MADADI 1-END

MADADI Page 1 to 10

Hankalinta a tashe ta nufi gidan Ramlatu, tana kuka ta zayyane mata abinda ke faruwa, a ganinta tinda Itace take gaba da Abbas din zata fada masa yaji tace dan Allah ta bashi hakuri yanzu ta yarda zata zauna da Halimatun a matsayin kishiyarta…….Ramlatu ta fusata ta dinga surutai tana aibata Halimatu da iyayenta a cewarta sam Abbas bai dace da auran muskiniya ba, saurayi dashi mai kyau da kudi da Ilimi yama za’ayi ya auri nakashshiya wacce take ci take sha a ‘karkashin alfarmarsa dan haka sai ta shiga bawa Halisa hakuri tace ta kwantar da hankalinta za taje ta same shi, insha Allahu zai aure ta………Da safe da wurwuri ta sauka a gidan kowa yayi mamakin zuwanta, ko gaisawa ba suyi da mutanan gidan ba ta nufi dakinsa, lokacin yana kokarin fitowa da shirin fita kasuwa! Yace.”A’a  barka da safiya kece a gidan.” Tace.”Eh gurinka nazo.”  Cike da mamaki yace.”Gurina.”? Tace”Eh yace.”To Kinga ni yanzu sauri nake zan fita ki bari na dawo ko kuma ki koma gida da yamma idan na dawo zan shigo gidan naki sai naji abinda yake faruwa.

Cikin d’aga murya kamar wata uwarsa tace”Yanzu kai Abbas ka rasa wacce zaka aura sai Halima muskiniya nakashshiya ashe dama anan ruwan idonka zai ‘kare gaskiya ka bani mamaki wallahi! Ga Yarinya mai hankali da nutsuwa ‘yar gidan mutunci mai kaunarka amma kace ka fasa auranta ka koma gurin wata banza wacce take ci da sha a ‘karkashin mahaifin…….’Daga mata hannunsa yayi fuskarsa a murtuke yace.”Wallahi ban san sanda zakiyi hankali ba! kullum kina girma kina cin ‘kasa!  Yanzu ke ko kunya baki ji ba ki shigo har dakina kina daka min tsawa da nuna min yanda zanyi, haifata kikayi da zaki dinga yi min haka? ina ruwanki da aurena da Halimatu idan ba zaki saka albarka ba to kiyi shuru da bakin ki dan ni wallahi duk abin nan da kuke yi ‘kara mun ‘karfin gwiwa kukeyi babu gudu babu ja da baya sai na auri Halimatu in yaso ku kasheta saboda ‘kiyayyya.” Fashewa tayi da kuka tana nuna shi da hannu tace”Ni kake zagi ko Abbas dama ai baka da mutunci baka dauke ni a bakin komai ba kuma kai dama ba’a fada maka magana kaji.” Yace.”Da kinzo min da lisilama zan fahimce ki amma kinzo kina yi mun hayagaga! a kunne ai kin san halina ni ba’a haka dani.” ratse ta yayi ya  futa dada dakin, kallo ta bishi dashi tana jijjiga kanta, dama tun yana yaro bata iya lankwasa shi gwara Alhasan shi tana fada masa magana yaji amma banda Abbas futo na futo yake da ita girgiza kanta tayi ta futa daga dakin.

To haka al’amura sukayi ta kasancewa kowa na fadar albarkacin bakinsa kan wannan auran yayin da Abbas ya shafawa idonsa toka ya tsaya kai da fata sai da yaga auransa da Halimatu ya tabbata sannan hankalinsa ya kwanta.

Gida gudu biyu iri d’aya Alhaji Sama’ila ya mallakawa Abbas da Magaji  Gidajen nasu na cikin unguwar *Gwangwazo* wajejen gidan Sarki.

kowanne ya tare da matarsa a ciki, Maryam matar Magaji ‘yar cikin gari ce dai-dai gwargwado tana da hankali da nutsuwa shiyasa tasu tazo d’aya da Halimatu suke zamansu lafiya,  kamar yanda mazajensu ke zaune da juna lafiya suma haka suke mutunta junanmu.

*3*

Halisa hankalinta yayi masifar tashi ganin irin uban gidan da’a kai Halimatu ga uban lefen da Abbas yayi mata atampopi da lesuka masu tsada kuka ta yini tana yi ta rasa nutsuwarta, mahaifiyar ma ba’kin ciki ne fal a cikinta zuciyarta tana aikace-aikacen ta na yau da kullum ta nayi wa ‘yar tata fad’an wautar da tayi, in banda rashin tunani da kuma jahilci ina kai ina kushe hallitar Allah  alhalin kaima baka wuce Allah ya mayar da kai wata hallitar ba, gashinan lokaci guda Allah ya juya al’amarinsa, tayi kuka tayi nadama gami da dana sani wanda hausawa suke kira da ‘keya ce.

