MADADI 1-END

MADADI Page 11 to 20

Bude idonta tayi ta wani fizge jikinta tana jan tsaki! Al’amarin sai ya bashi mamaki! ganin cewar d’azu suka gama magana da ita kan cewar komai ya wuce amma saboda ya ra’bi jikinta tana fizgewa, bai yi zuciya ba ya sake kai hannu zai janyota ta mike zaune tana ‘bata fuska tace”Nifa ba zan sake amincewa da bukatarka ba sai na yankewa kaina hukunci tukkuna dan gaskiya ni maganganunka na dazu basu shige ni ba.”

Ya mike zaune yana kallonta cikin d’umbin mamaki! yace.” Wane irin hukunci zaki yankewa kanki bayan wanda muka yanke d’azu na dauka yanzu dani dake mun zama d’aya, ashe duk maganar da mukayi dake dazu ta banza ce.” Tace.”Kawai ka rabu dani na cigaba da tunanin mafita ni ba zan sake amincewa bukatarka ba kaje idan an daura auranka da ‘karamar yarinya sai ka sauke bukatarka a kanta.” Cikin tsabar takaici yace.”Halisa ban ta’ba ganin mara hankalin mace irin ki ba wallahi kin girma amma har yanzu kin ‘ki hankali ‘Yar cikin ki Mufida ta fiki nutsuwa.”

Tace.”Duk dai abinda za kace a kaina kace ba zan amince da kai ba wallahi sai yarinyar nan ta shigo gidanka naga irin zaman da zakayi da ita.”

Murmushi takaici yayi cikin sigar ‘kuntatawa yace.”Zanyi zama da ita irin na ma’aurata kuma ba zaki hana ni na ji dad’ina da ita ba.” A fusace! taja tsaki! da fad’in “Kana tare da kunya kuwa duk ranar da ‘yayanka su kaga ka kwana a d’akin wacce suka d’auka a matsayin yaya a gurinsu, sai ka tanadi abinda zaka fada musu.”

Girgiza kansa kawai yayi ya dauki rigarsa yasa a jikinsa ya sauka daga bed din hanyar fita ya nufa jiri naso ya kayar dashi, gabad’aya ji yayi duniyar tayi masa zafi ko ina babu sassauci tabbas sai yanzu ne zai fara kukan rashin matarsa da yayi, a da baiyi kukan rashin Halimatu ba sai yanzu da Halisa da Naja’atu suke gwara kansa a bango….

‘Bangaran Naja’atu kuwa yanda taga rana haka taga dare daga zarar ta tuna da cewar gobe za’a daura mata aure da Abba Abbas din sai gabanta ya fad’i ta hau takure jikinta, ta jima tana sa’kawa da kwancewa da tunanin mafita a gareta, tana so gari ya waye ta kira Salim a waya ta sheda masa hukuncin data yanke…….Aikuwa tana idar da Sallahr asubahi ta shiga kiran wayar Salim din inda akaci sa’a yau ya tashi da wuri, ya dauki wayar cikin mayaudariyar miryarsa yace..”My Princess kin tashi lafiya.”? Murya a ‘kasa tace”Lafiya kalau my prince.” Ya wani narke murya irin yanda yake mata yana kashe mata jiki yace.”My Prince jiya kwana nayi da tunanin ki da begen ki har mafarki nayi dake muna kwance a gado d’aya kina bani kulawa.”

Ta rintse idonta hawaye na zuba tace.”My Prince Abba Abbas naso ya yanke mana jin dad’inmu bana tunanin zan iya mallakawa wani da namiji kaina sai kai! bana sha’awar kowa sai kai soyayyar ka kawai nake muradi! amma ina tunanin mafarkina dakai ba zai tabbata dan ganin yanda magauta suke ‘kokarin kassara mana rayuwarmu.” Mikewa zaune yayi yace.”My princess ki fad’a mun yanzu a wace matsaya aka tsaya dangane da maganar auranki da Abbah Abbas din.

Tace.”Komai yazo karshe My Prince jiya da daddare Baba Malam naji yana fad’awa Baba Talatu cewa gobe bayan sallahr juma’a za’a daura aurena dashi, wannan dalilin yasa na yanke hukuncin guduwa daga garin gabadaya su neme ni su rasa.”

Salim ya shiga goge gumi ma’kogwaronsa ya bushe sosai, yace.”Innalilihi wa’ina ilahi raji’un! abinda ya iya fad’a kenan, murya na rawa yace.”My bani da kuzarin yin magana yanzu saboda na shiga rud’u da tashin hankali jin wannan maganar taki, zan kira ki anjima kafin nan nayi nazari kan hukuncin da kika yanke.”

