BuhariGwamnatin TarayyaLabarai

Kokarin Buhari Na Fitar Da Mutum Miliyan 100 Daga Talauci: Gwamnatin Tarayya ta shirya kwashe almajirai akalla 1,000 a kan titin Abuja.

Hukumar da ke kula da babban birnin tarayya (FCTA) ta shirya kwashe almajirai akalla 1,000 a kan titin babban birnin kasar.

Mukaddashin Daraktan Sashen Kula da Jin Dadin Jama’a na Sakatariyar Cigaban Jama’a, Alhaji Sani Amar ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Alhamis a Abuja.

Amar ya ce matakin wani bangare ne na kokarin tabbatar da ganin an cimma kudurin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci.

“ Karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Dakta Ramatu Aliyu, ta ba da umarnin cewa a wani bangare na wa’adin da shugaban kasa ya ba wa ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci, muna sanya Almajirai horo kan sana’o’i da ilimi.

“Hakan zai sa su zama masu dogaro da kansu da kuma tabbatar da cewa su ma sun zama ‘yan kwadago, domin mabarata da Almajirai ba su da wani abu da ya wuce zagayawa da neman abin da za su ci.

“Don haka muka zagaya cikin gari muka gano wasu makarantun islamiyya da ke kusa da birnin, don mu fara.

“Muna iya fitowa da Almajirai 120 tare da sanya su sana’o’i daban-daban, kamar aikin kafinta, yin takalma da zane-zane.

“Yayin da lokaci ke tafiya kuma bisa ga manufarmu, za mu dauki sama da Almajirai 1,000 horon koyon sana’o’i daban-daban.

“A karshen horon da suka yi, za a gudanar da biki inda za a bai wa kowannen su kayan aiki da kudi.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button