MADADI 1-END

MADADI Page 11 to 20

Tana kwance kan bed din ta tsirawa rufin dakin ido, da alama ma ba tayi sallah ba, Ko kallon inda take baiyi ba ya dauki loptop dinshi ya kama hanya ya fita daga dakin, Halisa tabi bayansa da kallon ba’kin ciki tamkar ya tarwatsa mata zuciyarta…………..Saddiqa na tsaka da aiki a kicin taji an buga mata uwar tsawa! “Ke dan Ubanki waye ya baki dama ki shigo min kicin.”!? Jiki na rawa tace.” Abbah ne yace na dafa mana tea da indomee.” Da hannu ta nuna mata ‘kofar fita da fad’in “Fice ki bar min kicin ‘yar iska munafuka masu gadon mugun abu.” Saddiqa hawaye ne suka tawo mata, tayi saurin mayar dasu tana kokarin fita daga kicin din Halisa ta kai mata ran’kwashi a kanta tana zaginta. Da sauri ta ‘karasa ficewa daga kicin din hawayen da take ta kokarin mayarwa suka zubo…….Ganin yarinyar ta fito a firgice yasa ya kalleta yana tambayar ta menene.”? Tana share hawaye tace”Babu komai.” Tsawa yayi mata da fad’in “Ba zaki fad’a min menene ba.”? Tace.” Anti ce tace na fice mata daga kicin.” Yace.”Zoki zauna anan.” Kusa dashi ya nuna mata, taje ta zauna tana goge fuska, cikin tausasawa yace.”Kiyi hakuri ki daina kuka kinji ko.” ‘Daga kanta tayi tana goge hawaye, laptop din dake cinyarsa ya ajiye kan kujera ya mike ya nufi kicin din, Halisa na tsaye tana feraye doya ya shiga ya sameta……Babu walwala a tare dashi yace.”Me yasa kika hana Saddiqa ta had’a musu abun kari.”? 

Juyowa tayi dan ba tasan ya shigo kicin din ba, ganin fuskarsa a murtuke yasa itama ta murtuke tata fuskar tace”Ai sai ka tsaya ka gani idan nayi ban basu ba sai ka bata umarnin tayi musu meye wani zaka ce ta shigo min kicin.”!! Girgiza kansa yayi bai ce mata komai ba ya juya ya fita daga kicin d’in, sam bai dauka Halisa za tayi abinci ta bawa yaran ba dan ganin irin rigamar da sukayi ita dashi jiya shiyasa ya umarci Saddiqan ta shiga kicin domin ta samar musu da abinda zasu ci……..Suna zaune shida yaran Yaya Ramlatu tayi sallama ta shigo, turus tayi ganinsa zaune a palon, shima cike da mamaki yake binta da kallo, har ta’karaso ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa, Yaran ne suka shiga gaisheta ta dinga amsawa tana washe bakinta.

Cikin nutsuwa ya gaisheta ta amsa tana ta dariya kamar wacce ta shigo gidan da abin arziki, Tace.”‘Dazu Salim yake sheda min cewar anjima wai za’a daura auranka da Naja’atu hakane ko.” ? Yace.”Eh insha Allah bayan an sakko daga sallahr za’a daura anan massalacin jikin gidan Alhaji.”

Tace.”Allah ya sanya alkairi yasa haka shi yafi alkairi, amma banji dadi ba da baka fad’a min ko a waya ba sannan daga can gidan Alhajin ma babu wanda aka turo domin ya fad’a mun sam ba’a daukeni a bakin komai ba, ace maganar daurin auren ma sai a bakin Yarinyar mukaji dan da asussuba ta kira Salim tana kuka tana fad’a masa cewar za’a daura auran kuma idan an d’aura to zata gudu ta bar gari a neme ta a rasa, wannan maganar ta tayar min da hankali sosai saboda nasan yarinyar nan ta gudu to da kai da Salim zaku shiga cikin masifa, dalilin da yasa na umarci Salim din maza ya kira ta a waya sheda mata cewar bai amince da ‘kudirin data dauka ba, Kuma nace ya fad’a mata cewar shi tuni ya cire ta a zuciyarsa, dan haka ta daina tunanin guduwa a kansa ta zauna a gidan mijinta tayi zaman aure mai tsafta.”

