ALLON SIHIRI 7HAUSA NOVEL

ALLON SIHIRI 7

ALLON SIHIRI Littafi na bakwai 7

A Duk Inda Suka Wuce
Dakaru, Bayi, Barori Da Kuyangi Kamar Babu Mai Rai Acikinsu Sbd DuksuYazaunaKamar Gunki
Suna Masu Quramusu Idanu, Bakomaine Ya Haddasa Hakanba Face Ganin Tsananin Kyawun
Jaruma Suhailat, Gashi Kuma Wannan Riga Datasaka Ba Qaramin Kyawu Tayi Mataba, Da
Shigarsu Cikin Dakin Sai Suhailat Tasake Cika Da Mamaki, Ba Komaine Ya Haddasa Hakanba
Face Ganin Mahaifinta Sadauki Zahar Zaune Akan Kujera Cikin Tufafi Na Alfarma Tamkar Wani
BASARAKE, Koda Sadauki Zahar Ya Hango Suhailat Acikin Wannan Kyakyawan Shiga Wace
Taqara Fito Da Tsananin Kyawunta Da Kwarjininta Sai Ya Miqe Tsaye Cikin Matuqar Farin Ciki Ya
Tareta Suka Rungume Juna Sannan Ya Janye Jikinsa Daga Cikin Nata Ya Dubeta Cikin Alamu
Matuqar Damuwa Yace, Yake ‘yata Shin Kinada Lbrn Cewa Inda Zamuje Yanzu Taro Ne Na
Sarakai Da Manyan Masu Fada”aji, Jaruma Suhailat Ta Gyada Kai Tace Nasani Ya Abbana,
Kuma Ka Kwantar Da Hankalinka Babu Wani Sarki Ko Attajiri Wanda Ya Isa Ya Mallakeni Da
Qarfin Arziqinsa, Na San Wannan Ce Damuwarka, Kodajin Hak Sai Sadauki Zahar Yayi Murmushi
Yace Wannan Gsky Ne Yake ‘yata, To Amma Wane Mataki Zaki Dauka Don Kaucewa Hakan?
Kisani Cewa Dazarar Sarakan Sun Ganki Zasu Dimauce Kuma Sufara Tunanin Hanyoyin
Dazasubi Su Mallakeki Ta Kowanni Hali, Jaruma Suhailat Tasake Yin Murmushi Akaro Na2 Tace
Kada Kadamu Yakai Abbana Domin Tuni Nadauki Mataki Akan Hakan, Kai Dai Kawai Kazuba Ido
Kaga Abinda Zaifaru, Gama Fadin Hakan Keda Wuya Saiga Wani Hadimi Ya Shigo Cikin Turakar
Da Sauri Ya Dubesu Yace, Sarkine Yaturoni Nayi Muku Jagora Izuwa Fada, Batare Da Bata Lkc
Ba Jarumu Suhailat Da Sadauki Zahar Sukabi Bayan Wannan Hadimi Suka Nufi Fadar, Filin
Fadar Yacika Ya Batse Da Bil’adama Duk Inda Mutum Yahanga Babu Abinda Zaigani Face
Kawunan Mutane Rututu! An Kange Tsakiyar Filin Dawata Katangar Qarfe, Makada, Mawaqa Da
‘yan Rawa Sunjeru A Gefe Sahu Sahu Acan Sama Bisa Wani Gini Mai Tsawo Wanda Ke Dauke
Da Matattakala Sarakai Ne A Zazzaune An Shirya Kayan Ciye Ciye Da Shaye Shaye Agabansu,
Tuni A Wannan Lkc Anfara Gabatarda Sauran Jama’a Kuwa Sai Idanunsu Sakakafe Bakunansu
Suka Wangame Sbd Kallon Kyakkyawar Surar Dake Wucewa Ta Cikin Tsakiyar Fadar Wato
JARUMA SUHAILAT Tarada Muqarrabanta Nan Take Sarki Lubainu Da Dakkannin Sarakuna
Dake Kewaye Dashi Suka Mimmiqe Tsaye Dao Tarbar Jaruma Suhailat Da Tawagarta, Sudai
Sarakan Sunyi Zaton Cewa Suhailat Wata Shahararriyar Sarauniyace Daga Wani Bangare Na
Duniya, Donhaka Basusan Sa’adda Sukakama Risinawa Ba A Gareta Suna Gaisheta, Shikansa
Sadauki Zahar Anzata Cewa Sarkine Sbd Kwarjininsa Da Yanayin Shigar Dayayi Irinta Manyan
Sarakai Ce, Cikin Hanzari Sarki Lubainu Yatarbi Jaruma Suhailat Da Mahaifin Sadauki Zahar
Yarakasu Harzuwa Inda Aka Tanadarmusu Suka Zauna Sannan Shima Yakoma Gaban
Karagarsa Yatsaya Ya Fuskanci Jama’a, Nanfa Fadar Tayi Tsit! Kamar Mutuwa Tagifta Aka
Zubawa Sarki Lubainu Idanu Ana Sauraronsa Aji Bayanin Dazaiyi, Sarki Lubainu Yayi Gyaran
Murya Sannan Yace Yaku Manyan Baqi Da Dukkanin Jama’a Dake Wannan Wurin, Ina Yimuku
Barka Daxuwa Wannan Babban Taro Wanda Mukasabayi Aduk Shekara Awannan Birninamu Mai
Albarka Na Istambul, Bayan Haka Inamaiyiwa Jama’a Busharada Cewa Wannan Tarona
Banatarone Nadabam,kumanamusamman Wandabamutabayin Kamarsaba Sabodawannankaron
Munada Wadansu Bakinamusamman Masu Dumbinbaiwada Darajakamar Yaddakukaga
Shigowarsu Akarshe Izuwacikinwannantaro.Wannanmanyanbaki Sunzoda Zakwakuran Sadaukai
Kuma Jarumaihar Gudaashirin Wadandazasu Yigasar Karfindantseda Dakarunbirnina,inamaiyiwa
Jama,a Albishirdacewa Nimainacikin Jarumandazasuyi Wannan Gasarjarumtaka;kodasarki
Lubainuyazo Nan Azancensa,saimutanesukarude.Dashewa,gami-datafi.Sabodasun,san.Irin
Tsananin JARUMTAKARSA Da Sadaukantakarsa Don Hakasuna Son Kallon GUMUZUR,
Al’amarin Jaruma Sahailat Da Mahaifinta Sadauki Zahar Kuwa Koda Sukaji Cewar Sarki Lubainu
Mazai Shiga Wannan GASAR JARUMTAKA, Daza Ayi Sai Sukakamu Datsananin Mamaki Kuma
Tsoro Yadarsu Acikin Zukatansu Domin Basu Taba Zaton Cewa Hakan Zatafaruba, Cikin Kaduwa
Jaruma Suhailat Tadubi Zahar Cikin Qaramar Murya A Daidai Kunnensa Tace Yakai Abbana
Yanzu Meye Abinyi? Idan Harmuka Bari Saski Lubainu Yashiga Wannan Gasa Muza A Cinye,
Sadauki Zahar Yanumfasa Yace Maganarki Dutsece Donhaka Ina Ganin Cewa Nima Zanshiga
Gasar Sbd Natareshi, Jaruma Suhailat Ta Girgiza Kai Tace A’a Bazaka Tareshiba Nice Dai Dai
Dashi Domin KAREN BANA SHIKE MAGANIN ZOMON BANA Yadda Yake Taqama Da Quruciya
Daqarfi Nima Haka Nake Taqamadasu Kaikuwa Shekarunka Sunfara Nisa, Zai Iya Amfani Da
Wannan Dama Yayi Saurin Galabaitar Dakai Donhaka Kawai Kabarni Dashi, Sarki Lubainu Yaci
Gabada Bayani Yana Mecewa Yaku Jama’a Yanzu Batare Da Bata Lkb Ba Ina Kira Ga
Wadannan Manyan Baqi Namu Dasu Fitoda Jaruman Gasarsu Guda Ashirin Su Gabatardasu A
Tsakiyar Filh Sannan Muma Mu Gabatar Da Namu, Bayan Nan Za’ayi GASAR JARUMTAKA
Guda Daya Jal! Awannan Rana Sannan A Cigaba Da GASAR NISHADI Koda Gama Fadin Hakan
Sai Sarki Lubainu Yakoma Kan KARAGAR MULKINSA Yazauna. Muhadu gobe in Allah yakaimu.
