MADADI Page 11 to 20

*????️MADADI!!????*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE????*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION????????️*
_’Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~~~~~~~~ *16* Ya jima a dakin yana sa’kawa da kwancewa kafin ya fito palon, inda ya sameta a takure a kan kujera har yanzu bata daina zubar da hawaye……Saboda jin haushin maganar data fad’a masa yasa ya kama hanyar fita dan baya so ya zauna a gidan zuciyarsa ta tunzira shi a kanta, dan ya lura koda ‘kuruciya a tare da ita to da akwai iskancin dan iskancin ma yafi yawa a tare da ita, gabad’aya ya lura ta raina shi kuma ta daina ganin girmansa, wannan d’abi’un da take masa na ‘bata masa rai sosai da sosai! Yana dab da fita yaji ta ri’ke masa hannu, ya juyo fuskarsa babu walwala yana kallonta yace.”Me zanyi miki kuma.”? Cikin rawar murya tace”Dan Allah zan bika dik inda zakaje kada ka barni ni kad’ai wallahi ba zan iya zama ba.” Shuru yayi yana kallonta na minti biyu kafin yace.”Jeki dauko hijab din’ki.” Da sauri ta saki hannunsa Hijab dinta dake kan kujera ta d’auka tasa ya nuna mata ‘kofar fita da hannunsa, da sauri ta fice tana sauke ajiyar zuciya, kwana d’aya tayi a cikin gidan jin ta take tamkar a cikin ‘kaya, kulle ‘kofar palon yayi yazo shigeta ya nufi motarsa….Bin bayansa tayi da saurin gaske, ta ma rigashi bude motar ta shiga ta zauna tana zazzare ido, sai da ya gama magana da maigadinsa sannan ya shiga motar, yana zama tace.”Jakar kayana na manta ban dauko ba kuma tana d’akin Yaya Halimatu.” Ya kalleta cikin rashin walwala yace.”To meye amfanin daukar jakar kaya ke a tunaninki ina zan kai ki.”? Tace.”Na dauka zaka mayar dani gidan Baba Malam.” Girgiza kansa yayi yace.”Ba can zan kaiki ba zan kai ki gidan Halisa ku zauna da yara zuwa dare sai mu dawo gidan tare.” Fashewa tayi da kuka tace”Dan Allah ka daka mu dawo ni wallahi akan na zauna gidan nan gwara na zauna a gidan Anti Halisan yafi.” Yace.”Kina ganin zaki iya zama a gidan.”? Da sauri tace”Eh zan iya.” Ba tare da yace komai ba ya bud’e kofar motar ya fita, cikin gidan ya koma ya shiga, jakar kayanta dake dakin Halimatu ya dauko mata ya fito.Ganinsa dauke da jakar kayanta yasa ta sauke ajiyar zuciya,tana ganin gwara ta zauna a gidan Halisa akan ta zauna ita kadai a wannan uban gidan wanda ake bata tsoro, bayan mota yasa jakar, ya shiga ya zauna ya tada motar ya fita daga cikin gidan……..Tana ganin sun hau kan titi ta sauke ajiyar zuciya wacce ta sanya shi dan kallonta da gefan ido, ya dauke idonsa tare da maida hankalinsa gurin draving din da yake………….Motar tayi tsit! na kusa minti goma kafin yayi gyaran murya a nutse ya ambaci sunanta! ta kalleshi tare da amsawa, Yace.”Ina so inyi miki wata tambaya bana son ki munafurce ni ko kuma ki ‘ki fad’a min gaskiya.” Tayi shuru tana wasa da yatsun hannunta, Yace.”Me yasa bakya so kiyi rayuwar aure dani.”? Kallonsa tayi ya gyada mata kansa a nutse yace.”Amsa nake so ki bani bance kuma ki bani amsar da zata ‘bata mun rai ba.” Tace”Saboda na dauke ka a matsayin mahaifina shiyasa nake ganin kamar haramun ne nayi rayuwar aure da kai.” Yace.”Waye ya fad’a miki haka? shiru tayi Ya cigaba da cewa” Aure a tsakanina dake ba haramun bane Naja’atu, dan na ri’ke ki kin girman a hannuna hakan ba zai hanani na raya sinnar ma’aiki dake ba mutukar Allah ya kad’dara hakan a tsakanina dake, mutane nawa ne sukayi irin wannan auran na *MADADI* kuma auran yayi albarka, inaso ki sani da badan mutuwa ta raba tsakanina da Halimatu ba to da babu abinda zai sanya ni naji sha’awar auranki, na kwadaitu da auranki ne dan ina ganin kamar zaki maye min gurbin matata ta gurin kyawawan halaye gami da sadaukarwa, ashe