MADADI 1-END

MADADI Page 11 to 20

 Yana fitowa palon ya gansu a zaune duk sunyi tsuru-tsuru Mussadiq ma gyangyadi yake, Ya kalli Saddiqa data had’a tagumi hannu bibbiyu har yanzu zuciyarta na jin ciwon abinda Naja’atu tayi musu a d’azu duk da take yarinya wacce bata gama mallakar hankalin kanta ba ta gane ba ‘karamar ‘kiyayya Naja’atu keyi wa Abbansu ba, sai ta dinga tunanin to wai meye aibunsa da har zata dinga ‘kinsa da kuma zaginsa, sam bata ta’ba tsammanin haka daga gareta ba…… a nutse yace.”Saddiqa kuje ku kwanta kinji ko, dukkaninku ku daina damuwa ku saki jikinku a gidan nan gidanku insha Allah ba zaku samu wata matsala ba.” Saddiqa murya na rawa tace”To Abbah.” Ya sunkuya yana d’an tashin Mussidiq ya tashi yana mutsika ido, ganin Abbansa yasa ya bude idonsa sosai, Abba Abbas d’in ya rike hannunsa ya mike tsaye………Shi da kansa ya rakasu d’akin dama gado uku ne mai dauke da madaidaiciyar katifa da pillo da bargo, Mufida ta gyara nata ta kwanta, Abbah Abbas da kansa ya shimfidawa Saddiqa da Mussadiq sabon bedshirt ya gyara musu sosai sannan suka kwanta, Ya tsaya kansu yayi musu addua sosai kana ya fita daga dakin tare da kulle musu kofa………….To bayan barin Abbah Abbas daga gurin Malam Baba shima Abbah Magaji sallama yayi masa kancewar kafin ya shiga gidansa zai tsaya ya siyi dik abinda za’a bukata gurin daurin auran, Malam yaji dadin hakan yace.”Dashi kafin ya tafi ya shiga gidan Alhaji domin ya sheda masa abinda ke faruwa, koda Alhaji yaji bayanin da Abbah Magaji yayi masa sai ranshi ya ‘baci! ya za’ayi sun riga sun gama magana da Abbah Abbas din kan cewar ya janye maganar auran yarinyar kuma dan yaga baya gurin zai sauya magana, yaji haushin hakan ya dauki laifi kacokan ya d’orashi kan Abbah Abbas d’in, Dan ‘kin tsayawa ma yayi ya saurari bayanin da Abbah Magaji ke masa, ya sauko daga samansa, kai tsaye futa yayi daga gidan, Abbah Magaji na binsa a baya……..Malam Baba yayi mamakin fusatar Alhajin kasancewar yasan shi d’in mutum ne mai saurin fahintar abu da kuma sau’ka’kawa cikin ko wane al’amari…….Da ‘kyar Baba Malam da Abbah Magaji suka fahimtar dashi ya gane cewar ba laifin Abbas din bane sune suka tursashi……Alhaji Sama’ila yayi shuru yana ta nazarin al’amarin, daga bisani kuma addua yayi da fatan alkairi tabbas tunda Allah yayi haka to babu alkairi a cikin auran Naja’atu da Salim d’in,……Shine ya sake ‘karfafawa Abbah Magaji, cewar yayi ‘kokarin tana dar duk abinda ake bukata a gurin daurin aure tabbas babu makawa gobe auran Naja’atu da Abbas sai ya d’auru………Sai misalin goma da rabi sukayi sallama da juna kowanne ya shiga gidansa cikin fatan alkairi ga junansu………Baba Malam kafin ya kwanta sai da ya sanar da Baba Talatu abinda ake ciki na irin hukuncin da suka yanke cewar Za’a daura aure gobe dan jan lokacin bashi da amfani, Baba Talatu taji dad’in hakan sosai kuma tayi fatan alkairi dangane da al’amarin…..Naja’atu dake takure kan shimfidarta a lokan rumfar luf!! tayi kamar mai bacci tana sauraran maganganunsu, sai da taga sun shiga daki, da niyar kwanciya sannan ta mike a hankali ta dauki wayarta dake kusa da ita ta mike ta fita daga dakin ……..Daya dakin ta nufa tana shararar da hawaye, xaman ‘yan bori tayi tana toshe bakinta domin kada sautin kukan da take ya fita suji, wayar ta kunna hannunta na kyarma ta shiga laluben numbar Abbah Abbas d’in, tana jin idan bata zageshi ba zuciyarta na iya bugawa………Yana zaune a palo shi kadai da Loptop a gabansa yana duba sa’konnin abokan kasuwancinsa na ‘kasashen waje, Kiran wayar ta ya shigo wayarsa dan duban wayar yake hankalinsa na kan typing din da yake cikin loptol din, koda yaga numbar Naja’atun baiyi gaggawar dauka ba, ya janye idonsa ya cigaba da abinda yake Naja’atu! ta dingi kiran wayar tamkar zata kashe masa dodon kunne dole ba yanda ya iya ya daga wayar tare da gyaran murya babu wasa a cikin muryarsa yayi sallama….

