MADADI Page 11 to 20

Halisa taja ajiyar zuciya tare dayin ‘kwafa, tace”Maganar ki haka take Yaya Ramlatu bari na kawo miki dan abinda ke hannuna dan Allah kiyi min kokari akan al’amarin.” Yaya Ramlatu tace”Kada ki damu zan shiga na fita insha Allahu maganar auran zata rushe ke idan ma Allah ya kaddara auran to wallahi ba zamu k’yalesu suji dad’in rayuwa ba.” Halisa ta gyada kanta tana dan jin sassauci acikin zuciyarta, bedroom dinta ta nufa, minti biyar ta fito hannunta rike da kudi ‘yan dubu dubu. Ta mikawa Yaya Ramalatun da fadin “Dubu ashirin ne zuwa gobe sai ki aiko a kar’bi dubu talatin din zanyi duk yanda zanyi na dauki key din gurin da yake ajiyar kudi na dauka.”
Yaya Ramlatu ta mike tana gyara yafan mayafinta tace”Nima daga nan zan wuce gidan *’Yar shagamu* (wata hatsabibiyar ‘kawar Ramlatun ce)Ta cigaba da cewa……”akwai wani malami da mukayi hirarsa kwanaki da ita tace ya iya aiki idan dare baiyi ba zamuje idan kuma dare yayi to da sassafe zamu buga sammako dan kada muje mu tarar da mutane.” Halisa taji wani sanyi a ranta tace”Yaya Ramlatu nagode kawarai da kaunar da kike nuna min hakika ina alfahari dake a cikin ‘yan uwan Abbas kina nuna min kaunar da mahaifiyarku ma bata nuna min.”
Yaya Ramlatu ta dafa kafadarta tace”Kada ki damu cikin ko wane irin hali ina tare dake, maganar Hajiyarmu kuwa dama can tafi kaunar Halima a kanki saboda gidan Malam Baba sun riga sun gama dasu daga ita har Alhajin, dan baki ga yanda suke murna da wannan al’amarin ba, Hajiya har da kuka tana ‘kokarin yi min baki akan nace auran Abbas da yarinyar bai dace ba, shine fa take kuka har dayi min gorin abinda Abbas din keyi wa Salim.”
Halisa ta shiga girgiza kanta, cikin ‘kunar zuciya tace”Ai ba sai kin fad’a mun ba dama tuntuni na san Hajiyarku bata sona ko lokacin Halimatu tafi nuna kulawarta a kanta, to kinga kuwa dole taso wannan al’amarin ni na rasa me nayi mata ta tsaneni.”
Yaya Ramlatu tace”Wallahi duk sharrin daga gidan Malam Baba yake gabadaya fa sun gama da zuciyoyin jama’ar gidanmu nice kadai na gagaresu.” Halisa na jin d’aci a ma’kogwaronta tace”Insha Allahu sai mun karya alkadarinsu.”
To sallama sukayi da juna inda Yaya Ramlatu take sake tabbatar mata da cewar yanzu idan ta fita gidan *’Yar Shagamu* zata nufa domin su tattauna yanda al’amarin tafiya gidan malam zai kasance.
Koda Naja’atu ta koma gidan Malam kai tsaye dakinsu ta shige taje ta kwanta kan katifa, ta dinga kuka tana birgima kan katifar! sai sambatun surutai take da kiran sunan Halimatu wai ta mutu ta bar baya da ‘kura mutuwarta tana nema ta zame mata barazana ga rayuwarta………..Sautin kukan tane ya cikawa Baba Talatu kunne da sauri ta fito daga kicin ta nufi dakin, nan ta tarar da ita sai burgima take kan katifa tana dukan kanta da kanta kamar wata mahaukaciya sai surutai takeyi da fad’in in dai aka daura mata aure da wani ba Salim ba to sai ta kashe kanta ta kashe wanda aka aura mata……Baba Talatu ta shiga dakin hankalinta a tashe ta birkitota wani wawan mari ta kifa mata a fuskarta tana wani irin huci!! Rintse idonta tayi ta mike zaune hannunta kan kuncinta idanunta a rufe amma hawaye ne kawai yake zurara.