Naku khamis idris Muhammad
[1/23, 00:53] +234 808 677 7945: e
ALLON SIHIRI Littafi na Bakwai 7 Part B A Sannan Ne Sadauki Zahar Da Jaruma Suhailat
Sukamiqe Tsaye Suka Kira Jama’arsu Suka Koma Gefe Daya Acikin Filin Fadar Sunaware
Sadaukan Dazasuyi Wannan Gasa, Bayan Sungama Ware JARUMAI Goma Sha Takwas Sai
Jaruma Suhailat Ta Sanya DAMARA Akan Rigar Dake Jikinta Takawo Takobi Ta Saqaleta A
Kubin Cinyarta Ta Dam, Sannan Tariqe Garkuwa Ta Shiga Cikin Jaruman Gasar Ta Tsaya, Nan
Take Shima Sarki Lubainu Yacire Alkyabbarsa Ya Sanya Damara Ya Dauko Tasa Takobin Da
Garkuwa Sannan Yashiga Cikin Jaruman Gasar Yazamo Cikon Na Ashirin, Tuni A Wannan Lkc
Sarakai Da Ragowar Jama’a Yan Kallo Sun Cika Da Tsananin Mamaki, Bakomai Ne Yabaiwa
Mutane Mamaki Ba Face Ganin Yadda Wannan Mace Mai Tsananin Kyau Tashiga Cikin Wannan
GASA TA JARUMTAKA Dakuma Dalilin Dayasa Shima Sarki Lubainu Yashiga Gasar Bayan
Angama Ware Jaruman Gasar An Kawosu Tsakiyar Fili An Tsayar Domin A Fitarwa Da
Kowannensu Abokin Gwaminsa Sai Zuciyar Jaruma Suhailat Tabuga Da Qarfin Gaske Bakomai
Ne Ya Haddasa Hakan Ba Face Ganin Yadda Gaba Dayan Mutanen khamisidrismuhammad: Batu
Sai Jama’a Suka Rude Da Shewa Gamida Tafi Sbd Basirar Da Aka Shirya A Wannan Gasa Tayi
Ma’ana Sosai Nan Take Jaruman Gasar Su Ashirin A Bangaren Baqi Suka Balayi Daya Rak! Suka
Rinqa Zuwa Gaban Wannan Akushi Sai Dai Kawai Abude Musu Akushin SuMuhammannu Su
Dauko Dutse Take Sai A Duba Dutsen A Ga Sunan Wanda Ke Jiki A Bayyan A Matsayin Abokin
Gwamin Wanda Ya Dauko Dutsen, Wani Ikon Allah Jaruma Suhailat Ce Ta Qarshe A Layin Kuma
Sauran Jaruman Nasu Guda Goma Sha Tara Babu Wanda Ya Dauko Dutsen Mai Sunan Sarki
Lubainu, Koda Akaga Jarumi Nasha Taran Bai Dauko Sunan Sarki Lubainu Ba Sai Filin Fadar
Yarude Dashewa Gamida Kuwa Sbd Angane Cewa Lallai Sarki Lubainu Ne Abokin Gwamin
Jaruma Suhailat Aikuwa Tana Dauko Dutsen Ana Dubawa Aka Ambaci Sunansa Koda Jaruma
Suhailat Ta Waiga Inda Sarki Lubainu Yake Suka Hada Idanu Saita Ga Yayi Mata Murmushi
Kuma Fuskarsa Acike Take Da Annuri Gami Da Farin Ciki Bisa Mamaki Sai Sarki Yaga Jaruma
Suhailat Ta Maida Masa Martanin Murmushi, Al’amarin Daya Qara Jefashi Cikin Matsanaicin
Farinciki Ke Nan Yaji Kamar Ya Fashe Da Kukan Murna. Su Kuwa Sauran Jama’a ‘yan Kallo
Babban Bakin Cikinsu Shi Ne, Sarki Lubainu Da Jaruma Suhailat Ba Za Su Yi Wasansu Ba Sai a
ranar karshe, amma sai aka ci burin wannan rana. Nan take aka buga gangar fara gasa, aka
kirawo jarumi na farko daga cikin bakin jarumai mai suna FAIRUZ. A can bangaren jaruman Birnin
Istambul Kuwa, Sai aka kirawo wani jarumi mai suna SAIHUF, Jaruman biyu suka fito tsakiyar fili
suka fuskanci juna. Koda ‘yan kallo suka dubi fairuz da saihuf sai suka cika da tsananin mamaki
bisa ganin wani abin al’ajabi da aka gani a tare da su. Jaruman biyu dukkaninsu sun kasance
samari matasa wadanda shekarunsa ba za su haura ashirin da biyar ba. Tsawonsu da kaurin
jikinsu, kai! har da kamannin fuskokinsu ma ya kusan zuwa iri daya sak! kai kace hassan
Matsanaicin F arinciki Ke Nan Yaji Kamar Ya Fashe Da Kukan Murna. Su Kuwa Sauran Jama’a
‘yan Kallo Babban Bakin Cikinsu Shi Ne, Sarki Lubainu Da Jaruma Suhailat Ba Za Su Yi Wasansu
Ba Sai a ranar karshe, amma sai aka ci burin wannan rana. Nan take aka buga gangar fara gasa,
aka kirawo jarumi na farko daga cikin bakin jarumai mai suna FAIRUZ. A can bangaren jaruman
Birnin Istambul Kuwa, Sai aka kirawo wani jarumi mai suna SAIHUF, Jaruman biyu suka fito
tsakiyar fili suka fuskanci juna. Koda ‘yan kallo suka dubi fairuz da saihuf sai suka cika da tsananin
mamaki bisa ganin wani abin al’ajabi da aka gani a tare da su. Jaruman biyu dukkaninsu sun
kasance samari matasa wadanda shekarunsa ba za su haura ashirin da biyar ba. Tsawonsu da
kaurin jikinsu, kai! har da kamannin fuskokinsu ma ya kusan zuwa iri daya sak! kai kace hassan
da hussain Ne, Sukansu Jaruman Biyu Abin Yayi Matuqar Basu Mamaki, Basu San Sa’adda Suka
Qurawa Junansu Idanu Ba Sunayin Murmushi, Ana Buga Gangar Fara Gasar Kuma Maimakon
Sufara Dazare Makamansu Sai Suka Miqawa Juna Hannu Suka Gaisa Al’amarin Da Ya Burge
‘yan Kallo Kenan Aka Kama Yi Musu Tafi Gami Da Jinjina Bayan Fairuz Da Saihuf Sun Gaisa Sai
Suka Saki Hannun Juna Sukaja Da Baya Taku Biyar Biyar Sannan Kowannensu Yazare
Takobinsa Sukayi Kallon Kallo Na Tsawon Yan Daqiqu Kawai Sai Suka Rugo Izuwa Ga Juna
Suka Kacame Da Azabbaben Yaqi Mai Matuqar Ban Al’ajabi Cikin Gagarumar Jarumtaka SARA
DA SUKA Ba Sassauci Amma Sai Gashi Kowannensu Na Iya Kare Duk Hare Haren Da Dan
Uwansa Kekai Masa, Babu Abinda Yaqara Daurewa Mutane Kai Face Ganin Yadda Yanayin
Salon Yaqi Fairuz Da Saihuf Yazo Iri Daya Sak! Tamkar Wanda Ya Koya Musu Yaqi Mutum Daya
Ne, Sai Da Saihuf Da Fairuz Suka Shafe Kusan Daqiqa Dari Hudu Da Tamanin Sunayin
Azababben Yaqi Kuma Kowannensu Yanayin Yaqin Ne Da Dukkan Qarfinsa Dakuma Niyyar Kai
Abokin Gwaminsa Qas Amma Sai Hakan Ta Gagara, Babu Shirisuka Jada Baya Suka Tsaya
Suna Haki Sbd Tsananin Gajiya A Lbcn Da Kowannensu Yayi Sharkaf Da Gume, Kawai Saisuka
