MADADI Page 11 to 20

Hannunsa ta ri’ke ya zauna kusa da ita murya na rawa tace”Mussadiq bani da lafiya zuciyata na daf da tarwatsewa.”!! Da sauri yaron ya d’ora hannunsa saman goshinta yana fad’in “Yaya Naja’atu kanki ne yake ciwo ? sannu bari na kira Abbanmu a waya ya kawo miki magani.” Girgiza kanta tayi tana kokarin mikewa zaune tace”Mussadiq wannan ciwon nawa Abbanmu shine ya haddasa mun shi dan Allah kace dashi yayi hakuri ya k’yaleni.” Mussadiq ya dinga kallonta cikin mamaki yace.”Yaya Naja’atu Abbanmu ba zai cutar dake ba kiyi hakuri ki aureshi ki zauna dashi.”! Taji wasu hawaye na kokarin kufce mata, wai kowa sai yace tayi hakuri ta zauna dashi to wai ta yaya zata iya zama dashi alhalin bata sonsa kuma a matsayin Uba take kallonsa, abunfa da wahala wai (gurguwa da auran nesa) mikewa tsaye tayi a hankali ta fita daga dakin, Shi kuma Mussadiq din ya dauki wayarta ya nemi numbar Abban nasu ya shiga kira.
Koda yaga Numbar Naja’atu na kiransa bai ‘ki dauka ba, sai dai babu walwala a tare dashi yayi sallama! sai kawai yaji muryar Mussadiq yana fad’in “Abbanmu nine Mussadiq na kira ka da wayar Yaya Naja’atu.” Murmushi yayi yana jin wani farin ciki yace.”Na gane ka Magajin Abbah Ina fatan lafiya ina Naja’atun take.”? Mussadiq yace.”Yanzu taje yin sallah bama ta da lafiya sai kuka takeyi tana cewa wai dan Allah ka ‘kyaleta.”!! Shuru yayi yana nazarin maganar yaron daga bisani yace.”To shikkenan kace mata na kyaleta tunda bata son Allura ba zan kawo likita yayi mata ba.” Mussadiq yace.”Ba wannan ba Abba naji tana cewa kada ka aure ta ita tafi so ta auri ancle Salim Abbanmu tunda bata so ta zauna tare da kai ka kyaleta ta auri wanda take so.”!! Abbah Abbas ya jima yana mamakin maganar yaron, kuma yana mamakin abinda yarinyar take yi na rashin kyautawa! wato yaran take zaunawa dasu tana nuna musu a zahiri bata kaunar Ubansu har tana bawa ‘Dansa sa’ko ya bashi! ranshi ya ‘baci sosai da sosai! sai kawai yayi ‘kokarin bagarar da maganar ta hanyar fad’in “Ina Saddiqa take kace mata nace ku shirya gobe zan aiko Salim ya dauke ku xaku koma makaranta ranar Monday.” Yace.”Tom zan fad’a mata Abbah.” Yace.” Yawwa ka gaishe min da Baba Talatu da kyau.” Yace.” Za taji Abbah.” Kashe wayar yayi ya shiga nazarin irin iskanci da wulakancin da yarinyar ke masa, zai iya hakura da duk irin cin fuskar da za tayi masa amma kuma ba zai lamunci ta dinga cin fuskar ‘yayansa ba, hakan da take yi zai sanya ransu ya ‘baci! su shiga halin damuwa da maraicin mahaifiyarsu.
To da wannan ‘bacin ran ya shiga gidansa……In da yaje ya tarar da tashin hankalin Halisa dan ko zama bata bari yayi ba tabi shi d’aki! ta shiga zazzaga masa rashin kunya gami da farfad’a masa duk maganar da tazo bakinta kana kuma tace” Sai dai ya za’ba ita ko Naja’atu dan wallahi ba za tayi kishi da Ya tayi da kanwa ba.
Babu Abinda yace mata ya shiga bandaki domin yin wanka zuciyarsa tamkar zata tsaga kirjinsa ta fito dan tsananin ‘bacin rai!!!! Koda ya fito samunta yayi a kwance ‘kasan ties tana kuka had’e da wata iriyar fuffuka tana burgima ‘kasan ties kamar mai iskokai! Ya shirya tsaf ya tsallaketa ya fita ya barta a dak’in! Bin hanyar da yabi tayi da kallo hawaye na sharara ta mi’ke zaune tana cizon tsaya wato Abbas ko gani yayi zata mutu ba zai tanka mata ba kenan ballanta ya fada mata magana mai dad’i! aikuwa a zuciye ta mi’ke tsaye! tana rangaji! da had’a hanya, ta nufi kicin d’inta.
