Hausa Novels

Lu’u Lu’u 45

K’us k’us k’us kawai ke tashi ana yi ana kallon kallo ana jiran fitowar ta, dayawa sun zo ne dan su ji me za ta fad’a haka me mahimmanci da sai yanzu za ta fad’eshi bayan mahaifinta yanzu aka kaudashi? Shin sabon tsarin da suke tunanin zata kawo musu ne za ta fara da gaggawa haka? Ko kuma dai game da rasuwar mahaifinta ne ?

Da gudu gudu fadawan suka fara shigowa suka layu a ind zata fito ta tsaya sun k’ame sos1i sun kuma cije ba wasa, hakan yasa kowa yayi shiru ya kuma nutsu aka zu a ido kan k’ofar da suka shigo.

K’was ! K’was! Sautin takalminta masu tsini suka shaidawa kowa shigowarta, girman kujerarta da d’aukakar da Allah ya bata yasa kowa dake nan hatta da Juman dake tsaye tana hawaye a jikin Bilkees, da ita kan ta Bilkees da Kossam sai da suka rusuna tare da masu rusunawa, wani irin kwarjini ne Allah ya bata, musamman yau data fito fuskar nan a had’e, dole duk wani dake k’aqa da ita ya bata girman da Allah ne ya mallaka mata.

Tsaye tayi inda fadawan suka gyara tsayuwarsu su ma kamar yanda take fuskantar mutane, kowa da kowa taje kallo kafin ta d’an gyara muryarta a nutse ta had’e tafukan hannayenta tace “Gaisuwa a gareku.”

Amsawa sukayi da “Gaisuwa sarauniyar mu.”

Yanda suka amsa kamar gurin zai tsage biyu, yanda ta sake nutsuwa tana kallonsu yasa su ma suka yi shiru suka maida hankalinsu kan ga.

A nutse cikin dattako da k’arfin hali tace ” Jama’ar Khazira, na san kowa na cike da son jin dalilin da ya sa na tara wannan taron yanzu da gaggawa, ba komai yasa na kira taron nan ba sai wasu abubuwa da ke kan faru.”

Gyara tsayuwa tayi ta kallesu da sigar mamaki tace” Shin mutanen Khazira zuciyarku ta mutu ne da har wasunku suke bacci da mafarkin ni Zafeera zan zo na canza muku rayuwarku? Wacece ni? Me kuka d’auke ni? Ni ma mutum ce kamar ku, me yasa da aka zauna aka fad’a muku tatsuniya a kai na kuma kuka yarda? Ba kowa ba ce ni kuma ban ga wata tsiya da zan iya tsinana muku ba, labarin zuwana duniya ya isa kunnen masu ci da ceto ne a cikin kowane irin addini tare da tasirantuwa kan son d’aukar fansa, hakan yasa aka k’ullawa iyayena mak’ark’ashiyar da su kansu suka yarda zasu haifi zab’abb’iya, ku ji da kyau, ni nan na fad’a babu wani zab’abb’e bayan fiyayyen hallita wanda ba’a haifa ba ba kuma za’a haifi kamar sa ba.”

A sanyaye muryarta na rawa tace” Duk wasu abubuwa da nake yi ko ake gani a tare dani ba komai ba ne fa ce k’udurcewa da kukayi a ranku lallai ni d’in zab’abb’uyarku ce, idan har akwai wani abu da zan iya cewa ubangiji ya min da ba kowa ya ma ba, ba zai wuce canza yare da na ke yi ba musamman idan raina ya b’ace ko kuma na shiga mamaki, bayan wannan babu wani abu daya zama daban da na ku yan uwa na, da wannan nake kira gareku a matsayinku na mutane masu daraja, ku mik’e tsaye ku saka yayanku su yi karatu, ta hakane ci gaban da kuke tsammanin zan kawo muku ni kad’ai, bilyoyin matasa irina zamu kawo muku shi, ku kashe Zafeera a zuk’atanku, ku manta da wata Zafeera a shafin zuk’atanku, ku dage sannan ku maida tunaninku ya zama yanda zaku kawo ci gaba da hannayenku a k’asarku, jiran wani ya kawo maka ci gaba shi ke mayar da kowace k’asa baya, amma idan kai mai k’asar kayi tunanin ciyar da k’asar ka gaba, to za ka cimma nasara.”

