Al-Ajab

Mai jego ta kashe jaririnta ta hanyar caka masa wuka bayan da kakar jaririn ta bada shawarar hakan

Wata Matashiya ta kashe jaririn da ta haifa, ta hanyar caka ma Jaririn wuka wanda sanadiyar hakan jaririn ya rasa ransa.

Rahotanni sun ce, mahaifiyar matan kuma kakar jaririn, ita ce ta dauki wuka da kanta, ta bai wa ‘yartata’ sannan ta umarceta da ta kashe jaririn saboda kawai yarinyar tayi cikin shege.

Wannan lamari dai ya faru ne a garin Olocha-Adogba dake yankin karamar hukumar Awgu dake jihar Enugu a ranar bakwai ga watan da muke ciki na Nuwamba.

Gaskiya Ta Fi Kwabo ta jiyo cewa, mahaifiyar Jaririn wato Ada Joy Okonkwo mai shekaru 18, ta haifi jaririn ne sakamakon cikin shege da tayi, wannan shi ya fusata mahaifiyarta mai suna Christiana Okonkwo, ‘yar shekara 60, inda ta dauko wuka da hannunta ta bata sannan ta ce ta kashe jaririn da ta haifa.
Yanzu dai mai jegon da tayi wannan danyen aiki da kuma mahaifiyar ta da ta sanyata ta aikata suna hannun ‘yan sanda.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button