Yana zaune gurin cin abinci yaga fitowarta kallo ya bita dashi yana jan tsaki a fili ya shiga bude kwanonin abincin da ta jera kamar gaske! wayam! babu komai a ciki amma saboda tsabar iskanci da iya shega na Halisa ta shirya tevur kamar ta shirya lafiyayyan abinci……Takaici ne ya kamashi ya tsirawa hanyar data bi ido, kawai sai ya hangota ta fito daga kicin d’in hannunta ri’ke da shar’be’biyar wu’ka sabuwa dal da alama daga cikin kwalinta ta cire, kai tsaye ta durfafo inda yake jikinta na tsuma da rangaji! take fad’in “Wallahi yau koni ko kai a gidan nan Abbas na gaji da wannan abun da kake min ni ka sake ni ma na huta da ganin wannan takaicin auran wannan yarinyar da zakayi masifa ne a gare ni da kai baka sani ba sai sanda nayi maka illah a rayuwarka sannan zaga gazgata maganata.” ……….Mufida ta shigo palon tana sanye da uniform na makaranta ta hango abinda ke faruwa, a guje ta jefar da jakarta tayi kan mahaifiyar tata dake dumfarar mahaifinta da dalleliyar wu’ka! tana nema ta caka masa! ” Cikin karaji!! tace” Mommy meye haka? me za kiyi? Wayyo Abbanmu ka gudu.”!! Tafad’a tare da zuwa ta rungumeshi tana jansa wai ya gudu. Shi kuwa yana tsaye turmin danya bai razana ba, wato wai-wai d’in da yake ji a gari a na cewar mata na kashe mazajen su idan za’ai musu kishiya abun yazo kansa, jira kawai yake ta ‘karaso da wukar yaci ubanta! Halisa ido a rufe ta ‘karasa inda suke Mufida na kuka tana jansa da fadin “Abbah mu gudu kada ta caka maka wu’ka Abba me kayi mata n………..Gani tayi ya kama duka hannuwan Mahaifiyar tata ya murd’e da iyakacin karfinsa Wu’kar ta su’buce ta fad’i ‘kasan gurin! Ya kai mata wani lafiyayyan mari! da bayan hannunsa, wani ‘karamin jini ne ya fito daga hancinta, kafin ma ta dawo hayyacinta ya sake kifa mata wani a d’aya gefan, sai kawai yaga ta yanke jiki ta fad’i ta shiga turje turje tana taune harshenta……….Aljanunta ne suke ka da ita a gurin ta dinga turje-turje tana taune harshenta farar kumfa nata fitowa daga bakinta, Halisa na ‘karyar aljanu ashe dama tana dasu da gaske! sosai take burgima a gurin tana ta wasu gwalantu wanda ba wanda yake ganewa a cikinsu, Mufida ta nufe ta tana kuka zata ta’ba ta, ya hanata Yace.” Je ki cire uniform din’ki idan ta gaji da iskancin da take zata tashi.”
Tsakanin Uwa da D’a sai Allah tace”Abbah duba fa kaga abinda take wannan abun ba ‘karya bane dan Allah kayi wani abu kai.”
Tsayawa yayi tsai yana nazarin Halisan da abinda takeyi Eh kwarai kuwa wannan abun da take yasha bambam dana ko yaushe dan haka sai ya umarci Mufidan ta kawo masa ruwa a kofi, da sauri ta taje ta dauko masa, ya kar’ba ya shiga tofa ayatul’kursiyu da fala’ki da nasi ‘kafa bakwai bakwai kana ya iske inda take, ruwan tofin ya guntsa a bakinsa ya shiga fesa mata a jiki, sai da yayi haka sai uku tukkuna sannan ta daina burgimar da take yi ta daina gwalantun surutan da take yi jikinta ya shika sosai tayi lakaf gumi duk ya jika mata jiki, Mufida na kuka taje ta rungumeta tana kiran sunanta…………….
