MADADI 1-END

MADADI Page 1 to 10

Ita kuwa Halimatu ganin yanda yake kula da kanwarta yasa ta rage jin zafinsa a zuciyarta, addua takeyi kullum Allah ya karkato da hankalinsa kanta tabbas tasan abinda yake yi ba a hayyacinsa yake ba, tunda tasan irin kauna da son da yake mata, babu shakka Halisa ba’a haka ta barshi ba.

To Haka dai Halimatu ta cigaba da zaman hakuri a gidan, tana ji tana gani mijinta yafi karfinta dan sai yayi wata biyu uku bai kwanta da ita gabadaya an cire masa sha’awarta a cikin  zuciyarsa.

*IDAN RABO YA RANTSE*

Ranar Juma’a bayan an sauko daga massalaci ya dawo gida a gajiya  ga kuma sha’awar dake damunsa tun daran jiya dan kwana sukayi rigima da Halisa ta yanko masa uban kudi wai sai ya bata sannan zata amince ya biya bukatarsa, shi kuma yace ba zai bayar ba sai ta fada masa abinda za tayi dasu, nan ta shiga inda-inda! ya fahimci bata da hujja sai yace ba zai bayar ba, shine tayi fushi tace itama ba zata bashi kanta ba, da yake mutum ne mai zuciya kawai sai ya kyaleta ammafa daurewa kawai yake dan baida hakuri ta wannan ‘bangaran……Washe garin ranar Halisa naganin ya futa itama ta shirya ta futa itama ta nufi gidan Yaya Ramla domin tafada mata abinda yake faruwa…….koda ya shigo gidan kai tsaye gurin Halisa ya nufa gabadaya idonsa a rufe yake bukatarsa kawai yake so ta biya yanzu ya amince zai bata kudin mutukar dai zata biya masa bukata.

Ya dubata ciki da waje bata gurin, rai a ‘bace ya nufi gurin Halimatu, suna Tare! Da Naja’atu a palo tana koya mata karatu ya shigo bakinsa dauke da sallama!

Naja’atu ta mike a guje taje ta d’ane jikinsa tana fad’in “Oyoyo Abbana.”! Dariya yasa ya mi’ka mata kumatunsa kamar yanda suka saba! aikuwa ta manna masa kiss a gurin! shima yayi mata sannan ya sauketa kasa, yana d’an ya mutsa fuska ya kalli Halimatu dake ta faman yi musu dariya! hannunsa ya mi’ka mata da fad’in ” Ranki ya dad’e zo muje daki ina da magana.” Halimatu ta tsira masa ido tana kallonsa da mamaki a tare da ita!

Gira ya daga mata yana yi mata wani irin kallo. Girgiza kanta tayi ta sunkuyar da kanta ‘kasa, lallai wato sai yau take da amfani a gurinsa kenan!  duk sanda yake cikin halin sha’awa tana ganewa.

Ji tayi ya kamo hannunta ya mikar da ita tsaye, gudun kada yayi abun kunya a gaban Yarinya yasa tayi saurin cire hannunta tace”Kaje ganin nan zan shigo.” Babu kunya ya nufi bedroom dinta yana wata irin tafiya.

Zama tayi kan kujera tana kallon Naja’atu na rubutunta sai da ta tabbatar abinda take ya dauke mata hankali sannan ta mike a nutse ta bishi dakin.

Wannan had’uwar tasu ta firgita Halimatu gabad’aya mijin nata ya sanja mata hallitarsa ma kamar ta sauya, ya zage karfi a kanta yana bugunta babu tausayi da jin ‘kai irin wanda yake mata, sosai yake sarrafata salo-salo duk ya fice daga hayyacinsa itama sai wuya yake bata, kukan wahala take masa tana bashi hakuri ya saurara mata haka, sam ba haka ya saba yin mu’amula da ita ba, da kyar ya saurara mata ya kwanta gefanta yana maida numfashi……..To tun daga wannan had’uwar Ubangiji ya zartar da ikonsa ciki ya shiga ya zauna daram a mahaifar Halimatu, cikin kuma da bai bayyana kansa ba sai da yayi wata hudu tukkuna sannan Allah ya bayyana shi, saboda ita kanta Halimatu bata san da ciki a jikinta ba kasancewar ba ko wane wata take al’ada ba shiyasa duk ta rikirkice, ta dinga kokwanto a kan ciki…….Kai tsaye asibiti ya dauketa sukaje, likita ta dubata sosai dan har scanning akayi mata ciki wata hudu kuma yana cikin koshin lafiya. Abbas ya rasa inda zai saka kansa saboda farin ciki, tun a mota ya kira wayar mahaifiyarsa ya sheda mata abinda ke faruwa, Hajiya Abu tayi murna da farin ciki sosai ta kuma yi addua kan Allah ya sauke ta lafiya……..Halisa kwanan kuka tayi da taji labari wai Halimatu nada ciki, ya akayi haka ta faru? wai dama mijin nata ashe yana lallabawa gurin Haliman yana biya bukatarsa bata sani ba, lallai zai shigo ya sameta…….Shi kuwa da farin ciki a tare dashi yake sake jaddada mata k’aruwar da ya samu! ta hasala! sosai ta dinga zazzaga masa rashin kunya kamar zata zage shi! aikuwa ta fuskanci ‘bacin rai! dan lafiyayyun marika tasha wanda hakan bai ta’ba faruwa ba tsayin shekarun auransu, Yayi mata gargadi sosai kan tsaurin idon da take masa kana kuma ya dauke mata wuta gabadaya ya daina kulata, ya tare sashen Halimatu!! 