Ji Anbuga Ganga Alamar Cewar Su Ajiye Makamansu Suyi Gumurzu Da Hannu Ai Kuwa Sai
Kowannensu Ya Gyara Tsayuwarsa Suna Masu Dunqule Hannayensu, Koda Aka Aka Sake Buga
Ganga Sai Suka Rugo Da Gudu Suka Sake Kacamema Da Sabon Azababben Yaqi Yazamana
Cewa Suna Kaiwa Juna Naushi Da Bugu Hannu Daqafa Ba Sassauci, Kowannesu Na Karewa Iya
Qoqarinsa Gami Damaida Martani, Wannan Karon Saida Fairuz Da Saihuf Suka Shafe Rabin Sa’a
Cif! Suna Wannan Gumurzu Amma Dayansu Yakasa Kai Daya Qasa Kuma Sun Kasa Yiwa Juna
Illah, Koda Ganin Haka Sai Suka Jada Baya A Karo Nabiyu Suka Yi Cirko Cirko Suna Kallon
Junansu Kowannensu Yakama Yin Tunani Na Qarshe Akan Yadda Zai Sami Nasara Akan Dan
Uwansa, Bayan Shudewar ‘yan Daqiqu Kadan Sai Suka Rugo Dagudu Izuwa Kan Juna, Koda
Yarage Saura Taku Hudu Kacal Su Hadu Sai Kowannensu Yadaka Tsalle Sama, Aikuwa Suna
Haduwa A Saman Sai Suka Doki Qirazansu Da Qafafunsu Take Duk Su Biyun Suka Fado
Qasatim Suka Bugu Akan Qasa Da Gadon Bayansu Sukayi RAGAS Nanfa Filin Wasan Yarude
Da Shewa Aka Kama Yimusu Jinjina Bisa Ganin Yadda Kowannensu Yayi Bajinta, Koda Saihuf
Yamiqe Tsaye Sai Yaje Da Sauri Inda Fairuz Ke Zaune Yamiqa Masa Hannu Ya Tasheshi Tsaye
Suka Dubi Juna Cikin Murmushi Yace Ashe Akwai Mai Kamata A Komai A Duniya? Kodajin
Wannan Tambaya Sai Fairuz Yace, Nima Nayi Matuqar Mamaki Da Ganinka Yakai Wannan
Sabon Aboki Nawa Kodajin Haka Sai Saihuf Ya Rungume Fairuz Yace Ina Godiya Ga Allah Da
Yabani Aboki Na Farko A Rayuwata Wanda Yadace Dani, Ina Gayyatar Izuwa Gidanmu Yanzu
Domin Muje Muci Abinci Tare, Kuma Muyi Hira Mu More Kodajin Wannan Batu Sai Fairuz Ya
Janye Jikinsa Daga Cikin Na Saihuf Yadubeshi Cikin Murmushi Yace Nakarbi Wannan Gayyata
Taka Amma Kuma Shugabata, Dajin Wannan Batu Sai Saihuf Yadubi Fairuz Yace Yanzu Kana
Nufin Kace Wannan Kyakkyawar Budurwa Yar Uwarka Cekuma Itace Shugabarku? Fairuz Yayi
Murmushi Yace Wannan Gsky Ne Yar Khamis Idris Muhammad
[1/23, 00:53] +234 808 677 7945: ALLON SIHIRI Littafi takes 8 Part D Khamis Idris Anan Cikin
Gidaan Sarautar Kuwa Zamu Qara Matakan Tsaro Ninkin Nada, Duk Wanda Ya Kasance Baqone
Kuma Bashida Wata Alaqa Da Cikin Gidan Sarautar Nan Baza A Barshi Yashigaba, Kaiko
Ganinsa Akayi Yana Kai Kawo A Qofar Gidan Sarautar Za A Kamashi A Bincikeshi, In Bashida
Gsky Akulleshi A Kurkuku Ko Kuma Akaishi Kotu Ayanke Masa Hukuncin Daya Dace Dasu,
Nikaina Yanzu Zan Kasance Acikin Zakwaquran Dakarun Dakaru Hudun Daza A Zaba Wadanda
Zasu Jagoranci Rundunoni Hudu Ta Mayaqa Izuwa Iyakokin Qasarmu Hudu, Koda Sarki Zairuf
Yazonan A Zancensa Sai Kowa Yakamu Da Tsananin Mamaki Bisajin Cewa Sarki Zairuf Zai Bar
Kan Karagar Mulkinsa Yabar Fada Yatafi Daji Domin Kare Qasarsa Da Jama’arsa, Nan Take
Sarki Zairuf Ya Sallami Dukkan Mayaqan Bisa Yarjejeniyar Sun Amince Da Shawarar Dayakawo,
Kowannensa Yatafi Cikin Nutsuwa Da Shawarar Da Sarki Zairuf Yakawo, Amma Banda Sadauki
Ramazan, Domin Shiya Tafi Gidane Cikin Tsananin Baqin Ciki Da Tashin Hankali, Badon Komai
Ba Sai Sbd Fiyeda Shekara Ashirin Baya Yan Qullace Da Sarki Da Sarki Lubainu Bisa Wani
Hukunci Da Aka Yankewa Mahaifiyarsa Bisa Laifi Qarya Dokar Fatauci, A Lkcn Da Al’amarin
Yafaru Sarki Lubainu Yana Da Kwana Shida Ne Kacal! Akan Karagar Mulki, Kuma Aranar Ne
Sarki Lubainu Yakafa Sabbin Dokokinsa, Dokar Data Shafi Mahaifiyar Sadauki Ramazan Kuwa
Itace, Ba A Yarda Bafatake Yakwashi Kayan Abincin Daya Haura Buhu Arba’in Baya Fita Dasu
Izuwa Wata Qasar Sbd A Wannan Lkc Masu Hasashe Sun Gano Cewa Za’a Yi Fari A Shekarar,
Aranar Da Aka Qafa Wannan Doka Neda Tsawon Rabin Sa’a Guda Kacal Aka Kama Mahaifiyar
Sarkin Yaqi Ramazan Tafitar Da Keken Doki Shida Na Kayan Abinci A Sirrance Domin Takaisu
Can Wani Gari Inda Ake Samun Kazamar Riba, Kayan Abincin Sun Kai Kusan Buhu Dari Biyu Da
Arba’in Koda Aka Kama Masu Dauke Da Kayan Aka Matsasu Sai Suka Fadi Mai Kayan, Nan
Take Sarki Lubainu Yatura Aka Kamo Babar Sarkin Yaqi Ramazan Aka Kaita Kurkuku Aka Kulle,
Bayan Kwana Uku Da Faruwar Haka Sai Sarkin Qaqi Ramazan Yazo Fada Yafadi Gaban Sarki
Lubainu Yaroqi Alfarmar Ayiwa Mahaifiyarsa Afuwa A Saketa, Kuma Abata Dukiyarta, Koda Sarki
Lubainu Yaji Buqatar Sadauki Ramazan Sai Ransa Yabaci Ya Dubeshi Afusace Yace, Yakai
Sarkin Yaqi Kayi Sani Cewa Duk Sarkin Dayake Son Yayi Mulki Na Adalci Dole Ne Yafara Nuna
Misali Akansa Ko Zuri’arsa Kona Jikinsa, Idan Har Muka Yiwa Mahaifiyarka Afuwa Munbai Wa
Sauran Mutane Irinta Qofar Aikata Irin Laifin Data Aikata, Kodajin Wannan Batu Sai Hankalin
Sarki Yaqi Ramazan Ya Dugunzuma Ainun, Yazube Qasa Wanwar A Lkcn Da Idanunsa Suka
Cikoda Kwallah Kamar Zai Yiwa Sarki Lubainu Sujjada Yace, Ya Shugabana Mahaifiyata Mace
Ce Mai Tsananin Son Dukiya, Idan Harka Rabata Da Wannan Hajah Tata Zata Iya Hadiyar Zaciya
Ta Mutu! Kodajin Wannan Batu Sai Sarki Lubainu Yamiqe Tsaye Daga Kan Karagar Mulkinsa
Yajuyawa Sarki Yaqi Ramazan Baya Sannan Yace, Na Rantse Da Darajar Abin Bautarmu Ko
Uwata Tace Ta Aikata Wannan Laifi In Dai Tana Raye A Doron Kasa Ba Zan Yi Mata Afuwa Ba
