NOVELSUncategorized

KWARATA 23

???? —— 23

          Har gari ya waye ban sake komawa bacci ba , da safe bayan na gama duk abinda nakeyi na fara kiran lamba 4 , lamba 3 wato d c o kuma na haɗashi da Amisty bana iya wata mu’amula dashi saboda gaskiya baida tsabtataccen baki danni Allah yayi min ƙyanƙyami idan na raina maka tsaftar baki tou na raina maka kuma bazan yadda inyi wata mu’amula dakai ba gaskiya.


       Lamba 2 wato Bello shi yana nan kuma muna tare har yanzu babu wani abu daya shiga tsakani na dashi saidai ina fereshi yadda ya kamata ina kwalkwalar kuɗinshi babu dare babu rana, daya bani haƙuri ma cewa nayi saiya nemo min Babana sannan zan ƙyaleshi !



      Lamba 1 Alhaji ne kuma ya rigamu gidan gaskiya , na goge komai nashi a wayana daga number har vidio babu abinda na bari,

    Lamba 4 shine mijin Zalifa kuma yanzu shine abun hari na, ɗan wasa na, domin shine zan jijjiga zanyi wasan kura dashi kuma saina lashe kaf tattalin arziƙishi saina cinye komai zan maidashi matsiyacin ƙarfi da yaji, idan kuma yana da rabo akaina tou in sameshi mai tsafta idan dai ɗan gayu ne kamar Dikko zan riƙe mishi wuya ya zama abokin tafiyana…

     Kiranshi nayi amma har ya tsinke bai ɗauka ba , haka tsarina yake kira ɗaya nakeyi idan ba’a ɗauka ba bana sake kira , idan kuma ya biyo kiran ina maraba dashi ,

      Daga tsakar gida naji Amisty ta luƙaƙa wata irin ashariya irin na shararrin “yan tasha , saida gabana ya faɗi , ban gama saita kaina ba naji taci gaba da cewa na rantse da girman Allah wannan karon bazan bar Sultana tayi haƙuri ba , saita wulaƙanta shi ko waye ubanshi …

Da sauri na miƙe na fito tsakar gida jikina sai kyarma yakeyi saboda ni hayani da zage zage ɗimautani sukeyi , ina fitowa na kalli Amisty nace wai mene ne ? Kusa dani Amisty ta matso tace ke wai mu Hafsa zata tonawa asiri , kallon inda Hafsa take tsaye nayi sannan nace wai miye ?

       Wayar Hafsa, Amisty ta miƙo min tare da cewa shiga kiga cht insu da Dikko , bayan ta tura mishi saƙo ta whatsapp ya kirata tsakanin minti 10 bayan tura saƙo, kiji zagin da yayi miki Mother ƙarshen hukuncin da yayi yasa an rushe shagonmu kuma yace idan dai yana lumfashi kika fito karuwanci yace sai yayi miki wulaƙancin da ko ance ki faɗi kalmar iskancinci da bakinki sai kince kin tuba , 

       Yace zai baki azaba mai azaba ɗaya daga cikin irin azabobin daya tanadar miki shekaru biyu masu zuwa , kuma idan kinyi taurin kai yace zai tafi dake ya ɓatar dake inda babu wanda zai sake jin labarinki daƙiƙiyar banza dake….

        Zuciyata ta kawo maƙoshi amma ban nuna ɓacin rai ba nace ma Amisty wai duk inji shi Dikkon yace haka ? Amisty tace imana kinsan dai bana miki ƙarya idan baki yadda dani ba ki samo wani ya karanta miki duk duniya Sultana babu wanda nake ma soyayya irin wacce nake miki , nabar uwa da uba na zaɓe ke , rayuwata da komai nawa sadaukarwa ne a gareki idan ba duk abinda na faɗa miki Dikko ya rubuto ya turo ba Allah ya tsine min albarka !

        Murmushi nayi sannan na kalli Hafsa nace to ke Hafsa mi ya kawo har kukayi magana na da Dikko ? Latse banzan bakinta tayi sannan tace niba magana nayi mishi ba shine yayi min maganarki , Amisty tace ke jira kiji zan ubanki ƙarya zan miki ko me kike nufi ne ? Kallona Amisty tayi sannan tace vidionmu ta tura mishi da hotuna kuma itace ta faɗawa Dikko muna da shago inba haka ba ya akayi yasan wurin harya zo ?

