ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 21 to 30

*Alhaji Job’e Marusa* d’an asalin garin *Mayo Barwa* ne, cikekken bafullata ni ne, duk cikin zuri’arsu shi kad’ai ne yayi karatun boko, shima wani Yayan Mahaifinsa *Bukar* ne ya d’aukeshi ya koma wajensa da zama a kudu, sana’ar Yayan Mahaifinsa shine siyar da Fata, babban dila ne kuma hamshakin mai kud’i ne, be tab’a haihuwa ba hakan yasa ya d’auki Alhaji Marusa ya koma dashi gidansa. Baffa Bukar yana da mugun son kanshi, daga matansa sai masu masa fadanci kawai yake sakar ma bakin aljihunsa, sannan mugun mutum ne, sam baya so yaga wani ya fishi, zai iya kashe rai akan abun duniya, kuma be yarda da asara ba, zamansa a kudu ya k’ara masa rashin imani, yana da babban matsafi wanda yake masa aiki, yafiso akoda yaushe ya kasance shine a sama. 

Haka Alhaji Marusa ya taso duk wani bakin hali na Baffansa ya d’aukeshi, a k’asar waje yayi karatunsa acan ya kara koyo mugayen halaye, sam ibada bata dameshi ba sai yaga dama, hatta da azumi ciyarwa yakeyi wai ulcer yake da ita. 

Bayan daya kafu da kanshi sai Baffansa ya basa babban jari ya fara shigo da kaya daga k’asashen waje, cikin lokaci k’ank’ani Allah ya bashi abinda yake nema, hakan yasa ya tashi ya koma Lagos da zama, gidan da yake zaune kanshi abun kallo ne, domin shine ake kira da Aljannar duniya, dan Alhaji Marusa mutum ne mai son jin dad’i. 

Wani zuwa da yayi k’asar waje acan ya had’u da wani abokinsa da sukayi karatu mai suna *Herry*, bature ne, sana’arsa siyar da miyagun k’wayoyi, bayan daya samu labarin Alhaji Marusa yana kasuwancin kai kaya k’asar najeriya sai ya bashi shawarar ya fara siyar da kwayoyi zaici riba sosai. 

Jin harkar k’aruwa yasa Alhaji Marusa ya amince, nan ya fara saka miyagun kwayoyi acikin kayan da yake shigo dasu, yana shigo da shaddodi, su taliya da sauran kayan masarufi, acikin kwalayen ake saka miyagun kwayoyin ta yanda za’aga kamar kayan gaskiya ne a ciki, hakan yasa da wuya a kama kayan Alhaji Marusa da laifi, musamman da yake saye manyan kwastam da k’ananan su. 

Sam beda matsala da bodar Lagos shiyasa yafi son shigo da kaya tanan, matarsa d’aya da yaransa biyu yasa aka cire mata mahaifa dan baya son haihuwa, ko kauyensu baya zuwa sai dai yayi masu aike, haka baya son wani nashi yazo inda yake, danshi be yarda da jininsa ba yafi son mutanan gari, acewarsa besan su ba idan sukayi masa abu zai iya masu rashin mutunci.  

Brr. Barau tun yana k’aramin lauya yake masa aiki har ya zama babba, ya kware a harkar aikinsa, domin Allah yayi masa wata baiwa, ya iya tsara zance, idan yaso maida k’arya gaskiya babu wanda zai iya gano gaskiya, hakan yasa yayi saurin d’aukaka domin lauyen manyan mutane ne. 

Zuwan Alhaji Maiwada bodar Lagos yasa Alhaji Marusa ya fara sanin meye damuwa akan shigo da kaya, gashi Baffansa ya jima da rasuwa da tuni ya kai sunan Alhaji an d’aure bakinsa, ganin zai caza masa kai yasa ya had’a masa wannan sharrin. 

Shi da Mr. Kallah aminan juna ne, sunfi shekara goma sha atare, kowa yasan sirrin kowa, kuma Mr. Kallah shine yake goya masa baya a duk wani abu da zaiyi. 

***

*Garba Bala* shine asalin sunansa, bamaguje ne daya fito daga garin *Malumfashi* cikin kauyen *K’afur*, yayi karatun boko sosai, yana da masifar kok’ari, ya rik’e muk’amai da yawa daga baya ne ya maida sunansa *Mr. Kallah*, idan ka ganshi bazaka tab’a cewa bamaguje bane, zaka masa d’aukar cikekkan musulmi, hausa abakinsa dama gadonsa ce, domin kowa yasan yanda maguzawa suke jin hausa, rashin hasken musulunci daya rasa shine ya banbantasa da musulmai, amma acikinsu yake komai, shigarsa da mu’amalarsa duk irin na musulmai ne. 

