MADADI Page 1 to 10

Jikinsa ne yayi sanyi ya zauna kan kujera yana kokarin mayar da kayansa, tabbas yasan wani abun da yake a gidan baya kyautawa sam be san meya sa ba yanzu kwata kwata baya damun cikakken satisfaction da Halimatu! bata da ni’ima kuma bata gamsar dashi kamar yanda Halisa ke gamsar dashi, gashi Halisa ta iya salo-salo shi kuma haki’kanin gaskiya yana so a dinga kula dashi kan shimfida.
Halisa ta fito daga kicin da abinci a hannunta, mikewa yayi da fad’in” Bana jin zan tsaya cin abincin nan zan koma kasuwa yanzu.”
“Haba dai don Allah ka zauna kaci gashi da zafinsa dama ban jima da gamawa ba.” Girgiza kansa yayi ya nufi hanyar fita yana kallon agogon hannunsa da fad’in “Biyu da rabi yanzu na fada miki akwai mutanan dake jirana.”
Sakin bakinta tayi ta bishi da kallo tana girgiza kai, da sauri kuma ta ajiye plate din abincin taje bakin window ta d’aga labule tana le’kensa, gani tayi ya nufi gurin Halimatu, shi da yace sauri yake yi to mai kuma ya kai shi gurin ta……..Takaici kamar ya kasheta ta zauna kan kujera tana cizar yatsa.
Koda ya shiga palon samunta yayi zaune a kan kujera ta tsirawa guri guda ido tana kuka! yaji wani irin tausayinta ya kama shi, yana sonta baya son ganinta cikin damuwa shiyasa yaji wani irin rashin kuzari a jikinsa.
Kafin ya karasa inda take sai da ya tanadi kalaman da zai wanke kansa a gurinta.
Cikin wata mayaudariyar murya ya kira sunanta had’e da kamo hannunta, shuru tayi bata amsa ba, yace.”Ki gafarce ni hakika nasan ni mai laifi ne a gurinki, kin san dan adam ajizi ne, ina tausaya miki ne shiyasa bana so na dinga d’ora miki lalurata.”
Hannunta ta cire a cikin nasa tace”Wallahi ban ta’ba tsammanin haka daga gurinka ba, ashe dama duk wani abu da kake fad’a a baki ne? Halisa ko wata uku cikakku ba tayi ba ka sauya gabadaya ka daina kula dani baka sauke hakkina dake kanka, yausha rabon daka hada shimfida dani? ina tunanin tunda Halisa ta shigo gidan nan tsayin wata uku sai biyu ka kwanta dani shima sai dana nema sannan kuma abun har ya kai ka dinga satar kwanana kana kai mata, ina hankali da tunaninka suka tafi? idan ni bana ganinku ai Allah yana kallonku kuma kasan sai ya saka mun.” Jiki na kyarma yace”Na sani wallahi kiyi hakuri ki dauki hakan a matsayin tsautsayi! na fada miki ajizanci ne irin na d’an adam amma ba zan sake ba kuma inaso kice kin yafe mun.”
Tace” Sai ka fad’a mun sau nawa kana satar kwanana kana kai mata.” Da sauri yace.”Yau ne kawai shima kuma akashi aka samu.” Ta goge hawayenta a hankali tace”Na yafe maka amma dan Allah ka dinga kiyayewa kana kokarin sauke hakkina dake kanka.
Yace.”Insha Allah ki tayani addua nima cikin ‘yan kwanakin nan wani iri nake jina.” Tace.”Insha Allah zan cigaba dayi maka addua harkarshen numfashina.” Mikewa yayi yana fadin.” Muje ki rakani ko.” Ta mike tana mirmushi tamkar baiyi mata laifi ba suka jera tare suka futa har inda motarsa take.
Halisa har yanzu na tsaye bakin window tana kallonsu suka futo suka tsaya a bakin mota suna magana! gani tayi Halimatun na dariya tana kallonsa shi kuma ya kamo fuskarta ya sumbuta, ya shiga mota hade da daga mata hannu…….Zaman da’baro tayi kan kujera tana hargitsa gashin kanta, kai jama’a!! wai shin Halimatu wace irin macace ne? wacce bata da zuciya bata kishin kanta! ai idan itace mijinta ya saci kwananta ya kaiwa kishiyarta ranar sai ta kusa kashe shi da tashin hankali, amma ita duba dariya ma take harda rakoshi bakin mota.
