Hausa Novels

Lu’u Lu’u 24

 

D’oraw yayi da “Kin tabbatar kina lafiya? Babu wani abu daya faru?”

 

Amsawa tayi da “E yallab’ai.”

 

Jinjina kai yayi yace “Shikenan, yanzu ya maganar alk’awarinmu?”

 

A tak’aice cikin jin ya fara hawa mata kai tace “Zamuyi magana, zan sake kira anjima.”

 

D’if ta yanke kiran tana jan tsaki a zuciyarta tace “Kaga jaraba, me zanyi da kai ni kuma tsofai tsofai da kai.”

 

K’arasawa tayi ta shige ita ma ta samu hadimar bakin k’ofa tana jiranta, tana zuwa ta kalleta tace “Ki kaini wajen sarki.”

 

Da sauri ta kalketa jin wai ki kaini wajen sarki, rusunawa kawai tayi ta nufi hanyar da zata sadasu da shi d’in gabanta na fad’uwa dan bata san me zai mata ba idan har baya buk’atar ganin kowa ta kuma rakata gareshi d’in.

 

Saida suka jira a bakin k’ofar wani dogari ya musu iso, jim kad’an ya dawo ya ba wa Ayam d’in umarnin shiga abisa yarjewar sarkin, tana zura k’afarta akan wani mahaukacin tattausan carpet ta lumshe ido, wani irin sanyi ne ya ratsata tare da ni’imtaccen k’amshi ga wani irin shup shup da d’akin yayi, tana k’arasa shiga ta wara ido tana kallon ko ina, a take idonta suka hasko mata hoton mutanen da ta gani yanzu, wanda dayawa daga ciki kana kallonsu zaka san talauci ya musu katutu, amma dubi irin daular dake cikin gidan sarautar nan, ka rantse da Allah arzikin duk duniya aka tara a cikin gidan.

 

Jin bata ce komai ba sai kalle kalle take yasa sarki Musail gyara zamanshi yace “Ina jinki gimbiya.”

 

Da sauri ta dawo da hankalinta kan shi tana motsa bakinta a hankali tace “Amm..Pah, dama ina so ne zamuyi magana.”

 

D’ora k’afa d’aya kan d’aya yayi ya d’auki kofin glas d’in gefenshi da abun sha a ciki kalar ja ya kurba sannan yace “Ina jinki, zauna.”

 

Inda ya nuna mata ta zauna ta kalla sannan ta kalli kofin daya aje gefenshi, kai tsaye dai bata ce barasa bace, amma dai ta d’an ji tana shakku duba da kwalbar data gani zungureriya a ajiye, a hankali ta k’arasa ga kujerun na alfarma royal da kula k’irar Italy, zaunawa tayi kamar akan k’aya sannan ta kalleshi, ganin ya sakar mata murmushi ya sa ita ma ta saki murmushin.

 

Da fara’a ya sake fad’in “Fad’i mana gimbiya ta, ina jinki.”

 

A nutse cike da kunya ta fara alama da hannunta tana fad’in “Pah dama magana ce akan mutanen da suka zo gani na, sun zo da buk…”

 

D’aga mata hannu yayi yace “Gimbiya Zafeera, su ba mutane ne kamar kowane ba, talakawa zaki ce idan kina so na gane, ki dinga banbantawa.”

 

Baki sake ta kalleshi sai kuma ta jinjina kai tace “To Pah, dama shi ne suka fad’a min ruwa ma da suke sha su talakawa siya suke, bayan kuma d’aya daga cikin magabata ne suka samar musu da su dan su sha kyauta, amma yanzu wasu ne suka mayar da hakan kasuwanci.”

 

Irin kallon daya tsareta da shi yasa ta sunkuyar da kai, a dak’ile yace” Yanzu da kike fad’in duk wannan, me kike so na yi a kai?”

 

Cikin rawa da jikinta ya fara na tsoronshi da kwarjini yasa ta d’an muskuta tace” E to…ina ganin…idan..”

 

Sake d’aga mata hannu yayi yace” Dakat Zafeera, wa ya kitso miki duk wannan tsirfar da kika zo yanzu kike kora min? Yaushe kika zo nan d’in da har kika fara fahimtar matsalolin mutanen garin nan? Me kika sani? Me kike tunanin zakiyi?”

 

Yunk’urawa yayi ya mik’e tsaye tare da nunata yace “Kina ji ko, ba neman matsala bace ta kawoki nan, kin zo had’uwa dani ahalinki ne ba had’uwa da k’orafe k’orafen jama’ar gari ba.”

 

Komawa yayi ya zauna tare da nuna mata k’ofa yace “Zaki iya tafiya.”

 

Kamar zata fashe da kuka ta ske kallonshi tace “Pahh…ka ce zan had’u da Mah, kuma na ga har yanzu…”

 

Cikin jin haushi da tsawa yace “Kai! Wai me yasa kike da shan kai ne? Dama haka kike? Haka banzayen bayin nan suka raineki ko? Ki wuce ki bani wuri idan nasa an fito da ita zan sa a kiraki.”

 

Mik’ewa tayi tsaye ta kalleshi, ita bat1 gusa ba ita bata sauke idonta ba, k’ura masa ido tayi tana kallo kamar mai son tsaorata shi.

 

Wani d’ar d’ar ya fara ji zuciyarshi na yi har da harbawar da baisan dalili ba, sai ga sarki Musail a gaban ‘yarsa yana ta sissine kai, yana so dole ya kalleta ido cikin ido ya daka mata tsawa ta bashi waje, saboda ya nuna mata iko da izzarshi, amma kuma wani tasiri dake cikin idonta da suka ninka na shi kwarjini yasa dole yake kakkawar da na shi kamar mai jin kunyarta, gaba d’aya sai ya duburburce ya rasae zaiyi.

 

Ayam ma data fahimci haka sai ta ji ba dad’i ganin yanda mahaifinta ke mata, gyara tsayuwarta tayi tare da d’auke idonta daga kan shi, sanyaya murya tayi a nutse cikin ladabi tace “Ina so a fito min da sarauniya Juman, na zo ne dama saboda ita kuma idan na tabbatar da abinda nake son tabbatarwa zan bar nan da ita, ba sarautarku ta kawoni nan ba, saidai akwai abu d’aya da bana yarda da shi shi ne, *rashin adalci*.”

 

Juyawa tayi a tsanake ta dinga takunta har ta fita a falon na shi, yanda ya idonshi suka kakkafe ya bita da kallo kamar ya ga gawa, rufo k’ofar da akayi ne ya dawo da shi hayyacinshi, a zabure ya lalubo wayarshi dake kan d’aya k’aramin teburin gefenshi ya danna wasu lambobin, ana d’agawa sarki Musail yace “…

 

 

 

 

*Alhamdulillah*

The post Lu’u Lu’u 24 first appeared on 2gNovels.com.ng.

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button