Lallai Dole Ne A Kwace Wannan Dukiya Ta Mahaifiyarka Kuma Dole Ne Tayi Zaman Kurkuku Na
Tsawon Wata Shida! Koda Gama Fadin Hakan Sai Sarki Lubainu Yajuya Yafice Daga Cikin Fadar
Gaba Daya Yabar Sarki Yaqi Ramazan Tsugunne Aqasa Cikin Tsananin Baqin Ciki Yana Mai
Zubar Da Hawaye, Kamar Yadda Sarki Lubainu Yafada Haka Al’amarin Ya Kasance, Wato Saida
Aka Kwace Dukiyar Mahaifiyar Sarkin Yaqi Ramazan Gaba Daya, Kuma Aka Yanke Mata
Hukuncin Zaman Wata Shida A Gidan Yari, Kodajin Irin Wannan Hukunci Da Aka Yanke Mata,
Nan Take Ta Hadiyi Zuciya Tazube Qasa Matacciya, A Wannan Rana Sarkin Yayi Kuka Kamar
Ransa Yafita, Domin Har Dare Yaraba Yana Tsugunne Agaban Kabarin Mahaifiyar Tasa Yana
Kuka, Saida Yadawo Cikin Hayyacinsa Sannan Yaqurawa Kabarin Idanu A Lkc Da Fuskarsa Ta
Murtuke Izuwa Tsananin Fishi Dabaqin Ciki Mara Misaltuwa Yace, Yake Ummina Na Rantse Da
Darajar Jininki Dake Cikin Nawa Bazan Taba Yafewa Sarki Lubainu Ba, Lallai Komai Dadewa Sai
Na Dauki Fansar Ranki Akansa, Saina Rushe Daular Mulkinsa Na Jefashi Cikin Mugun Baqin Ciki
Makamancin Wanda Ya Jefani Daga Wannan Rana Sarkin Yagi Ramazan Ya Cigaba Da Qullatar
Sarki Lubainu Acikin Ransa Yana Tunanin Hanyoyin Dazaibi Ya Dauki Fansa Akansa, Amma Har
Akazo Wannan Lkc Da Sarki Lubainu Yakamu Da Wannan Cuta Bai Samu Mafitaba, Koda Yaga
Sarki Lubainu Yakwanta Ciwo Sai Farinciki Ya Lullubeshi Yaga Cewa Lallai Yasami Babbar
Damar Dazai Dauki Fansarsa, Kawai Sai Yamanta Da Batun Amanar Dake Tsakanin Iyayensa Da
Gidan Sarki, Tunda Dai Sarkin Yajuya Masa Baya Yaqi Yi Masa Alfarma, Nan Take Sarki Yaqi
Ramazan Ya Fadada Tunanin Sakan Yadda Haqqansa Zai Cimma Ruwa Domin Yakawar Da
Gwamnitin Sarki Lubainu, Bisa Wannan Dalili Ne Yakawo Wannan Gurguwar Shawara Afada Ta
Cewar A Aika Da Yan Leqen Asiri Izuwa Ga Iyakokin Qasar Maimakon A Aika Da Dakarun Yaqi, A
Zatonsa Sarki Sabon Sarki Zairuf Bashi Da Basirar Gano Illar Yin Hakan, Sbd Hakane Ma Lkcn
Dayaji Sarki Zairuf Yakawo Nasa Shawarwarin Masu Matuqar Muhimmanci Da Inganci Sai
Zuciyarsa Takadu Matuqa Yakamu Da Tsananin Mamaki Harma Yafara Tunanin Cewa Lallai
Wannan Tunani Da Basira Ba Daga Zairuf Bane Shi Kadai, Kodai Sarki Lubainu Ne Yatsara Masa
Wannan Dabara Ko Kuma Jaruma Suhailat, Domin Sune Kadai Suke Da Irin Wannan Kwarewa
Tayaqi Gami Da Sanin Tuggu Damakircin Samun Nasara, Lkcn Da Sarkin Yaqi Ramazan Yatafi
Izuwa Gidansa Bayan An Tashi Daga Fada Sai Yawuce Izuwa Can Wani Gida Nasa Dake Can Bayan Gari Inda Yake Tafiyar Da Harkokinsa Na Sirri, Amma Bai Wuce Kai Tsaye Ba Izuwa
Gidan Sai Daya Rinqa Zagaye Yana Yin Kamar Wasu Wuraren Zai Je Yarinqa Bin Hanyoyi Kala
Kala Don Kada Ya Kasance Wani Yalabe Yana Biye Dashi Bai Saniba, Duk Sa’adda Sarkin Yaqi
Ramazan Yayi Yar Doguwar Tafiya Sai Yai Wuf Yafada Cikin Wata Duhuwar Shida Dokinsa
Yabuya Yana Leqen Kan Hanya Kozai Gawani Dan Leqen Asiri Yana Binsa, Hakadai Ya Cigaba
Da Tafiya Har Sai Daya Tabbatar Dacewa Babu Mai Binsa Sannan Ya Cigaba Da Tafiyarsa Cikin
Kwanciyar Hankali, Har Ya Isa Wannan Gida Nasa Na Sirri Wanda Bashida Maqofci Akusa, Da
Isarsa Sai Wadansu Dakaru Guda Hudu Masu Tsaron Gidan Suka Rugo Suka Taryeshi Suna
Yimasa Barka Dazuwa Suka Kaamamasa Dokin Yasauqa, Sannan Yashige Cikin Gidan, Shidai
Wannan Gida Yaqawatu Ainun Daga Cikinsa Domin Mutum Nashigarsa Zai San Cewa Yashigo
Cikin Gidan Mashahurin Attajiri, Masana Damasu Bincike Sun Tabbatar Dacewa Indai Ba
Masarautar Birnin Istambul Ba Babu Zuri’ar Wacce Tafisu Sarkin Yaqi Ramazan Qarfin Arziqi
Dakudi Acikin Gaba Dayan Birnin Istambul Don Haka Mahaifinsa Sarki Yaqi Ramazan Yamutu
Yabar Dukiya Mai Dumbin Yawa Hakama Mahaifiyarsa Sbd Tuntana Matashiya Mahaifinta Daya
Kasance Gagarumin Attajiri Yafara Tafiya Da Ita Yawon Fatauci Zuwa Qasashen Duniya Tareda
Haja Mai Dumbin Yawa, Inda Itama Idanunta Suka Bude Sosai, Aqarshe Ma Lkcn Daya Mutu
Tagaji Dunbin Dukiya Maitarin Yawa, Yawan Da Ita Kanta Batasan Adadintaba, Kuma Ta Cigaba
Da Gudanar Da Harkokinta Na Fatauci Ta Tara Yara Da Mayaqa A Sassa Sassa Daban Daban
Na Duniya, Takai Cewa Tadaina Gudanar Da Fataucinta Da Mutane Gama Gari Saidai Manyan
Sarakuna Da Manyan Attajiran Dasuka Shahara Aduniya Wajen Dukiya Da Dunbin Kadarori Haka
Itama Mahaifiyar Sarkin Yaqi Ta Cigaba Da Tara Dumbin Dukiya Hartayi Aure Ta Haifi Sarkin Yaqi
Ramazan Wanda Ya Kasance Shine Danta Itama Guda Daya Tal! Saidai Wani Abin Mamaki
Kwata Kwata Mahaifiyarsa Ta Hanashi Yakoyi Harkar Kasuwanci, Maimakon Hakan Sai Ta Bayar
Dashi Gawani Tsohon Sarki Yaqin Abinin Don Ya Horar Dashi Yaqi, Arana Ta Farko Da Ramazan
Ya Halarci Horon Yaqin, Yayi Matuqar Shan Wahala Yadawo Gida Yana Kuka, Yana Shiga
Turakar Mahaifiyarsa Yasameta Tana Zaune Tanacin Inibi Ga Bayi Nan Suna Tayi Mata H
[1/23, 00:54] +234 808 677 7945: ALLON SIHIRI Littafi na Bakwai 7 Part E Lokacin da sarki
Lubainu Yadauki Tambulan Na Ruwa Inibi Yazuba Acikin Kofin Zinaren Yakama Sha, Itakuwa
Jaruma Suhailat Sai Tajuya Tatafi Masauqinta Zuciyarta Cike Da Saqe Saqe Gamida Wasi Wasi,
