Labarai

Mai magani yasa na sha fitsarina har sau 360 amma a karshe addu’a ce ga Allah ta magance mini matsalata – Inji wata mata Efezino Patrick

Wata mata ta bada labarin yadda ta warke daga wata cuta, wadda ta addabeta tun tana yarinya karama.

Da take shaidawa wakilin jaridar Punch, ta bayar da labarin yadda wani matsanancin ciwon ciki ya turnuke ta tun tana yar shekara 13 har na tsawon shekara bakwai7.

Matar ta bayyana yadda ta katse makaranta saboda cutar

Matar mai suna, Efezino Patrick wadda ‘yar asalin al’ummar Agbarha Otor ce, dake a Ughelli ta jihar Delta, ta bayyana yadda ta katse zuwa makaranta tun tana babbar sakandare aji na 2 biyu. A kalaman bakin ta, ta bayyana yadda abin ya fara a watan Maris na shekarar 2013, lokacin da ta kamu da wani matsanancin ciwon ciki, wanda mahaifiyar ta tayi tsammanin laulayin al’ada ne.

Wannan ciwo ya kara ta’azzara, wanda daga baya ya sanya cikin ta ya zama tirtsitsi, kamar bayan kwarya. An kai ta asibiti domin neman lafiya, inda a nan ne likita ya bawa mahaifiyar ta shawara da su nemi magani ta hanyar addu’a.

Mahaifiyar Efezino ta bazama neman taimako

Wannan shawara ta sanya mahainciyar Efezino, da yan uwanta neman taimakon addua a guraren ibada daban-daban, masu maganin gargajiya kala-kala, amma duk babu wani sauyi.

Yadda mai maganin gargajiya ya sanya ta shan fitsarinta

A irin yawon neman maganin ne, wani mai maganin gargajiya, yace da ita sai ta dinga shan fitsarinta dare da rana a kullum, har tsawon kwanaki dari da tamanin 180, wanda a kididdiga sai da ta sha fitsarinta sau dari uku da sittin 360, amma babu wata alamar sauki.

Dama kuma mahaifin ta, an neme shi an rasa. A sakamakon wannan matsala, auren mahaifiyar ta ya mutu.

A karshe dai, warakar wannan ciwo nata shine, komawa ga addua ba tare da neman agaji daga wajen kowaba sai na Allah.  Inda ta yanka shawara cewa ita da kanta zata roki Allah ya yaye mata wannan cuta, haka kuwa tayi, ta sukufa ba dare babu rana tana ta rokon Allah ya yaye mata, kuma Allah da yake maji rokon bayi ne ; sai ya yaye mata.

Yanzu ta dawo garai ta ci gaba da gudanar da rayuwar ta kamar ta kowanne mutum mai lafiya.

Asali LabarunHausa

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button