MAKAUNIYAR KADDARA 51

         A bazata ya saki murmushi mai sanyi da kai hannu ya shafi kansa, dan tana gama faɗa ta yanke kiran bata jira amsarsa ba. Ajiye wayar yayi yana miƙewa gaba ɗayansa idonsa akan Zinneerah dake cuɗa yatsunta cikin juna tana cigaba da kukanta  harda shashsheka.

      Batare da tunanin kanta ya nufoba sai ganinsa tai ya hawo gadon sosai, filo ƙarami ya jawo daga gefenta ya kishin giɗa, dan ɗaura gwiwar hannunsa ɗaya yay ya tallafe kansa da tafin hannun yanda yake iya kallonta da ƙyau, sai kuma ya saka yatsunsa biyu na ɗayan hannunsa ya tallafo haɓarta yanda zasu haɗa ido.

      Suna haɗa idanun kuwa tai saurin son maida nata dake kwarar da hawaye amma ya hanata wannan damar. Sai kawai ta shiga sake matso hawayen. Dan irin kallon ƙurullar da yake yima fuskar tata ne yake ƙara ƙarya mata zuciya ga kwarjininsa daya cika mata idanu.

           “Shi wannan kukan ba’a gajiya dashi?”. Yay maganar da muryar lallashi data sakata ɗago idanu ta sake kallonsa, yanda yay ɗan yi luuu da idanun nasane ya saka tsigar jikinta tashi, cikin harɗewar harshe tace, “Yayanmu!”.

       “Uhmyim ƙanwata”. Ya faɗa yana sakin haɓar tata da janye hannunsa daya tallafe kansa shima yana gyara kishingiɗar tasa da matsowa daf da ita yanda takejin har saukar numfashinsa shima yanajin nata. 

     Ganin yanda ta kasa ci gaba da maganar sai juya yatsun hannunta take a cikin na juna ya sashi ɗaura hannunsa akansu yana kallon zanen baƙin lallen da ja dayay matuƙar ƙyau a kansu, “Kuka ga amarya a ranar da aka kawota gidan miji cikar kamalace da bayyana adon mutuncinta, sannan kuma tarbiyyace da nuna tsantsar soyayya ga iyaye, sai dai idan yayi yawa yana gundurata. Karki damu da neman amsar duka tambayoyinki, a hankali zaki samu amsarsu. Inason mutum mai biyayya akan umarnina, banason hayaniya, banason taurin kai, banason ƙarya. Duk wanda zan rayu dashi inhar zai kiyaye waɗannan zaiji daɗin zama dani fiye da yanda yake zato. Bana yanke hukunci ga mai laifi da sauri ko cikin fushi har sai na bisa mataki-mataki wajen fahimtarsa da dalilinsa. Mun sami juna a yanayin da banso ba, sai dai ba hakan na nufin zanyi sakaci da damata bane, komu samu tsaurin idon bijirema hukuncin ALLAH dana iyayenmu, dan sun cancanci sadaukarwa koda ace mu zukatanmu basa buƙatar hakan, ina ƙyautata miki zato bisa ga wasu dalilaina, dan haka sai kiyi ƙoƙarin tabbatar mini da hakan”.

       Hannunta ɗaya ta zare daga cikin nasa a hankali ta share hawayen da suka jiƙe mata fuska.

     “Good” ya faɗa yana tashi zaune daga kishingiɗar da yayi. Sauka yayi gaba ɗaya a gadon Zinneerah na binsa da kallo ta ƙasan ido da ƙoƙarin ganin ta shanye hawayen dake shirin sake zubo mata. Akwatin daya gani a gefe ya ɗakko, ya ɗaurashi a gadon tare da buɗewa. Da kayan barci dake sama ya fara cin karo, batare da damuwaba ya ɗakko na saman kawai ya maida ya rufe. Takowa yay ya ajiyesu gabanta fuskarsa a tsuke kamar yanda ta santa, cikin rashin sakewarsa yace, “Ki tashi ki sauya kayanki ki kwanta”.

     Daga haka ya juya ya nufi ƙofa. Da kallo ta sake binsa tana share hawayen da suka ziraro mata. Yana fita ta ɗaura hannu duka a kai tana sake fashewa da kuka. A fili tace, “Na shiga uku ni Zinneerah ina ni ina zaman aure da Yayanmu? Wlhy yafi ƙarfina, matarsa tafi ƙarfina bazan iya da bala’inta dana Mammah ba”.

    Sai kuma ta zame ta kwanta tana jan numfashi dake sarƙe mata a ƙirji da ƙyar. Tabbas bazatace batason Yaya Abdul-Mutallab ba, dan ya cancanci zama abinso ga kowacce irin mace ciki harda ita da a yau zata iya kiran kanta mai sa’a ma, amma tasan yafi ƙarfinta ta kowanne fanni na rayuwar duniya, duk da tasan zata iya finsa a lahira itama wannan hukuncin ALLAH ne. Miyasa MAKAUNIYAR ƘADDARA zata rasa a inda zata jefata sai cikin rayuwarsa?. Ta inama zata fara kwatanta zaman aure dashi itako?.

             “Idan nace bana son abu sau ɗaya to a kiyaye mini, inba hakaba zan ɓata ran mutum kamar yanda ya shirya ɓata nawa”.

     Ta tsinkayi muryarsa a bazata batare data san ya sake dawowa ɗakin ba. Zumbur ta miƙe zaune da kwasar kayan barcin daya ajiye mata tana sauka a gadon batare data yarda ta kalli ko sashen da yake ba. Kamar ƙyaftawar ido ta afka toilet ɗin ɗakin.

        Tea cup ɗin hannunsa ya ajiye a bedside drawer yana ƙoƙarin zaro wayarsa datai alamar shigowar saƙo. Ganin no ɗin aunty Zakiyya ta sakashi buɗe saƙon dan yasan Mammah ce.

       _Ina ƙara tabbatar maka karka taɓa yarinyarnan Abdul-Mutallab, dan zaka gamu da ɓacin raina da baka taɓa ganiba a tsahon shekarun rayuwarka talatin da huɗu_.

       Murmushi ne ya suɓuce masa, yaɗan girgiza kansa da faɗin, “Mammah problem”. Akan laɓɓansa. sai ma ya kashe wayar baki ɗayanta ya ajiye ya ɗauka lap-top ɗinsa daya shigo da ita ya shiga hidimar kunnawa dan akwai abinda yake son yi daya shafi business ɗinsa da wani abokin harkarsa mai turo masa kaya daga dubai……………✍

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button