Murya na rawa Baba Talatu tace”Naja’atu idan baki kashe kanki kin kashe Alhaji Abbas ba bakya kaunar Allah! Wai shin ke d’in wace irin yarinya ce butulu mai manta alkairi! yanzu da abinda zaki sakawa da wannan bawan Allahn kenan? wannan wace irin ‘kiyayyace kike nuna masa ‘karara? meye bai miki ba? ki sani idan da mutuwa bata ratsa tsakaninsa da matarsa ba ke baki isa ya kalleki ba ballanta yace zai aure ki dan saboda baki dace daki auri nagartaccen namiji kamar wannan ba! meye laifinsa? meye kuma illarsa!? Muna tsaka da alhani gami da rad’ad’in mutuwar ‘yar mu mai biyayya kina nema ki d’ora mana ciwo! ashe bamu isa dake ba? ashe kuma Halima bata cancanci sakayya al’kairi a gurinki ba? Idan kin auri mijin Halimatu babu wanda zai kai ki Jin dad’i itama kuma zata samu farin ciki alkairin da kikayi mata kin auri mijinta bayan babu ranta kin tallafi ‘yayanta! to wallahi duk sanda na kara jin kinyi wani mummunan furuci kan wannan bawan Allahn sai ranki ya ‘baci! sai na fad’awa Magaji duk abinda kike yi tunda ni da malam kin raina mu bakya ganin mutuncin mu.”!! Baba Talatu ta kare maganarta cikin tsantsar ‘bacin rai gami da jin takaicin abinda ‘yar tata takeyi.
Baba Talatu fita tayi daga dakin ranta a ‘bace! hakika yarinyar bata ta’ba ‘bata mata rai ba irin yau! ita rasa gane meye abin gudu a game da wannan auran da suke kokarin had’awa, a iya tunaninta da tsinkayen ta tana ganin kamar gata sukayi wa yarinyar har indai sun had’ata aure da mijin ‘yar uwartata dan hausawa na cewa Naji dad’i shine gari ba nasa baba……..Baba Talatu na fita daga d’akin ta zame a hankali ta kwanta kasan ledar dakin tana takure jikinta ta cigaba da kukan rashin mafita, a lokacin ji take yi dama Allah zai dauki ranta ta huta daganin wannan masifar………. Koda Saddiqa da Mussadiq suka shiga dakin suka sameta a kwance tana kuka! Mussadiq ne kawai ya tsaya a kanta yana mata magana ita kuwa Saddiqa saboda tasan ko kukan me takeyi yasa ta juya ta fita daga d’akinta ranta a ‘bace! hakika tana jin ba’kin ciki da takaicin irin ‘kiyayyar da take nunawa mahaifinta, shiyasa itama ta soma jin haushinta akan irin abinda takeyi kan al’amarin.
Mussadiq ya ‘karaci maganarsa ko kallonsa ba tayi ba haka ya fita daga dakin jikinsa duk a sanyaye! haka suke shiga damuwa koda can idan sun ganta tana kuka ko rashin lafiya daga su har mamansu da Abbansu duk su damu duk da bashi da wayo sosai shima ya fahimci cewar Antin tasu bata ‘kaunar zaman aure da babansu……..Zama yayi kusa da Saddiqa tana gyarawa Baba Talatu wake suna hira jefi-jefi ya kalli Baba talatu da fad’in “Baba me akayiwa Yaya Naja’atu take kuka.”? Baba Talatu tace.” Kyaleta Mussadiq ka fita daga sabgarta kaji ko.” Mussadiq yayi shuru jikinsa duk yayi sanyi………To Har aka idar da sallahar azuhur Naja’atu na kwance a daki tana juye-juye zazza’bi me zafi ne ya rufe ta wanda ya hanata mikewa taje tayi alwala tai sallah.
Saddiqa ta shiga dakin domin yin sallah ta kalleta itama ta kalleta babu wanda yace komai a tsakaninsu, Saddiqa ta gyara dadduma ta tayar da sallaharta, koda ta idar mikewa tayi ta fita daga dakin ba tare da tace komai ba, to sai hakan da tayi ya bata mamaki sosai! kuma ya nuna mata cewar yarinyar fushi take da ita, jikinta ne yayi sanyi sosai ta rinste idonta murya na rawa tace”Ba laifi na bane laifin zuciyata ne Saddiqa bana ‘kin mahaifinku sai dan zuciyata ta riga ta gama makancewa da kaunar Salim, a dai-dai lokacin da muke sanya rai da bukatarmu zata biya a dai-dai lokacin kuma za’a kawo mana cikas a rayuwarmu ha’kika rayuwarmu nida Salim na cikin kalubale mai girma mutukar akace baza’a daura mana aure da juna ba.”
Muryar Mussadiq taji a kanta, tayi saurin bude idonta tana kallonsa……Mussadiq duk yaji abinda take fad’a ya fahimci wata maganar wata maganar bai fahimce ta ba, Yace.”Yaya Naja’atu ki tashi kiyi sallah kici abinci mu tuntuni munyi sallah munci abincinmu.