MADADI 1-END

MADADI Page 1 to 10

Haihuwar *Saddiqa* ta janyo masa bud’i da alkairai da yawa, harkokin kasuwancinsa suka bude sosai yake harkar gwangila na gina gidaje da  ma’aikatu da sauransu……..Wani  ‘katon gida yake ginawa a cikin unguwar *Danbare* sabuwar unguwa ce da masu kudi suka siyeta suke ta gasar gidana gida a gurin, gaskiya gidan da yake idan aka gama aikinsa  babu shakka zai zama abun kallo a gurin jama’a.

Halisa ta haihu lafiya lau  ta haifi namiji kamar yanda Scanning ya nuna mata, sai dai kuma cikin ikon Allah kwanan yaron d’aya a duniya ya koma…..Ihu! ta dinga zabgawa tana kuka dan rashin tawakkali cewa take wallahi Halima ce tayi mata asiri d’anta ya mutu saboda tana bakin cikin ita bata haifi d’a namiji ba.

Abba Abbas tun yana rarrashinta har ta si’ke shi haushinta ya rufeshi, ya shiga nuna mata illar abinda takeyi, Allah ne ya bata kuma ya kar’bi abinsa dan me zata d’orawa wani! sai da yayi mata kaca-kaca! sannan ta daina ikirarin cewar Halima ce tayi mata asiri.

***

Bayan shekaru uku Halimatu ta sake haihuwa inda ta haifi ‘Da namiji! Wanda wannan haihuwar ta janyo tashin hankali sosai a gidan dan iskokai Halisa ta dinga tayarwa na ‘karya dana gaskiya tana yun’kurin kashe maijego da jaririnta……Babu arziki ya tarkata ta ya kaita gidansu  dan al’amarin yafi karfinsa haka kawai yana ji yana gani ta illata masa d’ansa.

Ashe iskanci ne Halisa na ganinta a gidansu, sai ta dawo hayyacinta mussaman da mahaifinta ya samo malamai, masu ru’kiya suka dinga jibgarta, babu arziki ta dai-dai ta nutsuwarta ta dinga kiransa a waya yazo ya  dauketa taji sauki!

Shi kuwa dama tuntuni ya yanke shawara kan cewar zai raba musu gurin zama, dan gudun aikata mummanan aiki idan baya nan shima ya fahimci duk wani abu da Halinsan keyi sharri ne da ba’kin kishi da ganin kyashi!

Gidansa dake *’Dan bare* suka tare shida Halimatu da ‘yayansa kana yasa aka gyarawa Halisan wanda suka bari  ta zauna a ciki  yana ganin hakan shine yafi alkairi a tare dasu baki daya…

Wannan al’amari ya sanya zuciyar Halisa kusan bugawa, gidan da take kulafucin zama a cikinsa shine zai ce ba zai je da itaba, kuka taci ta koshi tana tunanin mafita babu shakka ta ko’ina Halima tayi mata zarra! ta haihu har sau biyu kuma  ta tare a sabon gida. tabbas dole ne ta nemawa kanta mafita yanzu ne ta sake gazgata maganar Yaya Ramlatu inda take cewa mugun sihiri iyayen Halimatu sukayi akan Mijin nata, itama idan hakane to tabbas zama bai kama ta ba.

To da yake yanzu bata da matsalar kudi yasa ta d’auki d’amarar shiga malamai  domin bukatarta ta biya, duk ranar da ya kasance ba a gidanta yake ba to idan ta fita tun safe sai yamma zata dawo gida tare suke yawace yawacen malamansu da Yayar mijin nata…..Yaya Ramlatu bata da matsala saboda mijinta matafiyi ne shiyasa takeyin abinda take so a gidan, haka zata fuce ta  watsar da ‘yayanta a tsakar gida, kishiyarta Sakina mutuniyar kirki ita ke mata dawainiya da ‘yayanta tayi da nata, tabbas albasa ba tayi halin ruwa ba, dan da Ramlatu ta gado halin iyayen nata to ba zata aikata abinda take ba.

*????️MADADI!!????*

_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE????*

~~~~~~~~~

*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION????????️*

_’Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_

