MADADI Page 1 to 10

Yace.”Ni dai na fad’a miki wallahi duk sanda kika ‘kara ci mata fuska ko kikayi mata gori kan wani abu da aka kawo shi gidan nan sai ranki ya ‘baci!! Cikin ‘bacin rai tace”To ai shikkenan tunda uwata ce ita sai na kwanta ta takani saboda tana da daurin gindi a gurinka, akan me? kai da ita kuna cin arzikina amma kuma kuce sai nayi muku biyayya wallahi ba zai yuwu ba.””! Takarasa maganar tana buga cinya.”! Cikin fusata yace.”Zanyi maganin ki ai shashasha mara tunani meye abinci da kike gori a kansa, meye kuma tufafi wanda zasu lalace su barki da mutum! to zanje na samu Alajin da kaina zan fad’a masa bana bukatar k’wayar abincinsa a gidana ko ya aiko dashi na dawo sai an mayar.” A fusace ya mike ya futa daga dakin….Shuru tayi tana tunani addua take kada Allah yasa yaje gurin mahaifinta da wannan maganar tabbas tasan idan yaji matsalar daga gurinta ne to babu shakka ranta sai ya ‘baci.
Aikuwa misalin karfe biyar da rabi na yamma ta fito daga wanka kenan wani yaro ya shigo gidan yana fadin “Wai Ramlatu tazo soro mahaifinta ne yazo.
Gabanta ya fadi da sauri tasa kayanta ta futa da tabarma a hannunta, tana zuwa soron sai taga Sakina a durkushe suna gaisawa da Alhajin, shuru tayi tana jinsa yana bata hakuri dangane da abubuwan da suke faruwa, koda ta gaishe shi ‘kin amsawa yayi ya rufe ta da fad’a sosai yace kuma ta bawa abokiyar zamanta hakuri! tana kuka ta shiga bawa Sakina hakuri! Tace ” Babu komai ta mike ta shiga gidan, Alhaji ya kalleta da fad’in “Wallahi Sakina duk sanda mijinki ya sake kai ‘karar ki gurina to babu ni babu ke! dama ashe mugun hali ne dake ko? to na kara jin na kawo muku wani abu gidan nan kiyiwa wani gori ranar sai na ‘bata miki rai! Hakuri take bashi tana share hawaye, ransa ya a ‘bace! ya futa daga soron ya barta a tsaye hannunta ri’ke da tabarma…….To tun daga ranar Sakina ta samu lafiya a gidan Yanzu Ramlatu ta daina yi mata gori da kallon banza amma dai duk da haka idan ‘yan wulakancin na kusa tana ta’bawa sai dai kawai ta kau da kanta domin dai a zauna lafiya.
****
Irin kulawar da Abbas keyi kan Halimatu ya sanya iyayensu suka ga kamar sonta yake yi, shi kuma ba haka bane a zuciyarsa kawai yana tausaya mata ne a matsayinta na mace kuma mai nakasa, Halima bata da lafiyar k’afa sosai kafarta ta dama ta samu tawaya tun tana yarinya anyi magani na hausa dana Asibiti tafiyarta bata dai-dai ta ba, sai kawai suka hakura suka bar mata hallitarta da alama haka Ubangiji ya hallice ta, kafarta ta dama itace take da nakasa ta inda in tana tafiya take jefata, Amma a fuska Halima bata da muni kyakkyawa ce sosai mai madaidaicin tsayi! komai nata cikin nutsuwa take gudanar dashi.
Magaji ya fitar da matar aure A lokacin da iyayensu suka bukata, shi kuma Abbas din har yanzu ya rasa wacce zai tsayar a matsayin uwar ‘yayansa! Mutum ne mai ruwan idon tsiya ko wace mace ba tayi masa ba! Da kyar da ya tsayar da Halisa a matsayin matar da zai aura gidansu na bayan layi! kuma Halisa kawar Halima ce tare ma suke tafiya makaranta, Allah sarki Halima tunda Taji labarin Abbas zai auri kawarta sai ta rasa nutsuwa komai nata ya tsaya cak! bata san tana sonsa ba sai da taji zaiyi aure! damuwa ta shiga sosai ta rage walwala har sai da iyayenta suka gane!
Da yake Baba Talatu macece mai saurin fahimtar abu nan da nan ta fahimci abinda ke damun ‘yar tata! Ta sameta tayi mata fada da nasiha sosai tace”Kada ta janyowa kanta lalura mutum baya ta’ba auran mijin da bana sa ba, dan haka ta cigaba da addua Allah itama ya za’ba mata miji nagari.” Duk da wannan nasihar da mahaifiyar ta tayi ma bai sanya ta daina damuwa ba, ita gani take waye zai aureta tana da nakasa (gurguwa) tana ganin watakila ma haka zata ‘kare rayuwarta ba tayi aure ba.
