RANA DAYA BOOOK 2 CHAPTER 13

CHAPTER 13
BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number????????
ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925
Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama????????????????ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana
Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki
ya nafi dakim Nafisa sai ya tuna yau a gurin Salma yake. Ya juya ya nufi dakinta.
Tana kan Darduma a can kuryar dakinta, tunda
tayi sallah ta kasa tashi, ga faduwar gaba don
lokaci-lokaci sai ta dafa Kirji. Matuka ta tsorata da
fushin Shatima, har yana fadin zai mata duka!
Tana jiyo sallamar Shi tsoro da fargaba suka
hanata amsawa. Ya aje• hularshi a kan kujera ya
nufi kicin. Ya dauko goran ruwa guda daya, ya zauna.
Duk da babu sanyi da ya daga sai da ya sha fin rabi, sannan ya aje goran. Yayi ajiyar zuciya. Ya
dauki wayarsa ya kira Nafisa, tana dagawa ya ce ta kawo masa jakarsa nan dakin Salma.
Babu-gardama Nafisa ta dauko ta nufo dakin Salma. Da alamu wannan bacin ran na Shatima ya saka matan nashi, shiga taitayinsu, musamman Salma.
Tayi sallama a Rofar dakin ya daga murya ya
Ce Shigo mana, kin coge kamar wadda za a cinye
ta.” Ta shiga ta mika mishi tare da fadin “An lafiya?” Ba tare da ya kalleta ba ya ce, “Lafiya?”
Ta wurga, ido tana kallon falon Salma, cikin
mamaki duk da take ji a family ana cewa su Salma
matsiyata Ne bata yi tsammanin tsiyar har ta kai
haka ba.
Ta taba baki tare da fadin “Uhum!” Ya dago
daga kokarin da ya ke na ciro Laptop a Jaka ya ce,
“Ya ya?” Ta girgiza Kai tare da sake kallon dakin
ta ce, “Babu komai,
‘ Ya ce, “To kina iya tafiya.
Ya fahimci dakin take ma wanna yatsinan.
Salma da ke ciki tana jin su. Lokacin tana ta
shawara a kan ta fito ko kar ta fito? Jin fitar Nafisa
sai ta yi ta maza ta fito.
Cikin tafiya tamkar Wahainiya ta nufi kicin. Ta
dauko Tiren da ta jera kuloli guda biyu, daya farar
shinkafa daya miya. Sai dan karamin kwanon silba
da ta zuba naman yau farfesun shi tayi.
Ta bude dan kwandon da ta yanka ganyen latas
da kokumba, shima ta dora.Ta.zo ta dire tiren, kan ya zube ma saboda
yanda jikinta ke Bari ta sauke daga tiren ta jere, ta koma ta dauko cokali da plate, da goran ruwa da kofi.
Ta dago da niyyar tambayarshi ta zuba.mishi, sai suka hada ido. Cikin sauri ta sadda kanta har da dauke numfashinta. Domin ta zaci zai antaya mata mari ne.
Jin shiru ta sake dagowa. Muryarta na rawa taCe.
“Yaya in zuba maka?”Na koshi.
- Ya fada a daKile. Da gudu ta mike kuma a rikice zata yi daki, tamkar ya kwashe da dariya sai ya dake yace.Ke” Kamar zata saki fitsari ta tsaya cak amma ta kasa waiwayowa.
Ya ce,
“Zo nan ki kwashe kayanki, ko nine zan kwashe miki?”
•Ganin rawar jikin tata zubar da abincin a kofar kicin, da rasa me zata yi sai ta fashe da kuka. Yana kallonta yayi murmush: ya dauke kai Ta kwashe ta kai kicin, tazo ta haye gado ta kudundune.
Lokacin ne Shatima ya samu dama har ya yi dariya sosai. Sai kuma ya ji zuciyarsa tayi masa sauki. Ya yarda da batun Likitoci, da suka ce dariya tana rage damuwa.
Yana bude aiki zai fara, sai •yaga sakwanni a
Emel din sa. Tun karfe uku sakon ya shigo cikin akwatinsa, suna da meeting a Abuja karfe tara na safe.
Yayi hamdala da yaga sakon yanzu, da sai da safen zai gani.
Dole Zai yi bukin din jirgin safe na karfe
takwas.Salma bata yi bacci sosai ba, tana jin Shatima
ya shigo har da gyara mata kwanciya. Tana jin shi yayi alwala ya tada nafila.
Da asubahi ta tashi tayi sallah, ta fito zuwa kicin. Kan sallaya taganshi yana karatun Alkur’ani, irin dan Karamin nan.
Taje ta dafa ruwan zafi, sannan ta soma suyar
dankali kafin shida ta hada komai. Ta fito ta samu ya fito wanka yana cikin dakinta yana saka kaya.