      Hafsa tace tou naje na faɗa Amisty kiyi magani na , ai tun kafin ta gama rufe bakinta Amisty ta rufe ta da duka tana cewa amanar ƙungiya zaki ci dan ubanki , an yadda dake zaki ci mana amana , ko an faɗa miki muma bamu iya karatun da rubutawa ba ? Tana magana tana dukan Hafsa , kokowa har ƙofar gida saboda cikin gida mata sun kasa ansar Hafsa dama su “yan gayu basu iya faɗa ba sai sakata suka iya…

         A ƙofar gida dakel masu aikin rusa tsohon gidanmu suka raba faɗa , kuma sukayi sasanci cewa da Allah mu daina faɗa ayi haƙuri , candai ake basu haƙuri niko wuri na samu na zauna wai nice daƙiƙiya , kamar ni abokin hamayya zai faɗa cewa ni daƙiƙiya ce , wallahi wannan kalmar tafi komai muni a rayuwata , itace kalmar da aka taɓa faɗamin ta ɓatamin rai kuma tamin ciwo ta kartar min zuciya har sai da naji masassara ta saukomin , wai ni Dikko yace ma daƙiƙiya , gumi naji yana bimin kumatu ina kai hannuna na shafo kunci na naji lema , ganin ruwa a hannuna ya tabbatarmin da kuka nakeyi….

Bayan an raba su Amisty shine suka zo kusa dani suka zauna hada Hafsa dan kunsan su “yan duniya basu fushi duk yadda aka cakusa dole sai an koma an jone , kowa tambayata yakeyi abinda yasa nake kuka amma banyi magana da kowa ba , Hafsa ce ta fara bani haƙuri akan abinda tamin murmushi nayi amma ban mata magana ba ,

        Muna na zaune ƙofar gida a saman dandamali har su Nana mun jera layi babu mai mayafi a cikinmu mundai fito karuwan na zahiri da zahiri, saboda wancan hannu duk Dikko ya cinyesu babu gida ko ɗaya filin wurin ne kawai saboda duka wurin ya sayeshi harya tsallako gefen gidanmu yaci gaba da siyewa.

        Muna nan zaune muna jiran tsammani Umar yazo , yaron Dikko wanda ya yakaini gidan Alhaji , yana fitowa daga mota ni ya fara gani , shegiyaaaaa , ashe da kina nan ina kuɗi na da kika cinye “yar damfara ?

       Murmushi nayi da gefen bakina sannan nace zaki ya shiga gaban ɓauna , idan dai wanda ya mutu zai dawo tou ka kwantar da hankalin ka kuɗinka zai dawo aljihunka babu ɓata lokaci ,

       Aiko kuɗina baza su ciwo wurinki ba sai kin bani abuna , dariya nayi tare da cewa wallahi basu ansuwa wurinka bakai ba kayan banza ko Dikko naci gabanshi naci uwarshi naci ubanshi a iskanci ai shine dai kake taƙama dashi ko ?

      Kusa dani Umar yazo yana ƙoƙari wanka min mari na riƙe hannunshi tare dayin wani irin lafiyayen fito , babu ɓata lokaci “yan dabana suka bayyana , kallonsu nayi tare da cewa ku shiga dashi ciki ku bashi ruwa yasha , ɗaukarshi sukayi sama sukai cikin gida dashi , saida suka bashi kashin bala’e sukai mishi lullusar fitar hayyaci , saida suka tabbatar jikinshi yayi tsami sannan suka tillo banza ƙofar gida…

      A lokacin ni kuma ina saman mota ta nayi kwanciyata , yayin da Amisty ke gefe na tana shan sigari A ` i da Saude kuma suna zaune kan dakali suna lido, Nana da Karima kuma nace su koma cikin gida saboda su matan aure ne ,

     Dakel Umar ya miƙe ya shiga motarshi yaja ko masu aikin da yazo dubawa bai duba ba ya tafi , bai zame ko ina ba sai wurin “yan sanda , muna ƙofar gida zaune muka ga motar “yan sanda , wai anzo kamani , 

      Bayan mun gama magana dasu nace su jirani ina zuwa , cikin gida na koma na shirya cikin shiga ta alfarma, wata riga na ɗauka na saka a leda bayan nasa anyi mata kitar wulaƙanci ga kuma jikina da yasha sahun akaifun Hafsa nasa ta yayyakushe ni dan na shirya ƙullawa Umar sharri na gaske.

       Dani da Hafsa da Amisty da A ` i da Saude muka tafi domin ni sune sheduna , mu biyu a gaba ukku a baya , cikin mota ta muka tafi saboda itace motar kece raini Hafsa ta tuƙa har muka isa police station, Umar na zaune a waje jini sai bin jikinshi yakeyi tuni ya kira Dikko ya faɗa mishi, Dikko yace da an kamoni a rufeni duk abinda yake zai shigo katsina gobe idan Allah ya kaimu , dan hankalinshi ya tashi da yaga dukan da nasa akayi wa Umar.

