MADADI Page 1 to 10

Alhaji Sama’ila mai kwano wani attajirin mai kudi ne a cikin unguwar wanda yayi suna sosai dan idan kana neman gidansa daga bakin titi ka ambaci sunansa za’a nuna maka Alhaji Sama’ila mai kwano mutum ne mara ganin ‘kyashi mai kaunar dan uwansa da ma’kotansa, Yana da ‘yaya Uku kacal wanda matarsa Hajiya Abu ta haifa masa su, Biyu maza mace d’aya, amaryarsa mai suna Hajia Rabi bata ta’ba haihuwa ba tsayin shekarun da sukayi a tare! Yana zaune da ita haka dan shi mutum ne mai mi’ka al’amuransa ga Allah yasan tabbas Allah ne ke bada haihuwa kuma shine yake hanawa.
*Ramlatu* itace babba a cikin ‘yayansa sai wanda yake bin ta, Abbas sai Alhasan shine na karshe! tunda su Abbas suka taso a cikin unguwar nan suka ga yanda mahaifinsu ke mu’amula arziki da makotansa sai suma suka fara kwantantawa, hakan yayi wa mahaifin nasu dadi sosai ya kuma ‘kara nuna musu cewar hakan da sukeyi shine dai-dai dan cikin jinsin mutunan da Allah ya hallita a duniya babu wanda yafi wani a gurinsa sai wanda yafi bauta masa, kada su nuna sunfi karfin yin mu’amula da wanda suka fi rufin asiri, to babu shakka watarana Allah zai iya ‘kwace damar dake hannunsu ya mi’kawa wanda suke ganin bai isa ba……Wannan dalilin ya sanya suka saki jikinsu da kowa suke mu’amula a cikin unguwar tamkar sauran mutane.
‘Karamin gida ne madaidaici mai kofa gami da dakalin siminti a kofar gidan, gidan na kallon gate din gidan Alhaji Sama’ila hanya ce kawai ta raba tsakaninsu! Malam Baba shine mai wannan gidan, kamilin mutum nitsatstse mai kamala da dattako, malam baba mutum ne shi mai yawan ibadah da karatun al’kur’ani kusan duk azimin yana zaman tafsiri a kofar gidansa, inda Alhaji Sama’ila ke sawa ana fito da sadaka daga gidansa, akwai jituwa mai kyau a tsakaninsu dan sai nace halinsu ne yazo daya na gudun duniya shiyasa suke zaune lafiya da kowa, Alhaji Sama’ila ya dauki ragamar gidan Malam Baba a hannunsa ba wai dan shi malam din ya gaza ba Malam na futa sana’arsa kuma sa’i da lokaci al’amajiransa na kawo masa abun arziki gidansa babu yunwa ko kad’an! malam nada ‘Yaya Uku wanda suka haifa tare da matarsa Baba Talatu Babban cikinsu shine Adamu wanda yaci sunan mahaifinsa sai suke kiransa da Magaji, Halimatu itace ta biyu sai kuma Naja’atu da tazo a karshe! Lokacin da suka haifeta har sun cire tsammani da sake haihuwa sai kuma Allah ya kawo cikinta, lokacin Halimatu na daf da kammala secondary skuul lokacin tana da shekara goma sha shida a duniya.
Tsakanin Abbas da Magaji akwai jituwa sosai suna abota mai kyau da tsabta komai nasu tare sukeyi karatu tare su d’inka kaya iri daya hula iri d’aya takalmi iri daya kai hatta da agogo iri daya suke daurawa! Sai kuma Allah yasa shekarunsu suka zo daya da juna yanzu haka suna matakin shekaru talatin da d’aya koda biyu Lokacin ne kuma iyayensu suka fara yi musu maganar aure dan sun riga sun mallaki hankalin kansu! kuma suna zuwa kasuwa suna harkokinsu, Alhaji Sama’ila yanzu ba ya fita kasuwa sosai su ya d’ora kan harkokinsa na yau da gobe! Alhaji Sama’ila nada shaguna sama da talatin a cikin kasuwar sabon gari kuma dukkanin rumfunan sa harkar siye da siyarwa akeyi a ciki, suna harkar kayan rufin gida da kofofi da ta gogi sannan kuma yana da gidajen bulo suna buga bulo da harhad’a intar lock da ties, mutane da yawa naci da sha a karkashin wannan bawan Allahn, to ganin ‘Yayansa sun kai munzali ne yasa ya d’ora su kan harkokinsa na kasuwa kwata-kwata baya nuna bambanci tsakanin Abbas da Magaji Abinda zaiyi wa d’ansa Abbas shi yake wa Magaji, har jama’ar unguwa na surutu kan cewar ba haka kawai Baba Malam ya barshi ba wasu suna gani kamar yayi masa asiri ne domin ya mallake shi shida dukiyarsa, wannan cece kucen da mutane keyi bai dameshi ba, dan saboda yasan Malam baba ba zai ta’ba cutar dashi da zuriarsa ba.
