MADADI Page 11 to 20

Baba Malam kam yana fita ya samu Abbah Abbas din da maganar lallai yau da daddare yake so Naja’atu ta tare a dakinta tunda an daura aure to maganar aja wani lokaci bai taso ba……..Abba Abbas din ya nuna masa cewar ba wai ya’ki maganarsa bane yana so yayi d’an gyare-gyare a gidan, shiyasa yace sai nan da sati biyu…..Baba malam fafur ya’ki yarda da maganarsa Yace bai amince da wani gyara ba za’a kai Naja’atu ta zauna a d’akin ‘Yar uwarta a yanda yake.
Abbah Abbas baya son yayi ta jayyaya dashi sai kawai ya amince da hakan.
Sai da yayi sallahr isha’i a ‘Kofar na’isan sannan ya nufi gidan nashi, Halisa ana zaune a palo anci kwalliya cikin wani uban less tayi ado da gold hannu da wuya da kunne, tayi kyau dai-dai gwargwado, suna zaune ita da yaran suna kallo amma kallo daya za kayi wa su Saddiqa ka gane a tsorace sukayi ko motsin kirki sun kasa yi, shigowar Abban nasu yasa suka sauke ajiyar zuciya suna masa sannu da zuwa….Ya amsa musu yana kokarin shiga dakinsa.
Halisa ta mi’ke tabi bayansa, yana tsaye yana kokarin cire babbar rigar shaddar dake jikinsa, Halisa aka ‘karasa kusa dashi kamar ba ita ba ta taimaka masa ya cire rigar ta ninke rigar ta ajiye gefan gado aka wani kalleshi ana fari da ido cikin kissa tace”Ango kasha ‘kamshi.”! Dariya ta bashi amma beyi ba yace.”Nayi miki kama da ango a haka.”? Murmushi tayi tana ta’be bakinta tace”Sosai kuwa gakanan sai ‘kyallin goshi kake.” Yasa dariya yana kallonta yace.”Ba haka ango yake ba ango zaki sameshi cikin walwala da farin ciki komai nasa sabo amma ni duba ban ma sa sababbin kaya ba fa, kuma yaushe zanyi ‘kyallin goshi bayan har yanzu na kasa samun kwanciyar hankali dake.”
Wani fari tayi da ido tace”Zaka samu kwanciyar hankali dani idan baka tauye min hakkina ba ni kuma zan baka kulawa wacce tafi ta da.” Yace.”To naji maganarki kuma ina rokan Allah ya bani ikon kwakwanta adalci a tsakaninku, nima inaso ki dauke kanki kan dukkanin abinda zai faru a nan gaba inaso ki ri’ke yarinyar nan bisa gaskiya da amana, kece babba dan haka ki ri’ke girmanki ni kuma zan baki mamaki sosai ba zan ta’ba juya miki baya.” jin furucinsa yasa taji wani farin ciki ya cika mata zuciya, Toilet ta shiga ta hada masa ruwa yaje ya wanka ya fito ya shirya cikin sabuwar jallabiya milk sannan suka fito tare, Halisa sai wani ririta shi take, ta hada masa abinci da yaji magani ya zauna yaci da bisimillah a bakinsa…..Sai bayan da ya kammala cin abincin ne ya sheda mata cewar Naja’atu zata tare a dakinta yau dan abinda mahaifinta yace kenan….Cikin ‘kokarin danne bala’in kishin da ya taso mata tace”To yau kana nufin acan zaka kwana kenan.”? Kai tsaye yace mata “Eh.” sunkuyar da kanta tayi ba’kin ciki kamar ya kasheta, Yace.”Idan kina ganin kema zaki zauna a haka ba tare da anyi miki gyara ba gobe kina iya komawa.” Tace”A’a ni bana gaggawa na fiso ka sanja min kujeru da labulaye da kayan gado duk wani abu da babu a can inaso ka samin kafin na tare.”
Yace.”Kada ki damu insha Allah cikin satin da zamu shiga za’a kammala komai.”
To sai kusan goma da rabi ya bar gidan, Halisa ji take kamar ta dawo dashi amma ba yanda ta iya dole ta hakura ta kyaleshi ya tafi ta nufi dakinta cikin takaici da damuwa.
Naja’atu taci kukanta ta ‘koshi bayan ‘Yan kaita sun watse! tsoro ne ya cika mata zuciya gidan ya dinga yi mata gizo gani take kamar zata ga Yayarta, motsin kirki ta kasa yi sai makyarkyata take ita kadai a takure a d’aki! kamar mujiya duk ta tsargi kanta……Mi’kewa tayi cikin tsoro taje ta murzawa ‘kofar d’akin key ta barshi a jiki dan bata so ma idan ya shigo gidan ya shigo inda take, takurewa tayi kan bed tana kuka had’e da kiran sunan Allah, ‘Yar uwarta kawai take tunawa tana zabura!
