MADADI Page 1 to 10

Aikuwa dai bayan watsewar taron suna da ya shigo gidan Halisa sai da ta fuskanci ‘bacin rai sosai dan cewa yayi ta ajiye masa ‘yarsa ta fice masa a gida tunda dama abinda ta shirya yi kenan shiyasa ta damu sai tayi taron suna dan haka ta ajiye masa ‘yarsa ta bar masa gida, kuka wurjan-wurjan ta dinga yi tana bashi hakuri tana kuma gaya masa yanda al’amarin ya kasance cewar ita sanda abun ya faru ma tana daki bata da laifi.
Jin tana ambatar sunan Shamsiyya a maganar yasa ya ‘kwala mata kira tana zaune a palo tayi tsuru tsoronta Allah tsoronta annabi kada yace ta bar masa gida, Da sauri ta shiga dakin, yace”Kece mai gwada yanda matata Halima take tafiya ko.”? Girgiza kanta ta shiga yi tana rantse-rantse! Yace.”Duk abinda kukayi wa Ubangiji ku dashi ne dan haka bana bukatar ganin ki a gida nan ki dauki kayanki ki tafi.” ai ta haihu babu wani sauran aiki yanzu.” Hannu ya zira cikin aljihu ya dauko dubu daya ya mika mata da fadin”Ki shiga mota.” Kar’ba tayi jiki a sanyaye ta fita daga dakin, zuwa tayi ta shiga hada kayanta tana kukan takaici taso ta zauna a gidan har sai ranar da Antin nata tayi ar’bain sai ta tafi amma mutsiyaciyar Yarinyar nan Naja’atu tasa an koreta……Abba Abbas bai bar gidan ba sai da ya tabbatar da cewar Shamsiyya ta bar gidan sannan hankalinsa ya kwanta ko sallama baiyi da Halisan ba yayi tafiyarsa.
Gidan Yaya Ramlatu ya nufa koda taga yanayin da yazo mata dashi sai tasha jin jikinta, ta shiga yi masa rawar jiki, ya dinga kallonta takaici kamar ya kashe shi, Ramlatu ta girma amma bata san ta girma kullum abubuwa take irin na marasa tunani, ganin yanda take rawar jiki a kansa ne yasa ya sassaura zuciyarsa ya shiga nuna mata illahr abinda takeyi take kuma tara mutane na wulakanta masa matarsa hakuri ta bashi kamar gaske tace insha Allahu ta daina……..Yaji dadi sosai hakan yasa ya zauna sukayi hira irin ta ‘yan uwantaka.
Fushi sosai ya shiga yi da Halisa duk domin ya nuna mata kuskuranta a ganinsa idan da bata bada goyan baya ba to babu wanda ya isa yaci zarafin matarsa da iyayanta, Halima ba tayi musu laifin komai ba amma sun dauki karan tsana da tsangwama sun dora mata.
*BAYAN SHEKARU UKU*
Lokacin Naja’atu nada shekara goma sha shida a duniya komai nata ya fito a zahiri macace doguwa mai fadin ‘kugu da cikar kirji bata da haske sosai amma ba za’a sata a layin bakake ba fatar ta mai kyau ce mai kuma wahalar samu, tana da kyau a fuska da jikinta wannan dalilin yasa bata fiye yin kwalliyar fuska ba, kuma bata sanya mayafi sosai tafi amfani fa hijabai saboda ta tsani kallon da maza ke mata a duk sanda zata fita babu hijab a jikinta takan fuskanci ‘bacin rai sosai! maza sun dinga kallonta kenan har da masu tsayr da ita, shima Abban nasu ya fahimci yarinyar nada wani irin jiki mai daukar hankali duk wani lafiyayyan namiji, wannan dalilin yasa kullum idan yana gida zasuje wani gurin idonsa a kai! idan sun saka hijabin da be rufe musu jiki sosai ba sai yace suje su sanja wani, sosai yake kula dasu da takatsantsan a kansu. mussaman ita Naja’atun da ya lura tana kan lokacin balagar ta….to a dai dai lokacin ne kuma suka gama secondary ita da Ilham ‘Yar gidan Baba Magaji ita kuma Saddiqa na aji ss1 aji hudu kenan……. Lokacin kuma Halimatu nada tsohon ciki haihuwa ko ya yau ko gobe…….. a wannan lokacin ne kuma sha’kuwa gami da soyayya mai kar’fin gaske ta shiga tsakanin Salim da Naja’atu, hatta da manya sun san da maganar! mahaifiyar Salim wato Yaya Ramlatu kwata kwata bata kaunar al’amarin ta zuba musu ido ne kawai tana kallonsu! Ita kuwa Naja’atu soyayyar da takewa Salim din tasa ta manta wacece mahaifiyarsa tana gani ita in dai Salim din zai aureta babu ruwanta da masifar Mahafiyarsa, Abbah Abbas kuwa ganin yanda suke kaunar junansu sai al’amarin yayi masa dadi sosai yana fatan Allah ya tabbatar da alkairi a tsakaninsu, kenan shi ya kasance waliyyin mutum biyu Salim din da ita Naja’atun.
