MADADI 1-END

MADADI Page 11 to 20

Yaya Ramlatu ta share guntin hawayen fuskarta a sanyaye tace”Hajiya ban san al’amarin zaiyi miki zafi haka ba dan Allah kiyi hakuri idan ranki ya ‘baci kuma insha Allahu zan umarci Salim ya janye maganar auransa da yarinyar Allah yasa haka shi yafi alkairi.” 

Jin abinda tace ne yasa Naja saurin kallonta hawaye na tsere a fuskarta shikkenan magana ta ‘kare! jiki a sanyaye ta mike ta fita daga palon.

Salim na driving maganar dake damusa nata cin zuciyarsa, ya dan kalli Kawun nasa dake bayan mota shi da ‘Kaninsa suna magana, Yace.”Kawu ina da magana da kai.”! Babu walwala a tare dashi yace.”Ina sauraranka.” Da kyar iya cewa “Dama kan maganarmu ta kwanaki ce.” Kamar be san komai ba yace.”Wace irin magana kenan.”? Salim cikin dakewar zuciya yace.”Maganar Naja’atu mana a cikin ‘yan kwanakin nan gabadaya zuciyata ta kasa daurewa sai nake ganin kamar akwai wani abu da zai faru dan Allah ina so kaje ka nema min auranta kamar yanda kayi min al’kawari a kwanakin baya.”

Shiru motar tayi babu wanda yayi magana, Abbah Alhassan mamakin maganar da Salim din yayi yake ashe dama soyayya ce a tsakanin Salim da Yarinyar? to me yasa dan uwan nasa yasan da soyayyar dake tsakaninsu ya bijiro da bukatarsa.

Shuru Abba Abbas yayi ba wai dan bashi da abin cewa ba, sai dan ganin cewar shi a gurinsa a bin kunya ne ace yana maganar aurensa da Salim d’in, yafi so yaron yaji maganar a bakin wani idan yaso ya gane ruwa ba’a sa’an kwando bane….

Shurun da yayi tasa jikin Salim yin sanyi, tabbas yanzu ya gazgata maganar Naja’atu cewa Abba Abbas din da gaske yake ba gudu babu ja da baya.

Yaji wani irin d’aci! a ma’kogwaronsa! dishi-dishi! yake gani a idonsa tsabar bakin ciki da ‘bacin rai! Ga wani masifar kishin Kawun nasa dake sasakar zuciyarsa! Wai yau an wayi gari wanda yake tunanin shi zaiyi masa wakilcin aure shine yake kassaya dashi………Shi kuwa Abbah Alhassan ganin ‘Dan uwan nasa bai ce komai ba yasa yaja bakinsa yayi shuru haka suka isa kasuwar kowa na sa’ke-sa’ke a zuciyarsa mussaman Salim da yake jin shigar zazzafan zazzabi a jikinsa.

Yaya Ramlatu na fita daga gidan Alhaji Kai tsaye unguwar gwangwazo ta nufa gidan d’an uwan nata……..Halisa na zaune a palo tana kallo Yaya Ramlatu ta shiga da sallama a bakinta……Halisa ta mike tana mata barka da zuwa taje ta kawo mata abinci da ruwa da lemo kana ta zauna suna gaisawa.

Yaya Ramlatu sai da ta cika cikinta ta ‘koshi tukkuna, ta kalli Halisan tace”Kin san gagarimar maganar da nake tafe da ita kuwa.”

Halisa taji gabanta ya fadi! a sanyaye tace”Ban sani ba Yaya sai kin fad’a.”

Murmushin takaici Yaya Ramlatu tayi kafin tace”Kina zaune da baki a bud’e har kin samu damar zama kiyi kallo ana can ana shirya miki kasassa’ba.”!! Halisa miyau ya dauke daga bakinta tace”Yaya Ramlatu dan Allah fad’a min abinda ke faruwa.” 

Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace”Mijinki Abbas nacan yana neman auran budurwa ‘yar cikinsa, auran cuta da ha’inci Auran da duniya za tayi turr! dashi.”!

Halisa ta zabura! ta dafe kirjinta gabanta na wani irin buguwa tace”Aure kika ce Yaya Ramlatu.””? Tace”Kwarai kuwa.” Tafada tana tabbatar mata da gaskiyar magana 

Wani irin gumi ne ya shiga tsiyaya daga jikin Halisa! “Aure!aure! kalmar ma ba babu dadin ji a kunnanta, wato duk ladabi da biyayyar da take masa da nuna masa kulawar da Halimatu take masa bai sa yaji sha’awar aure ya fita daga ransa ba? ashe duk abinda takeyi masa na kulawa a banza take mutuwar Halima ko sati biyu ba’ayi ba amma har ya fara kokarin aure, shin wai dame ta gaza ne a gurinsa……wasu hawayen takaici da bakin ciki ne suka shiga sauka a kumatunta…..Yaya Ramlatu tace.” Ai ba kiyi kuka ba ma tukkuna sai kinji yarinyar da zai aure.”! Bakinta na rawa tace.”Wacece.”? Kai tsaye Yaya Ramlatu tace”Naja’atu ce.” Sai tayi kasa’ke tana kallonta tunani takeyi wacece ma Naja’atu! dan a lokacin gabadaya kwakwalwarta ce ta toshe ta mance a inda tasan mai irin sunan.”

