MADADI 1-END

MADADI Page 1 to 10

Abbah Abbas shida Mussadiq sunyi iri daya cikin babbar riga da ‘yar ciki hularsu iri daya hakanan takalman su iri daya, agogo iri d’aya, sunyi kyau sosai dan kafin su fita sai da sukayi hotona sannan ya kira Salim dan  Yayarsa Ramlatu  a waya ce yazo ya daukesu…….Salim dan kimanin shekaru ashirin da biyar a duniya matashin saurayi mai jini a jiki d’an kwalisa ne sosai kuma yana kan lokacinsa dan babu abinda Abbah Abbas baya yi masa na rayuwa ya dauki yaron tamkar d’an cikinsa, shine ya tsaya masa kan karatunsa har yayi degree kuma ya d’ora shi kan harkokin kasuwancinsa Salim yasan  wasu daga cikin sirrinkan Abbah Abbas amma kuma bai san wasu ba, Salim tun kafin Naja’atu ta kai girman haka yake sonta yana so  su kammala secondary tukkuna ya tunkari Kawunsa da maganar tabbas yasan shi zai shige masa gaba gurin ganin ya mallaketa, amma dai duk da hakan yana ta kokarin kafa gwamnatinsa a gurin Naja’atun, itace take nuna masa bata gane me yake nufi ba.

Koda Salim yayi tozali da Naja’atu kasa nutsuwa yayi ya dinga kallonta yana sosa kansa ga wani shegan mirmushi a fuskarsa, Naja’atu ta ‘bata ranta tana kallon Abban nasu dake gyara babbar rigarsa domin shiga mota, murya na rawa tace”Abbah kace ya daina kallona.” Abba Abbas na gyara zamansa a motar ya kalli Salim yana d’an ‘bata fuska yace.”Kai bana son shashanci ka shigo mota mutafi na lura da kai tun d’azu ka damu yarinyar nan da kallo sai wani sosa kai kakeyi na fad’a maka ba zan baka itaba sai da amincewarta.” Salim yasa dariya yana kallonsa Yace.”Haba Kawu dube ni fa kaga ni da kyau! ni ba irin mazan da mata zasu ce basa so bane, ni nasan nan gaba kadan Ita dakanta zata furta maka ni take so.” Abbah Abbas na murmushi yace.”Ni dai na fada maka malam ka nemi yardar ta dan cikin ‘yayana babu wacce zanyiwa auran dole.” Salim yace.”Insha Allahu Naja’atu tawa ce.”  Mussadiq ya rike hannunsa da fadin”Nima ina so ka auri Yayarmu.” Rank’washin sa Naja tayi ya shiga motar yana kuka, Halima ta d’auka Abban nasu zaiyi mata fada mai yasa ta dakeshi sai taji yana cewa”Kai Mussadiq bana son rashin kunya ka tsokane ta ta hukuntaka kuma sai ka kama kuka.” Mamaki sosai ya rufe Halima! Girgiza kanta kawai tayi dan bata da bakin magana tana iya yiwa Naja’atu fad’a yace dan me shiyasa tayi shuru da bakinta, hakika kulawar da yake nunawa a kan ‘kanwartata tana burgeta haka nan suma su Baba malam suna jin dadi yanda Abbas din ya r’ike musu ‘yarsu tamkar shi ya haifeta, duk abinda zaiyi wa ‘yayansa shi yake mata wani sa’in ma har yana bambamta ta dasu gurin wani abun.

Gabad’aya Naja’atu kasa sakewa tayi a gidan sunan ganin yanda jama’a ke musu wani irin kallo wasu ma sai nuna su sukeyi, dalilin da yasa kenan ta zauna guri guda tana kalle kalle…….Halima kam kasa zama tayi ta mike ta shiga cikin mutane ana hidima da ita duk da irin kallon banzan da suke mata hakan bai sa ta koma ta zauna ba, ta kau da kai tana ta shiga jama’a cikin fara’a ana gaisawa da ita.

Tana zaune a palo wasu ‘yan uwan Halisa suka shigo suna she’ka dariya d’aya daga cikinsu tana fad’in “Ku tsaya kuga yanda kishiyar Anti Halisa take tafiya.” duk sai su katsaya suna kallonta, sai ta shiga cangala ‘kafarta d’aya tana cillata kamar yanda Halima keyi idan tana tafiya! Dariya suka kwashe da ita suna tafawa! Shamsiyya tace”Kuma wai a haka a nakashe take matar so a gurin miji.” Duk sai suka ri’ke bakinsu suna kallonta ‘karin bayani suke jira tayi musu! Shamsiyya ta bud’e bakinta za tayi magana taji saukar mari a fuskarta!

