Lu’u Lu’u 30

Cikin k’asaita ba tare daya d’auke ido daga gareshi ba yace “Waye kai?”
Fuskarshi babu alamar rusunawa, idonshi tsaf suke kallon cikin na sarki Musail wanda ba kowa ke haka ba, fuskarshi babu alamar ladabi ko zai girmamashi, a gadarance ya furta “Umad.”
K’ank’ance ido sarki Musail yayi yace “Ba sunanka na tambaya ba, waye kai na ce?”
Da sauri Haman dake gefe a tsaye tun sanda Ayam ke burususuwa tana fad’owa ya mik’e ya matso, cikin ladabi da girmamawa sam ya ma manta da tsarin da suke a kai yace “Yallab’ai, shi ne ai abo…mai tsaron lafiya ta.”
D’auke kai yayi ya kalli Haman d’in yana yatsina fuska, kallo ya k’are mishi sai ya ga indai ba wani abu ba kuma, a zahiri dai kam sam Umad bai yi kama da wanda zai zama abinda Haman d’in ke fad’a ba, duba da wasu b’oyayyu da kuma bayyanannun yanayi dake tattare da Umad.
Da sauri sauri Zafreen ta fito daga d’akinta hannunta rik’e da waya, tana zuwa ta tsaya cak tana kallonsu tace “Pah, me yake faruwa a nan?”
Kafin ya bata amsa kuma ta kai kallonta kan Umad, da wani irin zumud’i ta nufeshi bata tsaya komai ba ta fad’a jikinshi ta kwanta tayi luf da dariya a fuskarta tana fad’in “Yallab’ai, kai ne a nan ma?”
D’agowa tayi daga jikinshi ta kalli fuskarshi yanda yayi sororo da al’ajabin dama arharta har ta kai haka? Cikin farin ciki tace “Yallab’ai ni ka biyo ko? Na sani da ma kai ma kana so na.”
Zura hannunta tayi cikin na shi hannun ta mak’ale masa kamar za’a rabasu, Juman kallonta take da mamakin irin yanda ta ballagazar da kanta haka, kamar ba wannan mai izzar da d’agawa ba? Gashi babu kunyar kowa haka take tsaye da kayan jikinta, farin wando na jeans iya cinyoyinta da riga kalar pink mai siraran hannaye, duk da kyanta ya bayyana da kyakyawar surarta, amma dai babu kimarta a idon masu kallonta haka kuma darajarta.
Tunda ta fad’a jikinshi Ayam ta ji fad’uwar gaba tare da jin wani haushi ya taso mata da takaici, har saida ta kasa b’oyewa ta ja d’an k’aramin tsaki ta d’auke kai daga kallonsu tana yatsina fuska, haka kawai abun ya b’ata mata rai har tana jin da zata samu damar keb’ewa da shi a yanzu data tuhumeshi akan me da ta rumgume shi bai tureta ba? Bata sake kallonsu ba saida ta ji Musail yace “Ina kika san shi?”
Cikin zumud’i da rashin kunya tace “Pah ai a makarantar da na je a nan yake koyawa.”
Wani kallo Dhurani ya masa yace “Idan kuma malami ne kai, ta ya ka zama mai bashi tsaro?”
Wani kallo ya wurgawa Dhurani da alamar b’acin rai yace “Aikin gwamnati na ke, duk wanda ya tari gabana zan yi.”
K’ura masa ido Juman tayi ta kasa d’aukewa har saida murmushi ya sub’uce mata, sak kallon yayanshi take masa Urab, hakan yasa har ya fahimta ya d’an karkata idonshi ya kalleta, cike da kunya da girmamawa ya rusuna idonshi tare da kanshi a ladabce yace “Barka sarauniyata.”
Sake murtuke fuska sarki Musail yayi ganin sai matarshi ya sakar ma fuska amma shi ya maidashi kamar wani sakarai ma, jinjina kai yayi a b’oye sannan ya kalli Haman yace “Sannu da zuwa.”
Rusunawa yayi ace “Barka yallab’ai.”
Muryar Juman ce ta dawo dasu da ta kalli Umad tace “Sannu ko?”