Yaya Ramlatu tace”Kina mamaki! ko da jin wacce mijinki zai aura bari na ‘kara tabbatar miki da maganar, Abbas zai auri Naja’atu kanwar matarsa Halimatu yarinyar da ya ri’keta tun tana ‘karama yayi mata komai tamkar ‘yar cikinsa! shine yanzu zai maye gurbin ‘yar uwarta da ita.” Halisa ta dinga jin hajijiya tana daga xaune! rintse idonta tayi tana tunano siffofin Naja’atu a idonta!!! a gigice ta bude idonta ta zabura ta mike tsaye tare da cewar “Wallahi ba zaiyi wuba !! ba zan yarda da wannan cin amanar ba! Ni Abbas zaiyi wa haka? me nayi masa a duniya zai had’ani kishi da yarinya ‘karama ‘yar cikina! kutumar uban nan kayyasa!! sai ta zube kasan kafet ta fashe da wani mahaucin kuka tare d’ora dukkanin hannuwata a kanta.

*????️MADADI!!????*

_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE????*    

~~~~~~~~~

*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION????????️*

_’Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_

~~~~~~~~~

 *10*

Wani irin kuka Halisa takeyi tamkar wacce aka aiko mata da mutuwar iyayenta, ta d’ago kanta tana kallon Yaya Ramlatun fuskarta gaje-gaja da hawaye tace”Yaya Ramlatu ina zan saka kaina da wannan abun kunyar! shin wai me yake damun d’an uwanki ne? Ya rasa wacce zai aura sai ‘yar cikinsa yarinyar da ya ri’ke tamkar shi ya haifeta amma saboda tsabar abun kunya yace zai aureta tsofai-tsofai dashi zai auri ‘yar ‘karamar yarinya babu shakka wannan karon komai zai faru tsakanina dashi sai dai ya faru dan na rantse da Allah ba zan bari ya tozartani ya had’ani kishi da matsiyaciyar yarinyar nan da na riga nasan matsayinta a zuciyarsa ba.”

Ya Ramlatu ta sauke ajiyar zuciya tana fad’in “Ai shiyasa nima dana ji labarin hankalina ya tashi sosai! Kishi da irin jinin Malam Baba ai bala’i ne wane irin daurin gindi ne Halimatu bata samu ba a gurin Abbas din, ai wallahi kece abar tausayi mutukar kika bari ya auri yarinyar nan to ki rubuta ki ajiye auran ki ya ‘kare tsakaninki da mijinki.”

Yaya Ramlatu ta ‘kare maganarta cikin karfafa maganar ta gami da ‘kokarin ‘kara ingiza zuciyarta.

Goge fuskarta tayi tace”Yaya Ramlatu ai na fad’a miki wallahi tallahi sai dai ya za’ba ko ni ko yarinyar nan dan ni ba zanyi kishi da Yayarta ba itama nazo nayi da ita ba, wannan karon duk abinda yake ji dashi dai-dai nake dashi zai dawo gidan ya same ni.”

Yaya Ramlatu ta dauki lemo ta kur’ba tace”To ai dik da haka ba zama za kiyi ba dole ki d’an nemi taimako dan baki san irin shirin da iyayen yarinyar suke a kan al’amarin ba, dan wannan tsinannan Malam Baba mugun mutumi ne babu irin surkullan da bayayi.” Halisa tace”Yaya Ramlatu ni yanzu gabadaya ma banda kuzarin zuwa gurin wani malami da sunan taimako nifa gabad’aya auran Abbas ya fice min daga rai ya dawo ya sake ni.” Ta’karasa maganar cikin rawar murya. Yaya Ramlatu tace”A’a ba za’ayi hakaba ke yanzu idan kika kashe auranki saboda wannan yarinyar ai kin cutar da kanki! kada kice ya sake ki kawai idan ya dawo ki daga masa hankali ke macece kin san hanyoyin da zaka hanashi nutsuwa da kwanciyar hankali gefe guda kuma zamu sa malamai su taimaka miki insha Allah sai zuciyarsa ta karye yaji sha’awar auran ya fita daga ransa da kansa zaice ya fasa.”

Halisa tayi shuru tana tunani! Yaya Ramlatu tace”Dole ki futo da kudi aje a taimaka miki ni gaskiya bazan so ki bar dakin ki ba, ki zauna kici ubansu daga shi har yarinyar idan Allah ma ya kaddara sai ta shigo gidan sharri kad’ai ya isheta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button