MADADI 1-END

MADADI Page 1 to 10

Ta’karashe maganar cikin gursheken kuka mai karfi.

Baba Malam yace.”Ai dama ba cewa muka yi dole sai kin so shi ba, cancanta muka duba shiyasa muka yanke wannan hukuncin saboda haka ina so ki cire maganar ko wane namiji a cikin ranki domun kuwa mutukar ni ne na haifeki to baki da miji sama da Mijin ‘yar uwarki wato Alhaji Abbas, zaki aure shi ko bakya sonsa nan gaba idan kinyi hankali zaki gane abinda muke nufi dayin hakan.”

Da rarrafe ta isa inda yake ta ri’ke hannunsa jikinta sai kyarma yake tace”Wallahi Baba malam zaku jefa rayuwa ta cikin garari saboda na fada muku iya gaskiya shine ni ba zan iya zaman aure dashi ba, na farko yayi min tsufa kuma abun kunya ne ace ya aure ni alhalin Ni ‘yarsa ce bayan haka kuma yasan shine waliyi na gurin daurin aurena da Sali…….Abba Magaji ya fusata! ya kai mata mari da bayan hannu! jikinsa na tsuma! yace.”Dan ubanki har wata cancanta kike nema? dame kika fi Alhaji Abbas din ? da har kike kiransa tsoho! ana nuna miki abinda ya dace dake kina  maganar abin kunya, kina nufin dukkaninmu bamu san abinda ya dace ba kenan? to wallahi tallahi na ‘kara ji kin bud’e baki kinyi wata magana anan gurin sai na futar miki da jini shashashar banza da wofi.”

Shuru tayi jikinta sai rawa yake hawaye kuwa kamar an bude famfo! sai famar girgiza kanta take tana toshe bakinta tamkar wata zautacciya.

Tausayi ta bawa Baba malam ya kalli Alhaji Magajin a nutse yace.”Yarinyar nan taurin kaine da ita ina ganin zamu sake zama mu tattuna kan maganar, bana so ayi abu daga baya kuma azo ana dana sani.

Alhaji Magaji yace.”Malam babu wani zama da za’a sakeyi idan wata magana ta fito daga ‘bangaran mu ba zasuji dadi ba, tunda kaga sune suka zo mana da maganar  yana da kyau mu basu goyon baya kan abinda suka zo mana dashi duk mutumin da ya nuna yana kaunar had’a zuria da kai to ka tabbata ba ‘karamin so yake maka, hakika nasan abokina Abbas yaji dadin zama da Halimatu shiyasa ya bukaci a bashi Naja’atu ta zame masa *MADADIN TA* dan haka tunda mun riga mun gama magana  babu dadi kuma aje ace musu wani abu daban.”

Baba Malam yace.”Yarinyar ce take bani tausayi bana son wannan kukan da take yi yana d’aga mun hankali amma tunda kace haka shikkenan Allah ya sanya alkairi cikin al’amarin ya kauda kowace irin fitina da zata biyo baya.

Baba Talatu dashi Magajin suka amsa da “ameen” Mikewa yayi yai musu sallama da niyar tafiya gida dan lokacin goma na dare ma ta wuce! Fatan sauka lafiya sukayi masa ya dauki hularsa da key dinsa ya fita daga gidan.

Cikin tausawa ya kalleta da fad’in”Ki tashi kije ki kwanta komai yayi tsanani maganinsa Allah kuma ina so ki zauna kiyi tunani kan wannan hukuncin da muka yanke a kanki, mune muka haife ki ba zamu cutar dake ba, da mutumin nan da ba nagartacce bane to da baza mu amince da bukatarsa ba to mun tabbatar da cewar idan muka dauke ki muka bashi muna da tabbacin zai kula dake kamar yanda ya kula dake a lokacin da baki san kanki ba.”

Mikewa yayi ya shiga da’ki bayan ya gama maganarsa, Baba Talatu ta jima tana rarrashinta kafin ta mike itama tabi bayan Malam din suka barta ita kadai a tsakar gidan tana kukan zucci.

Mamaki take sosai! wai ashe dama Abban Abbas din ne   ya bukaci auranta  ita duk a tunaninta su Baba malam ne,  girgiza kanta kurrum take tana mamakinsa, to ta aureshi tayi yaya  dashi? ta yaya za ta iya  rayuwar aure dashi? lallai ma! ita abun ma mamaki yake bata ko kunya bai ji ba yace zai aureta bayan yana amsa sunan Uba a gurinta, gashi kuma yasan da maganar Salim hummm! aikam ba zata yarda ba duk yanda za tayi sai ta rushe wannan auran, sam ba zata auri tsoho dan shekara hamsin ba  haka kawai sun gina soyayyarsu da masoyinta yazo yayi musu kutse a rayuwarsu ko kunya baya ji zai zo da wannan maganar!  ‘Kwafa tayi ta mike ta shiga d’aki!

