MADADI Page 1 to 10

Ransa idan yayi dubu ya ‘baci! shin wai me yake damun Ramlatu ne? ina ruwanta da matarsa ina kuma ruwanta da rashin haihuwarsa, idan zai mutu bai haihu ba bai dameta ba shine yaga zai iya zama da matarsa a haka, shi kam ya rasa wace irin ‘kiyayya Ramla keyi wa Halimatu, hakuri ya bata sosai yace zai same ta yaja mata kunne kan kada ta sake zuwar masa gida.
Jin abinda ya fad’a yasa hankalinta ya tashi sai ta dinga bashi hakuri tana nuna masa illar abinda zai aikata, mutukar ya tunkari Ramlatu da wannan maganar to babu shakka ya sake rura wutar gaba mai zafi a tsakaninsu, kuma ita ba zata so su samu matsala da ‘yar uwarsa ba, Nuna mata yayi ya hakura ba zaije gidan Ramlatun ba……..Washe garin ranar kafin ya tafi kasuwa sai da ya tsaya gidan Ramlatun sukayi ta babu kyau babu dad’i a tsakaninsu, dan ya nuna mata mahimanci da matsayin Halima a gurinsa kuma ya nuna mata cewar itama ta tsaya a matsayinta na ‘yar uwarsa mutukar tasan wata fitina ce zata kaita gidansa to kada ta sake zuwar masa gida, dan tuntuni shi ya riga yasan Allah ne ke bada haihuwa ba wani mahaluki ba! Ramlatu kuka taci ta ‘koshi ‘dan uwanta da take alfahari dashi shine yazo ya ci kata mutumci a gaban kishiryata lallai babu shakka dole sai ta tashi tsaye kan Halima dan da alama Iyayenta suna tsaye a kanta gurin ganin ta mallake mata d’an uwa.
*Kaji rigima ta Ramlatu ke ba uwar Abbas ba komai ba amma kina kishi da matarsa, Uwar miji aka sani da kishi da matar d’anta Uwar mijin ma irin wacce bata san abinda take ba.*
Abbas zuciyarsa wasai yaje kasuwa yayi harkokinsa……koda suka tashi daga kasuwar kai tsaya ‘Kofar Na’isa suka nufa dan ji yake idan bai fad’awa mahaifiyarsu abunda Ramla ke masa ba za’a iya samun matsala nan gana gwara ya fada mata ta kira ta ta ja mata kunne.
Hajiya Abu ranta ya ‘baci sosai tace”Ni dik abinda ke faruwa a tsakaninsu ban sani ba wallahi amma Wannan yarinya anyi babbar kwabo wallahi dan taga matar taka mai saukin hali ce shiyasa take mata cin kashi a ko’ina amma kayi hakuri ka kuma bawa Halimatun hakuri insha Allah zan aika yara har gidanta su kira min ita zan mata tsakani da matarka duk sanda ta sake zuwa gidanka domin ta kuntatawa matarka to babu shakka na samu labari da Alhaji maihifinku zan had’ata….
To tun daga wannan rana Halimatu ta samu lafiya Ramlatu ta saurara mata da gorin haihuwa ammafa sa’i da lokaci suka had’u a wata sabgar sai ta yar mata da habaici al’amarin Ramlatu sai addua.
*****
Halisa ce ta shiga kara kaina a gidan, mussaman ranaku guda biyu Juma’a da Lahadi ranakun da ta tabbatar da cewar maigidan nan bai futa sai taci uwar kwalliya ta sanyo turare mai ‘kamshi tazo ta yini a gidan! idan sun had’u dashi tana nuna masa kamar babu wani abu a ranta, ta hakura dashi kawai ta zuwa ziyara ne gurin ‘kawarta! Sai dai ya girgixa kansa kawai ya shareta dan shi ba yaro bane ballanta ta raina masa hankali………Ita kuwa Halima zuciyarta ce ta shiga sa’ka mata wani abu! tana ganin tunda dai har yanzu Halisan bata da tsayayye mai zai hana ya aureta ya had’asu tunda ta lura da Halinsa tayi hankali kuma duk wasu alamu da take nunawa a kan mijin nata ta gane sabida shi take zuwa gidan……..Koda ta sameshi da maganar cewa yayi zaiyi shawara zai fada mata kome ya yanke!
Kwana biyu ta sake tuntu’barsa da maganar ya dinga kallonta yana mamakinta yace.”Ke kina ganin idan na auri Halisa na had’aku babu matsala kuma zaki iya zama da ita.”?