Abbah Abbas ya shigo gidan cikin motarsa, gurin parking ya nufa, yayi parking din motar yana fitowa maigadi ya ‘karaso ya mika masa hannu suka gaisa, maigadin yace.”Alhaji Ashe ka daura aure to ubangiji Allah ya sanya alkairi ita kuma Hajiya Allah ya jikanta da rahama. Abba Abbas ya amsa cikin kulawa kana yayi masa sallama ya nufi cikin gidan……..Ko’ina shuru sai hasken tarwai a palon, kujera ya samu ya zaune yayi shuru yana jin wani irin yanayi a jikinsa! Gidan da yayi rayuwa da Halimatu yau shi zaiyi rayuwa da kanwarta Yarinyar da bai ta’ba tunanin zai aureta ba……Ya kai minti ashirin zaune a palon kafin ya mike cikin rashin kuzari ya nufi d’akin da yake tsammanin tana ciki…..
A hankali Ya murd’a handile d’in d’akin yana so ya bud’e kofar sai yaji ta a rufe ya murd’a sosai nan yaji alamun key a jiki! Dan buga ‘kofar yayi da hannunsa…….A furgice! ta mike zaune tana zare ido! Ya sake buga kofar dakin had’e da kiran sunanta! jin muryarsa yasa taja tsaki! ta koma ta kwanta.
Cigaba yayi da kiran sunanta yana d’an bubbuga kofar a hankali…………Ta sake mi’kewa zaune murya na rawa tace”Waye.”? Ajiyar zuciya ya sauke jin muryarta hankalinsa ya kwanta da yaji tabbacin tana cikin gidan, Yace.”Bud’e kofar ki kar’bi abinci kici.” Kai tsaye tace”Bana ci.” ta koma ta kwanta! Tsaye yayi a bakin ‘kofar d’akin yana d’an tunani Ya sake dan buga kofar hade da kiran sunanta.
Tace”Abbah dan Allah ka kyaleni kayi tafiyarka wai dole sai naci abinci ni bana bukatar duk wani abu da zai fito daga hannunka.” Yace.”To naji bud’e kofar ina so nayi magana dake.”
Tsaki taja tace”Ni ba zan bud’e maka ‘kofa ba kawai kayi tafiyarka.” Ajiyar zuciya ya sauke yace.”Okey shikkenan yanzu dai kin bani dama na koma inda na fito ko? kai tsaye tace”Eh hakan sai yafi min kwanciyar hankali.” Girgiza kansa yayi ya matsa daga jikin ‘kofar, ledar dake hannunsa ya ajiye kan center teble ya juya ya fita daga palon, yana fita ya fito da key daga aljihunsa ya kulle kofar palon kai tsaye ya nufi inda motarsa take…….
*????️MADADI!!????*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE????*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION????????️*
_’Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*15*
Kai tsaye da ya fita daga gidan Naja’atu gidansa na gwangwanzo ya nufa domin bashi da inda zaije in ba nan din ba, maigadinsa na gidan ya bude masa kofa ya shiga da motarsa ya gyara Parking a nutse ya fito daga motar ya nufi cikin gidan, shuru palon da alama itama Halisan ta dade dayin bacci, kai tsaye bedroom dinsa ya nufa dan ganin kamar hakan shine maslaha koda ya shiga dakinsa bai jira wani abu ya zare jallabiyar jikinsa, yai saura daga shi sai singlet da gajeran wando ya kwanta kan gadonshi tare da rufe jikinsa da bargo, cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya dauke shi…….Komai gajiya da dad’in bacci asubah nayi yake tashi saboda tsabar sabo da yayi da tashin asuba jikinsa har bashi yake lokaci yayi, karfe hudu da kwata ya tashi ya nufi toilet a gurguje ya daura alwala ya fito ya zura jallabiyarsa, dadduma ya hau yayi nafila(raka’atanilfijir) yana idarwa yayi addua yanda ya sawwa’ka kana ya mi’ke ya fita…….Dakin Halisa ya nufa domin tashinta, ya tarar da ita tana sharar bacci, tsayawa yayi a kanta yana dan bubbuga bed din da kiran sunanta, Halisa firgigit ta tashi zaune tana kallonsa, cike da mamaki tace” Yanzu ka shigo gidan ne.”? Girgiza kansa yayi yana kokarin fita daga dakin yace.”Ai anan na kwana lokacin dana shigo kinyi bacci ki tashi kiyi sallah.” Ya bud’e kofar dakin ya fita.