MADADI 1-END

MADADI Page 11 to 20

‘Kasa tayi da kanta! Baba Talatu tace”Kina so ki janyowa kanki damuwa da ciwo da kinyi halin Halimatu da ba kiyi mana gardama ba, Halimatu komai muka umarceta dashi tana mana biyayya dai-dai gwargwado amma ke tun jiya ake magana daya dake, idan kika bujirewa umarninmu baki kyauta mana ba kuma baki kyautawa ‘Yar uwarki ba, a yanzu babu abinda za kayi kisa ta farin ciki illah ki zama *MADADIN TA* Ki tallafi abinda ta bari gasu nan suna kallonki.” Ta nuna su Saddiqa dake zaune.

Shuru tayi ta kasa magana ba wai dan bata da abin cewa ba kawai dai bata son suyi ta sa’insa da iyayenta…..Baba Malam dai shuru yayi ya dauki kofin kununsa yana sha yana had’awa da kosan sa dake cikin wata silba dake gabansa.

Saddiqa ce ta zuba mata kunun ta ajiye mata a gabanta sannan ta mi’ka mata abun da ‘kosan ke ciki tace”Yaya Naja’atu gashi nan ki karya kema.” Kallonta tayi sai taji zuciyarta ta tsinke! sosai yaran suke bata tausayi Saddiqa ta damu da ita sosai koda can bata son taga ‘bacin ranta, tabbas a wannan lokacin ne ya kamata tayi mata sakayyar abun alherin data dad’e ta nayi mata.

Domin Saddiqar taji dadi yasa ta dauki kofin kunun tana kur’ba a hankali tana had’awa da kosan dake gabanta, Baba malam na gama karyawa sai ya dauki redion sa ya mike yana kallonta yace.”Idan kun gama kun kintsa ku shiga gidan Alhaji dake dasu Saddiqa ku gaishe dasu.” A sanyaye tace”Inasha Allah.” takalmansa dake bakin kofa yasa ya fita daga gidan hannunsa ri’ke da redionsa.

Suna gama karyawa sai sukayi wanka suka shirya tsaf! Naja’atu da Saddiqa suka shirya cikin kaya iri daya hatta da d’inkin jikin atamfar iri daya ne komai iri daya Abbah Abbas ke musu baya bambamta su sai da gurin d’inki na Naja’atu yana d’ara na Saddiqa da wani abun, milk din hijabi toyobo ne a jikinsu ya sauka har ‘kasa! Suna kokarin fita daga gidan da nufin shiga gidan Alhaji Sama’ila, Shi da Salim suna kokarin shigowa cikin gidan.

‘Kamshin turaransa ne ya tabbatar mata da cewar shine Kafin ma tayi wani yunkuri sun shigo Shine a gaba Salim na take masa baya, Yana sanye da farar shadda kar ‘Dinkin tazarce har kasa, da adon surfani a wuyan rigar da hannunta kansa sanye da farar hula mai ratsin ‘baki! a zahiri idan ka kalleshi ba zaka ce ya kai shekarun da yake dasu ba, za’afi tunanin shekarunsa ba sufi 43 zuwa 45 ba, Abbah Abbas mutum ne dan gayu mai yawan ado da kwalliya, kuma ma’abocin kamshi shiyasa kullum baka ganin tsufasa, dan idan yace ya kai matakin shekara 50 a duniya da yawa wasu ba zasu yarda ba, sai dai kuma masu nazari da tunani idan sukayi masa kallon tsanaki a zasu fahimci cewar ya kai shekarun da ya fad’a d’in………Da gudu Mussadiq yaje ya rungumeshi yana fad’in ”Oyoyo Abba.” Yana d’an murmushi ya bashi hannunsa tare da fadin”Barka da Asuba magajin Abbah.” Mussadiq na dariya ya rike hannun mahaifin nasa suka gaisa sosai……..Saddiqa na murmushi tace”Abba ina kwana ka tashi lafiya.”? A nutse ya d’aga kansa yana kallonsu ita da Naja’atun Yace.”Lafiya lau na tashi Ina zakuje da sassafe haka.”? Yana kallon Naja’atu yayi maganar.”!

 A kanta a kasa ta gaishe kafin tace”Zamu shiga gidan Alhaji ne mu gaisa.” Yace.”To babu damuwa nima yanzu zan shigo gidan.” Kokarin ratse ta yake ya shiga cikin gidan, tayi saurin bashi hanya, tana sunkuyar da kanta, gani tayi yau fuskar sa babu walwalar da ya saba yi mata koda yake ai dole dama ya kasa sakin jiki da ita saboda yasan abinda yayi.