Wayarta ta dauka ta kira Yaya Ramlatu! ta daga wayar suka gaisa, Murya na rawa tace”Yaya al’amura fa sun dagule wallahi! ban san wane irin so Abbas kewa Halimatu ba! daga aiki ya fara sai kuma ya karye! gashi itama kamar mayya duk abinda za’ayi mata bata fushi, ‘karewa ma kwananta ya kawo min a maimakon taji haushi sai ma take dariya harda rakoshi bakin mota.” Yaya Ramlatu ta shiga girgiza kanta tace” Nasha fad’a miki Uwarta da Ubanta ba’a zaune suke ba dan ita bata da kuzari da ‘kafar yawon gidajen malamai Ubanta ‘kasurgumin dan tsubbu ne duk wasu asararai yana dasu, ina kyautata zaton yayi aiki mai zafi akan Abbas din, amma duk yanda zanyi sai nayi na wargatsa shirinsu.” Halisa tace”Ni wallahi yanzu babban burina ta fita ta bar min gidana sannan naga na samu ciki na haihu.” Ramlatu tace” Kada ki damu zaki haihu ita kuma zata fita ta bar miki gidanki zaki zauna tare da ‘yayanki insha Allah zanyi miki kokari akan wannan lamarin.” Tace”Nagode Yaya Ramlatu! Sallama sukayi Ramlatu tace”Yauwa dama inaso kiyi dubara a gurin mijin naki ki samu ‘yan kudi masu kauri sai ki kawo min dasu nake so naje a taimaka miki.” Tace”Insha Allah zanyi kokari kamar nawa .” Tace”Dubu hamsin ma ta isa.”
Ajiyar zuciya ta sauke tace” Zan duba inda yake ajiyar kudinsa idan ya bar key din a jiki zan dauko zan kawo miki anjima dan nafi so ayi komai da zafi-zafi.”
Ramlatu tace”A’a kada ki daukar masa kudi ya gane fa.” Tace”Ai suna da yawa ba zai gane ba tunda kusan kullum sai ya shigo dasu kafin ya kai banki.” Tace”To shikkenan ina sauraranki idan kin kawo min ni kuma nayi miki al’kawari komai yamma zan tafi gidan *Yar Sa’adu.”*
Halimatu kuwa zuciyarta fes ta futo daga bangaranta ta nufi na Halisa domin yi mata sallama tana so taje su gaisa da iyayenta sannan kuma ta shiga gidan Dan uwanta su gaisa da matarsa Maryam, abinda yasa Maryam ta rage shigowa gidan saboda zuwan Halisa dan bata so wata hatsaniya ta tashi a tsakaninsu sunanta ya fito, dama kuma ta lura da irin wulakantaccen kallon da Halisa ke mata, shiyasa gabadaya ta dauke kafarta daga gidan, sai dai sa’i da lokaci ita Halimatun ta shiga su gaisa.
Halisa na kokarin zaro kudi cikin drowar taji sallamar Halimatu a palonta, da sauri ta zabura ta futo palon tana kallonta, Halimatu ta fahimci rashin gaskiya a tare da ita, girgiza kanta tayi tace”Halisa zan je gida mu gaisa dasu Baba Malam sai nadawo.” Cikin ya’ke tace”To sai kin dawo dan Allah ki mi’ka min gaisuwata gurinsu.”
Tace”Zasuji insha Allah.” Juyawa tayi ta fita, Halisan ta rakata da wulakantaccan kallo tana cin laya a kanta…..Tsaki taja ta koma dakin ta cigaba da ciku-cikun dauko kudin daga drowar da take a kulle dan ba taga key din ba amma dan jaraba sai da tasan yanda tayi ta zura hannunta ta zaro kudin duk sun ya mutse, da kyar ta samu ta ciro dubu talatin da biyar ta hakura haka, kaya ta sanja ta zuba kudin a jaka tasa kai ta fita daga gidan ba tare da maigidan ya sani ba.
Baba Malam da Baba Talatu sunji dadin zuwan ‘yar tasu duk sanda ta kai musu ziyara sukan yi murna da farin ciki ganinta cikin nutsuwa da wadata!
Bayan taci abinci sai suka shiga hira da mahaifiyarta Na’ajatu ce ta shigo gidan hannunta rike da buhun kayan wasanta duk tayi bud’u-bud’u da jikinta, Baba Talatu ta harareta da fadin” Kin gama yawon wasan naki yunwar cikin ki ta koro ki ko.”‘? Zum’bura bakinta tayi tana kokarin yin kuka. Baba Talatu tace”Ai sai ki nemi me baki abinci dan banyi dake ba dama na fada miki tunda baki zuwa makaranta to zakiyi ta zama da yunwa.” Kuka ta fashe dashi ta jefar fa buhun kayan wasan nata tana kallon Yayar tata. Halima ta riko hannunta tana rarrashinta, kwanciya tayi a jikinta tana kuka cikin rashin iya magana sosai tace”Ni ba zani makaranta malam ya dakeni ba kuma sai an bani abincina.” Halimatu ta dinga dariya tana kallonsu suna drama Baba Talatu tace”To sai naga wanda zai baki abinci a gidan nan.” Kuka take sosai tana fad’in “Ni sai an bani abinci yunwa nake ji.”