~~~~~~~~~

 *PEGEN YAU NAKU NE*

*My Son Najib Sa’id*

*Abue Sale alqurami*

*Bashir Saleh*

*Umar Abbas Yusif*

*Muhammad Karim*

Ina mutukar godiya da kulawarku a kaina da ‘kokarin yi min sharing ina rokon Allah ya sadaku da alkairin duniya dana lahira Allah ya za’ba muku abinda yafi alkairi a rayuwarku????????

~~~~~~~~~~~~~~~

*6*

A takaice dai duk wannan fad’in tashin dasu Halisa sukeyi a kan Halimatu ba suyi tasiri a kanta ba, saboda halimatu ta kasance mace mai ibada kuma dukkaninsu bata nufe su da sharri ba shiyasa kullum Ubangiji ke kara kareta daga sharrin su da makircin su, duk wani asiri da sukeyi baya tasiri idan ma yayi baya dadewa yake karyewa, ta inda Halisa take samun galaba akan Abbas din shine ta gurin shaye-shayen magungunan mata to tana d’an janye hankalinsa watarana dan gaskiya irin magungunan da Halisa take sha suna da tsada har dana turawa sha take ita dai burinta ta janye hankalin Abbas din ya wulakanta matarsa uwar ‘yayansa, abinda Halisa bata sani ba kuwa shine irinsu Abbas asiri baya saurin kama su idan ma ya kama su to baya wani tasiri a jikinsu zai karye!  saboda Abbas mutum ne me yawan azkar da karatun al’akurani mai girma gashi sallahr asubah bata wuce shi, shiyasa  duk wani asirin da suke masa baya zama a jikinsa.

Halisa tun haihuwarta ta farko take samun matsala daga zarar ta samu ciki baya yin kwari zai zube, ta shiga tsananin damuwa da tashin hankali!  ganin ‘Ya’yan Halimatu sunyi wayo har sun soma zuwa makaranta gashi mahaifinsu naji dasu yana yi musu hidima kamar hauka, ai babu shiri ta bazama yawon gidajen masu magani har gurin ‘Yan bori zuwa take su bata magani tazo ta jika tasha, ta yini tana amai, da murkukusu, amma taki ta gane hanya madaidaiciya ta fawwalawa Allah domin shine mai bayarwa da hanawa, Kullum kokarinta ya za’ayi ta haihu ko ta halin ‘kaka. Abbas ganin ta tashi hankalinta dan har ramewa tayi sai yayi musu viza domin zuwa ‘kasa mai tsarki su roki ubangiji hakan be mata dadi ba taso ita ya kaita kasar waje likitoci su dubata idan ma dashe za’ayi mata zata amince ita gani take idan sukaje saudian ba zata sanja zani ba! Gabadayan su dashi da iyalinsa suka nufi kasa mai tsarki, Halisa ta dinga wani iyayi tana shige masa gani takeyi ai saboda ita  aka zo kasar! Halima dai sai dai tayi mata dariya kawai dan ita wataran idan Halisa na wani abu har dariya take bata, tana kallonsu zasu shirya su fita ita da Abbas wai zasuje asibiti sai dai tayi musu fatan dawowa lafiya, ta lura shima mijin nasu na biyewa Halisan ne dan kawai a zauna lafiya.

Ita kuwa Naja’atu mugun haushin Halisan take ji dan ta soma hankali a lokacin, idan taga tanayi wa mamanta wani abu ranta ‘baci yake sai tayi yun’kurin magana sai Halimatun ta hanata,  sai dai tayi ‘kwafa kawai! ita hakurin mamanta ta har mamaki yake bata, kuma a duk sanda za taga  Abban nasu yana magana da Halisa sai taji haushinsa, tashi ma take ta bar gurin, wani lokacin kuma idan taga sun shiga daki da Halisan sun dade kuka take zuwa taci ta koshi! ta fito tana kumbura fuska, Halimatu ta gane yarinyar na kishinta shiyasa takejin ciwon abinda ake mata,  ta kuma fahimci yarinyar za tayi kishi  sosai dalilin da ya sanya take yi mata ‘yar nasiha a fakaice! Naja’atu kam jinta kawai take yi tana ganin kamar wani abun ma itace take bada goyon bayan Halisan nayi mata, ‘kiri-kiri sai suna zaune a guri daya Halisa zata tsiri wasu abubuwa wanda  suke sawa ta janye hankalin Abban nasu! duk sanda haka ta faru taga ya tashi yabi bayan halinsa ji take kamar zuciyarta zata babbake! ko ya fito bata kulashi idan yazo yana musu magana banza take dashi sai dai yai ta tambayar Halimatu ko wani abun ne yake damunta  Halimatu tasan abinda take fad’a masa  maganar ta wuce! Naja’atu gabadaya daina walwala tayi ta daina sakin fuskarta, rashin kunya  takeyi wa Halisa a duk sanda tasa mata baki a cikin maganarta dan Halisa akwai katsalandan daga zarar tazo taga suna hira da wasa da ‘yan uwanta su Saddiqa da Mussadiq sai tazo ta dinga buga musu tsawa tana hantararsu, aikuwa dama a ciki take da ita, tace watarana suna wasa tazo tana yi musu tsawa! Tace”Mu dan Allah ki daina zuwa kina takura mana muna maganarmu ke waye ya takura miki eye? ina cewa abinda kike so shi kikeyi saboda haka ki daina zuwa kina mana tsawa mtwsss!.” Takarasa maganar tana jan tsaki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button