Tana shiga dakin taji shashshekar kukan Saddiqa suna kwance ita da Mussadiq a katifa ta rungume shi sai kuka take!

A gigice ta kunna haske wayarta, tana haske su! Saddiqa ta rufe idonta tana sake takure jikinta guri guda……”Ke Saddiqa menene? dama ba kiyi bacci ba.”? Saddiqa ta mike zaune tana goge fuskarta, ‘Karasawa tayi ta zauna gefan katifar tana kallonta, a sanyaye tace”Meye kika kuka? nafada miki ki dainawa Mamma kuka idan kina so ta dinga samun rahamar ubangiji.”

Saddiqa ta goge fuskarta tana kallonta tace”Ni ba Mamma nakewa kuka ba,  nasan abinda nake yi a halin yanzu Mamma babu abinda take da bukata a gurinmu sai addua ba kuka ba.” 

A d’an sanyaye tace”To me kikewa kuka.”? Saddiqa ta kalleta wasu hawayen na sake zubo mata tace”Yaya Naja’atu me yasa kike nuna ‘kiyayyar ki ‘karara a kan Abbanmu.”!? Gabanta ne ya fad’i! sai tasha kunu! tace”Wace irin magana ce wannan Saddiqa? kada kice min kema kina goyon bayan na aureshi.”

Saddiqa taja majina tana goge hancinta tace”To menene aibu a ciki? dan kin auri Abbanmu ai ba wani abun bane kuma ba ke kad’ai ce kika ta’ba auran *MADADI* ba Yaya Naja’atu idan kika maye gurbin mahaifiyarmu zamu ji dad’i sosai dan Allah kiyi mana wannan alfarmar ki daina nuna ‘kiyayyar ki a fili.”

Shuru tayi tana nazarin maganar yarinyar! Wai shin da suke ta wannan maganar ta yaya zata fara ne? wane matsayi zata ajiye shi miji ko mahaifi? bafa zai yiwu ba.! Ta kalli Saddiqan data kura mata ido tana jiran amsarta tace”Saddiqa   nayi wa Abbanku ‘kan’kanta kuma shima yayi mun  girma bayan nan kuma ni matsayin mahaifi yake a gurina bazan iya rayuwar aure dashi ba, kuma ki daina tunanin ina ‘kinsa wallahi bana ‘kinsa saboda Abba Abbas yayi min abinda ba zan ta’ba mancewa dashi ba, kawai dai bana  tunanin zan iya rayuwar aure dashi.”

Saddiqa tace”To idan baki aureshi ba kin san dole yayi aure  kuma  gabadayan mu bamu san matar da zai aura ba, kinga zamu shiga halin ‘kaka na kayi tunda dai kin san ba ‘kaunar mu Anti Halisa take ba, kinga rayuwarmu na cikin ‘kalubale nida Mussadiq.”

“Eh gaskiya ne duk maganar da kika fad’a to ai ba dole sai kun zauna tare da matansa ba, sai ku dawo gidan Alhaji da zama ko kuma ku dawo gidanan nan nasan Baba Talatu zata ri’ke ku to meye abun tashin hankali.

Saddiqa ta shiga girgiza kanta zuciyarta na wani irin d’aci! tace” Yaya Naja’atu kin manta  maganar Abbanmu kenan kin san fa yasha fad’a cewar mutuwa ce kawai zata rabashi da ‘yayansa bana tunanin zai amince ya kawo mu nan mu zauna ke ko gidan Alhajin da kike magana ba zai barmu muje ba duk da cewa gidansu ne.”

Naja’atu shuru tayi tana tunanin al’amarin Babu shakka zaman Saddiqa da Mussadiq hannun Halisa gagarimun had’ari ne zata iya cutar dasu ta ko wace siga! Itace zata rike su tamkar uwarsu, to ita kuwa ko a mafarki bata tunanin zata koma gidansu a matsayin matar mahaifinsu, insha Allahu ta bar gidan har abada.

Ganin Saddiqan ta tsura mata ido yasa tace”To ki kwanta kiyi bacci zanyi tunani kan maganar ki.” Saddiqa taji farin ciki ya rufe ta tace”To shikkenan Yaya Naja’atu nagode Yaushe zaki gama tunanin.”? Kallonta tayi na minti biyu tace”Ke dai tunda nace zanyi to zanyi duk hukuncin dana yanke zan fada miki.”

Saddiqa tace”To Ubangiji Allah yasa naji alkairi.” Amin tace a takaice, Saddiqa ta juya ta kwanta tana adduar Allah yasa ta amince da maganar ta………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button