MADADI 1-END

MADADI Page 1 to 10

Halisa ta fusata sosai hannu ta fitar ta tsinka mata mari tana d’ura mata ashar! sai ambato  sunanan Baba malam take tana zagi! Naja’atu ta dinga kuka tana fad’in “Allah ya isa ba kakana kike zagi ba naki kike zagi!

Halimatu tazo tana doke bakinta cikin ‘bacin rai tace” Ashe baki da kunya Naja’atu.” Tana kuka tace”Mamma kina ji fa tana zagin Baba Malam me yayi mata? wallahi sai na fad’awa Abbanmu.” Kai tsaye ta nufi dakin da yake kwance yana bacci! Halisa da Halimat suka bita da kallo cike da mamaki! Halisa mamakin yarinyar take na mayar da uban wasu nata komai akayi sai tace Abbanta ko a gidan ubanwa ya zama Ubanta oho.

Yana tsaka da bacci yaji kukanta a kansa, ya bude idonsa da sauri! yana kallonta a tsaye a kansa tana goge fuska hawaye wani na sake zubowa, mikewa yayi zaune ya kamo hannunta ya zaunar kusa dashi.

Cikin tausasawa yace.”Waye ya saki kuka.” ? Cikin shashsheka tace”Gata can Anti Halisa muna wasa da dariyarmu tazo tana hantarar mu wai sai mun tashi mu bata guri zatayi kallo, shine dan nayi magana ta mareni har da zagin Baba Malam.”

Ransa ya ‘baci! Yace.” Kan wane dalili zata tashe ku a guri kuna wasa? saboda za tayi kallo sai ta hantareku! hannunta ya ri’ke suka mike a tare suka fita palon 

Halisa da Halima na tsaye sai musayar yawu suke Halisa na fad’in “Wannan iskancin da ‘kanwar taki take yayi yawa haka kawai saboda samun guri ta mayar da uban wasu nata to tun wuri ki fada mata ba ubanta bane kada ma ta dauka tanada gadonsa.”

Halimatu ta bude baki kenan za tayi magana ta hango fitowarsu yana rike da hannunta, Halisa ta kallesu ranta idan yayi dubu ya ‘baci! Hura hanci ta shigayi tace”Au! zuwa tayi ta taso ka daga baccin.”?

Ya ‘bata fuska sosai yace.”Koda bata tasheni ba dama dai-dai wannan lokacin nayi niyyar tashi, shin me yaran nan suke miki kullum kike matsa musu bakya barin su su huta.”!

Halisa ta rik’e bakinta cikin mamaki take dubansa! Yace.”Magana nake miki.” Ganin yanda yasha kunu ne yasa ta sassauta murya saboda tasan halinsa sai tace”Kawai dan nace su tashi su bani guri zanyi kallo shine fa yarinyar nan ta hau yi min rashin kunya harda zagina.”

Da sauri tace”Ni wallahi sharri tayi min ban zageta ba.” Halisa tace”To nayi miki karya ko.” Zumbura mata baki tayi ta murguda mata shi! Halisa ta shiga jijjiga kanta tana mamakin saken da yarinyar ta samu a gurin maigidan, kauna da son da yakewa yarinyar ta lura ko ‘yayansa bayayi wa.”

Yace.”Kawai saboda zaki zauna kiyi kallo sai ki tashesu mai suka tsare miki! bana so ki sake hantarar min ‘yaya duk wani abu da nake nema a duniya saboda su nake nemansa, kafin Allah ya bani sai da na cire tsammani dan haka dole ne na kyautata musu dan bana son abinda zai ‘bata musu rai! duk abinda suke su zasuyi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kamar yanda kema kikeyin abinda kike so.”

Halisa takaici kamar ya kasheta, har ta bud’e bakinta zata ce “Ai ita wannan d’in da kake magana a kanta ba ‘yar ka bace…….Sai kuma ta sanja shawara, tace” Shikkenan me ‘yaya nima Allah ya bani.” Tana ‘kare maganarta sai ta fashe da kuka ta nufi daki….Jikinsa ne yayi sanyi kuma, Halimatu ta kalleshi murya na rawa tace”Haba Abban Naja’atu ba haka ya kamata ka yanke hukunci ba! kasan kowaye akayi wa haka dole yaji rashin dadi, yarinyar nan Naja’atu itace tayi mata rashin kunya kamata yayi ka fara hukuntata tukkuna.”

‘Dan ya mutsa fuskarsa yayi kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa, hannun Naja’atu dake cikin nasa ya saki ya juya ya nufi dakin da Halisan ta nufa 

Ita kuwa Naja’atu bata so hakan da yayi ba taso ya kyaleta taje tayi kuka taji ciwon a ranta kamar yanda take yini tana ‘kuntatawa mamanta rai to itama yau ta d’and’ana taji.