Kashe wayar yayi ya zauna yana tunani…….Ashe dai dattijon nan da gaske yake sai ya dasa masa ‘kunci da ba’kin ciki! to kuwa in dai ya kasance cewar ya samu nasara a kansa gurin auran Naja’atu to shi kuma zaiyi amfani da damar sa, a gurin ita Naja’atu duk wani abunda yake bukata a gurin yarinyar ba zai same shi ba sai ta zame masa mafisa wanda da kansa zai gaji ya saketa, koda ya saketa shi ba auranta zaiyi ba yana so ya kawai ya dasa masa ‘kunci da ‘bacin rai kamar yanda ya dasa masa a zuciyarsa.

Mikewa yayi ya shiga cikin gidan…Yaya Ramlatu na kicin tana kokarin kunna wuta, taga shigewar d’an nata, sai da ta kunna wutar ta d’ora ruwan kunu kan murhun, sannan ta bi bayansa, koda ta shiga dakin gani tayi ya takure kansa hade da dafe kansa, Kafin ma tayi magana taga yana hawaye.

Tace.”Salim lafiya me yake faruwa.”? Cikin tsabar bakin ciki yace.”Yaya ‘Dan uwanki bashi da kirki ya kasance mutum mai son kansa, ya cuce ni ya cutar da rayuwata kuma ya yaudare ni da yasa na amince masa na daukeshi a matsayin uba ya ha’ince ni, yarinyar dana ‘kwallafa raina a kanta yau xa’a daura masa aure da ita, ba zan ta’ba mantawa da wannan mutumin ba.”

Yaya Ramlatu ta dinga mamakin maganar tace.”Kai waye ya fad’a maka yau za’a daura auransa da Naja’atu da har kake wannan maganar……A fusace! yace.”Ita yarinyar ce ta fad’a min yanzu ta kirani a waya tana kuka tare da sheda min hukuncin data yanke kancewar zata gudu daga garin gabadaya.”

Shuru Yaya Ramlatu tayi takaici da bakin ciki kamar ya kasheta, lallai Abbas bai da alkawari kamar dai yanda Salim din ya fada hakane Abbas yafi son kansa akan kowa bai duba soyayyar dake tsakanin Salim d’in da Naja’atun ba sai da ya shiga ya fita ya raba tsakaninsu……Tace.”To shikkenan sai ka hakura ka fawwala wa Allah tunda Allah yasa ya samu nasara a kanka, maganar Naja’atu zata gudu ta bar gari bata taso ba dan idan hakan ya kasance to kowa zai d’ora zarginsa a kanka, dan haka kace mata baka amince ba, dan bana son abinda zai janyo min ‘bacin ran iyayena.”

Yace.”Idan ya kasance Naja’atu ta tare gidan Kawu Abbas wallahi tallahi nayi al’kawari sai na ‘kunsa masa ba’kin ciki da takaici kamar yanda ya ‘kunsa min, tunda dai Naja’atu ni take so ai magana ta ‘kare zuciyarta tana hannuna shi kuma yana tare da gangar jikinta.”

Yaya Ramlatu tace”Duk wani iya shege da rashin arziki da zaka yi masa ban hanaka ba, kaje kayi domin shima yaji idan da dad’i abinda yayi maka d’aurin aure suje suyi babu inda zanje.” Yace.”To dama me zaki je kiyi a gidan gabad’aya ma da Alhajin da ita Hajiyan basa kaunarki da suna kaunar ki ba zasu bari haka ya faru ba, sunfi kaunar Kawu Abbas d’in saboda yana da kud’i.” Yaya Ramlatu ta dinga girgiza kanta takaicin da ba’kin ciki dik ya cika mata zuciya.

Da asubah da kafin ya tafi massalaci sai da ya shiga ya tashi yaransa domin suyi sallah, koda ya fito daga dakin nasu bai ko kalli dakin Halisa ba dan har yanzu haushinta yake ji yana ganin duk wani kokari da ya kamata yayi a kanta yayi zai dauke mata wuta gabad’aya dan ba zai cigaba da rarrashinta taba tana masa iskancin da taga dama.

Bayan ya dawo daga massalaci ya koma dakin nasu nan ya tarar dasu sunyi sallah suna zaune Saddiqa da Mufida suna magana, dukkaninsu suka shiga gaishe shi ya dinga amsawa cikin nutsuwa da kulawa, ya kalli Saddiqa a nutse yace.” Saddiqa ki shiga kicin ki dafa muku tea da abinda kike ganin zaki iya.” Tace.”To Abbah.” Mikewa tayi tana kokarin cire hijab d’inta shi kuma ya fita daga d’akin, Kai tsaye d’akin Halisa ya nufa domin ya dauki loptop dinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button