Mama Ramlatu babbar Yaya gasu Abbas tayi aure a cikin unguwar dan gaba dasu kadan cikin unguwar Tudun wuzurci! wanda ta aura yana da rufin asiri dai-dai gwargwado amma tana da kishiya, Ramlatu wata irin mata ce mai izzah da ta’kama! bata da hali mai kyau! Tayi ta wulakanta kishiyarta kasancewar ta yar talaka gorin yau daban na gobe daban! a duk sanda Alhaji Sama’ila zaiyi mata aiken kud’i ko kuma tufafi sai ya had’a da kishiyarta kafin ta bawa kishiyarta sai ta gama yi mata gori sannan! Ita kuwa da yake mai hakuri ce sai dai kawai ta girgiza kai ta kyaleta, gabadaya Ramlatu bata dauko halin mahaifinta da ‘yan uwanta ba.
Lokacin data haifi ‘Danta na fari! sosai Mahaifinta ya gatantata daki guda aka cika mata da kayan barka, shi kuwa maigidan mota guda ta kayan abinci ya sauke masa, aikuwa Ramtalu ta samu abunda take so shiga take tana fita tana sakin habaici da gori! Cewar da abincin ubanta mutum ke rayuwa sannan kuma da tufafin ubanta mutum ke tun’kaho! Allah Sarki Sakina kishiyarta tasan da ita take, sai ta shiga daki taci kunanta ta koshi kuma ta dauki aniya kan cewar idan mijin nasu ya dawo zata fada masa abinda ke faruwa a gidan dan gaskiya ita ta gaji da wulakancin da matarsa keyi mata, gabadaya ta lura Ramlatu bata san mutunci ba ba kuma tasan mai kyautata mata ba, tunda ta haihu take hidima da ita ta kasa zama ta hutu kullum a tsaye take amma babu sannu bare nagode kullum cikin fada mata bakar magana take to gaskiya ta gaji hakurinta yazo karshe kudi ai ba hauka bane.
Maigidansu na dawowa bayan yaci a binci ya huta sai ta shiga fada masa abubuwan da suke ta faruwa a gidan wanda shi bai san dasu ba, tabbas ransa ya ‘baci sosai kuma ya sheda halin matarsa Sakina tana da hakuri sosai da kawaici ba zata takali Ramla da rigima ba duk da cewar itace Uwargida amma ta hakura da komai burinta ta kawo zaman lafiya da daidaito a gidin! Yace.”Kiyi hakuri insha Allahu zan sameta nayi mata fad’a amma kada irin haka ta sake faruwa kiyi shuru da bakin ki duk abinda ke faruwa tsakanin ki Ramla ki sameni ki fada mun zanyiwa tufkar hanci.” Tace.”To insha Allah.”
Lokacin da ya shiga dakin Ramlatu tana zaune gefan gado taci uwar kwaliya da less an turo dauri gaban goshi kana kallonta zaka fahimci ‘Yar Alaji ce hannunta da kunnata gami da wuyanta duk Gold ne sai walwali take…Zama yayi kusa da ita ya mika hannu ya kar’bi yaron dake hannunta da ta gama bashi nono ya tofa masa addua kana ya kwantar dashi ya fuskanceta…….Babu cikakkiyar walwala a tare dashi yace.”Yanzu Ramlatu abinda kikewa Sakina a gidan nan ya dace.”!? Wani irin shan kunu tayi ta kumbura fuska tace”Me nayi mata ashe! zaunar da kai tayi tana fad’a maka karya da gaskiya ko.”? Yace.”Abinda Sakina za tayi nasa ni haka kuma abinda Ramla za tayi nasa ni dukkanin ku nasan halin ko wacce ba wai ina so nace Sakina tafi ki a gurina ba A’a dik matsayin ku d’aya a zuciyata, amma ki sani abinda kikewa abokiyar zamanki bai dace ba! wace iri ce ke mai manta alkairi? menene Sakina ba tayi miki ba, ina cewa gabadaya sai da kika daina girki sai dai ta dafa ta kawo miki har d’aki kuma hakan bai hanaki kwana da miji ba! idan muguwa ce ai zata hanaki ki kwana dani ba tunda itace take girki amma ta dafa ta baki kici kina kwance kuma ki rasa sakayya da zaki mata sai irin wannan.”!! Fashewa tayi da kuka tace”Shikkenan to ai ba sai ka futo fili ka nuna kafi kaunarta a kaina ba, amma meye haka daga zuwa babu tambayar ba’asi sai ka kama wasu maganganu ai bani ce nace tayi min girki ba ita taga zata iya ta dauka tayi ni ba burgeni tayi ba, kuma koda ba tayi min girki ba zansa a turo mai aiki daga gidanmu tazo ta kula dani har na haihu.”