Ita kuwa Halisa tunda ta fahimci Halima na shiga damuwa a duk sanda taje mata da maganar Abbas sai ta dauki d’amarar muzguna mata kullum kan hanyarsu ta zuwa isilamiyya sai tayi mata zancensa da irin soyayyar da sukeyi, Halima tayi shuru bata tanka mata, ita kuwa Halisa tai tayi mata dariya………..Akwai lokacin da Abbas yaje zance gurin Halisa ta tsare shi wai dole sai ya fad’a mata tsakaninsa da Halimatu! mamaki sosai ya kamashi Yace.”Halimatu kanwata ce amma babu wata soyayya a tsakanina da ita.” Halisa tace”To idan kai baka sonta ita tana sonka dan ba kaga halin damuwar da ta shiga ba lokacin da ta samu labarin abinda yake tsakanina da kai, dan haka gaskiya gwara kayi wa tufkar hanci tun kafin tafiyar tayi nisa duk da take kawata bana tunanin zan iya zaman kishi da ita.”
Mamaki ya rufe shi da yake mutum ne mai tsare gida sai yace.”Okey yanzu kina so ki nuna min ga yanda zanyi kenan? Idan na fahimce ki kina so kice ke ba zaki zauna da Halimatu ba a matsayin kishiya ko me.”? Da sauri tace”Kwarai kuwa ai naga kusancin dake tsakanin gidanku da gidansu ne ina tunanin idan iyayenta suka fahimci halin da take ciki a kanka zasu ce ka aure ni kuma bana so gaskiya shiyasa nake so tun kafin tafiya tayi nisa kayi wa tufkar hanci.” Ya girgiza kansa yana kallonta yace.”Bari kiji Halisa ni ba irin mazan da mata zasu zauna suna tsarawa magana bane! abinda nasa kaina shi nake yi ke baki isa kice ga yanda zanyi ba, bani da ra’ayin zama da mace d’aya ki rubuta wannan ki ajiye bayan na aureki zan sake auran uku mutukar Allah ya bani iko saboda haka sai ki daura d’amarar zama da kishiya Halimatu kuma da kike magana na jawa kunne a kan tana sona to kin sanya ma naji sha’awar auranta zan aureku rana d’aya tunda dama ‘kawayen juna ne.” Da jin abinda ya fada sai ta mike a fusace! tace”Wallahi sai dai ka za’ba ko ni ko ita dan na rantse da girman Allah ba zanyi kishi da gurguwa ba.”!!! Ya bude bakinsa yana kallonta cikin tsananin mamaki! lallai Halisa muguwar jahila ce yanxu me bambamcin muskini da mai lafiya? saboda jahilci da hauka kishi ma sai ta za’bi da wanda za tayi! Ya mike tsaye fuskarsa a murtuke yace.” Tunda kin rantse ba zakiyi kishi da Halimatu ba to nima kuma ba zan janye ‘kudirin dana dauka a kan auranta ba, saboda haka sai kije ki r’ike duk wani abu da nasa aka kawo miki da niyyar auranki na bar miki, ki samu wani mijin ki aura ni kuma zanje na auri muskiniya sai naga abinda zai cinye ni.” Yana ‘kare maganarsa ya futa daga soron gidan nasu. durkushewa tayi kasan soron ta fashe da kuka tana data sanin abinda ta aikata, tun farko ta lura Abbas din ba irin lusaran mazan da mace ke tursasawa bane yana da wani irin baud’addan hali tabbas kamar yanda ya fad’a din babu me sashi yayi abinda baiyi niyya ba mutukar ba iyayansa ba.
Tofa al’amarin yayi tsanani dan Abbas yaja tunga ya tsaya kan maganarsa kan cewar ya janye maganar auransa da Halisa saboda wasu dalilai saboda haka Halimatu itace matar da ya za’ba a matsayin uwar ‘yayansa, Baba malam da Alhajinsa suka dinga bashi hakuri suna rarrashinsa, kan yayi hakuri ya auresu gabadaya, nan ya futo ya fada musu abunda ke faruwa! Yace.”Halisa tayi mummunan furuci ga Halima kuma tayi izgili ga hallitar da Ubangiji yayi mata, dan haka to shi ba zai auri macan da zata dinga kokarin nuna masa yanda zaiyi ba, saboda haka shi ya janye maganar auranta Halimatu yake so. Baba Malam da Alhaji Sama’ila ba suji dadin faruwar al’amarin ba kasancewar mahaifin Halisa din mutumin kirki ne duk tare suke zama bakin titi ranar juma’a da yamma, dan haka sai suka yanke shawarar fada masa halin da ake ciki, suna kuma fatan Allah yasa hakan shi yafi alkairi. Koda mahaifin Halisa yaji yanda al’amarun suka kasance sai hankalinsa ya tashi sosai! babu shakka yarinyarsa tayi wa kanta wauta ba kad’an ba ta cutar da kanta kuma shi sam baiga laifin Abbas ba, da irin hukuncin da ya yanke yana bala’in son yaga jajurtaccen namiji mai tsayuwa kan magana daya………….Halisa tasha fada sosai gurin mahaifinta yace.”Tunda ba zata auri mai mata ba to taje ta nemo wanda bashi da mata wanda kuma yayi mata alkawarin da ita kadai zai zauna, mutukar ta kawo masa komai illarsa da rashin nagartarsa to shi kuma zai daura mata aure dashi tunda itace taji ta gani.