*????️MADADI!!????*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE????*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION????????️*
_’Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*12* Cikin wani mawuyacin hali Halisa ta tashi duk jikinta yayi mata mugun tsami! ga wani irin ciwo da kanta ke mata, da kayar ta rarrafa ta shiga dakinta ta zauna bakin gado tana ri’ke kanta, a maimakon tayi addua kawai sai ta fashe da kuka tana fad’in mugwayen kalmomi a kan mijin nata saboda kawai yace zai yi mata kishiya shine take addua Allah yasa ya samu karayar ariki komai nasa ya lalace! Allah yasa ya taulace ya zama wanda bashi da cin yau bare na gobe insha Allahu kuma Naja’atu sai ta zame masa masifa a rayuwarsa, tana kuka take wannan surutan tamkar wata mahaukaciya, Cikin wannan yanayi suka shigo gidan shi da yaran gabad’aya dan dubara yayi wa Baba malam yace zai tafi dasu Mussadiq saboda zasu koma makaranta, baba malam baiji dadin haka ba dashi da Abba Magaji sun fahimci cewar abinda Naja’atu tayi musu ne yasa yaji sha’awar dauke yaransa…….Kai tsaye Dakinsa ya nufa yana so ya samu nutsuwa sosai kafin ya tunkari Halisan dan ya fahimci dole sai ya karyar da kansa mussaman yanzu da ya dauko nauyi ‘yayansa ya d’ora mata………Mufida da Saddiqa Mussadiq suka nufi bedroom din Halisan nan suka tarar da ita ba yanda take sai sambatun surutai take da alama dai har yanzu mutanan nata basu gusa daga jikinta ba, Mufida taje ta zauna kusa da ita tare da dafata tana kiran sunanta………Saddiqa da Mussadiq a bakin kofa suka tsaya saboda dama can sun san halin masifar Halisan ba kaunarsu take ba sai taga Abbansu take yi musu magana da wasa da dariya, shiyasa suka kasa ‘karasawa, Halisa ta juyo tana kallon ‘Yarta Mufida ganin su Saddiqa a tsaye a bakin kofa yasa ta mike tsaye a furgice tace”Ku dan Ubanku waye ya kawo ki gidana maza ku fuce mun daga d’aki shegu tsinannu ‘yayan asara.”! Saddiqa da Mussadiq suka zabura! a tsorace suka fita daga d’akin sukaje suka nemi kujerar palo suka zauna jikinsu sai rawa yake dama can Saddiqa da Mussadiq suna masifar tsoron Halisa Naja’atu ce take musu maganinta…….Mufida na goge hawaye tace.”Mommy ya kike zaginsu su Yaya Saddiqa ne fa ‘yan uwana.” Wani irin bahagon mari ta kifawa yarinyar tana huci! tace”Zanci Kutumar ubanki wallahi shegiya munafuka ni zaki fad’awa su d’in ‘Yan uwanki ne? Wallahi duk ranar da kika ‘kara kiransu da sunan ‘yan uwanki sai naci ubanki.” Mufida tana kuka tace”To mommy me yasa kika tsanesu bayan mamansu ta mutu dan Allah ki daina yi musu abinda kike musu babu kyau.”! A fusace! ta sake gaura mata wani mari tana wata irin fuffuka tace”Tashi dan babanki mara mutunci ki bar min dakina ko kuma yanzu na sumar dake.” A gigice! yarinyar ta mike hannunta dafe da kuncinta ta fita daga dakin tana kuka, wanda yayi dai-dai da fitowarsa daga daki yana sanye da jallabiya ruwan toka, Ganinsu Saddiqa sunyi muzu-muzu a zaune yasa jikinsa yayi sanyi ya kalli Mufida dake dafe da kunci tana kuka, yace.”Menene? Cikin rawar murya tace”Mommy ce ta mare ni tace na fito mata daga d’aki. Ba tare da yace.”Komai ba ya kama hanyar dakin Halisan, Har yanzu tana zaune gefan gado ta had’a tagumi babu maganar sallah a tare da ita, cikin nutsuwa ya shiga dakin bakinsa dauke da sallama, Kallonsa ma ba tayi ba ballanta ta amsa masa sallamarsa, gefanta ya zauna yana kokarin ri’ke hannunta ta fizge a fusace! ta mike tsaye tana nunashi da hannu tace”Kaga dan girman Allah ka fita ka bani guri naji da abinda ke damuna baka da abinda zaka ce dani.” Yaji zafin maganarta amma sai ya danne ya mike ya iske inda take, Rungumeta yayi a jikinsa yayi amfani da wata murya wacce ya tanade ta dan rarrashinta, yace.”Haba Halisa wai duk me yayi zafi ne kike nema ki zautar da kanki akan abinda bai kai ya kawo ba! Menene abin damuwa dan nace zan auri Yarinyar nan Naja’atu? idan kin kwantar da hankalinki kin ri’ke girmanki sai kinfi daraja da kima da martaba a idona! Shin wai baki ga yanda Halimatu ta sadaukar da rayuwata a kaina ba, bana shakka ko tantama