi da rainin wayau tana wani cakal² da cingom irin na riƙaƙƙin "yan bariki , hmmm Mai gilashi tayi tare da cewa suna na Sa'adatu Mai gilashi...... Saida Sharifa ta sake cakal׳ tace ai na sani. Kina ina ne haka ? Mai gilashi ta tambayeta. Kin aikeni ne ? Murmushi Mai gilashi tayi tare da cewa , dani dake babu wanda ya aiki kowa ko yasa nake tambaya , inda kike kawai nake so ki faɗamin..... Zaki zo ne ? Dariya mai Mai gilashi tayi cewa ai hannun haggu ba baƙon inda kike amfani dashi bane ba. Yanzu dai ba wannan ba , naji ance zakiyi aure ? 

Cike da ƙwarin guiwa tace eh , waye zaki aura ne ? D ‘ K , ba naki bane ba. Sharifa tace nawa ne , Mai gilashi tace ƙarya kike ba naki bane ba… Sharifa tace wallahi saina auri D ‘ K , kamar ya kikejin shi ne ? Shine duniyata , zaki iya faɗamin ko adadin mutane nawa suka bar duniya ne duk soyayyar da suke mata ne ? Suna santa kuma sunajin daɗin ta , amma dole sun tafi sun barta suna can ƙasa sun kwanta badan ransu yaso ba dalilin yasa kikaji nace ba naki bane ba yana da dubunki , amma kuma tunda kika kirashi da duniyarki tou ba naki bane ba. Me yasa kika ce haka ne ? Mai gilashi tace yawwa, bara na baki misali. Hafsa Jiddah Mardiyya Yusra ga kuma Sharifa matarshi na gida , ita ta gidan ƙaddara kawai bata a lissafi tunda an aureta. Nawa zai aura a cikinku nawa zai bari bai aura ba ? Su waye su ? Sanin su waye su da matsayinsu a wurinshi ansar tambayarki tana wurin D ‘ K ki tambayeshi abinda yace miki ki kirani ni zan buɗe miki yadda abun yake , tana faɗin haka ta tsinke wayarta…..

1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Back to top button