Naja’atu ce tsaye a tsakiyarsu tana zubar da hawaye itace kuma ta mari fuskar Shamsiyya! Wacce take gwada tafiyar Halimatu ta nuna murya na rawa tace.”Yanzu hallitar Allah kike gwadawa? Ke baki ji kunyar abinda kika yi ba Allah yayi hallitarsa yanda yake so kina gwada kuna dariya kema fa baki wuce Allah ya mayar dake haka ba.”!! Afusace Shamsiyya tace”Dan kutumar Ubanki  ta gwada d’in!  shegiya yar karoro! har ni zaki tsinkawa mari! lallai zan nuna miki nafi ki zafin kai!! kafin Naja ta ankara ta rufeta da duka! Sai sauran ma suka shiga taya ta suka rufar wa Naja’atu da duka har sai da ta durkushe a gurin!! Ihu! takeyi tana kokarin kwatar kanta….

Halisa ta fito daga daki a guje! jama’ar dake waje suka shigo palon suna tambayar abinda ke faruwa.

Shamsiyya tana hura huci! ta shiga fada musu karya da gaskiya. Yaya Ramlatu tazo ta tsaya a kan Naja’atu tana zaginta ta uwa ta uba! Naja’atu kasa motsi tayi dan ta daku sosai! Halima ce tazo ta kama hannunta ta mikar da ita, tana kuka itama tana kuka su Saddiqa da Mussadiq na kuka! abin gwanin ban tausayi! Ita kuwa Yaya Ramlatu kamar kara zugata akeyi ta tara mutane sosai sai aibata Halima da Naja’atu take da iyayensu kowa na tofin ala tsine a kansu! Halisa ganin abin ya kwa’be! yasa tazo tana bawa Ramlatu hakuri saboda tasan idan maigidan ya samu labarin abinda ya faru to babu shakka al’amura zasu ‘baci! dan rayukan kowa sai ya ‘baci! da kyar ta rarrashin Yaya Ramlatu tayi shuru taja tawagarta suka fita harabar gidan domin cigaba da rabon abinci………Halisa ta dinga yiwa su Shamsiya fada kan abinda suke kokarin janyo mata, dukan Naja’atu da sukayi yana nufin abubuwa da yawa a gareta hakan na iya barazana ga auranta, shiyasa bayan ta shiga dakin tasa Mussadiq ya kira mata Naja’atun! K’in zuwa tayi sai da Halima ta rarrasheta sannan ta shiga dakin.

Halisa ta kwantar da kanta tana fadin “Naja’atu kiyi hakuri kinji ko abinda su Shamsiyya sukayi miki kinga dai a gabanki na hukunta su kuma nayi musu fada dan Allah kada ki fadawa Abbanku.” Zum’bura bakinta tayi tace”To me yasa baki rama mun dukan da sukayi min ba! Ni wallahi bazan yarda ba sai na fada masa sun zageshi sun zagi Baba malam sun dake ni kuma sun kushe hallitar Allah.”

tana k’are maganar ta ta fita daga dakin, Halisa rakata tayi da kallo baki a sake.

Tana fita daga dakin ta dauki wayar Mamanta wani guri ta ‘buya ta kira numbarsa, ganin numbar Halimatu yasa ya dauka da sauri yace”Ranki ya dade yaya ina fatan komai lafiya.”? ai kawai sai yaji fashewar kukan Naja’atu a kunnansa! Ya mike tsaye  da sauri! Yace”Naja’atu lafiya kike kuka yi shuru ki fada mun abinda akayi miki?” cikin sar’kewa tana jawo numfashi irin na sharri ta shiga wassafa masa abinda ke faruwa a gidan sunan.” Ranshi idan yayi dubu ya ‘baci! Yace.”Daina kuka kinji ko? zan dauki mataki wato Halisa ta tara mutane ne dan ta tozarta ni! babu laifi ki  bawa maman taki wayar zamuyi magana.” Tana shashsheka da goge fuska tace”To.” Zuwa tayi ta kaiwa Halima wayar da fadin “Gashi Abbanmu zaiyi magana dake.” Halima ta fita daga cikin mutane ta samu guri tana amsa wayar, Jinsa a  fusace! yasa ta sassauta mirya tana so ta fahimtar dashi yaki sauraranta yace.”Zai turo Salim yanzu yazo ya daukesu ya mayar dasu gida ita kuma Halisa zata gamu dashi.” Kafin ma tace wani abu ya kashe wayarsa…..Kasa’ke tayi da waya a hannunta tana mamakin wannan al’amari! gabadaya idan Naja’atu zata fada masa magana baya tsayawa yayi nazari zai hau kai ya zauna, tabbas ba sune suke da laifi kan faruwar hatsaniyar ba, to amma yana da kyau yabi komai a sannu tasan halinsa da mugun zafin zuciya zai iya aikata abinda ba shikkenan ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button