Tana Mai Tambayar Kanta Acikin Zuciyarta, Shin Wani Irin Matakin Tsaro Kuma Sarki Lubainu Zai
Dauka Akaina Da Jama’ata Alhalin Zamu Iya Baiwa Kanmu Kariya Daga Kowanne Irin Hari
Daza’a Kawo Mana? Kuma Ai Babu ‘yan Fashi Ko ‘yan Harin Sumame Acikin Dajin Dake
Kewayen Birninsa Ko Cikin Birnin Bare Yaji Tsoro Ko Za’a Kawo Mana Harin MAMAYAR
BAZATO! Hakadai Jaruma Suhailat Taci Gabaga Da Wannan Tunani Har Ta Isa Dakinta Ta
Kwanta Akan Gado, Kwanciyarta Kedawuya Sai Barci Ya Saceta Sbd Har A Sannan Maganin
Barci Da Likita Ya Shayar Da Ita Bai Gama Sakintaba, Kashe Garikuwa Da Farkon Yammaci
Jaruma Suhailat Tayi Shirin Fita Farauta Daji, Amma Sataqi Sanarda Mahaifinta Sadauki Zahar,
Shikansa Sarki Lubainu Din Bata Sake Sanar Dashiba, Kawai Saita Debi Zakwaquran Dakaru
Guda Huhu Kacal Daga Cikin Jama’arta Suka Ficn Daga Cikin Birnin Istambul Dayake Jaruma
Suhailat Tasan Cewa Idan Ja Baiyana Kanta Fili Mutane Ne Zasuta Binta Suna Kallonta Sbd
Kyawunta Saitayi Bad Dakama Tayi Shigar Maza Aka Nada Mata Rawani Aka Kumayi Ma Gemu
Da Gashin Baki, Maimakon Suyi Shigar Mafarauta Sai Sukayi Shigar Fatake, Tundaga Nesa
Dakarun Sumame Da Sarki Bauzur Ya Baiwa Kwangilar Sato Jaruma Suhailat Suka Hango
Matane Biyar Sun Fito Daga Cikin Birnin Istambul Acikin Shigar Fatake Sai Suka Fito Daga Inda
Suke Boye Suka Musu Qawanya, Sudai Wadannan Dakarun Sumame A Cikin Shigar Baqaqen
Kaya Suke Kuma Sun Rufe Fuskokinsu Da Baqin Rawani Idanunsu Kadai Akegani Kuma Suna
Dauke Da Takubba, Wuqaqe Da Kwari Da Bakag Kuma Adadinsu Yafi Dubu, Kawai Sai
Shugaban Dakarun Sumamen Wani Garjejen Qato Mai Qirar Sadauki Tamkar Zanashi Akayi, Ya
Dubi Su Jaruma Suhailat Yadaka Musu Tsawa Yace Kukuma Suwaye, Daga In Zuwa Ina?
Kodajin Wannan Tambaya Sairan Jaruma Suhailat Yabaci Taga Cewa Ai Wannan Tambaya Ce
Ma Tarainin Wayo! Har Tabudi Baki Zata Bashi Amsa, Amma Saita Tuna Cewa Tanayin Magana
Zata Tonawa Kanta Asiri Aji Muryarta Agane Cewa Ita Macece, Don Haka Sai Tayi Shiru, Take
Daya Daga Cikin Dakarun Nata Yadubi Shugabau Dakarun Sumamen Yace, Mu Fatakene Daga
Birnin Hasur, Kuma Mungama Cin Kasuwane Acikin Birnin Istambul, Yanzu Muna Kan Hanyarmu
Ta Komawa Birninmu, Kodajin Wannan Batu Sai Shugaban Dakarun Sumamen Yabushe Da
Dariya Lkc Guda Kuma Ya Turbune Fuskarsa Yasake Daka Musu Tsawa A Karo Na Biyu Yace,
Yaku Wadannan Qananan Kwari Kadaku Maishemu Sakarkaru Ku Raina Mana Hankali, A
Inakuka Taba Ganin Fatake Babu Hajah Kuma Babu Kudin Dasuka Samo Na Ciniki, Kun Cika
Fuskokinku Da Tarin Gemun Banza Kamar Wadansu Bokaye, To Kusani Cema Muba Barayi
Bane, Domin Munsani Cewa Ba Ayin Sata Anan Birnin Istambul, Muna Neman Wata Mace Ne
Guda Daya Wai Ita Jaruma Suhailat! Ta Tunda Yanzu Daga Cikin Birnin Kuke Kokuma Yanzu
Nan Takobina Tasha Jinanku, Kodajin Wannan Batu Sai Dakarun Jaruma Suhailat Suka Dubi
Junansu Suk Dariya Sbd Sun R Kwatsam! Sai Jaruma Suhailat Taga An Harbo Wadansu
Qananan Allurori Sun Tsire Dakarun Nata Shida Acikin Wuyansu Sun Zube Qasa Matattu, Cikin
Tsananin Fishi Da Mugun Baqin Zafin Nama Jaruma Suhailat Tadaka Tsalle Sama Daga Kan
Dokinta Tana Mai Zare Takobinta Tayi Shawagi Akan Dakarun Sumamen, Kafin Taduro Qasa
Tasare Kawunan Mutum Arba’in Sai Ga Jini Na Tsiri Ta Cikin Dungulmin Wuyansu, Koda Ganin
Haka Sai Dakarun Sumamen Suka Taso Mata Gaba Dayansu Suka Afka Mata Da Yaqi, Nanfa
Jaruma Suhailat Tarinqa Ragargazar Dakarun Sumamen Tamkar Tana Sassabe A Gona Duk
Inda Tasa Gabanta Sai Dai Kaga Maza Na Zubewa Qasa Rututu, Koda Shugaban Dakarun
Yaqura Jaruma Suhailat Idanu Yalura Da Yanayin Yaqinta Saiya Dakawa Yaran Sa Tsawa Suka
Jada Baya Suka Bar Jaruma Suhailat A Tsakiyarsu Tana Fuskantar Shugaban Nasu, Shugaban
Yanuna Jaruma Suhailat Da Dan Yatsansa Na Hagu Yace, Na Rantse Da Gemun Ubana Wannan
Jaruma Suhailat Ce Tayi Shigar Maza! Idan Kin Isi Ki Baiyana Kanki Nagani!! Kina Zaton Ni
Wawane Harda Bazan Iya Shaida Yanayin Yaqinkiba Alhali Naga Duk Irin Gumurzun Dakikayi Da
Sarki Lubainu? Koda Shugaban Dakarun Sumame Yazo Nan A Jawabinsa Sai Jaruma Suhailat
Tasa Hannunta Tacire Rawanin Dake Kanta Gamida Gemun Data Saka A Fuskarta Tayi Wurgi
Dasu Kyakkyawar Fuskarta Ta Bayyaxa Qarara Afili, Koda Ganinta Sai Shugaban Dakarun Ya
Bushe Da Mahaukaciyar Dariya Mugunta Yadubi Jaruma Suhailat Yace, Yake Sarauniyar Matan
Duniya Kiyi Sani Cewa Ba A Turomu Domin Mukashekiba Komu Lalata Wannan Kyakkyawan Jiki
Naki Ba Wanda Gaba Dayan Dinaren Duniya Bazai Iya Siyansa Ba, Ina Mai Shawartarki Daki
Miqa Wuya Agaremu Mukamaki Salin Alin Mukaiki Ga Shugabanmu Don Cika Aikinmu Idan Kuma
Kinqi Tozamu Yi Amfani Da Hanyar Dazata Fisshemu, Kafin Shugaban Dakarun Yagama Rufe
Bakinsa Tuni Jaruma Suhailat Ta Tari Numfashinsa Tanamai Dakamasa Tsawa Tace, Yakai
Wannan Qaton Banza, Karen Farautar Azzalumai, Maza Kasanar Dani Wanda Ya Aikoku Ku
Kamani Ku Kaini Gareshi Ko Yanzunnan Kuzama Abincin Ungulaye!! Kodajin Haka Sai Shugaban
DakarunYa Tuntsire Da Mahaukaciyar Dariza Sannan Yadubi Sauran Yaran Nasa Yayi Musu
