MUTUM DA DUNIYARSA 2

*_????HASKE WRITER’S ASSO…._*
*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_Ya rabbi kabani ikon fad’ar abinda zai amfanar da al’ummarka, ka tsare harshena daga fad’ar abinda zai cutar daku da ni baki d’aya._*????????????
_Ya ALLAH ka gafartama mahaifina abin alfaharina da dukkan y’an uwa musulmai da suka rigamu kwanta dama????????????_
*_Wannan littafi tukuycine a gareku my sweet sisters, ina gidiya da karamcinku gareni, alkairin ALLAH yakai gareku a duk inda kuke._*????????????????
_Billy s Fari_
_Ummu Basheer_
_Fareeda Musa sweery_
_Ai’sha Manshat_
_Hafsat writer d’in Hafiz_
__________________________________
*_[2…..]_*
……………. Zakari dai yataho da Yagana kano cikeda farin ciki, sunkumazo sun zauna lafiya har ALLAH yabata ciki itama, a lokacinne kuma yahaya shima yadawo kano suka cigaba da kasuwancin atanfofi da shaddoji shida d’an uwansa Zakari.
To a wannan Karon dai Yagana ta Haifa masa Namiji, wayyo zokaga murna da tsalle da shirin suna Na bajinta, ragoma biyu aka yanka kuma manya-manya. Ansha shagalin suna yaro yaci suna Nuhu. Sai dai kash bayan suna da kwanaki uku yarasu, wannan Abu yasaka Zakari takaici, harda kukansa rurus, kaikace wani babban mutumne yarasu.
Babu dad’ewa Yagana takuma samun wani ciki, Zakari ya shiga tattalin ta kamar zai maidata a ciki, dan a ganinsa Namijin za a kuma Haifa masa. Sai dai kuma shi Ubangiji babu mai