Halima ta rufeta da fad’a kan abinda tayi tace”Wallahi duk sanda na sake ganin Kinyi mata tsaki sai ranki ya ‘baci ko an fada miki sa’arki ce.” ? Kuka tasa ta nemi guri ta zauna tana fad’in “Mama kina ji fa tana zagin mahaifinki Baba malam Kinyi shuru dan nayi magana sai kice nayi laifi .”

Jikinta a sanyaye tace”Dan ta zage shi sai me? ni nasan ba Ubana ta zaga ba nata take zagi saboda haka na fada miki babu ruwanki da ita har mu bar ‘kasar nan.” Shiru tayi kawai ba tace komai dan gaskiya ita ba zata dauki cin kashi da wulakancin da Halisan keyi mata ba

 haka suka cigaba da zaman doya da manja tsakanin Halisa da Naja’atu babu sassauci kowa najin haushin dan uwansa, Naja’atu taci alwashi kan cewar duk sanda Halisa ta sake kuntatawa mamanta rai to itama sai ta ‘kir’kiri abinda zai janyo musu fad’a a tsakaninta da Abbansu, Halisa tunda taga take-taken Naja’atu da irin iskancin da take mata sai ta shiga taitayinta ta rage yiwa Halima wasu abubuwan na rashin arziki badan komai ba sai dan sanin matsayin Naja’atu da tayi a zuciyar maigidan nasu, tasan idan ta tsananta ranta ne kawai zai ‘baci a banza.

Sati biyu sukayi a kasa mai tsarki suka dawo gida, Likita ya d’orasu Akan magani, kan cewar in dai Allah ya nufa da akwai sauran rabo a junansu to zasu haihu………….Wata uku da dawowarsu Halisa ta samu ciki murna ta dinga yi tana adduar Allah ya zaunar mata dashi, to shima maigidan yayi farin cikin ganin cikin yayi wata hudu bai samu matsala ba, sai ya umarce data zauna ta daina aikace aikacen gida, mai aiki yace zai dauko mata, tace ya bari zata dauko ‘yar yarta sai ta dinga taimaka mata, aikuwa hakane ya kasance Unguwar

 Aisami

 ya kaita da kansa taje ta dauko Shamsiyya ‘Yar yarta budurwa ce ‘yar kimanin shakara goma sha hida ta girmi Naja’atu da shekaru biyu, Shamsiyya irin masu shegen iyayi ne gata mummuna amma saboda tsabar shafa mai tayi fari da haske! murna  sosai Shamsiyya tayi da zuwanta gidan Halisan tasan kafin ta dawo gidansu sai ta sauya  tayi ki’ba dan gaskiya ko zuwa gidan sukayi da ziyara basa dawowa ranar da sukaje sai sun kwana  dan har daukar kawayenta takeyi ta kaisu gidan tana musu iyayi kanwar mamanta na auran *Alhaji Abbas Dan kwagila*……..To cikin ikon Allah Halisa ta haihu kalau ta samu ‘ya mace sai dai ba haka taso ba  taso ta haifi d’a namiji dan gaskiya Mussadiq ya tsone mata ido. Ita kuwa Yaya Ramlatu har akayi suna cikin yada habaici take mussaman idan taga  Halimatu tazo gidan sai ta tsiri shige da fice tana sakin maganar da duk tazo bakinta……..”Duk cikin da ya haifi mace watarana shi zai haifi namiji Halisa ki kwantar da hankali gabadaya dangi munfi bukatar mu samu zuria dake dan haka tunda kin fara dasa ‘kwan ki a gidan Abbas to kiyi abinda kike so babu me ce miki don me.!! Ire-iren maganganun da Yaya Ramlatu keyi kenan Shamsiyya na taya ta, Halima bata ta’ba tanka musu ba abinda ya kawota takeyi ta tafi.

Ranar suna da kyar Abbah Abbas ya lalla’ba Naja’atu ta shirya ya kaisu, dan cewa tayi ita ba zataje ba bata da lafiya wanda shi da Halima duk sun san ‘karya take yi kawai rashin jituwar dake tsakinta da Halisan yasa tace ba zataje ba…….kwalliya sukayi sosai gabadayan su harshi angon ‘karni suna sanye cikin dakakkiyar shaddar galila mai kalar sararin samaniya(sky blue) sun yi iri daya da juna Halima da Naja’atu da Saddiqa! dinki iri daya ne a jikinsu doguwar riga ce wacce tasha uban stone work da aka kashe kudi gurin yin sa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button