Wata Inkiya, Take Suduka Suka Dauko Wani Siririn Dututu Mai Kamada Qaho Suka Hurashi Sai
Ga Wadansu Irin Allurai Sunfito Daga Cikin Bututun Sunyi Kan Jaruma Suhailat Zasu Tsittsireta,
Cikin Baqin Zafin Nama Nagaban Kwatance Jaruma Suhaila Ta Daka Tsalle Sama Tayi Amfani
Da Takobinta Da Garkuwarta Ta Karkade Alluran Wadanda Adadinsu Yakai Dubu Biyu, Aikuwa
Sai Kaiqayi Yakoma Kan Masheqiya, Ma’ana Su Alluran Suka Koma Kan Wadanda Suka Hurosu
Suka Sossokesu Suka Zube Qasa Suka Kama Barcin Dole, Kafin Jaruma Suhailat Tadora Qasa
Ta Dirqa Bayan Shugaban Dakarun Ta Dora Kaifin Takobinta Akan Wuyansa, Nanfa Jikin
Shugaban Dakarun Yakama Qyarma Sbd Yaga Mutuwa Muraran! Jaruma Suhailt Tadubi
Shugaban Dakarun Tace, Maza Ka Sanar Dani Ubangidanka Wanda Yaturoka Ka Kamani Inba
Hakaba Kuwa Yanzu Nan Zan Sharbe Maqogwaronka Da Wannan Takobi Nawa, Kafin
Badakaren Yabude Baki Yayi Magana Tuni An Gabzawa Jaruma Suhailat Wawan Naushi
Aqeyarta Ta Bayan [8/13, 12:15] khamis idris muhammad: Ta Kawai Sai Ta Sulale Qasa
Sumammiya, Bawani Bane Ya Baiyana Awajen Ba Tsulum Yasumar Da Jaruma Suhailat Face
Sarki Bauzur, Koda Sarki Bauzur Yaga Yasami Wannan Nasara Sai Ya Bushe Da Dariyar Farin
Ciki, Sannan Yadubi Shugaban Dakarun Yadaka Masa Tsawa Yace, Sakaran Banza Tunda
Kakasa Idi Aikinka Baka Da Sauran Cikon Kudi Awajena, Kayata Kanka Kona Qasasa Aikin Da
Jaruma Suhailat Tabari Yanzunnan, Dajin Ha Badakaren Yajuwa Da Baya Yaruga Izuwa Cikni
Daji Batare Da Ya Yarda Yayi Ko Waiwayeba, Cikin Matuqar Farin Ciki Sarki Bauzur Yasunkuya
Ya Ciccibi Jaruma Suhailat Da Hannayensa Biyu Sannan Yabace Bat! Daga Wajen Tamkar Bai
Taba Baiyana Awajenba, Sarki Bauzur Baisake Bayya Ako Inaba Sai A Wannan Gida Daya Kama
Haya Wanda Ke Can Bayan Garin Birnin Istambul, Kaitsaye Ya Shige Da Jaruma Suhailat Izuwa
Cikin Turakar Barci Yaturo Qofar Turakar Ya Kulleta Sannan Yaje Ya Shimfideta Jaruma Suhailat
Akan Wani Gado Na Alfarma Jikinsa Na Karkarwa Kuma Cikin Zaquwa Da Doki, Yai Sauri Yatuje
Rawanin Kansa Kuma Yacire Alkyabbarsa, Yanashirin Afkwa Jaruma Suhailat Kenan Kawai
Saiyaji Katangar Dakin Taruguje, Tsakiyarta Yafaso Saiga Sarki Lubainu Yaratso Ta Ciki Tamkar
Bayyanar Walqiya Daga Sama, Kafin Sarki Bauzur Yayi Wani Yunquri Tuni Sarki Lubainu Ya
Gabza Masa Wani Wawan Naushi Aqirji, Sbd Qarfin Naushin Sai Da Sarki Bauzur Yafado Qasa
Acikin Tsananin Galabaita Yakasa Miqewa Tsaye, A Lkcn Ne Sarki Lubainu Yadubi Sarki Bauzur
Cikin Tsananin Fishi Yadaka Masa Tsawa Yace, Kai Tsohon Annamimi Kuma Maci Amana, Kayi
Sani Cewa Taguwar Manya tafiqarfin Wuyan Yara! Wane Kaika Ce Zakayi Taraiya Da
Masoyiyata? Tokasani Cewa Wannan Babban Laifi Daka Aikata Sai Hukunci Ya Shafi Gaba
Dayan Jama’arka, Kodajin Wannan Batu Sai Sarki Bauzur Ya Yunqura Dakyar Yamiqe Tsaye
Sannan Yazare Wadansu Gajerun Adduna Guda Biyu Daga Kuibin Cinyoyinsa Ya Kwarara Uban
Ihu Sannan Yadubi Sarki Lubainu Cikin Tsananin Fishi Da Qiyayya Yace, Yakai Tsohon Abokin
Gaba, Kayi Sani Cewa Nadade Ina Tanadin Wannan Rana Wacce Zamuyi GABA DA GABA
Dagani Saikai! Kaine Kadai Sarkin Da Yatsone Mini Ido Akaf Wannan Nahiya Gaba Daya! Kaine
Kadai Wanda Nadade Ina Shakka, Amma Yanzu Danaga Wannan Kyakkyawar Budurwa Kuma
Naga Kana Neman Mallaketa Saina Kawarda Haqurin Da Nadade Inayi Tsawon Shekaru, Bazai
Taba Yiwuwa Kafimu Mulki, Kudi Da Daukaka Ba Sannan Kuma Ace Ka Auri Macen Da Babu
Kamarta Akyau Aduk Duniya! Naso Nacika Burina Na Sanin Wannan Kyakkyar Budurwa Kafin Kai
Domin Ina Nasami Hakan Nagama Dakai Koda Kuwa Ka Kasheni Ka Malleketa Amma Tunda Ka
Katsemin Burina Tofa Yanzu Sai Abinda Hali Yayi! GANI GAKA, Kuma DAGANI SAIKAI, Gakuma
Tauraruwar Matan Duniya Jaruma Suhailat Akwance A Gabanmu Cikin Halin Suma, Idan Kasami
Nasarar Kasheni Shikenan Saika Dauki Abarka Kutafi, Idan Kuma Nine Nasamu Nasara Kasheka,
Zanje Nakame Birninka Nahau KARAGAR MULKINKA Kuma Na Aure Jaruma Suhailat Nabarwa
Duniya Tarihin Da Har Abada Baza A Taba Mancewa Daniba, Koda Sarki Bauzur Yazonan A
Zancensa Sairan Sarki Lubainu Yabaci Zuciyarsa Takama Tafarfasa Kamar Zata Qone, Nantake
Shima Yazare Takobinsa Kuma Yacire Garkuwarsa Ajikin Cinyarsa Yariqe Ya Fuskanci Sarki
Bauzur Suka Kama Hararar Juna, Daga Can Kuma Sai Duk Subiyun Suka Dako Tsalle Sama
Sukahadu Acikin Iska Suka Ruguntsume Da AZABBBEN YAQI, Yazamana Cewa Suna Kaiwa
Junansu Sara Dasuka Cikin Tsananin Zafin Nama, JURIYA DA BAJINTA, Faruwar Hakan Keda
Wuya Sai Jaruma Suhailat Ta Farfado Daga Dogon Sumanda Tayig Koda Tabude Idannunta
Tadubi Dakin Datake Ciki Kuma Taga Sarki Lubainu Da Sarki Bauzur Suna Fafata Qazamin Yaqi
Saita Cika Da Tsananin Mamaki, Kawai Saita Miqe Zaune Ta Zubawa Su Sarki Lubainu Idanu
Tana Mamaki, Ba Komaine Yabata Mamaki Ba Face Ganin Cewa Ashe Akwai Gwarzon Jarumin
Da Zai Iyada Sarki Lubainu Bata Saniba, Saida Su Sarki Lubainu Suka Rugurguje Gaba Dayan
Katangun Wannan Dakin Dasuke Gumurzu Aciki Sbd Masifaffen Yaqin Dasuke Fafatawa, Ita
Kanta Jaruma Suhailat Inda Badon Tana Tsale Tsale Da Kauce Kauce Ba Datuni Sun Cutar Da
