Magidanci ya shiga hannun ‘yan sanda bayan ya dirkawa diyar sa ‘yar shekara 13 ciki

Jeremiah, wanda yake zaune a rukunin gidaje na FIRRO kusa da Adesan, Mowe, a karamar hukumar Obafemi-Owode, ta jihar Ogun, ya shiga hannun hukuma bayan matar sa ta kai karar sa wurin ‘yan sanda. Jaridar The Punch ta rahoto.
An tabbatar da cafke wanda ake zargin
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana batun kamun a cikin wata sanarwa ranar Juma’a. Oyeyemi yace an cafke wanda ake zargin ne bayan mahaifiyar yarinyar ta shigar da korafi a ofishin ‘yan sanda na Mowe.
Kakakin hukumar yace:
Mahaifiyar yarinyar tayi korafin cewa ta gano cewa diyarta na dauke da juna biyu, sannan da ta tambayi yarinyar sai tace mata mahaifinta ne ya sadu da ita. An kai yarinyar asibiti inda aka tabbatar da cewa tana dauke da cikin wata hudu.
Bayan ya karbi korafin, DPO na Mowe, SP Folake Afeniforo, ya tura jami’an sa cikin gaggawa zuwa gidan wanda ake zargi inda aka taso keyar sa. Bayan yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ya yiwa diyar ta sa ciki, amma yayi ikirarin cewa asiri aka masa lokacin da ya aikata.
Ya gayawa ‘yan sanda cewa ya rika mafarkin saduwa da matarsa wacce suka dade da rabuwa, kafin ya gano cewa ashe da diyar ta yake saduwa.
Za a cigaba da gudanar da bincike kafin tura wanda ake zargin kotu
Oyeyemi ya kuma kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya bayar da umurnin a turo wanda ake zargin sashin hana safarar mutane da bautar da kananan yara, na hukumar domin cigaba da gudanar da bincike.