Jinjina kai yayi a ladabce yace “Sannu ranki shi dad’e.”
Yatsina fuska sarki Musail yayi yace “Mu je mu ci abinci.”
A sanyaye Ayam ta mak’ale kafad’a tace “Ni dai na k’oshi.”
Juman ma sama da k’asa ta kalleshi tace “Ni ma haka.”
Hannun Ayam ta kama zasu bar wuri ta kalli Umad tace “A ci lafiya.”
Hanyar masaukin Ayam suka nufa inda sarki Musail ya bisu da kallo, a ciki yayi k’wafa alamar zku sani sannan ya nufi wajen cin abincin ba wai dan yana buk’ata ba sai dan bak’inshi.
Rankayawa sukayi kan teburin Umad na ta k’ok’arin b’amb’are hannunshi cikin na Zafreen amma ta rik’e gam, har saida suka isa duk suka zazzauna, tsaye ya so yi dan sake k’ara fahimtar komai na gida da takon kowa, amma sai Zafreen ta zaunar da shi da k’arfi har saida Musail ya kalleta yace “Ke!”
Sai kuma ya d’auke kai yana girgiza kan shi, haka aka zuzzuba abincin kowa ya fara ci.
Cokalansu kad’ai ke k’ara a wurin, cikin siririyar murya Zafreen ta kalli sarki Musail tace “Pah, kasan na jima ina fad’a maka ban samu wanda ya dace dani ba a garin nan?”
Zuba mata ido yayi shi dai bai ce komai ba, d’orawa tayi da “To yanzu na samu, wannan ne.”
Ta k’arashe tana nuna Umad da ka rantse baya jin yaren ta, duk da dai d’in gaskiya bai cika jin yaren slovaque ba, amma dai yana ji jefi jefi saboda yanayin aikinshi da shige shige da kuma sa kai.
Haman a dake ji jefi jefi da Khatar da kuma Adah duk kallonta sukayi dan Dhurani tafiyarshi yayi bai tsaya ba, sarki Musail ma kallonta yake yi kamar ya wanka mata mari, haushin hakan yasa bai ce k’ala ba sai Haman daya kalla a nutse yace “Me ye sunanka?”
A ladabce ya amsa da “Ranka shi dad’e sunana Haman.”
Jinjina kai yayi irin na dattawa yace “Haman Abraham Joshua kenan?”
Gyad’a kai yayi alamar e, lumshe ido yayi alamar gamsuwa, a tsanake ya sake furta “Me ye aikinka? Kuma a ina ka fara sanin Zafeera? Me kuma ya sa kake son aurenta?”
Cikin d’ar d’ar Haman yace “Yallab’ai na kammala karatu na, inda nake da burin mahaifina ya sama min aiki a babbar ma’aikata, Zafeera kuma mun fara had’uwa ne a Giobarh, saidai ban mata magana ba a saida na fara sanin wacece ita, ina kuma so ne na aureta dan ina sonta.”
Wani hamshak’in murmushi sarki Musail ya saki yace” Bayan son da kake mata, sai kuma wane dalili?”
A hankali ya karkata ya saci kallon Umad da shi ma ke kallonsu ko abincin baya ci, sai kuma ya kalli sarki Musail yace” Saboda yar babban gida ce, ita ce ta dace ni.”
Sauk’akk’en murmushi ya saki ya d’an fara tsakurar abincin yana fad’in” Mu ci abinci yanzu, nan da awa biyu zan had’aku da ita dan ku tattauna, idan kun fahimci junanku mahaifinka na zuwa nan ranar d’aura muku aure za’a saka.”
Wani k’ayataccen murmushi Umad ya saki a ranshi ya ayyana” Lallai ma, ku gama duk shirin ku, na wa ne zai yi aiki a k’arshe.”
Haka suka ci gaba da cin abincin da tattaunawa tsakanin Haman d’in da sarki Musail, bayan su babu wanda ya saka musu baki banda Zafreen dake ta k’ok’arin d’aukar hankalin Umad d’in tana ta washe masa baki.
*Alhamdulillah*
The post Lu’u Lu’u 30 first appeared on 2gNovels.com.ng.
[ad_2]