Abbah Abbas ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Yaya Ramlatun yace.”Dukkanin abinda ki kaga yana faruwa to dama can haka Allah ya ‘kaddara zai faru, ko a mafarki ban ta’ba tsammanin wai zan auri yarinyar nan ba, sai dai kuma babu yanda Allah baya tsara al’amarinsa, mutuwar Halimatu ta janyo min sha’awar auran yarinyar domin ina ganin yarinyar tarbiyar tace kuma zata zame min *MADADIN TA* ta gurin kyawawan halaye da sauransu, sai dai kuma ashe ba haka al’amarin yake ba , Allah shine ya hallici Halimatu ya kuma Hallice Naja’atu a bigire d’aya, sai kuma ya bambamta musu halaye, Halin Halimatu daban Halin Naja’at daban, A jiya mun zauna da Alhaji mun tattauna magana kan cewa na janye bukatata tasan auran yarinyar, zan kuma shige gaba gurin ganin Salim ya mallaketa, a lokacin da naje wa da Baba Malam da maganar shi kuma ya nuna bai amince ba, yace yarinyarsa bata da miji sai ni saboda ni yayi ra’ayin bawa auran ‘yarsa, dik yanda naso na fahimtar dashi ya kasa fahimta, haka nayi musu sallama na dawo gida ina fatan Allah yasa hakan shine alkairi a gare mu baki d’aya.

*????️MADADI!!????*

_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE????*

~~~~~~~~~

*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION????????️*

_’Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_

~~~~~~~~~

*14*

 Yaya Ramlatu zagin Baba malam kawai take a cikin zuciyarta amma a Zahiri dariyar ya’ke tayi tace”To ai shikkenan ni a gurina da kai da Salim din duk d’aya ne, kuma na zaunar dashi nace masa ya cire yarinyar daga cikin ransa gabadaya domin kai ba tsaransa bane ballanta ya had’a neman aure da kai.”” Abba Abbas yayi murmushi yace.”Kwana biyu ma bana ganinshi a kasuwa ko kiransa nayi a waya baya d’auka nasan duk akan hakane.” Tace.”Ai yanzu komai ya wuce na nuna masa dama can kai kafi cancanta daka auri yarinyar.” Murmushi yayi yana girgiza kansa, gaskiya bai tsammaci zai zauna da Yaya Ramlatu haka suyi magana ta fahimta ba yaji dadi sosai da sosai data fahimce shi.

Yaya Ramlatu a gidan ta karya kummalo suka shiga daki ita da Halisa, suna ‘kulle-‘kullensu, Halisa ta fad’a mata duk yanda sukayi da mijin nata da maganar zai bata kudi ta had’o lefe kuma zai sanja mata mota bayan haka kuma yace ta fadi duk abinda take so zai bata kudi ta siya…..Jin haka yasa Yaya Ramlatu tace”Kinga aikin malam ya fara yi ko ai dama na fad’a miki sai Abbas ya dawo tafin hannunki sai yazo yana miki rawar jiki, dan haka ki daina d’aga hankalin ki kan auransa da yarinyar nan nasan idan muka ri’ke Malam mai al’mutsutsai! a hannunmu to bukatar mu zata biya dama kuma babban burin ki shine ki mallaki Abbas a hannu ina ganin nan da ‘kan’kanin lokaci zaki mallake shi da duk wani abu nashi tunda har ya bud’e bakinsa yace miki dashi da duk wani wanda yake ‘kar’karshinsa a ‘kasan ki suke to kinga kuwa ai sai ki godewa Allah ki sake tanadar kudi masu kauri domin tukwici ga malam bisa ga aikin alherin da yayi miki.” Halisa tace.”Nifa Yaya Ramlatu sai nake gani kamar dan zai yi aura ne yasa yake kwantar da kansa ba wai asiri ne yayi tasiri a kansa ba, ki duba fa ki gani tsayin shekaru nawa muka dauka muna yawan bin malam tun Halimatu na raye asiri baya tasiri a jikinsa, sai yanzu.” 

Yaya Ramlatu ta ‘bara rai tace”Kada ki sake wannan maganar, wato duk kokarin da nake miki bakya gani sai kin ‘karya ta ni! kin ‘karya ta aikin malam to babu ruwana wallahi idan kika lalata a aikinki, kada ki sake cewa na taimaka miki, inaso ki sani ko wane malami da irin kalar aikinsa, wani da ruhainai yake aiki wani kuwa da turawan aljanu yake aiki wani kuwa da ba’ka’ken aljanu yake aikinsa, to shi mai al’mutsutsai da ba’kaken aljanu yake aikinsa, idan kin san ba’kar wuyar da muka sha nida ‘Yar shagamu kafin mu je zauren malam d’in sai kin tausaya mana, amma kin samu aiki yayi shine kike ‘karyata wa to wallahi babu ruwana.”

Halisa ganin ran Yaya Ramlatu ya ‘baci sai ta shiga bata hakuri tace”Ba wai ina karyatawa bane nasan kina kokarina akaina kiyi hakuri dan Allah.” Yaya Ramlatu tace”Koda can ma ba wai asirin ne baya tasiri a jikinsa ba yana tasiri sai dai yana saurin karyewa ne saboda yawan addua da zama da alwala dashi mijin naki yake, amma nasan wannan aikin da akayi masa zai dade kafin ya bar jikinsa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button