Mr. Kallah yana da son kud’i, matuk’ar zaka yaga masa zai iya tsaya maka, sai dai yana da matuk’ar wayau, domin shi mutum ne mai aiki da kwakwalwa, duk yanda zaiyi abu baya bari aganosa, shiyasa a zahiri mutane suke masa kallon mai gaskiya da amana, wannan halin nasa yaja masa k’arin matsayi sosai, wanda a yanzu haka shine shugaban kwastam na k’asa, a Abuja yake zaune da matarsa ta farko, matarsa ta biyu kuma tana Lagos, gidansa na Lagos babban gida ne, waje guda ya ware ya gina katafaren ofis, idan yazo hutu anan yake aikinsa danshi mutum ne wanda baya son zaman banza. 

Duk wani mai kasuwanci matuk’ar yana shigo da miyagun kaya to yana da alak’a da Mr. Kallah, saboda yana goya masu baya yasa suke cin karensu babu babbaka, sai wanda yaso yake ma k’arin matsayi, idan kuma yaga baka binsa yanzu zai canza ka da wani. Alokacin da aka kawo sunan Alhaji Maiwada akan abashi shugaban kwastam na lagos yaso ya hana saboda yasan halinshi, amma gudun maganar mutane yasa ya amince dashi, sai gashi yazo yana caza masu kai. 

Wannan shine labarin *Mr. Kallah* da *Alhaji Marusa*

***** *****

Washe gari Alhaji Maiwada ya tashi da k’arfinsa, domin yaji sauki sosai, zugin da yake ji a zuciyarsa ma yayi sauki sai damuwar da baza’a rasa ba, bayan da likita yazo ya aunashi yaga jinin ya sauka. 

Zaune suke a falo bayan sun gama karyawa. Alhaji Mansur ne ya kalli Alhaji yana fad’in naji dad’i dana ganka katashi ahaka yau, dama kuma haka akeson bawa ya kasance mai tawakkali da yarda da K’addara, Alhaji nafi kowa saninka, nasan abinda zakayi da wanda baza kayi ba, kada ka damu da kallon da mutane zasuyi maka, Allah yasan baka aikata abinda akace ba, kuma shine zai saka maka akan zaluncin da akayi maka, dan haka kada kasa damuwar komai aranka, ka d’auka wannan dukiyar Allah ne ya baka kuma gashi zai amshe abunsa, dan haka kada kaji komai zamu biyasu abinda kotu tace, insha Allahu sanadiyar wannan kud’i da zaka basu sune zasu zamo silar lalacewar tasu dukiyar. 

Hannu yasa a aljihu ya ciro wata takarda, bud’eta yayi yana fad’in d’azu aka aikota daga hannun kwamishna, sunzo sai suka ba Madu, iya yawan kud’in da za’a biyasu ne aka rubuta aciki, kuma wata guda suka bada idan yacika ba’a basu ba zasu amsa da kansu. 

Naira miliyan saba’in yace ya kashe akayan da suka b’ace hada kud’in daya kashe na zuwansu nan. Aje takardar yayi yana dafe kai. Murmushi Alhaji Maiwada yayi yasa hannu ya d’auki takardar yana kallo. Kuka kawai Ummun Ra’eez takeyi jin makudan kud’in da zasu biya. 

Gyara zama Alhaji yayi yana fad’in Alhaji Mansur zansa wannan gidan nawa akasuwa. Da sauri Alhaji Mansur ya kalleshi jin abinda ya fad’a. Jinjina kai yayi yana fad’in wallahi gidan nan ya fitar mani arai, da nasan gina gidan nan zai jawo mani irin wannan zargin bazan tab’a ginashi ba, dama na ginashi ne saboda muji dad’in rayuwa nida iyali na, sai gashi hakan ya jawo mana tashin hankali, da zan samu wanda zai bani kud’in gidan nan ayanzu wallahi bazan sake kwana aciki ba. 

Girgiza kai Alhaji Mansur yayi yana fad’in baza’ayi haka ba, dama abinda suke so kenan su rabaka da wannan gidan, idan sukaga kasa shi akasuwa burinsu zai cika, dan haka bazaka siyar dashi ba, zamusan yanda za’ayi. 

Murmushin takaici Alhaji Maiwada yayi yana fad’in kayi hakuri Alhaji Mansur, ina d’aukar shawarar ka, amma a wannan karon ko Alhajina ne yace kada na siyar da gidan nan bazan jishi ba, kwanciyar hankalina shine nabar gidan nan, na ciresa araina hakan zaisa na samu natsuwa. 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button