MADADI 1-END

MADADI Page 1 to 10

Tsuru tayi ta tsirawa guri guda ido tana tunanin yanda za tayi ta rusa wannan gagarimin al’amarin daya tunkaro ta,  kira ne ya shigo Wayarta dake gefanta, ta dauka hannu na rawa, a kunne tasa wayar, ta fashe da kuka ‘kasa-‘kasa tace”My prince kaji abunda Abbah Abbas ya ‘bullo dashi ko.”

Salim dake kwance kan katifar sa yace.” Menene ya faru ni banji komai ba.” Juyawa tayi tana kallon bayanta, dan bata so tayi wata magana ya kasance Saddiqa taji, sai da ta tabbatar da bacci takeyi sannan ta sake sassauta murya ta shiga fada masa abinda ke faruwa…….Mi’kewa zaune yayi da sauri! lokaci guda gumi ya tsatstsafo masa, yace.”Da gaske kike wannan maganar ko kuma dai tsokanata kikeyi.”? 

“Humm! wane irin tsokana wallahi tallahi da gaske nake wai Abba  Abbas  shine ya bude bakinsa yake fadawa su Baba malam yana so ayi masa *MADADI* dani!!!

Katifar da yake kai ya doka! da hannunsa da ‘karfi! Yace.” Kai kaji wata tatsuniya! shi yanzu dan girman Allah baiji kunyar fad’ar wannan maganar ba!!? To shin wai  ko ya manta abinda yake tsakanina dake ne da har zai bijiro da wannan tatsuniyar.”

Tace”Oho! ni gani nake kawai san zuciya ne yama za’ayi yace haka bayan shi da bakinsa ne yace.”Mu daidaita kanmu zai daura mana aure kuma saboda mutuwa ta ratsa tsakaninsa da matarsa sai yace a mayar masa dani a *MADADINTA.”*

Salim  yayi wani murmushi na takaici yace.”Ke nifa na daina mamaki! wallahi zai aikata dama yanda yake wani kula dake da wani takatsantsan a kanki akwai alamun tambaya dama so yake matarsa ta mutu ya aure ki! saboda haka ni kuma wallahi bazan bar masa ba, to in banda ma rigima ina ke ina shi! shekara hamsin har yake tunanin auran yarinya ‘yar ‘karama kamar ki 16years fa to idan ya aure ki yayi yaya dake? mtwwss.”!!

“Humm! ni wallahi Salim mamaki ma ya hana ni nace komai ba kaga yanda su Baba malam suke murna ba,  wannan ai tauyewa mutum hakki ne. Ni duk na rasa ma yanda zanyi.”

Yace.”Kece kuwa kike da yanda za kayi, tun kafin yafiya tayi nisa ki kokarin ganin kin rusa maganar ni kuma gobe idan Allah ya kaimu  idan naje daukarshi domin zuwa kasuwa zanyi masa magana akan inaso yazo gurin Baba malam kan maganar auramu sai naji me zaice.”

Tace”To yauwa kayi masa hakan nasan dole kunya tasa ya kasa magana ni wallahi duk mutuncin sa ma ya zube a idona mtssssw!!! Takarashe maganar tana jan tsaki!

Yace.”Baby ki daina wani damuwa ki kwanta kiyi bacci bazan bari wannan al’amari ya tabbata ba, duk yanda zanyi to zanyi  na rusa al’amarin.

A sanyaye tace”Tom shikkenan my Prince kayi bacci mai dad’i kaji ko.” Yace.”Ke ina wani maganar bacci mai dadi a gurina Wannan dattijon na nema yasa zuciyata ta buga.”!!

“Hummm! kawai tace dan ta rasa ma abin cewa, kashe wayar tayi ta zurfafa cikin tunani da nazari! gabad’aya bata so tayi masa rashin kunya saboda shi mutum ne mai muhimanci a gurinta to amma tunda ya ‘bullo  da wannan maganar kashi hamsin na ‘kima da mutuncinsa suka zube a gurinta.

Numbarsa ta laluba ta dinga kallon numbar kamar shi take kallo, shawara take da zuciyarta shin ta tura masa text ko kuwa, wata zuciyar tace” Idan kika tsaya lako-lako kan wannan al’amarin to za kiyi kuka da idonki…….Da sauri ta shiga rubuta masa text kamar haka.

_Assalamu alaikum Abba nmu barka da dare ina tafan kana nan lafiya? Abbah wata magana naji daga bakinsu Baba malam kuma sun ce kaine kazo musu da maganar shine nake so naji daga bakin ka._

Tana tura masa text din ta kashe wayar! kwanciya tayi tana takure jikinta  hawaye ne ke kokarin ‘kwace mata tana  kokarin hana shi  fita.

Sai bayan da ya dawo daga sallahr asubahi ne ya kunna wayar tasa, aikuwa text din ne ya shigo yayi saurin bud’ewa yana dubawa…………Ya karanta ya kai sau biyar ya girgiza kanshi! lallai To bata yarda ba kenan tana so taji daga bakinsa, shi kam bai san abinda zaice mata ba,  kawai sai ya share bai mayar mata da amsa ba, ya cire jallabiyar jikinsa, ya kwanta rigingine kan bed din yana tunanin rayuwa, Halisa ce ta shigo dakin jikinta sanye da hijab kamar wata mutuniyar arziki, tun bayan mutuwar Halimatu wata shiriya tazo mata takeyi  komai cikin  rashin kuzari.

*????️MADADI!!????*

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button