        Office ɗin d c o aka kai case inmu , ga gaske ni kuma gani nazo da kwarata masu biyawa mutum buƙatarshi , dan suma sunyo shiga mai ɗaukar hankali duk namiji mai lafiya ya gansu sai yaji hankalinshi ya tashi ,

        Kujera Amisty ta jawo min na zauna sannan suka koma bayana suka tsaya , shigo da Umar akayi a daidai lokacin da ni kuma na fara gaishe da mai girma d c o , kafin ya ansa gaisuwar tawa Umar ya miƙa mishi waya Dikko ya sake kira domin ya faɗawa Dikko munzo station in ,

      Faɗa Dikko yakeyi tare da cewa bai ce a jira aji abinda ya haɗamu ba kawai rufeni yace ayi , D C O yace ranka ya daɗe ai sai anyi binceke Dikko yace ba abinda za’a bincika umarni yaba d c o a rufeni kawai , d c o zai sake magana Dikko ya daka masa tsawa dole d c o ya dauke wuta , jikina fa yayi sanyi amma ta maza nayi tare da miƙewa na anshi wayar daga hannun d c o nace Dikko faɗa a cikin waya bashine ke nuna jarumta ba , kuma rufeni na kwana a ofishin “yan sanda bashi ne zai nunamin kai cikakken jarumi bane ba , 

        Kaine kaɗai maganin fitsarata idan ka isa kazo kayi magani na basai kasa an kulleni ba , kuma kake cewa kar ayi bincike kasan abinda shi yaron naka yayi min ne ? Cikin ɗaga murya nace tou mutunci na fa zai buɗe kaga yadda ya yayyage min jiki ? Kuma da aka mishi magana cewa yayi kai ka tsaya mishi ya hau duk macen da yaji tayi mishi, kuma D C O ya faɗa maka idan bai yayyageni ba , da sauri Dikko ya rufe idanuwanshi tare da matse gwangwanin maltinar da aka kawo mishi baisha ba , azabar matsa yasa gwangwanin ya fashe maltinar ta watse…

       Har a zuciyarshi ya yadda da abinda na faɗa mishi dan yasan Umar manemin mata ne na ƙarshe yayin da Umar ke cewa wallahi mai gida ƙarya takeyi kawai naje duba masu aiki tasa “yan daba sukai ta dukana ! Cikin wata irin hayagaga Dikko yace rufemin baki ɗan iska mutumin banza idan na sake jin maganar ka saina ci mutunci ka wallahi ,

       Tausasa murya yayi tare da cewa ba d c o wayar , miƙa mishi nayi Dikko yace da gaske ya yayyakushe ta ? D   C O yace Eh ranka ya daɗe , to dole zaice Eh tunda ga sahun akaifa a jikina ya fito sosai, nidai bansan yadda suka ƙare ba  D  C O yace muje kawai ,

       Muna shiga mota na sauke ajiyar zuciya , kai Dikko ɗan bala’e ne na ƙarshe baida mutunci gaskiya Allah ya rufamin asiri yau da sauro da zarnin fitsari ya hanani bacci , kallon Amisty nayi sannan nace kinji ɗan bala’e da saboda ni zaizo lallai dana yabawa aya zaƙinta , dariya nayi tare da cewa aidai mun daki banza….

        Bayan wata ɗaya…

          A halin yanzu suna na ya fara zagawa a cikin gari, domin dai harkar iskanci ta buɗe mana sosai muna ganin maza daga shiyyoyi da dama , a cikin gidana nan maza ke zuwa su zaɓi macen da suke so a tafi hotel acan ake raƙashewa, yanzu bamu da shago domin Dikko ya saye wurin kuma yasa an rushe shi , tou ina gidana anan nake baje kolin iskanci na dani da yarana…

Cikin wannan wata bakin gwargwado kowa ya samu ci gaba na rayuwa Nana namiji yake zuwa wurinta ta kora mishi sharfi akan kayan mata da maza , itama a hankali idonta ya fara buɗewa ta iya gogayya da maza , dan daga ita har Karima yanzu bata mazansu suke ba,

       A fanni na kuwa ni har yanzu ban samu tsaftataccen namiji kamar Dikko ba , amma idan aka zo tafiya da mace ni nakeyin ciniki namiji ya bani kuɗi kuma itama macen idan ta dawo zata bani kasafi na , tunda kafin a tafi nasan ko nawa za’a baki , na zama kawaliya kenan..