Gyara tsayuwa ta sake yi tace” Jiya zuwa yau ne kawai ‘ake sarauniyar Khazira, kafin mahaifina ya bani mulkin nan na fad’a masa bana sha’awarsa, dan na fi buk’atar siyasa akan sarauta, a yanzun ina sarauniya ne kawai dan na fad’a muku ku tsaya da k’afafunku sannan ku tsayar da shugaban da kuka ga ya cancanta ya mulkeku, amma ni Ayam…zan ajiye mulkin nan sannan na tafi tare da *mijina* dan na masa bauta a gidan aurenmu, ina fata ba zaku fahimce ni ba daidai ba? Sannan ba zaku kirani marar adalci ba, na sani ta ko ina wani babban matsayi ne ke bibiyata, amma dai mulkin Khazira ya fi k’arfin iyawar Ayam, duba da yanda mahaifina ya rayu a tsakanin makirai, wanda hakan yasa ban rayu tare da su ba sannan aka dinga farfagandin cewa mahaifina yana son kashe ni, sannan ni ce zan zama silar mutuwarsa…”

Hawaye ne suka sauko a kumatunta ta d’an sunkuyar da kai, jima kad’an ta d’ago ta share hawayen tace” Na yarda a wannan karan, na yarda ni ce zan zama silar rasuwarsa, tunda gashi duk ni na jawo komai….”

Fashewa tayi da kuka ta sunkuyar da kanta, a hankali ta d’auke kambun da yake kanta ta d’ora akan farantin da wata hadimar ta matso tana fad’in” Ba zan iya rik’e wannan ba, gashi nan a ba wa wanda ya cancanta.”

Yanda abun ya daki zuciyar kowa yasa talakawa wasu suka fara kuka suna fad’in” Hugabarmu kar kiyi saurin d’aukar wannan matakin, zamu so ki mulke mu kamar yanda marigayi yayi mahaifinki, zamu zama masu biyayya a gare ki.”

Girgiza kai tayi a sanyaye tace” Idan har akwai wani abu da zan iya yi muku a yanzu bai wuce na baku shawara kan ku samu madogara, ku samu ak’idar data dace da ku, nufina ku shiga addinin musulunci, dan shi ne zai haska muku rayuwarku har ku kai ga gacin da kuke da buk’atar kai wa.”

Wasu ne suka amsa da” Addinin musulunci?”

Jinjina kai tayi tace” Addini na, addinin mahaifiyata, addinin mahaifina kuma addinin mijina, duk da mahaifina yana addinin musulunci, bai samu damar janyo ra’ayinku ba saboda magauta, amma ni ina mai baku shawara da in kun ji zaku iya ku shiga, dan addini na ba addini bane da ke tilasta wanda baya ra’ayi shi ga, sharad’in shi dai ne idan ka shiga baka fita, idan kuma ka fita bisa bayar da mashirmancin dalili to hukuncin kisa na hawa kan mutum.”

Cire sark’ar nan tayi ta mik’awa wata hadimar, sake had’e hannayenta tayi za ta musu sallama, sai kanta ya sara da k’arfi sosai, d’an lumshe idonta tayi sai kuma ta bud’e ta kallesu da kyau, a sanyaye sosai yanda ba kowa ya ji me ta ce ba tace” Na barku lafiya.”

Bud’e ido tayi sosai ta taka k’afata ta kuma juya da niyyar barin wurin, mugun jiri ne ya kwasheta sai kuwa ta sulale tayi k’asa ta fad’i, musulman ciki ne suka furta” Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un!”

Inda hadiman dake kusa da ita suka rufa a kan ta, da gudu Juman da Kossam du sukayi kanta.

*Umad* dama bai halarci taron ba yana d’akinshi yana kallon komai ta na’ura saboda tunda ya ji maganar taron hankalinshi bai kwanta ba, dan haka ya dasa na’urar d’auka yake kallo ta computer, ganin haka kuma shi dai bai ga alamar harbi ba haka kuma ba alamar wani abu daya faru.

Da mugun saurin da bai san yana da shi ba ya mik’e da gudu ya fito a d’akin ya nufo d’akin taron, yana zuwa ya ratsasu ya wuce ya tallabeta ya mik’e, da sauri su Juman duk suka rufa masa baya suka bi bayanshi har saida ya kai ta d’akin Juman din ya sauke a kan gado, da azama ya kalli Juman yace “A kira likita.”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button