Ita, Hakadai Suka Cigaba Dakaiwa Junansu SARA DA SUKA Cikin Mugun Nufi Har Izuwa
Tsawon Sa’a Guda Batare Da D ayansu Yasami Nasarar Koda Lakutar Jikin Dayaba, Bisa Dole
Sukaja Dabaya Taku Shida Sukayi Cirko Cirko Suna Haki Da Kallon Juna Tamkar Zakaru, Kawai
Sai Sarki Bauzur Yawatsowa Sarki Lubainu Kibiyoyin Tsafi Sama Da Guda Dubu Suka Taho
Dagudu Cikin Iska Zasu Tsireshi, Amma Suka Kamada Wuta Suka Qone Qurumus Suka Zama
Toka Tunma Kafin Su Iso Jikin Sarki Lubainu Nanfa Suka Cigabada Dakaiwa Junansu Miyagun
Hare Hare Daqarfin Sihiri Amma Duk Abanza, Domin Sihirin Tsafin Yaqi Yayi Tasiri Akan
Kowannensu, Koda Ganinhaka Sai Sarki Lubainu Ya Bushe Da Dariya Sannan Dubi Sarki Bauzur
Yace, Tabbasa Na Yarda Kadade Kana Shiri Da Tanadi Akan Wannan Rana Dazamu Hadu, To
Amma Kasani Cewa Ba’asan Maci Tuwoba Sai Miya Taqare! Kuma Masu Salon Magana Sunyi
Gsky Dasuke Cewa Kyan Fada Akwana Anayi! Domin A Sannanne Ake Sanin Waye Jurarre
Kuma Waye Gwani Mai Nasara? Yanzune Zamuyi Yaqi Da Dukkan Tsagwron Qarfin Damtsenmu
Dakuma Kwarewarmu A Yaqi. Idan Na Kasheka Tabbas Qasarka Da Jama’arka Sun Zama Nawa,
Idan Kuma Kaine Ka Kasheni Nayarda Kasata Jama’ata Dakuma Masoyiyata Jaruma Suhailat
Sun Zama Naka, Sarki Lubainu Yajuya Ya Kalli Jaruma Suhailat Yace, Yake Masoyiyata Ina Mai
Roqonki Da Koda Kinga Sarki Bauzur Zai Sami Nasara Akaina Kada Ki Taimaka Mini, Idan Harya
Kasheni Kema Saiki Kwaci Kanki A Hannunsa Don Nasan Zaki Iya Samun Sa’ar Hakan, Koda
Gama Fadin Hakan Sai Sarki Lubainu Yaruga Izuwa Kan Sarki Bauzur Suka Runguntsume Da
Sabon AZABABBEN YAQI Akaro Nabiyu Amma Wannan Karon Sai Sukb Sauya Salon Fada Suka
Hada Dakaiwa Junansu Naushi Da Bugu Da Hannu Daqafa Gamida Kai SARA DA SUKA!
Wohoho!! Idan Qarfi Ya Hadu Daqarfi, Kuma Gwani Yayi Karo Da Gwani Sai Gumurzu Yazamo
Abin Al’ajabi, Kuma Abin Tsoro Mai Dadin Kallo, Shikansa Sarki Lubainu Yayi Matuqar Mamaki
Yadda Akayi Sarki Bauzur Yakeda Wannan Gagagarumin Qarfi Da Jarumtaka, Haka Kuma
Yaboye Kansa Tuntuni Baiyi FITO NA FITO Dashiba, Ya Tsaya Yana Shakkarsa Alhalin Yanada
Wannan Babban Shiri [8/13, 12:16] khamisidrismuhammad: Haka, Saida Suka Shafe Sa’a Guda
Suna Wannan BAKIN ARTABU, Kwatsam! Sai Sarki Bauzur Ya Shammaci Sarki Lubainu Yadebo
Ruburbushin Qasar Gini Yawatsa Masa A Ido, Kafin Sarki Lubainu Ya Mutsttsike Idanunsa Tuni
Sarki Bauzur Ya Danqara Masa Sara Aqirji, Take Wajen Yadare Jini Yai Tsartuwa, Amma Sbd
Tsananin Juriya Da Jarumtaka Ko Ihu Sarki Lubainu Baiyiba, Kuma Duk Da Haka Idanunsa Arufe
Suke Sai Yayi Amfani Da Kunnensa Yagano Inda Sarki Bauzur Ke Tsaye Don Haka Sai Yadaka
Tsalle Sama Ya Shallake Sarki Bauzar, Ta Baya Ya Danqarawa Sarki Bauzur Martanin Sara A
Gadon Bayansa, [8/13, 12:16] khamis idris muhammad: Take Shima Bauzur Bayansa Ya Dare
Jini Yai Tsartuwa Da Feshi, Bai San Sa’adda Yakurma Uban Ihu Ba Sakamakon Tsananin Zafi Da
Zogin Dayaji, Duk Subiyun Sai Suka Kife Qasa A Lkcn Dajini Kezuba Ajikinsu, Cikin Firgici Jaruma
Suhailat Ta Yunqura Zata Ruga Izuwa Kan Sarki Lubainu, Amma Sai Yadaga Mata Hannu Yana
Mai Yimata Nunida Tadakata, Nan Take Sarki Lubainu Da Sarki Bauzur Suka Yunqura Cikin
Matuqar Qarfin Hali Da Juriya Suka Miqe Tsaye Duk Da Cewa Jiri Na Dibarsu Sakamakon Jininda
Suke Zubarwa Ajikin Nasu, Nan Fa Suka Tsaya Suna Kallon Juna Cikin Harara Da Tsananin
Qiyayya, Daga Can Sai Suka Sake Rugowa Da Gudu Izuwa Kanjuna Cikin Mugun Nufi, Kai
Dagani Kasan Cewa A Wannan MUGUWAR HADUWA Daza A Yi Dole Ne Cikin Biyu Ayi Guda,
Kodai Suyi RAGAS Wato Sukashe Junansu, Kokuma Dayansu Yasami Nasarar Kashe Daya,
Aikuwa Suna Haduwa Sai Kowannensu Ya Kaiwa Dan Uwansa Muguwar Suka A Ciki Amma Sai
Suka Kare Sukar Da Takubbansu, Tartsatsin Wuta Yatashi Akan Takubban, Kawai Sai Sarki
Bauzur Yasake Kawowa Sarki Lubainu Suka A Maqoshi, Cikin Baqin Zafin Nama Sarki Lubainu
Ya Sunkuya Tsinin Takobin Ya Soki Iska, Kafin Sarki Bauzur Yaqara Kawo Masa Wani Harin Tuni
Sarki Lubainu Yayi Wata Irin Katantanwa Aqasa Kuma Yatale Qafafunsa A Qasan Ya Sokawa
Sarki Bauzur Takobin A Ciki, Take Takobin Ta Lume Tafaso Gadon Bayan Sarki Bauzur Jini
Yafara Feshi, Kawai Sai Jaruma Suhailat Taga Sarki Bauzur Yaqame Atsaye Kuma Takobinsa Ta
Subuce Daga Hannunsa Tafadi Qasa, Sai Ga Jini Nazuba Ta Bakinsa, A Sannan Ne Sarki
Lubainu Ya Yunqura Domin Yamiqe Tsaye Amma Sai Yafadi Qasa Sakamakon Jirinda Yakwashe
Shi, Koda Ganin Haka Sai Jaruma Suhailat Tarugo Da Gudu Ta Sunkuci Sarki Lubainu Cikin
Dimauta Ta Azashi A Kafadarta Danufin Ta Ruga Waje Dagudu, Har Izuwa Wannan Lkc Sarki
Bauzur Natsaye Yazama Gawa Amma Bai Fadi Qasaba, Kawai Sai Jaruma Suhailat Taji Sarki
Lubainu Yace, Ciromin Takobina Daga Jikin Wannan Babban Maqiyi Nawa, Cikin Sauri Ta Waiga
Takama Qotar Takobin Ta Zarota Daga Cikin Sarki Bauzu Tana Zarewa Ne Gawar Sarki Bauzur
Takifeqasa Jaruma Suhailat Taruga Waje Da Gudu Dauke Da Sarki Lubainu A Kafadarta Ta Duro
Tsakiyar Gidan, Koda Dakarun Sarki Bauzur Suka Hango Gawar Sarkinsu Kwance A Cikin Dakin
Sai Dukkaninsu Suka Yarda Makamansu Suka Arce, A Guje Jaruma Suhailat Suka Isa Wajen