     Idan namiji yazo ya duba a cikin matanmu bai samu wacce tayi masa ba ya faɗamin irin mace da yake so ni zan nemo mishi ita walau budurwa walau zawara har matar aure ma ,

        Mijin Zalifa munyi waya dashi amma har yanzu bamu samu haɗuwa ba , yadai bada an kawo min kuɗi masu yawan gaske ta dalilin waya da mukeyi ta ɓatsa dashi , na siyar da motar da Alhaji ya bani nayi ciko na siyi mota ta gani ta faɗa , kuma ni nake tuƙa abuna domin yanzu na iya mota , jikina yaɗan ƙara ginuwa ya kuma goge hutu ya zauna dan dole dan idan baka san gidan da nake rayuwa ba zakace daga G. R. A  na fito, na ƙara waye kuma idanuwana sunyi fashewar da duk mutum yayi mamakinshi,

       Shirye muke cikin shiga mai nuni da mutanen gari ga naku , ma’ana maza ga matan bariki, biki akeyi a gidan ƙanin Babana yana aurar da ɗiyarshi, dan haka nace kowa ya shirya muje , mota ukku mukayi hada Zalifa, mota ta , ta Hafsa sai ta Zalifa sai napep ɗaya ta “yan daba…

       Tunda mukayi parking idanuwan jama’a ya dawo kanmu, fitowa nayi tare dayin magana ƙasa ƙasa nace gafa “yar gado nayi gado amma kuma har na zarce… 

Ina gaba tawagar karuwai suna bin bayana , duk wanda ya ganni sai ya kauda kai tare yin gulma ta , a cikin gidan biki kuwa hankalin jama’a ya tashi ganin iskanci dana taro bamai riƙuwa bane , ƙanin Babana yana tsakar gida shima da mutane ana ta mishi Allah sa alkairi dan ba’a daɗe da ɗaura auren ba , mazauni su Amisty suka nemomin na zauna na ɗauki ƙafa ɗaya saman ɗaya na ɗora…

       Kallona yayi tare da cewa Sultana haka kika zama karuwa ? Saboda shi irin mutanen nan ne masu sakin magana babu tsafta , murmushi nayi tare da gyara zaman ɗaurin kallabi na sannan nace Eh wallahi ai shine nazo na nuna muku tunda nasan duk wani ɗan uwa da abokin arziƙi yazo shine nazo wanda basu gani ba suma su gani….

Dariya Amisty tayi tare da buɗe jakarta ta jawo shigarinta ta banka mata wuta , saida taja ta bada hayaƙi sannan tace wannan gaskiya ne Mother , ƙanin Babana yace nan zaki zo ki kawo mana iskanci ? Tou ki tashi ki koma inda kika fito tunda ke kin lalace karki zo nan ki gurɓata mana tarbiyyar “ya “ya kije can ki ƙari iskancin ke ɗaya….

         Kallon Baba nayi tare da cewa gaskiya ne dan naga idan guguwa ta taso wuri ɗaya takeyin borinta amma tsawar hadari tana gaurayi kaf faɗin sararin samani , ruwan sama ko na sarari yake jeƙewa bai taɓa baa na cikin ɗaki kashi duk wanda kaga yasha kashin ruwa cikin ɗaki tabbas kwanon ɗakinsa ya huje , idan yayi dibara saiya doɗe wannan haryar da zai bawa ruwa damar shigo mishi ɗaki. Gyara zamana nayi tare da ci gaba da cewa duk na kirki baya san na banza amma ni mutanen kirki sune abokan rayuwa…..


       Miƙewa nayi tare da cewa ka bada tarbiyya a gida zamanin Sultana yana warware tuggun kowa , duk wanda ya kalleni a taron nan yace tir da halina ya saurari zuwan zamani na akan “ya “yanshi, har na fara tafiya na tsaya tare da juyowa nace yawwa idan kaga ɗan uwan naka Babana , ka faɗa masa cewa ina matuƙar kewarsa a kusa dani…

        Sallama nayi da duk wanda ya kamata tare da buɗe bakin jakata nayi alkairi , banga “yan gidanmu ba ko ɗaya amma nace idan sunzo ace musu ina nan tsohuwar anguwarmu , gidan karuwai kawai zasu tambaya za’a kawosu har ɗakin magaji Sultana , na ƙarasa maganar tare dayin murmushi sannan nayi gaba masu sauran imani suka bini da addu’ar shiriya yayin da wasu ke cewa ubana yajamin…

      Muna fitowa daga gidan kowa ya shiga mota muka ibi sararin hanya…..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button