Hausa Novels

Lu’u Lu’u 19

*19*

 

A ladabce dan san ya samu abinda ya ke so ya sunkuyar da kai yace “Sarki na, mhe zai hana ka zauna sai mu tattauna.”

A wulak’ance sarki Musail ya nuna kan shi yace “Da wa? Da ni? Ai har abada, ka manta rabuwarmu da kai ne?”

Murmushi Bikhatir yayi ya sake yin k’asa da kan shi yan tuna rabuwarsu ta k’arshe wacce basu sake had’uwar ba sai yau kuma yanzu, shekarun da suka gabata a baya gaba da gaba kuma ido cikin ido Bukhatir ya kalli sarki Musail yace _” Na yarda kayi nasara a kai na a kan ta, ban damu ba ko dan kana da mulki a hannunka ne kayi nasara a kai na, amma ka sani daga yanzu ni da kai gaba ce a tsakaninmu dan ka rabani da matar da nake da burin ta zama ta wa, shi kan shi wanda take so a matsayin abokin gaba na dinga kallonshi, kuma a kowace wucewar rana neman hanyar da zan kassarashi nake, na yi farin cikin mutuwarsa fiye da tunaninka, amma yanzu mutuwarka ita ce abar harina.”_

Sanyayyar murmushi ya kuma sako dan sai yanzu kalaman suka bashi dariya ma, sarki Musail ma murmushin yayi yace” Da alama ka tuna, dan haka ka gaggauta barin nan kafin na sa a cire maka kai, komata ka shigo.”

Dhurani ne ya sunkuya daf da kunnenshi yace” Ina ga fa zai fi mu saurare shi, haka kawai ba zai zo ba idan babi dalili mai k’arfi.”

Kallon shi yayi yace” Malami ina so ka sani duk wani abu da zai min barazana da rayuwata babu ni babu shi, ka fi kowa sanin haka.”

Kallonsu Bukhatir yayi yace” A gafarce ni ranka shi dad’e, maganar dake tafe da ni mai mahimmanci ce, magana ce akan gimbiya Zafeera, na san zaka so jin inda take? Tare da kuma wa take?”

Girgiza kai sarki yayi yace” Ta ya zan iya yarda da kai?”

Nuna masa k’ofa yayi yace” Gimbiya Zafreen, ai ta dawo cikin k’oshin lafiya, ko bata fad’a maka tare suke da yar uwarta a can ba a hannu na?”

Shiru sarki Musail yayi yana kallon fuskar Bukhatir, ya jima haka alamar yana ta tunani kafin ya jinjina kai ya taka a tsanake, wata k’ofa wacce wanda mai kallo zai yi tunanin ban d’aki ce ya bud’e ya nunawa Bukhatir yace” Akwai buk’atar muyi sirri?”

Da girmamawa yace” Me zai hana.”

Bin bayanshi yayi da ido sarki Musail ya ma Dhurani signar ya biyoshi, shi ma wucewa yayi a k’arshe suka bar Zeyfi tsaye dan sauran abokan tafiyar sjna farfajiyar gidan, ganin haka ita ma sai ta koma ta zauna tana gyara lullub’inta ta maida hankalinta ga kallo b’angare d’aya kuma tana tunanin ko me ya sa ya zo nan da ita kuma?

A ciki kuwa zazzaune sukayi suna ta kallon juna kafin sarki Musail yace “Ina jinka? Me yasa ka sace min yarana duka biyun?”

Murmusawa yayi ya sauke numfashi yace “Ba na sacesu bane dan na cutar da su.”

Da sauri sarki Musail yace “To me ka musu?”

Numfasawa yayi sosai ya d’an muskuta yace “A makarantar da su gimbiya suke akwai wasu makusanta na, daga bakinsu na samu labarin lallai ana bibiyarsu, da fari ban d’auki abun da mahimmanci ba saboda abunda ke tsakanin mu, amma a ranar da wata yar ajin su gimbiya Zafreen ta fad’a min ana shirin d’aukesu, sai na yi gaggawar tayar da hatsaniya dan na d’aukesu ba tare da hankalin kowa ya kai cewa su ne kawai aka rasa ba, sai dai kash ! Sarki Wudar yana da matuk’ar wayo da kuma mutane sosai, duk tsaron da nake ganin na ba wa gimbiyoyinmu saida ya d’auke mafi mahimmanci da tsadar.”

Nisawa sarki Musail yayi yana kallonshi yace “Kenan yanzu gimbiya Zafeera tana hannun Wudar?”

Jinjina kai yayi yace “Shakka babu.”

“Ta ina ya bi ya d’auketa a cikin gidan da kake ikrarin ka bata tsaro?”