Wani Doki Ta Dora Sarki Lubainu Akai Sannan Itama Tahau Ta Zabureshi Da Gudu Tanufi Cikin
Gari, Jaruma Suhailat Tana Cikin Gudu Akan Dokin Ne Saita Lura Cewa Sarki Lubainu Fa
Yasuma, Donko Motsi Bayayi, Kuma Har A Sannan Jini Na Cigaba Dazuba Ajikinsa, Nanfa Ta
Dimauce Ta Kurma Uban Ihu Kuma Tafashe Dakuka Tana Mai Qarawa Dokinta Qaimin Gudu Sbd
Gani Take Kamar Kafin Ta Isa Gidan Sarautar Sarki Lubainu Ya Mutu, Tundaga Nesa Damasu
Gadin Qofar Gidan Sarautar Suka Hango Jaruma Suhailat Dauke Da Sarki Lubainu Bisa Doki
Cikin Jini Saisuka Dimauce Suka Bude Qofar Dasauri Kuma Suka Busa Qaho Alamar Cewa Ba
Lfy, Aikuwa Sai Dakarun Gidan Sarautar Suka Kama Guje Guje Da Shirye Shirye Ana Debo
Makaman Yaqi Don Anzata Yaqine Ya Barke, Jaruma Suhailat Na Isowa Harabar Turakar Sarki
Sai Hadimai Suka Rugo Suka Karbi Sarki Aka Shigar Dashi Cikin Turakar Kuma Aka Ruga Aka
Kirawo Likitansa, Har Likitan Yagama Dinke Raunin Dake Kan Qirjin Sarki Lubainu Aka Sa Masa
Magani Bai Farfado Ba Kuma Ba Cikakken Numfashi A Qirjin Nasa, Inbanda Ma Likitan Ya
Tabbatar Dacewa Sarki Lubainu Bai Mutuba Da Kowa Yazata Ya Mutu Din, A Wannan Lkc
Turakar Sarki Lubainu Tacika Da Dukkan Fadawansa Da Hadimansa Anyi Jugum Jugum,
Wasuma Sun Dan Fara Koke Koke Masu Taurin Zuciyane Ke Zubarda Hawaye Kawai, Ita Kuwa
Jaruma Suhailat Kuka Take Tayi Sosai Tana Zubarda Hawaye Mai Yawa, Al’amarin Dayasa Kowa
Awajen Yagane Cewa Lallai Tana Son Sarki Lubainu, Bayan Likita Yadubi Gaba Dayan Hadiman
Sarki Da Fadawan Yace, Akwai Buqaqatar Kowa Yafita Yabar Sarki Dagashi Sai Masu Yimasa
Hidima Da Jaruma Suhailat Domin Sukadai Yake Buqata Ayanzu, Kada Kowa Yaqara Shigowa
Wajensa Hasai Bayan Yadawo Cikin Hayya Cinsa, Kodajin Haka Sai Kowa Yafice Akabar Jaruma
Suhailat Ita Kadai Zaune A Gefen Gadon Da Sarki Lubainu Ke Kwance Taqurawa Fuskarsa Idanu
Tana Zubarda Hawaye, Sukansu Hadiman Sarki Fita Sukayi Suka Tsaya Abakin Qofar Dakin
Suna Jiransuji An Kirasu Domin Aiwatarda Wani Umurni, Sai Da Darn Yaraba, A Lkc Da Jaruma
Suhailat Tafara Gyan Gyadi Sbd Dadewar Datayi Azaune Gamida Gajiya Sannan Sarki Lubainu
Ya Farfado Daga Dogon Sumanda Yayi, Kodaya Bude Idanunsa A Hankali Yaga Suhailat Zaune
A Gabansa Gyangyadi Sai Farin Ciki Ya Lullubeshi Bisa Ganin Cewa Lallai Jaruma Suhailat
Tadamu Da Rayuwarsa Tunda Gashima Takasa Tafiya Tabarshi, Kamar A Mafarki Jaruma
Suhailat Taji Ankirawo Runanta Suhailau!! Jaruma Suhailat Tafarka Firgigit! Tadubi Inda Sarki
Lubainuke Kwance Aikuwa Saita Kamuda Tsananin Mamaki Domin Ganinsa Tayi Azaune Yaqura
Mata Idanu Yana Murmushi, Cikin Tsananin Farin Ciki Jaruma Suhailat Ta Yunqura Zata
Rungumeshi Sai Sukaji An Kwankwasa Qofar Turakar Wani Hadimi Yace, Ya Shugabana Ga
Mahaifin Jaruma Suhailat Yazo Dubaka, Yafi Sa’a Hudu Tsaye Aqofar Dakin Nan Yana Jiran Ka
Tashi Kodajin Wannan Batu Sai Sarki Lubainu Yace Abudemasa Yashigo, Take Hadimin Yabude
Qofar Sai Ga Sadauki Zahar Ya Shigo Fuskarsa Cike Da Annuri, Jaruma Suhailat Tamiqe Tsaye
Taruga Gareshi Suka Rungume Juna Cikin Murna Sannan Ya Janye Jikinsa Daga Cikin Nata
Yamatso Gaban Sarki Lubainu Ya Risina Yakwashi Gaisuwa Yace, Barkanka Da Shallake Harin
Mutuwa Yakai Wannan Sarki, Tabbas Kayi Babbar Sa’a Daya Kasance Saranda Sarki Bauzur
Yayi Maka Aqirji Bai Taba Qasusuwanka Qirjinka Ba, Tsokar Nama Kawai Yadara, Amma Ka
Zubar Da Jini Mai Tsananin Yawa Wanda Shiyasa Ka Kusa Rasa Rayuwarka Gaba Daya, Koda
Gama Fadin Hakan Sai Sadauki Zahar Yajuyo Yadubi Jaruma Suhailat Fuskarsa A Murtuke Yace,
Amma Ai Duk Laifinkine Yake ‘yata Sbd Me Zakifita Farauta Daji Batare Dakinje Mini Sallama Ba?
Shin Kin Manta Ne Cewa Duk Sa’adda Zamu Fita Farauta Daji Saina Shafa Kanki? To Kisani
Cewa Wannan Shafar Kai Danake Yiwa Dukkan Jama’armu Tsarine Nake Baku Daga Dukan
Tsautsayi, Yanzu Ashi Kinjanyo Munyi Asarar Mutane Shida, Kinsa Matayensu Sun Zama
Gwaraye ‘ya’yansu Sun Zama Marayu, Yanzu Haka Suna Can Gaban Kabarurrukansu Sunata
Faman Kuka, Kekanki In Ba Don Sarki Lubainu Yanemi Yarasa Ba Kuma Yatafi Nemanki Datuni
Sarki Bauzur Yagama Lalata Rayuwarki, Waqilama Ya Kasheki Bayan Yagama Buqatarsa Dake,
Kisani Cewa Sau Tari Qarfin Mutum Da Iya Yaqinsa Bashike Bashi Nasara Ba Akwai Sa’a Sannan
Neman Shawara Gamai Aiwatar Dawani Lamari Yanada Matuqar Amfani Da Fa’ida, Shiyasa Ma
Akace Aikin Mai Shawara Baya Bace Saidai Kawai Ba Sirri Aciki, Ina Mai Horonki Kadaki Sake
Aikata Irin Wannan Babban Kuskurn Dakika Aikata, Lkcn Da Sadauki Zahar Yazo Nan Azancensa
Sai Hawaye Ya Zubowa Jaruma Suhailat Ta Durqusa Bisa Gwiwoyinta Agaban Sadauki Zahar
Tace, Ka Gafarceni Yakai Abbana, Tabbas Nayi Nadama Bisa Wannan Kuskure Dana Aikata! Ya
Abbana Kana Ganin Yanzu Dame Yakamata Nabiya Diyyar Mutanenmu Shida Dasuja Mutu?” Mu
Hadu A Littafi Nagaba wato na TAKWAS 8 Kuma na karshe Donjin Cigaban Wannan Qayataccen
Qasaitacce Labari, Dag Mai Dece Muku Kewa A Kullum Da Koyaushe. KHAMIS IDRIS
MUHAMMAD Shugaban Marubuta Littafin Yaqi. ABDUL’AZIZ SANI M/GINI.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button