ba haka abin yake ba, Allah yasa kun fito ke da Halimatu ta tsatso daya amma kuma halin kowa ya bambanta, shin meye aibuna da bakya so kiyi rayuwar aure dani? ko kina ganin ba zan iya dauke miki dukkanin bu’katunki ba ne? Shuru tayi kanta a kasa tana ta nazarin maganganunsa, Ya cigaba da cewa…..”Nasan babu irin sa’ke-sa’ke da zuciyar ki ba tayi miki a kaina, kina ganin kamar nazo da son zuciya a cikin al’amarin a matsayina na babba ba yaro ba na aure ki, kina ganin tamkar na cutar da rayuwarki ne tunda na hanaki auran saurayi wanda ya dace da rayuwarki ko ba haka bane”.? Kasa magana tayi, Ya cigaba da cewa” Nasan kin san da cewar Annabi Muhammad (slw) ya auri Nana Ayshatu tana ‘yar shekara tara, yayin da shi kuma yake da shekara Hamsin, to kuwa idan hakane aurena dake babu haramci a ciki tunda wanda akayi duniya dominsa ma ya auri ‘yar ‘karamar yarinya wacce bata kai matsayin shekarun da kike ba a yanzu, ina ganin ni na aikata sinna mai kyau tunda nayi irin abinda Annabi ya aikata.”……Naja’atu duk jikinta yayi sanyi da maganganunsa, Ya cigaba da cewa” Inaso ki san da cewar abinda kike tunanin wani saurayi mai tashen balaga zaiyi miki a zamantakewar aure to Matashin mutum kamata dan kimanin shekara hamsin zaiyi miki abinda yafi wanda kike tunanin shi saurayin zaiyi miki.” ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa” Mafi akasari ‘yan matan yanzu abinda ke damunsu kenan…. (((‘kalubale gare ku ‘yan mata masu tashe saboda ku na zauna nayi wannan littafin, dan akwai masu ‘karamar ‘kwa’kwalwar da za suce su baza su auri tsoho ba sai saurayi, toh wallahi bari na fad’a muku a wannan zamanin ba’a tsayawa za’ben miji, idan kikace xaki tsaya za’be-za’be to zaki tsufa baki yi aure ba, idan magidanci mai mata yazo auranki idan har anyi binkice mai kyau a kansa an gane cewar yana tsaye a kan gidansa da kula da iyalinsa to ki lalla’ba ki shiga daga cikin, idan kin tsaya kince ke sai saurayi to zaki iya auran saurayin kuma ki kasa samun biyan bukatarki, Samarin yanzu duk ‘yan bana bakwai ne kuma mafi akasari auran sha’awa suke daga zarar bukatarsu ta biya shikkenan zaki fuskanci kalubale, bance duka aka taru aka zama daya ba amma dai abinda yake faruwa na fad’a, idan kuwa kika auri wanda ya dan kwana biyu to shi yasan menene aure saboda ya dade a cikin inuwarsa zai ri’ke ki da kyau kuma duk wata soyayya da kike tunanin saurayi zaiyi miki to sugar Dady d’in da kika raina zaiyi miki wacce tafi ta saurayin domin shi tsohon hannu ne a harkar????)))) Abba Abbas ya cigaba da cewa” Abinda yake damun su kenan sai suce su baza su auri tsoho ba dan suna ganin kamar idan sun auri mai shekaru baza su more kuruciyarsu ba, wanda kwata-kwata ba haka bane sunyiwa abun mummunar fahimta ne, inaso ki zauna kiyi tunani mai kyau a kan wannan maganganun da mukayi dake, Na farko ni ban haife ki ba, ballanta ki dinga ganin kamar kin aikata haramci dan kinyi mu’amular aure dani! Na Na biyu kuma wad’annnan abubuwan da kike yi sun soma isata idan baki gyara ba to zan dauki mataki a kanki, ni ba yaro ‘karami bane ballanta ki dinga yi min iskancin da duk kika ga dama, a yanzu ni ina a matsayin mijinki ne ba Ubaba kamar yanda kike dauka a da to yanzu ba haka bane! Wallahi! duk ranar da na sake jin kin fad’i wata mummunar magana a kaina da aurana sai na ‘bata miki rai! na dauka kuruciya ce ke damunki sai kuma daga baya na gane rashin arziki ne, to ni ba lusarin namiji bane ke zaki fadawa kowa hakan tunda kin taso a gidana kinga yanda nake zamantakewar aure da mataye na, suna bani girma suna mutuntuni babu wacce take fad’a min bakar magana ko kuma taja min tsaki! dan haka nake gargadinki ki kiyaye aikata abinda zai janyo miki ‘bacin raina.”