Tsam! Ya tsuke cikin suit bulu me duhu, rigar ciki bulu me haske. Tayi saurin dauke kanta
lokacin da taga zai waiwayo. Ya iso gurinta, tayi saurin tsugunnawa tana fadin, “Ina kwana?”
Ta dauke numfashinta jin bai amsa ba, kuma
bata yi zato ba sai taji an kama kafadunta an mikar da ita. Idanunta a lumshe hawaye suna kwaranya.
Cikin taushin murya ya ce,
“Salma!” Ta bude
idanunta a hankali, sunyi jajir. Ya ce, ‘
“Wai kukan me ki ke yi haka?”
Cikin rawar murya ta ce,
“Ban san ranka zai baci ba, jiya wallahi da ba zan ce zan bi ka ba.
Ba zaton shi ta sulale Kasa kan gwiwarta.
“Ka yafe ni don Allah.” Ya zauna a kan kujera. “Tashi
ba kiyi min laifi ba, jiya ne raina yana baci ba laifinki ba ne.
- Ya dauki hankicin shi da ke gefe
Ya share mata hawaye.
Ya ce,
“Tashi ki kawo min abin karin.
” Ta ce,
“Na kawo.
” Ta juya don hada mishi shayi. Yana
kallonta tun da ya hada shayi a gabanta, shi kenan kullum haka take hada mishi babu kuskure
Suga da yake irin ta kwali yake amfani da ita ta san adadin da yake so. Ta mika mishi, sannan ta sa cokali me yatsu ta ciro
mishi yankan Biredi guda,uku, tasa a cikin plate,
sannan ta aje mishi kwai da dankali.
Ya ce,
“Sannu da Rokari, kina Koari sosai
Ta dube shi “Na gode.
” Cikin jin dadi ta nufi kicin
don kammala kayan da ta yi aiki da su. Yana goge baki da ‘yar takardar share baki. Ya ce, “Zan tafi Abuja.
Ta dan ware ido cikin mamaki ta ce,
*Kuma yaushe za ka dawo?”
Yace “Yau insha Allah
Ya nuna mata dubu daya a kan kujera, “Ga kudin namanki nan.
” Ta ce,
“To Allah Ya dawo da kai lafiya.” Ya shafa kumatunta “Na gode.
Ya fita ta koma kicin ta ci gaba da aikinta. Ya sallami sauran ya fita. Maigadi ya ce,
“Alhaji yau motar babu lafiya ne?” Ya ce, “A’a zan hau Jirgi ne zuwa Abuja, yanzu zan dauki motar haya ne.
YADDA ZAN FAHIMCI MUJINA
Na daya, na fahimci baya cin danyan kifi, na biyu ba ya son a shiga huruminsa in yana cikin fushi, na uku yana son komai a gaskiya.
Tayi murmushi da ta karanta, a fili ta ce,
*Insha Allah sai na gama fahimtar halayensa.
- Ta tashi ta maida littafin. Ta dauki kudin nama ta fita zuwa gurin Maigadi, sai aka kwankwasa Kofa
Yaje ya bude, cikin mamaki sai ta hango Yaya
Hadiza, cikin mura taje ta rungumeta. Ta dauki Amira don murna. Yaya Hadiza ta ce, “Duk cikin murnar za ki dauki wannan Katuwar yarinyar”?”
Da gudu ta dawo ta ba Maigadi sako ta Koma.
Hadiza ta ce “Kin gan mu sai yau ko?” Salma taCe Wallahi kullum ina ta kewar Inna, ya ba kuzo da ita ba?”
Tace
“Sai ta fita takaba sannan zata zo Suna ta hira, Hadiza tace
“Kin yi fari kin Kara dan Tsawo, amma ba kiba.
Salma ta Ce,kuma sai ina ganin kamar nayi Kiba.” Ta ce, ‘
“Kin dai yi kyau, Kila Kibar sai nan gaba.
Ranar ta yini har yamma suna hira. Ta ba Salma shawarar yanda zata dinga adana kudi
maimakon cin kilon nama kullum. Ta ce, “Na dari uku ya ishe ki, sauran sai ki ke adanawa. Sai ki ga kin tara kudin da za a gyara miki daki, duk abin da babu a sai miki kafin Allah ya ba ki ciki ki haihu mutane su zo.”
Salma tace
“Sai dai in tambaye shi in ya yarda, don bana son in yi masa rashin gaskiya, na kula ba ya son haka.
Hadiza tace Ke amma sakarai ce ko? Ance miki maza suna son a rage musu kudin cefane ne?”‘ Salma tayi shiru a ranta tace
*Don shawara na dauka, amma sai ya yarda, kawai wataran ya ganni da kudi ya ce ina na samo…?°
Hadiza ta katse mata tunani da cewa,
“Ke fa har yanzu sakara ce ko?” Salma ta ce,
“Naji Yaya Hadiza, zan adana.
“To ina ki ke zuwa kitso?”
sai dai in dan kama da kaina in yi kalaba