Ta kalli Saddiqa tace”Kuje gani nan zan biyo bayanku.” Saddiqa ta kalleta tana kallon Salim da yayi wani kici-kici da fuska yana kallonta ya wani zuba hannuwansa a cikin aljihun jins din dake jikinsa…..Saddiqa jikinta sanyi yayi ganin yanda Naja’atun ta wani d’aure mata fuska! sai taja hannun Mussadiq suka fita daga gidan

Salim ya tsira mata ido bayan fitar su Saddiqa yace.”Me kike fahimta ne daga gurin wannan Dattijon.”? Cikin sanyin jiki da sarewa da al’amarin tace”Ni wallahi har yanxu na kasa gane inda ya dosa, dazu dai munyi waya dashi na ro’ke shi akan ya janye kudirinsa yace.”zai yi shawara idan ya yanke magana zai fad’awa Baba malam abinda ake ciki.”

Cikin ‘kunar zuciya Salim yace.”Jikina baya bani cewar Mutumin nan zai hakura dake My Princess shin idan ya kasance shine ya samu damar mallakar ki ya zanyi da raina watakila ma ina jin shikkenan ‘karshen rayuwata ne yazo.” Cikin wata iriyar siga yayi maganar yana matsawa kusa da ita.

Hawaye ne suka ‘kwace mata tace”My Prince ka daina wannan maganar dan Allah insha Allah Allah ba zai bashi nasara ba, Ni bani da wani miji sai k……….Maganar ce ta ma’kale a bakinta sakamakon zuwansa gurin! Ya kallesu sunyi wani daf da junansu kamar zasu rungume junansu, kana kuma kallon yanayin su zaka fahimci suna cikin mayen son junansu a lokacin kome zasu iya aikatawa! Tsawa ya buga musu yana kallon Salim din Yace. “Kai meye haka ka tsaya daf da ita rungumeta zakayi ko me.”?

Salim yayi gaggawar barin kusa da ita yana sosa kansa irin na kunya yace.”Kawu kasan sau tari nakan shiga wani yanayi idan yarinyar nan na kusa dani, dan Allah Kawu kayi wani abu akan al’amarin aurena da ita.”

Kallon shashasha yake masa kafin yayi ‘kwafa ya kalleta tana ra’be a jikin bango tana goge fuska! Kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa, ya kalli Salim din rai a ‘bace! yace”Shige muje.” Salim ya shiga sosa kansa yana d’an kallonta ta ‘kasan ido ya fita daga gidan, shima ba tare da ya sake kallon inda take ba ya fita ranshi a ‘bace! wani irin kishi ne yake damunsa a zuciyarsa ganin abinda ya wanzu tsakaninta da Salim..

*????️MADADI!!????*

_(Ba Haram Bane!!))_

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE????*

*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION????????️*

_Kungiyar Masu Nazari Da aiki da Ilimi_

~~~~~~~~~~~~~~~

*9*

Cikin sanyi jiki da mutuwar jiki ta fita daga gidan, koda ta fita kai tsaye gidan Alhajin ta nufa tana tafiya kanta a kasa ga wani irin fad’uwa da gabanta yake, tana tunanin idan ta shiga gidan da wane irin ido zata kalli mahaifiyar Abbannasu matar data dauka a matsayin kakarta suke wasan jika da kaka da ita, yau an wayi gari wai itace take nema ta zama surukarta akwai kauna da fahimta a tsakaninta da Hajiyar tana ganin idan Abba Abbas din bai janye ‘kudirin sa ba zata nemi taimakon matar tunda mahaifiyarsa ce watakila idan tayi masa magana ya janye.

Tana shiga gate din gidan, ta hangi Abba Abbas din da Abba Alhassan ‘kaninsa da kuma Salim d’in a tsaye a jikin wata mota suna magana, Tun daga nesa take kallonsu Abba Abbas din! Tsaki! taja a zuciyarta ta kalli Salim dake kusa dashi, humm yaushe ma za’a had’a! Salim saurayi mai tashe mai jini a jika gashi dan gayu dan kwalisa, babu abinda yake burgeta a dashi sai ‘kayatacciyar fuskarsa mai dauke da siririn saje wanda yayi masa kyau sosai tana bala’in son Salim saboda kyawunsa kuma ya iya kwalliya mai burgewa, shi kuwa Abba Abbas ya wani bar gashin fuska (gemu ) ya cika masa fuska duk da cewa a gyare yake hakan bai burgeta ba, babban abinda yake ‘kara sawa ta sake jin tsanar auransa, shine tsali-tsalin furfurar data fara fito masa a gashin fuskarsa(gemu) Ai abin dariya ne ma ta nunawa kawayenta shine mijinta, gaskiya ita kam ba zata iya auransa ba, a tsarinta tafi son ta auri Saurayi wanda zasu mori ‘kuruciyarsu amma auran Abbah Abbas babban nak’asu ne a tattare da ita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button