Halimatu yanzu tana gidan aljanna saboda ta rabu dani da iyayenta lafiya, kuma ta mutu hanyar haihuwa, har na gama rayuwata ta duniya bazan ta’ba mantawa da Halimatu ba, a kwanakin baya kin soma kwaiwayon hali da d’abi’unta amma tashi guda zaki watsar da abin da kika fara na alkairi, wallahi auran Naja’atu da zanyi ba zai sanya ni na daina kaunarki ba, kin san dai kece macen dana fara furtawa kalmar so, ko Halimatu ma kece kika jawo na aureta, to itama Naja’atun ina so ki sani bani ne nace inaso ta zama *Madadin ‘Yar uwarta ba* Iyayenta ne suka nemi haka dan ko yanzu sai da na fada musu cewar maganar auran su barta suka nuna sai anyi So inaso ki kwantar da hankali ki samu nutsuwa ki kula dani da yarana gasu nan na kawo miki su ni kuma insha Allahu zan baki mamaki zan nuna miki ni d’an halak ne auran Naja’atu ba zai sa na juya miki baya ba.” Shuru tayi jikinta duk yayi sanyi da kalamansa tace”Nifa ban hanaka aure ba wallahi ko budurwar zaka aura to kaje ka aura amma banda yarinyar nan bana kaunarta saboda bata ganin girmana.” Yace.”Na fad’a miki fa cewa kece uwargidana duk ragamar mu tana hannuki har ita Naja”atun idan tazo a ‘karkashin ki take sai abinda kika tsara a gidan shi za’ayi.” Jin wannan maganar tasa yasa ta sauke ajiyar zuciya tace”Nifa wallahi nasan dadin baki ne kake mun yarinyar nan na zuwa zaka manta dani, dan haka gwara tun kafin tazo na san inda dare yayi min dan bana tunanin zan zauna da ita a karkashin inuwa guda.” Yace.”In banda abinki ba gidanku daya ba to me zai dame ki da ita ko wacce na gidanta idan wannan da kike ciki bai miki ba sai na sauya miki wani.” Tsaki taja tace.” bazan yarda ba wallahi sai dai ka had’amu gida daya dan bazan amince a cutar dani ba.” Yace.”To shikkenan duk abinda kike so shi za’ayi, Zan sa a gyara miki side d’inki dake gidana na *’Danbare* ina fata hakan yayi miki.” shuru tayi tana zum’bura baki, Ya saketa yaja hannunta suka zauna a nutse yace.”Ki fad’a mun duk abinda kike so na siya miki na fad’ar kishiya komai tsadarsa zan siya miki.” Tace”Sai nayi shawara tukkuna.” Dariya ta bashi amma beyi ba yace.”To shikkenan inaso na baki kudi kije ki had’o mata lefe kuma kema ki had’a naki hakan yayi miki.” Dadi ne ya rufe ta tace”To Hakan yayi amma inaso ka sanja min mota.” Yace.”An gama ranki ya d’ade! amma dan Allah daga yau sai yau kada ki sake aikata abinda kika aikata a d’azu! rashin hankali ne kawai kije ki dauko wu’ka kina so ki kashe ni! kina tare da shed’an a lokacin idan da tsautsayi sai ki aikata aikin dana sani ki ‘kare rayuwarki cikin uku’ba kuma ki mayar min da yara marayu.” Hanci ta sha’ka! cikin takaici tace”Haba ai wallahi idan ma nayi maka rauni ban huce bacin raina ba, kana kallonta ina magana ka tsalleke ni ka tafi ai dole zuciya ta ta tunzurani a kanka.” Yace.”Tom yanzu dai duk magana ta wuce Gobe insha Allahu bayan sakkowar sallahr juma’a za’a daura auran amma ina tunanin ba zata tare ba sai nan da sati biyu.” Halisa gabanta ya fad’i tace”Da wuri za’a daura auran ashe.”? Yace.”Baba Malam ne ya yanke hukuncin haka.” Cikin tsabar bakin ciki da takaici tace”Aikin banza aikin hofi ‘kwad’ayayyen tsoho mai son abin duniya ai dama dole ya gaggauta yin abun kodan bukatarsa ta biya.” ‘Bata rai yayi yace.”To yanzu zamu ‘bata dake kuma bana son wannan d’abi’ar taki ta zage-zage da rashin ganin girman manya.” Cikin fusata! ta mike ta nufi toilet tana surutai da ‘kananun maganganu, kallo ya bita dashi, Al’amarin Halisa dai sai gyaran Allah, yaji dadi sosai da ya shawo kanta cikin ruwan sanyi *(Tabbas haka maza ya kamata su dinga rarrashin matansu idan zasu ‘kara aure, sau tari wasu mazan sune suke ingiza zuciyoyin matansu ga aikata abinda ba shikkenan ba, idan ya kasance zaka ‘kara aure to yana da kyau ka dinga nuna kulawarka a kan matarka ta gida, kuma banda kiran wayar amarya a cikin gidan dan hakan ma na iya janyo muku samun sa’bani a tsakaninku*) Mikewa yayi ya fita daga dakin yana dan jin sassauci a cikin zuciyarsa tunda ya gama da matsalar Halisa yana ganin duk abinda zai biyo baya mai sauki ne.