A dai-dai lokacin da suke kokarin tafiya babbar makaranta, Allah ya saukar da ikonsa kan Halimatu gurin haihuwar cikin dake jikinta Ubangiji ya dauki ranta! bata tare data haife abinda ke cikin nata ba, mutuwar data girgixa zukatan al’umma da dama! mussaman Yaya Ramlatu da Halisa kwana sukayi suna sambatu da zabure zabure! Halima ta mutu da kalmar shahada a bakinta kuma ta mutu sanadiyar haihuwa babu shakka abun alfaharin ko wane musulmi kenan, duk wani mai kaunar Halimatu zai taya ta farin cikin samun rahamar Allah da tayi dalili kenan da ya sanya mijinta da iyayenta ke jin sassauci a cikin zuciyoyinsu idan suka tuna da cewar fa Halima tuntuni ta manta da rayuwar duniya domin ta riga ta gama dacewa, duk wanda zai budi baki alharin ta zai fad’a! Tabbas Annabi yayi gaskiya da yake cewa mutuwar mumini itace ke sawa mutane su girgiza kuma duk wanda ya mutu jama’a na fadar alherinsa babu shakka Allah yaso shi da rahamarsa.
*Ubangiji Allah kasa muyi kyakkyawan karshe ameen*
To Bayan kwana bakwai ne da rasuwar Halimatu al’amarin ya kasance…….
Inda su Baba Malam Alhaji Samaila Abba Magaji dashi kansa Uban gayyar suka zauna suka tattauna maganar yin *MADADI* da Naja’atu wato Naja’atu ta maye gurbin ‘Yar uwarta Halimatu data dauka a matsayin mahaifiyarta.
*A Pege na gaba zamu dawo ainihin labarin da muka fara da farko*
*NAGODE ‘KWARAI DA ADDUARKU A GARE NI NAGODE????????*
*????️MADADI!!????*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE????*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION????????️*
_’Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
_*Na gaishe daku ‘Yan ‘Kungiyata ta Manazarta Writers Association, Hakika ina jin dad’i had’in kanku, kuma ina alfahari daku mutu’ka! gabad’ayan ku ina rokon Allah ya d’aukaka min ku d’aukaka mai amfani Ubangiji Allah ya baku ikon rubuta abinda al’umma zasu amfana dashi*_
*PEGEN YAU NAKI NE*
*UMMU HANIFA*
Marubuciyar littafin
*ANYA MUTUM CE?????*
Ina mutukar alfahari dake ‘Yar d’akina Allah ya ‘kara miki basira da haza’ka, ki cigaba da rubuta littafai masu dadi da ma’ana♥️
*7*
Kanta a tsakanin cinyoyinta ta d’ora duka hannuwanta saman kanta ta takure kanta guri guda sai kuka take tana girgiza kanta, Baba Talatu ta dafa bayanta a sanyaye tace”Naja’atu yanzu kinji komai daga bakin malam ko? Alhaji Abbas bashi ne ya haife ki ba kamar yanda kike tunani, A’a ba haka bane shi d’in ya kasance miji ga ‘yar uwarki Halimatu Allah ya ji’kanta da rahama, wannan dalilin ne yasa su malam suka yanke wannan hukuncin a kanki babu laifi dan kin auri mijin ‘yar uwarki kuma dukkanin mu bamu aikata haramci ba kamar yanda kike tunani da farko, idan kin auri Alhaji Abbas hankalin mu zai kwanta saboda mun san zai ri’ke mana ke da kyau da amana kuma su Saddiqa da d’an uwanta Mussadiq zasuji dad’in kasancewar ki a matsayin matar babansu zasu dinga kallonki tamkar mahaifiyar su.” …………Fuskarta jage-jage da hawaye ta d’ago kanta tana kallon mahaifiyar tata, girgiza kanta ta shiga yi kana tace”Ni wallahi bazan iya zaman aure dashi ba, a Uba fa na daukeshi kuma ya za’ayi kuce zaku daura min aure dashi, bayan dukkanin ku kusan da maganar Salim wannan ai abun kunya ne a gurunsa ace ya aure ni bayan shine ya raine ni ya rike ni a matsayin ‘yarsa, kawai kuma saboda mutuwa ta ratsa tsakaninsa da matarsa sai kuce zakuyi masa *MADADI* dani ni wallahi bana sonsa.”