Halisa ta zama tamkar mahaukaciya gashi  *’Yar Sa’adu* bata gari ta tafi Nijar dama ‘Yar can ce kullum ita kenan a tafe gurin zuwa gidan Yaya Ramlatu, suna tattauna yanda zasu ‘bulluwa al’amarin, Ramlatu tsoron zuwa gidan takeyi saboda tasan halin ‘Kanin nata zai iya kunyatata shiyasa ta zauna a gida, Halisan na zuwa inda take…………….Sau uku yana dawowa gida ya tarar bata nan a’lamarin da ya fusata shi sosai, ya tsaya harabar gidan nashi yana kai kawo kana ganinsa kasan ransa a ‘bace yake, Tana shigowa ya buga mata tsawa da fad’in “Ta koma inda ta fito! gabanta ne ya fad’i baki na rawa tace”Wallahi naj…….Hannu ya daga mata yace.” Bana bukatar naji komai daga bakinki sau uku ina dawowa gida bakya nan ina kike zuwa ba tare da na sani ba? saboda haka ki fuce min daga gida sai nazo gidanku inaso kafin nazo ki fada musu inda kike zuwa.”

Halisa ganin yayi fushin mai tsanani yasa ta juya jiki a sanyaye ta futa daga gidan, kai tsaye gidansu ta nufa tana kuka.

 A takaice dai sai da Halisa tayi sati biyu a gidansu sannan Yaje yayi bikon ta iyayenta ran su ya ‘baci sosai jin irin abinda take aikatawa na fita yawo ba tare da izinin mijinta ba mahaifinta yace da Abbas duk sanda ta sake futa bata fada masa ba to ya sanar masa sai ranta ya ‘baci sosai! Halisa ta tsorata sosai d’a zaman  da tayi a gidansu  har jikinta ya soma sanyi tsayin sati biyu da tayi a gidan nasu ji take tamkar shekara biyu tayi, ganin ya shere ta da ita al’amarinta yasa jikinta yayi sanyi tana addua kada Allah yasa yace zai saketa…..To tunda ta samu yanzu ya mayar da ita sai ta dauki aniyar gyara kuskuranta a gurinsa amma dai duk da haka ba zata fasa yiwa Halima zagon ‘kasa ba.

Koda ta dawo  gidan d kafin ya sakar mata fuska sai da ta dade tukkuna sannan ya warware gabadaya, tun daga sannan ta kiyaye abinda zai dugunzuma masa zuciya wanda zai haifar da sa’bani tsakaninsu har ta kaishi ga korata gidansu.

***

Cikin Halimatu nada wata bakwai Allah ya bawa Halisa nata, Halisa aka dinga murna da zumudi ana iyayi! shi kuwa maigidan ya dinga biye mata da duk abinda take so burinsa kawai yaga  matayen nasa sun haihu lafiya shima  ya shiga sahun mutanan da ake kira da Abbah, duk da sunan da Naja’atu ke kiransa dashi kenan Abbana, ko Abban Naja, a duk lokacin da zata kirashi da sunan yakan ji wani iri dan saboda yasan ba shine ya haifeta shi dai yafi bukatar ‘yayansa na cikinsa su kirashi da wannan suna. 

*****

Lafiya lau Halimatu ta haihu inda ta haifi ‘yar ta mace ta d’an d’ebo kammanin mahaifinta gurin hasken fata gami da siririn hanci, Abbas mai kyau ne sosai irin namijin da mata keso yana da haske da cikin zati  dogo ne amma ba sosai ba, yana da manya ido da dogon hanci wanda ya kyata masa fuskarsa, amma kuma bashi da fara’a  da saurin sabo! Mutum daya ya amince dashi cikin abokansa shine Magaji  Yayan matarsa kenan Abba magaji yasan sirrinsa kamar yanda shima yasan nasa………..Halisa ganin Halima ta haifi mace sai ta dinga addua Allah yasa ita ta haifi namiji  dan tasan farin cikin da mijin nasu zaiyi sai yafi wanda yake yi a yanzu, hankalinta na masifar tashi a dik sanda taga ya shiga gurin Haliman ya jima bai fito takan shiga tashin hankali da damuwa saboda   tasan yana can yana shiriritar da ya saba da  shegiyar yarinyar nan Naja’atu da Babynsa wacce ya sanyawa suna Fatima amma sai suke kiranta da *Saddiqa* dalili kenan da ya sanya take Allah Allah itama ta haihu itama taga yana nuna kulawarsa a kan d’anta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button