‘Dif! tayi gabanta na wata irin fad’uwa! sakamakon jin sautin muryarsa mai cike da kwarjini da rashin wasa yasa ta mance abinda yasa ta kiransa a wayar sai mazari jikinta yake tana sha’kar hanci had’e da sauke ajiyar zuciya irin na wanda yaci kuka ya ‘koshi……..’Dan gyaran murya yayi a karo na biyu yace.”Dota ya akayi ne dare yayi baki bacci ba.”……Murya na rawa tace”Me yasa ka san ni ‘yar kace kake shirin aurena.”? Shuru yayi yana nazarin maganarta, Yace.”Eh abinda yasa nake kiran ki da Wannan suna (Dota) saboda nasan a matsayin shekaruna da Allah ya bani haihuwa da wuri dana haife ki kamar ki ko wacce ta fiki so ina ganin babu laifi dan na kira ki da wannan suna.”!A hasale! tace.” To tunda dai da bakin ka ka fad’a cewa a matsayin shekarunka da Allah ya baka haihuwa zaka iya haifeta ko wacce ta fini me zai sanya ka zubar da k’ima da mutunka a gurina ni da ka ‘rike kamar ‘yar cikin ka, ka sani ba da badan mutuwa ta ratsa tsakanin ka da matarka ba da kowa yana maka kallon matsayin uba a gare ni.” Murmushi yayi wanda har sai da taji sautinsa a kunanta Yace.”Nifa ban haife ki ba ki daina kirana Ubanki yanzu sunan da yafi kamata ki kirani dashi shine Mijin ki dan gobe idan Allah ya kaimu iwar haka kin zama matata”! Taji tamkar ta d’ura masa ashar! sai dai ta daure taja wani matsiyacin tsaki! mai ‘karfi! da fad’in “Amma dai anji kunya wallahi.”!! Kit! ta kashe wayar tana wani irin huci!!! Abbah Abbas ya dinga bin wayar da kallon mamaki! Yau shi yarinyar nan take jawa tsaki har tana kokarin zaginsa, Kasa hakura yayi ya sake kiran wayar! A fusace! ta d’aga ta bud’e baki za tayi magana, ya buga mata wata masifaffiyar tsawa! da fad’in ” Dan Ubanki ni kike zagi ashe baki da mutunci dama.”!? Jikinta ya shiga karkarwa domin tsawar da ya buga mata bata ta’ba saninsa da ita ba, kashe wayar tayi gabad’aya ta kwanta tare da takure jikinta tana kuka mai tsuma zuciya, ta kirasa a waya domin ta farfad’a masa magana mai zafi ‘karshe shi ya fad’a mata maganar data ya mutsa mata tunani har da zagin Ubanta……….Abbah Abbas ya ajiye wayarsa a fusace! ya rufe loptop din ya mike ya nufi bedroom d’in Halisa……….. *Sorry kuyi hakuri waya ta ta d’an samu matsala wallahi zaku ga yanayin typing din ba irin yanda na sababa……..Ina ro’kon Ubangiji Allah ya kawo mana zaman lafiya a wannan ‘kasa tamu ta Najeria Ubangiji Allah ka bamu nutsuwa da daidaito a tsakaninmu amin………MY FANS KADA MU MANTA DA SALATIN ANNABI A WANNAN RANA MAI ALBARKA SANNAN KUMA MU DAURE MU KARANTA ABINDA YA SAWWA’KA DAGA CIKIN SURATUL KHAFI.*

*????️MADADI!!????*

_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE????*

~~~~~~~~~

*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION????????️*

_’Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_

~~~~~~~~~

 *13*

Ranshi a ‘bace! ya aje loptop din kan wani tevur ya nufi toilet alwala ya daura ya fito ya hau kan dadduma ya tayar da sallahr nafila, raka biyu yayi ya daga hannunsa sama yana rokan Allah ya za’ba masa abinda yafi alkairi a rayuwarsa, kwata-kwata ji yayi auran yarinyar ya fice masa daga rai! a sabili da irin iskancin da wulakancin da take masa da shida ‘ya’yansa bai ta’ba tsammin faruwar hakan daga gurinta ba yana ganin barin auranta kamar shi yafi alkairi don baya so da girmansa da komai yarinya k’arama tazo tana fada masa maganar da duk ta gadama, mikewa yayi daga kan dadduma yaje ya kwanta kusa da Halisa, ya d’an janyo ta jikinsa, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button