Zama mai tsafta ne yake wanzuwa a tsakanin Abbas da Halimatu! tawayarta bata hanata sauke hak’kokin mijinta dake kanta ba, Tana kula dashi sosai dan wani sa’in idan yaga tana hidima dashi har tausayi take bashi dalili yanayin tafiyarta da rashin kuzarinta ma abin tausayi ne, amma abin na bashi mamaki sosai! kafin ya dawo daga kasuwa ta gama komai na gida tayi masa kwalliya mai burgewa. duk sanda ya shigo gidan yayi tozali da ita wani farin ciki ne yake rufeshi, wai shin meye aibunta ne? Halimatu bata da wani abu ko nakasu a gurinsa tinda duk wasu hakkokinsa tana saukewa kwata-kwata nakasarta bata dameshi ba zahirinta yake so ba wani abu na jikinta ba, zaman lafiyar da suke da juna ya sanya yake ji a cikin ransa zai iya zama da ita har’karshen rayuwarsa.

*****

Wata goma cif da auransu Maryam matar Yayanta magaji ta haifi d’a namiji, murna da farin ciki a gurinta tamkar ita ta haihu kullum tana gidan tare da mai jego tayi ta hidima da ita da jinjirin ‘Yan uwan Maryam suyi ta tausaya mata idan sunga ta wani abun na wahala sai suce ta zauna,  murmushi kawai take musu ta rabu dasu  idan kuma sun matsa mata takan ce dasu itafa babu abunda ba zata iya ba saboda haka su daina yi mata kallon mara lafiya da  rashin kuzari! To suma ganin ranta ya ‘baci yasa suka daina cewa da ita komai! kafin ma suzo ta shiga gidan ta gyara tsaf ta gyara yaron sannan ta had’awa maijego abun kari, sannan ta dawo gidanta tayi wanka ta shirya ta sake komawa, haka ta dinga zurga zurga har sai da akayi suna inda yaron yaci sunan Maigidanta Abbas sai take kiransa da Amir……………….KullumAmir a hannunta yake wuni sai dare take mayar dashi ko kuma idan ya bukaci nono sannan,  gabadaya dai ita Maryam haihuwar yaron tayi amma raino yana gurin Halimatu, idan ta dauki yaron tun safe to sai dare ita dashi.

Abbas bashi da matsala ta ‘bangaran wannan dan shima mutum ne mai son yara duk sanda ya dawo ya tarar da ita tana fama da takwaransa yakan ji dadi yayi ta addua Allah suma ya basu nasu mai albarka.

Shakaru uku da auransu Halima bata ta’ba ‘batan wata ba,  gashi har anyiwa Amiri ‘kanwa Ilham, Abbas tun yana daurewa dai har ya kasa hakuri yace ta shirya suje asibiti a dubasu, koda sukaje likita ya dubaso gabadayansu babu abunda ke damunsu kawai dai lokacin haihuwarsu ne baiyi ba, likita ya rubutu musu magani mai kyau yace suje suyi amfani dashi insha Allahu za’a dace…..Dukkaninsu a sanyaye suka koma gida, kuma ba suyi ‘kasa a gwiwa ba suna amfani da maganin kuma suna sake kula da kansu.

Ramlatu kuwa a duk sanda suka had’u da Halimatu a taro sai ta zage ta tayi mata gorin rashin haihuwa, duk taro na family dinsu sai ta tara mata mutane tayi ta nuna ta tana fad’in mugwayen kalamai a kanta, wata irin tsana Ramlatu keyi wa Halima ko ta mece oho! dan akwai ranar da tazo har gida taci mata zarafi da fad’in sun gaji da jiran gawon shanu dan su duk irinsu babu mara haihuwa saboda haka sun gaji da daci da ita idan ba zata haihu ba to zasu kawo wacce zata cika musu gida da ‘ya’ya.’

Wannan cin zarafin ya ‘bata marai rai sosai ta yini tana kuka dan ki girki ba tayi ba ballanta tayi wanka ta shirya kamar yanda ta saba, koda maigidan ya dawo rasa gane kanta yayi, tambayar duniya tayi masa shuru sai kuka take yi, tsayin shekaru uku da auransu bai ta’ba fuskantar irin wannan matsalar daga gurinta ba, da kyar ya samu yayi wanka ya futo palon tana dai zaune a inda take tana kukan da take, zama yayi kusa da ita yana sake rarrashinta kan ta fada masa abinda ke faruwa,  da kyar tayi masa magana tana hawaye gwanin tausayi tace ita taga ji  tunda bata haihuwa ya ‘kara aure ko kuma ya saketa dan cin zarafin da Yayarsa take mata ya isheta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button