Ya fad’a yana watsa mishi wani kallo, ba tare da alamar tsoro ko firgita ba yace “Na yi iya k’okari na wajen killacesu, saidai ko ma ta ya ya suka d’auketa a gidan nan na fi tunanin sa’ilin da sarki Wudar ya buk’aci mu keb’e ne ni da shi, to a lokacin mutanenshi suka d’auketa, ko kuma wannan d’an na shi.”

Jinjina kai sarki Musail yayi yace” Shikenan, zai gane yana tare da kadarata ma fi tsada da daraja a duniya.”

Da sauri Bukhatir ya kalleshi yace” Yawwa sarki na, ina so kayi iya k’ok’arinka wajen…”

Shiru yayi ya had’e maganarsa sakamakon kallon da sarki Musail d’in ya masa, sunkuyar da kan shi yayi yace” A gafarce ni.”

Wani malalacin murmushi sarki Musail yayi yace” Har yanzu ban ji zuciyata ta gama yarda da kai ba Bukhatir, kai ma nasan kana son ganin bayana, ka samu Zafeera kuma ka rabu da ita ta sauk’i haka, da wuya gaskiya.”

A ladabce yace” Ka yarda dani sarki na, babu hannu na a b’atanta, hasalima sanda sarki Wudar ya zo ya so yi min tayin gimbiya Zafeera da duk abinda ya mallaka, amma na nuna mana darajarta ta wuce haka.”

Wata yar dariya yayi yatsare shi da ido yace” Amma me ya kai shi gidanka a ranar data kasance tana gidanka?”

Kura masa ido yayi yace” Iyeh?”

Wani kallon firgitarwa Dhurani ya masa yace” Aka ce me ya kai shi gidanka a wannan lokacin? Wata k’ulalliya xe a tsakaninku ?”

Girgiza kai yayi yace” Kamar yanda na fad’a maka yana da mutane da dama da suke masa lek’en asiri, kar ka k’aryatani idan har na fad’a maka a masarautar nan ma yana da yan sa ido, dan ta hakane ya samu cikakken labarinta.”

Kallonshi yayi kamar zai hango gaskiya a fuskarshi sai kuma yace” Na yarda da abinda ka fad’a yanzun, amma Bukhatir…”

Ya fad’a yana mik’ewa tsaye ya d’ora da” Alamu sun nuna a matse kake da son ganin an samo gimbiya Zafeera, shin idan aka yi hakan me ye tukuicinka kai?”

Gaba d’aya gabansa ya yanke ya fad’i ya shiga tunanin abinda zai fad’a masa, amma yanda ya tsareshi da ido yasa dole ya sunkuyar da kai yace “Farin ciki ma ya wadace ni idan har d’iyar yar uwata ta fito a hannunshi cikin k’oshin lafiya.”

Dariya sarki Musail ya bushe da ita kamar wani mahaukaci ya dinga gaggab’awa, da k’yar ya tsagaita kuma kamar ba shi ba ya kalli Bukhatir fuska a hade yace “Shikenan, zamu gani.”

Juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya ba tare daya juyo ba yace “Ba dan kar ka fita kana fad’in ban iya tarban bak’i ba, da ko ruwa ba zan ba ka ba Bukhatir dan nasan manufarka a kai na, amma karamci na ya isa insa a wadataku da abinci ko dan labarin daka siyar min.”

Da mamaki Bukhatir ya kalli k’eyarsa cike da takaicin wulak’ancinshi, wato ya ma d’auki abinda ya fad’a masa a matsayin labari har kuma ya siya? Sarki Musail ne ya katse masa shirunsa sanda ya juyo a hankali ya kalleshi yace” Ya suke? Suna cikin k’oshin lafiya?”

Wani kallo Bukhatir ya mishi yana ji kamar ya mik’e ya shak’eshi, wallahi da yana da sarauta a lokacin babu abinda zai hanashi d’urawa Musail ashar saidai duk su k’one a nan, iyayen Juman fa yake tambayarshi, shi bai san komai ba dangane da yanda aurensu ya kasanxe da Juman, amma dai tabbas ya fahimci akwai barazana a ciki wacce ita ce ke d’awainiya da iyayenta har yanzu, tunda ya d’auketa daga garesu shekara ashirin da bakwai har yau bata tab’a taka k’asar Egypt ba ko da sunan taro bare da niyyar ganin mahaifanta, hakazalika su ma basu tab’a yunk’urin kawo mata ziyara ba, tsufa ya cimmu su sosai amma damuwarta ita ce ta k’ata tsofar da su, dan wasu lokuta har k’aura sukeyi daga masarauta su ware kansu gefen gari su hana kowa zuwa inda suke.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button