Cikin farin ciki tace”Zan zauna da ita tsakani da Allah nasan ko ta nufe ni da sharri zai koma kanta tunda ban cuce ta ba, sannan kuma ina so ka aureta kaga tanan za’a tabbatar da rashin haihuwar mu shin waye yake da matsala tsakanina da kai.”! Wannan magana da tayi sai ta sake sa masa ‘kwarin gwiwa shima yana so ya tantance waye mara lafiya a cikinsu, kai tsaye ya tunkari Halisa sa maganar, ranar kamar ta zuba ruwa a ‘kasa tasha dan farin ciki! ta dinga murna da godewa Allah! Yace.”Ina so ki zauna lafiya da Halimatu dan da yawun bakinta nazo nan neman auraki kada ki shiga gidana ki tayar mana da hankali mun gina rayuwarmu cikin mai kyau da inganci” Halisa taji wani irin d’aci a ma’kogwaronta! wato ma ba’a karan kansa yazo neman auranta ba sai da izinin matarsa! ‘kwafa tayi a cikin ranta! a zahiri kuwa cewa tayi” Haba Alhajina kada ka damu zan zauna lafiya da ita ai ko lokacin baya ma kuruciya ce ta janyo nayi wannan furucin amma ka daina kokwanto da shakku a kaina.”
Yaji farin ciki ya kamashi dama can yana son Halisa halinta ne baya si to tunda dai yanzu tayi hankali zai aureta su zauna tare cikin inuwa daya.
Ba’a wani ja dogon lokaci ba aka d’aura aure Halisa ta tare a dakinta, da yake gidane mai dauke da bangare uku sai kowa ya dauki d’aya, kasancewar babu yara a gidan yasa maigidan ke bin ‘Dakunan matayen nasa bai tare a nasa part ba din sai ranar da ya tara iyali tukkuna.
*????️MADADI!!????*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE????*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION????????️*
_’Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*Wallahu galibun Ala amrihi????????*
*4*
Sati biyu da shigowar Halisa gidan al’amura suka sauya, Halimatu ta kasa gane kan mijin nata gabad’aya Halisa ta ri’ke masa wuya ko yana kasuwa bashi da nutsuwar kirki mutukar bai dawo gida yayi tozali da ita ba, ranar girkin Halimatu sam bai da wani kuzari da walwala yakan dad’e ma a waje bai shigo ba, idan ma ya shigo d’in babu wani abun arziki da yake tsinana mata ba kwanciyarsa yake yi yai bacci! Halima ta shiga damuwa matsananciya ta rasa wanda zata samu ta fad’awa damuwarta gabakidaya Abbas ya sanja mata baya kula da ita sannan ba ya zama yaci abincinta kamar da idan tayi masa magana sai yace.”A koshe yake shine dalili, Ita kuwa Halisa data fahimci rashin jituwa a tsakaninsu sai ta sake zage damtse gurin ganin ta sake mallakarsa, kissar yau daban ta gobe daban, duk abincin da zata bashi sai ta bad’e shi da magani abun mamaki kuma Yayarsa Ramlatu itace ke kawo mata maganin mata dana mallakar zuciyarsa, ita dai burinta Halimatu ta wulakanta a gidan.
Ranar Asabar har ya futa kasuwa da jaraba ta ciwo shi ya dawo gida, a maimakon ya nufi ‘bangaran Halimatu tunda Girkinta ne sai kawai ya nufi bangaran Halisa, domin a yanda yake jin kansa yana ganin kamar Halimatu ba zata iya dashi ba, sai yanzu ya gane cewar Halisa ce dai-dai dashi dan tana iyawa da fitinarsa ita kuwa Halimatu rashin kuzarinta a ko’ina ma gwadawa take, ada hakan bai dame shi ba sai da ya auri Halisa ya gane cewar itace zata iya dashi, dan jaraba irin tashi baya tsayawa kan hallitar da Allah yayi masa duk karfi da kuzarinsa sai ya had’a da maganin ‘karfin maza, kullum akwai wanda yake kawo musu magani kasuwa suyi ta siya suzo suna gallabar matansu da daddare.
Halisa duk da tasan ba girkinta bane bai hanata nuna masa kulawa ba kar’barsa tayi hannu biyu suka shiga d’aki suka shafe awa kusan hud’u suna abu daya…………Halimatu ce ta shiga sashin tana sallama a palon taji shuru idanunta ne ya sauka kan hular maigidan da key dinsa na mota da kuma rigarsa kan kujera.
Tabbas kayan daya sa ya futa dashi ne a dakinta ya shirya kuma asali ma itace ta dauko masa kayan dole kuma tayi mamaki! kafin ta dawo daga tunaninta suka fito daga dakin a tare dashi da halisan daga shi sai gajeran wando, ji tayi yana fad’in “Zo ki bani abinci naci a gurguje na koma kasuwa na bar mutane na jirana.” Had’a ido sukayi ita dashi! sai ya wani dake! kamar ba mara gaskiya ba, ya bude baki zaiyi magana kawai sai ta juya ta fita daga palon.